Showing 27001 words to 30000 words out of 51341 words
suke jera mishi akai-akai har ya samu ya zauna kan tabarmar kuma kusa da Maman shi. bakinta har kunne take amsa gaisuwar shi, khadija ko sannu da zuwa tayi mishi kamin ta nufi bayin su domin had'a mishi ruwan wanka, da mamaki yabi khadijan da kallo kamin yace "Mama khadija ta girma sosai wallahi."
Murmishi Maman tayi kamin tace "to babana da haka kakeso tauyi ta zama? kaima baka ga irin girman daka yiba kamar ba babana ba, kakoma magidanci guda, kaje kai wanka sai kaci abinci ka huta likita bokan turai..."
A kunyace yabi bayan khadijan cikin d'akin wata nutsuwa yaji tana saukar mishi jiyake kamar an fiddoshi daga gidan yari musamman daya shaki kamshin d'akin matar shi. zama yayi gefen gadon su yana bin d'akin da kallo tare da tunano irin guruzun da suka sha shida khadijan shi, ai nan da nan tsigar jikin shi ta wani mimmik'e ya kama zare idanuwa.......
*MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
*πDR.AHMADπ*
29
*NA MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
Edit by *Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSO....*π‘
(Home of expert & perfect writer's)
Leb'unan shi ya lashe tare dabin khadijan da lumsassun idanun shi wadda ke tsaye tana ciro mishi kayan da zai saka idan yayi wankan cikin sanyin murya tace,
"Ya Ahmad ga ruwan can na had'a maka."
Mikewa yayi ya isa jikinta tare da rungumeta ya fara sunsunar gashin kanta da wuyanta hannu wanshi kuwa tuni sun jima da fara yawo ajikin ta muryar shi a shak'e yake furta "babyna kin girma da yawa kin zama babbar yarinya ki gaya min meye sirrin?"
Dariya tayi tare da zame jikinta daga nashi tace "kai mafa kayi girma tunda harka fini kalli furkarka ga saje ga gemo, sannan kakusa ninkani tsawo ma, kuma ji kirjinka kamar me koyon karfi komai na jikinka ya kara girma da yawa..."
Dariya kawai yayi tare da kwab'e kayan shi ya shige bayin ita kuma ta kwashe kayan tare da gyara wajan.
koda ya fito tuni harta gama shirya mishi abinci acikin falonsu, tana zaune ya kirata tare da cewa "ina kika ajiye k'aramar jakar nan?" Khadija ta shiga cikin kunyar d'aki ya biyota ta bashi jakar a gadon su ya zazzageta maya-mayai ne da turaruka kala-kala tana zaune gefen shi harya gama shiryawa, sannan ya kama hannun ta.
kusan duk ita ta ciyar dashi sabida wata sangarta ya kemata ta musamman. tunda ya gama cin abincin ya like a jikinta kamar wani babyn da aka yaye, ya hanata sakat har sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya bar gidan itako wajan mama ta koma bayan ta gama gyara d'akin.
********
kun sani dai basaina baku labarin yanda daren nasu ya kasance bs domin kun fahimci waye Ahmad tun farkon labarin nan, khadija jitayi kamar ranar ya fara saninta domin tasha kuka kamar kamar me sai dai sam be d'aga mata kafafa ba balle da yake ganinta ta girma jikinta ya bud'e yanda yake bukatar ta.
koda ya dawo masallaci da asuba kasa barinta yayi dan haka tana gyara jikinta ta lallab'a tayi tafiyar ta d'akin Mama ta haye bayan Aminu tayi kwaciyar ta kamin wani lokaci tayi barcin mai nauyin gaske. sam Mama bata hanataba domin tasan Ahmad d'in bawani hakurin kirk'i ne da shi ba.
Ya jima yana jiranta yaji shiru dole barci ya d'auke shi ba tare da yaso hakan ba.
Maman da kanta ta shirya musu komai na kayan karin kumallo, tare suka karya gaba d'ayan su Ahmad yanata hararar khadijan sai dai ita sam tamaki yadda su had'a idanunsu waje d'aya.
Hira suka dasa a cikin d'akin Maman yawanci shi ke basu labarin makaranta da sauransu har kusan sha biyu sannan yace zai fita yaje gidan su khadijan sannan zaije banki.
kira wajan tara ya tadda awayar shi duk na zainab shaf ya mata da ita ma sai a lokacin, wayar kawai ya d'auka ya bar gidan.
Yana fita gidan ta kuma kiran shi, kuka tasaka mishi lokacin da taji ya d'auki wayar, saida tayi ta gaji sannan yace "ke dai zainab sam kuka be miki wahala sabida Allah yanzu kuma menai miki da zaki sakamin kuka?"
Jitayi kamar ta kashe wayarta sabida haushi sai dai ba zata iyaba tana son Ahmad d'in kamar ranta cikin muryar kuka tace "yanzu sabida Allah Ahmad hakama zaka ce tun jiya da muka rabu baka neminiba sannan kuma nayi ta kiranka amma baka d'auka ba kuma yanzu har kace wai mekayi min dandai kawai kaga Allah ya jarabeni da sonka ko Ahmad?"
Murmushi yayi me sauti kamin yace "naji to kiyi hakuri amma dai aikema kin san na gaya miki inada wasu iyalin ko? kokuwa so kike yi in barta alhalin shekara fin biyu bamu tare sai jiya dana dawo kuma sai na Kama wani abun?"
Jin tayi shiru, yasa shi cewa "to shi kenan yanzu dai kiyi hakuri zan kiraki da yamma yanzu ina hanya zanje wajen babana shikenan ko?"
Cikin shagwab'a ta furta "to kaddafa injika shiru kaji?" dariya yayi sannan ya kashe wayar, ba laifi itama ya fara son zainab d'in domin yana jin dad'in kulawar da take bashi.
Ahmad gari ya shige domin be wai-wayi gida ba sai wajan tara na dare, shima kusan san yine ya maida shi gidan. koda yaje gidan gaba d'aya kowacce ta sakayo kofarta dan haka yana rufe gidan dakin su ya shige, kudundune ya hangi khadijan cikin bargo, murmushi kawai yayi ya shige toilet sai da yayi wanka ya gyara jikin shi sannan ya labab'o ta bayanta ya kwanta benemi abinci ba domin ya ciko cikin shi wajan yawon shi.
Cikin barci takejin yana lalubarta tare da kiran sunanta, A hankali ta bud'e idanunta tana kallon shi arrnta sam bata son ya kusance ta sabida sanyi takeji kuma bata son wanka, sai dai tasan bata da yanda zata yi idan ya nema dole ta bashi.
Tashi tayi taje ta wanko bakinta sannan tace mai "ga abincin ka fa ya Ahmad."
Jawota yayi jikin shi kamin yace "A'a naci tuwo da baba d'azu banajin yinwa sai dai taki kawai....."
Marairaicewa tayi kamin tace "Allah ciwo wajan keyi kabari har gobe nad'an k'ara warwarewa. Rungumeta yayi jikin shi kamin shima yace "kiyi hakuri amma bazan iya barinkiba nima nayi mamakin yanda na shige da kyar jiya kila sabida munjima bamu had'uba ne kiyi hakuri idan ina yi akai akai wajan zai saki kinji ko....?!"
Da zafi-zafi yake nemanta kaikace cinyeta zai yi da kyar ta samu ta temaka mishi yasami nutsuwa sannan ya barta tayi barci yana nanike da ita, tunanin yanda zai kawo zainab gidan ya fara baya jin zai sami matsala ta ko ina saita wajan mamanshi zai iya hakuri da khadija ita kadai amatsayin matarshi sai dai ba zai iya hakurin rashin haihuwar taba yana bukatar son yaga jinin shi zai jure komai matukar za,a barshi ya auri zainab sabida dalilin haihuwa kawai bawai dan khadija bata isarshi ba a'a yana samin nutsuwa fiye da duk yanda zai misalta, a haka har barci ya kwasheshi cike da tunanika kala kala.
Da asuba fitinar shice ta tasheta saida ya kuma samun nutsuwa sannan sukai wanka ya tafi masallaci, kokari tayi tafita domin shirya abin kari gabb'anta duk ciwo suke yi sai dai tasan dole ta d'auki juriya da hakuri tunda har ya riga ya dawo.
Sai da taci ta koshi sannan ta koma d'akinta har lokacin Ahmad be fitoba, dan haka wanka tayi ta shirya sannan ta haye kujera tayi kwanciyarta dan tasan tana shiga kai kanta gado to ya gama barcin kanta zai koma, kamin wani lokaci tayi barci itama.
Sai wajan sha d'aya na safe Ahmad ya tashi,murmushi kawai yayi daya ganta tana barci, sai da ya gama shirinshi sannan ya nufi d'akin Maman shi. bayan sun gaisa yayi breakfast d'in shi sannan ya fuskance ta duk da irin bugawar da zuciyar shi keyi mishi akan maganar da zai gaya mata.
"Ammh Mama dama akwai wata yarinya sunan ta zainab damu kayi karatu tare da ita 'yar funtuwace to mun dai-daita da ita zamu yi aure shine nace zan gaya miki..."
Zubami shi idanunta tayi tana yi mishi wani kallon kurilla amma sam takasa tankawa ma sabida tsananin mamaki da al'ajabi....!
*MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
[3/8, 11:16 PM] βͺ+234 805 777 9929β¬: *πDR.AHMADπ*
30
*NA MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
Edit by *Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSO....*π‘
(Home of expert & perfect writer's)
*T*ajima tana kallon shi tare da mamakin furucin Ahmad d'in, can dai ta numfasa tare da cewa,
"Toh babana aini sam bamma fahimci inda ka dosaba balle in fahimci abinda kake nufi, ai saika fahimtar dani sosai ko ta yadda zan gane."
Cikin jin nauyi yace,
"Mama wata yarinya ce da muka yi karatu tare da ita shine..shine dama muka kulla soyayya yanzu so take yi in aureta Mama."
Wani mugun kallo tayi mishi wanda yasa shi gaggawar saukar da kanshi k'asa, kamin ta d'ora da cewa,
"Toh naji amma bada yawuna ba, kuma na gaya maka, yo ban dama kai d'in butulu ne babana me yayi maka zafi da har zaka k'ara aure haka? sabida Allah duk irin k'ok'arin da yarinyar take yi akanka baka gani yanzu da abinda zaka saka mata kenan wai kishiya?
To ba dai da amince wata ba domin nid'in ba butulu bace irinka domin ban mance da irin halaccin da iyayenta sukai mana ba kuma bana fatan na mance shi har abada, tashi kabani wuri tun kamin ranka ya b'aci ma."
Cikin sanyin jiki yabar gidan gaba d'aya, nan da nan ya shiga damuwa domin ba k'aramar takura yake shaba wajan ita zainab d'in akan yaje gidansu domin tuni itama ta dawo gida.
Abangaren maman kuwa kullun korar shi take yi domin yanzu ko zaman hirama ta daina yi dashi, itako khadija bata san me ake ciki bama domin ko afuska babu wanda ya nuna mata akwai wani abu.
Ganin fin sati biyu yana ta fama da Mama kuma ya kasa shawo kanta dan haka kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar malam Mamuda da maganar domin bashi da wani uba bayan shi duk da yana tunanin be kyauta ba idan yaje mishi da maganar a matsayin shi na sirikin shi sai dai bashi da yanda zai yi dole shine zai iya shawo kan Maman shi d'in.
"Babyna kizo muje nayi miki wankan naga kamar kin gaji da yawa ko?"
Yak'en dole tayi mishi kamin tace,
"Eh ai kam na gaji amma dai kaje kayo wankan ka tunda kace fita zaka yi, ka gani banjima da dawowa daga makaranta ba kai kuma ina shigowa ka taramin wata gajiyar, yanzu barci na keji amma idan na tashi to zan kintsa kamin ayi la'asar sai ka dawo."
Cike da kauna ya sunbaci kuncinanta sannan yabar d'akin.
******
Daga masallaci suka dawo tare shida malam Mamuda suna tafe suna hira har suka iso gidan, azauren gidan suka zauna kamar yadda Ahmad d'in ya bukata.
Sunjima zaune shiru babu wanda ya tanka domin sai yanzu Ahmad d'in yake jin wani irin nauyi daya dabaibaye shi.
"Ahmad nifa babanka ne idan baka gayamin abunda ke tafe dakai ba wa zaka gaya mawa? karka damu zan fahim ceka insha Allah fad'i ina jinka."
Cikin nutsuwa Ahmad d'in yayi mishi bayanin komai, sunjima babu wanda ya kuma tankawa domin shikan shi malam Mamuda saida yaji babu dad'i domin har saida ya gaza hakuri ya tambaye shi, kodai akwai abinda khadijan kemishi amma yace babu komai kawai dai yanaso ya k'ara auren ne idan sunyi mishi izini.
Ajiyar zuciya malam Mamuda ya sauke kamin yace,
"Toh ai be kamata ai ita Maman taku ta hanaka yiba tunda har kana so, amma dai sai inga kamar daka bari aikin naka ya kankama kadda ka takura kanka kaji?"
Cikin jin nauyi da kunya Ahmad d'in yace,
"Baba dama ba yanzu ba ina so Maman ta amince ne tukunna, itakuma yarinyar agana da iyayenta sabida kadda tayi tunanin ko yaudarar ta zanyi, kuma ranar litinin zanfara zuwa aiki a babban asbt har ofis d'ina naje nagani kuma akwai albashi me tsoka sannan kuma ko yanzu akwai kud'i awajena Mama ce dama dai abin jin."
"Toh shike nan karka damu insha Allah da anyi sallar isha'i' zanzo gidan kaji ko?"
Cewar malam Mamuda.
****
kamar yadda ya gaya mishi kuwa haka aka yi domin daga masallacin ma kai tsaye gidan su Ahmad d'in ya nufa.
Khadija da murna ta d'a ne mahaifinta, shiko dariya kawai yake tare da furta
"zaki kayar da nifa khadija ke har yanzu baki san kin girma ba ne..?!"
kallonta yayi yana jin tausayinta kamin yace,
"Ina Maman taku take ne wajanta nazo."
"To baba kashiga tana ciki."
"Yauwa toh kiramin mijinki idan yana nan ya taddani wajan Maman taku."
Sam babu sakin fuska haka suka gaisa domin tasan dalilin zuwan shi wajanta. shi kanshi Ahmad d'in saida yasha jinin jikin shi balle da yaga sam babu walwala atare da ita hasalima ko kallon inda yake bata yi..
Hakuri sosai malam Mamuda yayi ma Maman tare da nasiha san nan ya d'ora da fad'in ta amince da auren domin babu wanda yasan me gobe zata yi.
"Haba malam yaushe ne zaka daina biyema shirman yaron nan?
toh nidai gaskiya ban amince ba sabida Allah duk irin kokarin da yarinyar nan take yi dashi shi begani shinema zai saka mata da kishiya? kishiyarma gogagga 'yar duniya tunda har waje tatafi karatu wama yasani ko iskancin su sukai tayi shida ita shine abin be ishe shiba zai aurenta, toni ban yadda ba in kuma yace dole sai yayi to sai dai ya saki khadijan domin bazan yadda ya tozar ta taba wallahi."
Cikin tashin hankali Ahmad d'in ya fara bata hakuri tare da gayamata cewar bazai iya rabuwa da khadijan ba kuma yana sonta.
Wata uwar tsawa ta daka mishi wadda ta tsoratashi da malam Mamuda kamin tace,
"Maza ka tashi ka ficemin a d'aki na kamin na illataka wallahi sakarai kawai shasha sha."
Jiyayi kamar yayi ta kurma ihu lokacin daya fita kuma sai yayi karo da khadija bakin kofa tanata zubar hawaye domin tajima da jin duk wata magana da suka yi.
Da sauri ya nufeta sai dai kamin ya k'arasa jikinta tayi waje sabida wani mugun takaicin shi takeji, tunaninta shine duk irin yanda take kyautata mishi amma shi tunanin shi naga wata kenan, kuka take yi sosai yana lallashinta, bayan shigarsu cikin d'akinsu sai dai ko sauraran shi ta kasa yi balle ta fahimci me yake cewa ma.
A bangaren Maman kuwa ba k'aramin aikin lallashi da nasiha malam Mamuda yayi ba kamin ya shawo kanta wanda har kuka sai da tayi sabida tsabar takaici, bata tab'a tunanin Ahmad d'in zai iya haka ba ta kunya ba, domin wannan abun kunya ne sosai sannan tasan yaja mata zagi wajan mutane kai ba itabama harta iyayen khadijan sai abin ya shafesu. koda ta amince sam kin yadda tayi ayi maganar yanda za agyra komai sai dai daga karshema cewa tayi sam babu ruwanta da hidimarshi yayi duk abinda yaga dama aishi ne ya d'aure mishi k'ugun yin auren.
Daga karshe dai dole malam Mamuda yabar gidan tare da tunanin yanda zai fara tsara hidimar fatan shi Allah ya bawa khadijan shi hakuri da juriya kodan tallafama maraya da yayi shima....
*MANAN KHADIJA*ππ»ββ
[3/8, 11:20 PM] βͺ+234 805 777 9929β¬: *πDR.AHMADπ*
31
*NA MAMAN KHADIJA*ππ»ββ
Edit by *Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSO...*π‘
*S*am k'in yarda tayi ya rabi jikinta, dole ya koma gefenta ya kwanta batare da tunanin bacci zai d'auke shiba. sosai ya kejin tausayinta musamman yanzu da baccin wahala ya d'auketa amma ajiyar zuciya kawai take saukewa, gawani zazzabi-zazzabi daya keji kamar zai rufeta.
Tun asuba yaso ko magana ta hadasu amma ina kalma daya ce ta iya d'aurewa ta furta mishi, itace ina kwana daga ita bata k'ara ba.
kayan jikinta kawai ta canza tabar mishi d'akin gaba d'aya, wajan Mama taje suka gaisa sannan tace,
"Me za a d'ora Mama?"
Wani tausayin tane ya kama Maman dan haka ta rungumota jikinta kamin tace,
"kiyi hakuri kinji, insha Allah babu komai kibarshi yayi auren tunda ya nace muzuba mishi ido kawai, dama saida nace ban yadda da karatun sa a k'asar wajeba amma malam yazo ya matsa gashinan tun kamin aje ko ina ya fara zuwa mana da sabbin abubuwa kiyi hakuri dan Allah kidaina damun kanki kinji d'iyata..."
Hawaye tashare kamin tafara magana cikin kuka-kuka,
"Mama ya Ahmad be kyauta minba duk irin abinda nake mishi amma shine zaimin kishiya Mama kofa haihuwa banyiba?"
"Nace kiyi hakuri kirabu dashi tunda yanzu babu yanda zanyi mahaifinki yazo ya kasa ya tsare bani da wani abun yi domin ina jin nauyin mahafinki kiyi hakuri kawai."
Lallashinta taci gaba dayi har garin Allah ya waye kamin su shiga kitchen tare suka yi kunun tsayima da alalen leda.
Babu wanda ya kulashi ko wajan yin breakfast d'in dan haka sai yaji duk ya kasa sakewa ballema ya karya din dole ya tashi yabar gidan batare da sanin inda za shiba.
Dariya Maman tayi tare da mik'ama khadijan hannu suka kashe kamar wasu kawaye, ko abokanan wasa.
"Mama bari naje nayi shirin makaranta kinsan munata shirye-shiryen jarabawar fita."
"Toh madallah a dawo lafiya."
****
Cikin sati d'aya Ahmad ya fara fita hayyacin shi domin sam cikin gidan yadaina mishi dad'i sannan ga aiki daya fara zuwa duk zuciyar shi babu dad'i ga kuma shirye-shiryen biki domin tuni malam Mamuda yayi jagora zuwa funtuwa sungana da iyayen zainab kuma komai ya dai-daita ansa biki nan da wata biyu masu zuwa.
Tsakanin shi da khadija kuwa sai gaisuwa babu ruwanta da fitinar shi yanzu shi yasa harwani kumari tayi jikinta ya murje, sai dai tayi wanka ta shirya ta fice wajan Mama. to shima da yake yanzu be zaman gidan idan yafita takwas na safe sai biyar da rabi na yamma yake dawowa, burinshi yanzu ya sai mota kozai huta da wannan zirga-zirgar da yake fama da ita.
*****
A b'agaren