Showing 21001 words to 24000 words out of 51341 words
abokananshi suna nan harda oganshi nan shima ya zauna aka ci gaba dayin hirar dashi harda masu yi mishi tsiya wai ina Matar shi ko tayi nauyi ne yayi banza dasu dan baya tunanin zai iya fallasa sirrinsu.
Sai wajan k'arfe goma ya dawo lokacin Khadija da Mama na zaune a tsakar gida suna hira ya shiga, kusa da Mama ya zauna yana furta,
"Washhh am tried Mamana."
"Babana kenan toh shi abinda ka fad'a a k'arshe mekake nufi?!"
Dariya suka yi shida Khadija ya kalleta itama ta kalleshi sai yaji tace,
"Kai Mama cewa fa yayi ya gaji."
"Au tohh! Uhmm kaji turawa toh Allah dai ya k'ara muku basira Mu ai karatun allo mukayi shima dakyar Matar babana take bari naje."
Duk sun tausaya mata daga nan ta dinga basu labarai har wajan goma da rabi sannan ta kallesu,
"Babana dare yayi Ku tashi ku shiga d'aki nima tafiya zanyi."
Shine ya fara tashi sannan Khadija ma tayi mata sallama suka wuce Mama ta bisu da kallo tana musu fatan alkairi cikin rayuwarsu.
Kwanan Ahmad uku yayi musu sallama ya koma makaranta cike da kewarsu gabaki d'aya yana sonsu yana jinsu a cikin jikinshi dan haka ya Kara d'aura anyar yin karatu mai d'orewa yadda zai ciki burinshi.
*****
Ahmad kam ta b'angaran karatu sai dai ace sambarka domin kuwa ya samu abinda yake so yana da kokari sosai kullum fatan shi ya cika burin shi na zama cikaken likita wannan shine mafarkin shi tun yana da shekaru shida a duniya.
Kullum baya iyayin bacci indai baiji muryar masoyiyar shiba kuma abar kaunar shi farin cikin shi mai kawar da duk wani buk'atunshi, yana son Khadija so mai tsanani so na hak'ik'a wanda babu algus domin tayi mai hallacci musamman iyayanta fatan shi kar Allah ya kawo lokacin da zai juya musu baya ko yayi musu wulakanci ta kowace hanya.
Ahmad kyakyawan mutum ne dogone yana da faffad'an kirji wankan tarwad'a ne yana da doguwar fuska mai d'auke da dogwan hanci gashin girar shi mai d'inbin yawa wadda ta k'arawa fuskar shi kyau da cikar zati, yana da d'an k'aramin baki zagayayye da idanuwa madaidaita sai kwantaccen gashin baki wanda ya fara fito mai hakan kuma ya k'ara kawata fuskar tashi.
Yana son karatu sannan yana da yawan ibada baya son yaga yau yayi abinda zai sab'awa ubangijinsa sai dai abisa rashin sani amma yakan yi iya bakin kokarin shi wajan ganin ya tsira da mutuncinshi da zuciyar shi. Ahmad ko a wajan d'aukar karatu baya zama kusa da mata duk yadda suke nanik'e mai baya yadda yw rab'u dasu domin sanin yadda zuciyar shi da gangarjikin shi take na yawan buk'atuwa hakan yasa sam baya basu fuska sukuma suna ganin shi as d'an girman kai.
Kwance yake bayan ya dawo daga practical daga shi sai gajeran wando da vest a jikinshi kewar matar shi Khadija duk ta addabe shi gashi basu da wani interval kullum sai sun shiga lap yana kokarin ganin yayi azumi sai dai wani sa'in daya sha ruwa zai ji yana da buk'atarta amma ba yadda zai yi sai dai kullum shine shan jikakiyar kanwa ko lemon tsami, gyara kwanciyar shi yayi tare da d'akko wayan shi ya fara laluben Khadija fatan shi kawai Allah yasa itane zata fara d'auka domin yana cikin wani hali, tana fara ringing ya fara murna cikin rashin sa'a yaji muryar Maman shi.
"Hello Ahmad ya karatun kai ma ya kake?!"
Da kyar ya samu ya tsaida ranshi guri guda sabida karta gane halin da yake ciki, cikin basarwa yace,
"Lafiya lau Mama yasu Aminu?!"
Shiru yayi dan bazai iya hira mai tsawo da ita ba kasan cewar dayayi zata gano halin da yake ciki, jin yayi shiru ne yasa Mama mik'ewa tsaye tana cewa,
"Babana bari na kaiwa Khadijan tana d'akin ta."
"Toh Mama na gode Allah ya bar min ke."
"Amin babana."
A kofar d'akin ta tsaya tana kwalawa Khadija kira wanda ke kwance kan kujera tana home work d'in da aka basu, da gudu ta fito jin Mama na kiranta tana zuwa ta mik'a mata wayar tare da cewa,
"K'arb'i nan mijin ki ne ya bugo."
Karb'a tayi sannan ta juya cikin d'akin bayan ta kara wayar a kunnanta, cikin zumu d'i ta fara magana.
"Yaya Ahmad ya karatu?!"
"My Khadija bana yi."
Khadija ta zaro ido cikin mamaki da al'ajabin maganar shi, hab'a ta rik'e tamkar yana ganinta kafin tace,
"Baka yi harma kuma kake fad'a Yaya Ahmad?!"
"Eh my Khady ai dole na gaya miki gaskiya sabida ke sirrina ce..."
"Toh Yaya Ahmad baka da lafiya ne kake kinyin karatu?!"
Kara marairaicewa yayi murya k'asa-k'asa yace,
"Eh..."
Zaro idanuwa Khadija tayi tare da dafe kirji tana salati, yanajin haka ya fara murmushi dan yasa ta damu da jin cewar bashi da lafiya cikin rawar murya tace,
"Yaya Ahmad ka dawo gida kaga can babu wanda zai kula da kai nan kuma kaga akwai Mama sannan nima zanyi jinyar ka dan Allah ka dawo kaji."
"No Khadija ciwon nawa ai be kai nan ba kin san me yake damuna?!"
"A'a Yaya Ahmad sai ka fad'a."
"Khadija ke nake b'uk'ata ina tsananin bukatarki a kusa dani na rasa yadda zanyi sha'warki ta kusa halakani yanzu ma bakiji yadda nake ji ba..."
Kirji ta dafe jin abinda ya fad'a cikin ranta kuwa cewa take yi,
"Ashe rashin lafiyar ta bani wahala ce, yo ni yanzu me Zan yi maka hakuri zakayi."
"Khadija naji kinyi shiru please kiyi wani abun mana."
"Yaya Ahmad yoni me zance maka?!"
"Khadija kin k'ara girma?!"
Ya fad'a cikin wata irin murya, dariya tayi mai sauti har tasa shima ya dara cikin dariyarta take kallon jikinta kamar yana ganinta tayi saurin rufe idanuwa da hannu, jin tayi shiru yasa shi kuma cewa,
"Uhmm meye ya k'aru a jikinki Khady na kinsan ina son naga kin k'ara girma I know zan samu abunda nake so a wajanki uhmmm.?!"
"Kai Yaya ka dena yi min wannan maganar ni wallahi sai sani jin kunya kakeyi."
"Toh naji yi min kiss wanda zai sa naji dad'in yin bacci..."
Dariya tayi sai da ta rufe fuska sannan takai wayar setin bakinta ta sakar mishi mai k'arar gaske kuwa sannan tayi saurin kashewa tana dariya, shima dariyar yayi sannan ya damke wayar a hannunshi yana tunaninta tare da jin kaunarta har cikin ranshi.
*MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
[2/20, 9:16 PM] βͺ+234 803 328 3071β¬: *πDR.AHMADπ*
21-22
*NA MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
Edit by *Hajja ce*π
*Β©HASKE WRITER'S ASSO...*
(Home of expert & perfect writer's)
*R*ayuwa tayi musu dad'i babu abinda ke damun su Khadija domin hankalinsu a kwance yake babu wani matsala ko kunci sab'anin Ahmad dake cikin damuwa da tsananin wahalar karatu dana bukatuwa, kullum ka ganshi yana cikin azumi baya shiga cikin mata duk kuwa da yadda suke manne mai amma baya basu fuska hakan yasa suke ce mai d'an wulakanci har sunanshi Ahmad yana sun b'acewa sabida yadda d'an wulakanci ya bazu a bakin matan school d'in.
Wajan 3months sannan ya samu ya dawo gida dan ya kasa jurewa kasan cewar yana jin zujiyarshi na neman fazawa akan hakurin da yake yi hakan yasa ya dawo gida.
Da murna suka tare shi musamman ma Khadija da take jin tamkar ta had'iye shi sabida tsananin kyau da wayeqa da taga mijin nata ya kara, yayin da shima d'in ya bita da wani shu'umin kallo akan idon Mama amma shi sam ya manta tana gurin sai da tace,
"Babana shiga d'aki kayi wanka ka huta sai Ku fito muyi hira."
Sosa keya yayi yana murmushi yayin da Khadija ta shiga cikin d'akin tana mai dariya shima yabi bayanta cike da kunya dan yasan Mama tasan inda ya nufa gara ma yayi dan ko beyiba yasan zata d'auka yayin.
Da zazzab'i me zafin gaske ta tashi, sosai take rawar sanyi, shi ko duk ya rasa inda zai sakata domin taji dad'in jikinta, jiya keyi kamar ya maido da abinda takeji gaba d'aya ajikin shi.
Sai da yayi kwanaki biyar a gida yana murewa da jin dad'a, shi kanshi yasan Khadija tana da hakuri da dauriya gashi bata mai korafi ko sau nawa zai nemeta kuwa, ana ya gobe zai tafi kwana na shida kenan da dare sai da ya wahalar da ita dan ji yake idan ya koma sai yafi wahala akan na baya kasan cewar ya kara girma sanartakarshi karuwa take hakan yasa be saurara Mata ba sai da ya tabbatar da baya tare da damuwa.
Da kyar ta samu tayi sallah da asuba sannan ta koma ta kwanta, saida yaga ta fara bacci sannan shima yayi sallar, ya gama kintsa kayan shi sannan ya rab'a gefenta ya kwanta tare da rumgumeta ajikin shi.
Sai wajan bakwai na safe sannan ya farka a hankali ya lallab'a ya kwantar da ita sannan ya shige toilet be wani tsaya jona ruwaba gyara jikin shi kawai yayi ba tare da ya tsaya wanka ba sabida beso lokaci ya kure mishi.
Fita yayi sai wani k'amshin amarci ya keyi, kallo d'aya Maman tayi mishi ta kauda kanta, duk'awa yayi ya gaisheta ta amsa mishi a sake sannan ya nemi waje ya zauna tare dajan abin karinshi.
kallonshi tayi kamin tace "khadija fa?"
Sumar kanshi ya shafa kamin yace "bata da lafiya Mama bata ta shi ba."
K'arfe takwas na safe ya fito daga d'akin su rataye da jakarshi, kuma komawa yayi ya sumbaci goshinta sannan ya koma yayi wa Maman sallama ya tafi cike da kewar matar shi ga zullumin halin daya barta a ciki.
Sai wajan tara na safe sannan Mama ta nufi d'akin khadijan domin ganin halin da yaron nata ya barta. ganin zanin gado shanye akan kujeru yasa kirjinta yayi wani irin bugawa, cikin sanyin jiki ta k'arasa kuryar d'akin kwance taga khadijan cikin bargo tana ta barci sai dai daga ganin barcin kasan ba wani dad'in shi take jiba.
Cike da tausayawa ta fara tashin ta a hankali khadija ta bud'e idanunta tare da kallon Maman suna had'a ido ta fasa kuka tare da furta "Mama ni wallahi ban son ya Ahmad kirabani dashi kinji wallahi kasheni zai yi kin gani ya yagamin abuna."
Ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka tare da kokarin bud'e rufar dake jikinta domin Maman ta gani.
kamar zata saka mata kuka sabida tausayi haka Maman take lallashin ta domin ta tabbatar da cewa Ahmad ya maidata babbar mace ta sosai addu'a me tarin yawa tayi musu tare da fatan alkhairi sannan take ta jona ruwa a heater domin yayi zafi.
Mama da kanta ta temaka mata ta gashe jiknta tsaf sannan ta canza kaya tare da komawa d'akin Maman domin karyawa. itako Mama tsayawa tayi ta gyare mata d'akin tsaf sannan tabi ta can d'akin nata.
********
"Kai mutumi na wannan walwali da kake yi duk na menene ga wani munafikin murmishi da yak'i barin fuskarka ya kamata ka gayamin meye sirrin?
Cewar Hamza cike da mamakin sauyawar abokin nashi domin tun da ya sauka garin shike nan ya keta murmushi.
Cikin sautin dariya Ahmad yace "kai dai bari kawai wannan sirrina ne ni kad'ai." Suna hira har suka zauna domin cin abinci fitowar su kenan.
Saida ya gama duk abinda ya keyi sannan ya kwanta gami da d'auko wayar shi so yake yi yaji ya jikin khadijan.
"Mama kunyini lafiya?"
"Lafiya lau babana ka sauka lafiya ko ya makarantar?
"Lafiya lau Mama."
'Dan jim yayi sannan a kunya ce Ahmad d'in yace,
"Mama ya jikin khadija?"
Murmushi tayi kamin tace "gata nan zaune kusa dani ina ga fushi take da kai shi ya sam taki d'aukar wayar sai dai ni na d'aka."
Da kyar Maman ta samu khadijan ta amshi wayar, sai kuma tayi shiru murmushi yayi kamin yace babyna kaddai fishi kike yi da mijinki kuma yayan ki?"
Hamza dake zaune gefen Ahmad yayi saurin dawowa kusa dashi tare da zuba mishi idanu hadda wani tallabe kumatu ya kosa ya gama wayar ya bashi bayani.
A b'angaren khadija kuwa cikin shagwab'a da haushi tace "kai Yaya nifa Allah munb'ata tunda kai mugune."
Cike da nishad'i yayi mata dariya kamin ya fara bata hakurin lallashi gamida kalaman kauna sai gashi kamin ta ajiye wayar suna dariya.
Ita kanta Maman farin cikin kasan cewar su take, shi yasa yau ta yini tattalin khadijan.
Koda khadijan ta ajiye wayar Maman kallonta tayi tace,
"Tashi kije ki shiga ruwan dumi irin na d'azu sai ki kwanta ki huta kinji."
Ta fita tana jin kunya sosai.
*****
RAYUWA ta ciga gaba da juyawa wasu na cikin farin ciki yayin da wasu ke bakin ciki wasu na murnar samun karuwar su wasu kuma na kukan rashin da suka yi, yayin da wasu suka yi kud'i wasu kuma suka talauce. Toh da ma dai ita rayuwar kullum da kalar yanda zata zo maka wataran ka koka wataran kuma ka dara kamin dai me gaba d'aya ta riskeka.
KHADIJA taci gaba da karatunta cikin kwanciyar hankali babu abinda ta rasa domin Mama tana bata kulawa sosai, sannan sukan yi waya da mijinta kullun wanda gashi yanzu harta saba da rashin sa.
AHMAD shima ana shi b'angaren komai yana zuwa mishi cikin kwanciyar hakali, kuma yanda ya keso babu ruwan shi da harkar da babu ruwanshi balle ayi maganar kula 'yan mata, idan buk'atar shi ta tashi sai ya tashi da azumi domin wannan karan ya sama ranshi bazai zo gida da wuriba, babu kalar shakiyan cin da abokinshi Hamza be mishi sai dai yayi mishi dariya kawai gashi yanzu ya daina kiran sunan shi sai dai yace mishi ME MATA.....
*MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
[2/21, 11:03 PM] βͺ+234 803 615 9696β¬: *πDR.AHMADπ*
23
*NA MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
Edit by *Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSO....*π‘
(Home of expert & perfect writer's)
*B*ayan wata takwas:-
Cikin ikon Allah komai na tafiya musu kamar yadda suke addu'ar samu daga ubangiji.
khadija ta canza sosai tak'ara girma da wayau jikinta ya fara bud'awa sosai musamman k'ugunta. _Domin kuwa duk yarintar yarinya tayi wannan bud'ewar matukar ba namiji ta sani ba sabida haka iyaye ya kamata mu lura da irin girman yaran mu yana yin da jikin su yake matukar uwa me kulace to kuwa zatayi gaggawar sanin halin da yaranta suke ciki. Dan mace tana girma kamar yadda muka sani sai dai akwai wanda take yi na musamman matukar namiji ya fara shiga jikinta._
Khadija ta k'ara wayewa sosai musam man akan harkar aurenta domin tasami uwar miji tagari kullum k'ara nusar da ita take yi akan abinda ya shige mata duhu. Ta iya kwalliyar d'aukar hankalin mijinta sosai shi yasa taci burin ganin ranar zuwan shi gareta, tana cikin matsananciyar kewarshi kusan kullum yanzu sai tamishi kukan yaki dawowa ya ganta ita ta gaji da rashin ya dawo haka. sai dai shima ya lallasheta domin shi kadai yasan halin da yake ciki na rashinta kusa dashi.
A gaggauce yake danna kayan shi cikin jaka ba tare daya tsaya ninke wasuba. hamza yayi dariya tare da dafa kafad'ar Ahmad d'in yace "lallai naga alamar yau dai khadija ta murza kambunta nasan yau inbaka gantaba har rasuwa zaka iya yi."
Dariya Ahmad d'in yayi kamin yace "kome zaka fad'i ka fad'a wallahi amma yau a bayan matata zan kwana tunda mungama exam din nan mezanjira toh...!"
Cike da shakuwa suka rabu lokacin misalin sha biyu na rana. Da yaji ya zauna cikin mota daram sannan ya lalubi wayarshi yakira gida, lokacin wayar na hannun Mama ita kuma khadija ta tafi kitso wajan Mamanta. Bayan sun gaisa yake shaida mata gashinan tafe insha Allah kuma d'an wake ya keso aiyi mishi na fulawa.
Cikin murna Maman ta bishi da addu'ar sauka lafiya domin sunyi masifar kewar shi.
"Aminu! Aminu!! kai fito mana."
Cewar Mama bakinta har kunne, sabida tsabar murna.
"Yauwa Aminu na ruga wajan aunty khadija kace ta taho gida idan angama kitson ga mijinta nan bisa hanya ya taho."
Yana fita ita kuma taci gaba da gyare gyaren gidan domin Ahmad sam beson kazanta duk da itama Maman irin matan nanne masu tsafta to amma ahaka sai yaga kamar bemishi ba shi yasa lokacin da yana gidan ya gwammace yayi share-sharen shi da kanshi.
"Mama ki daina d'ura min wannan tsumin wallahi wani lokacin marata har murd'awa take yi kuma nasan zumar ciki kesani jin hakan."
Maman khadija tayi dariya kamin tace "a'a khadija kadda kiyima zuma sharri domin zuma bata da wata illa ajikin mutum saima gyarashi da take yi kedai kawai wani abun ke damun ki, kumafa gata nake miki domin nasan duk ranar da mijinki yadawo to zaki gayama garin ku, shiyasa nake miki tallafi amatsayina na mahaifiyarki."
Duk saida suka mike ganin yanda Aminu ya shigo da gudu yana haki Mama tace,
"kai amma dai Aminu Allah ya shiryeka walahi kamar wanda aka jeho daga sama?"
Cewar Maman khadijan daketa zare idanu domin bak'a ramin tsoro tajiba. saida yayi dariya sannan yace "aunty Mama tace idan angama kitson kiyi sauri kitaho ga mijinki nan bisa hanya ya taho."
Tsalle d'aya tayi ta isa wajan hijabin ta kamin tafara dariyar murna "wayyo Allah na ya Ahmad zai dawo." Maman ta kalleta da murmushi kamin tace "ah lallai khadija ko irin kunyar nan ma babu?"
Dariya tayi kamin tayi mata sallama.
Da zumud'i tayi sallama kamin tace "Mama sanu da gida ashe ya ahmad yau zai dawo?" "eh yanzu ba dad'ewa ya kirani yake gaya min shine nace bari na aika miki koda abinda zaki yi kisanshi da kakale kakalen tsiya, "babu wani datti dakina mama amma dai bari ingani sainazo na tayaki aikin.
Cikin kankanin loaci takalkale ko ina sannan tasaka turaren wuta me dad'in kamshi,.
Koda da ta fita tuni har Maman tagama komai saura dakan yaji dan haka tana dakawa itama tashige d'aki domin yin sallar azahar domin tuni biyuna rana ta wuce.
Saida tai wanka sannan ta d'auro alwala bayan tagama sallarta ta zauna ta tsara kwalliyarta duk da cewa bata yi wata me yawa ba amma tayi kyau sosai cikin riga da siket na atanfa kamshi kawai jikinta keyi gashi anyi asa'a domin kanta yasha kitso.
Suna zaune suna cin abinci yayi sallama cikin gidan. Aminu ya han kad'e kwanon d'an waken shi ya cacumi yayan shi yana ihun murna. D'agashi samayayi yana dariya kamin yace "wai gaskiya kayi nauyi Aminu."
Zama yayi sannan suka gaisa da Maman kamin khadijan ta gashe shi,