Showing 39001 words to 42000 words out of 51341 words

Chapter 14 - DR AHMAD

19 Oct 2024

11096

kamin ta kalli agogo saida tabari duk sun shiga sallar azhar sannan ta lallab'a ta fice bayan ta ajema Ahmad 'yar guntuwar takarda a bedside table....








*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

[3/8, 10:38 PM] ‪+234 816 846 7910‬: *💗DR.AHMAD💗*

37

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


_Wannan shafin nakune domin naga kuna jin dad'in labarin nan *DR AHMAD*, toh gashi kuyi yadda kuke so dashi_.

*Sister Ag*💕
*Sis Safara'u murtala*
*Real mai dambu*
*Ummumuhammad*
*Miss Marok'i*
*Khairat up*
Da k'awata ta kaina
*Sis Shafa'@t Omar*



*"K*inga wannan abun khadija, toh ba komai bane face kanunfari sai mazarkwaila da zuma, kinga abu ukun nan na rantse da Allah wanda ya halicceni kenan babu wata d'iya mace da zata kama wa innan abubuwan batare da ta mallaki mijin taba. Temakon da zata d'ora dashi biyu ne shine iya kwanciya da biyayya shikenan zaki iya zama da kowane irin namiji komai taurin kanshi da miskilancin shi kuwa, sabida mu lokacin mu duk babu irin wad'an nan kayan haukan da ake saidawar yanzu sai 'yan dubaru wanda bazasu taba cutar dake ba balle lafiyarki. kinga ZUMA! ita kadai ta isheki k'arin ni'ima ga KANUNFARI shima haka sannan kamshi zai zauna ajikinki musamman baki da kasanki sai MAZARKWAILA, kin dai san ita rakece sabida haka zanyi miki nasiha daki kiyayi kanki da duk wani nau'in na magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi b'ata ne, sannan ko wane kalar magani zakisha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zai yi.

YANZU fa babu kalar kashin dabbar da baza ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface? yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meya kesa mutuwar aure tai yawa awannan zamani musamman a arewacin Nigeria, toh bako mai bane face maganin mata domin wani maganin daga randaki kai amfani dashi shikenan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba dan haka ki daure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman kiba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma inaso kadda hakan yajaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin wata matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasamu kud'i zataje ta siyo wasu ashe-ashe haka abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala in dai zaki dinga cin kayan marmari kuma ki rike wannan sirrin toh zaki gode min nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

Tashi Khadija tayi cikin jin kunya ta fita har tanajin tuntub'e da kifar d'akin...

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yana yin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake sai wani irin shauk'i daya taso mishi alokacin.

Sai da ya gaishe da Mama sannan ya wuce d'akin su ganin itama ta shige tana mai dariya.


BAYAN ISHA'I

"Mama dama wani wani tunani nayi shine nace bari nai miki bayani sai naji menene shawararki akai,

Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tareba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba(malam Mamuda) sai kuma a fara temakama dangi, amma me kika gani?"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka yakara bud'i ina fatan dai naka ne bawai bashin banki bane kaje ka d'akko?"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama?!"

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Ah to aida gaskiyata hakafa mutane suke yi yanzu kawai suje su ciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Yace,

"A'ah Mama wallahi nawa ne halak malak kidena saka ran Zan d'aggo abinda yafi karfina."

"Toh Allah ya kyauta ya kuma tabbatar maka da alkairi babana."

"Amin Mama na."

Daga nan ya fita ya koma d'akin su,

Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasakar mishi ihu tare da kiran,

"Wayyo Allah cinyoyi na.!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai sharri kayan mata, amma dai kekam anyi raguwa yoo babyna ina naga wani nauyin da zaki min wannan ihu?"

Tureshi tayi daga jikinta kamin tace,

"Uhmm'ehm au hakama zaka minko? Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in,

"Wayyo Allah ni Ahmad marayan Allah, babyna ba kece raguwaba nine nan mugun rago kekam ai na shaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado a asibiti kisa a gano abinda yasani kwanciya.."

"Ah'ah Allah dai ya kaimu kuma in gaya maka na tsumu zakasha mamaki.."

"Habba my Dijama kema kinsan indai akanki ne ni mugun ragone kuma dole shashasha wa..."

Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin zura harshanta cikin bakinshi dayake ta faman motsawa daga nan wasan ya canza salo....













*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/8, 10:39 PM] ‪+234 816 846 7910‬: *💗DR.AHMAD💗*

38

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*AFUWAN 'YAN UWA ANYI MISTAKE SO SORRY*😉

_Wannan shafin nakune domin naga kuna jin dad'in labarin nan *DR AHMAD*, toh gashi kuyi yadda kuke so dashi_.

*Sister Ag*💕
*Sis Safara'u murtala*
*Real mai dambu*
*Mmn Gausiya*
*Ummumuhammad*
*Miss Marok'i*
*Khairat up*
Da k'awata ta kaina
*Sis Shafa'@t Omar*



*C*ikin yaddar Allah Ahmad ya fara aikin gidan kamar yadda ya jima yana tsarawa, duk da cewa ginin bawai irin k'aryar nan ya shirya ba amma gaskiya yayi kyau kusan tsawannin wata d'aya kenan da sati biyu tun da suka fara aikin basu tsaya ba domin dama aiki in dai daka yan yinsu magana ta kare.

D'akin Mama ciki da falo ne kamar da sai dai yanzu an mai dashi na zamani kuma hadda karamin toilet a ciki, gefen nata d'akin Aminu ne dai-dai shi duk ya zuba musu kayan amfani dai-dai matsayin aljihun shi.

Sai d'akin su ciki biyu ne sai falo a tsakiya sannan toilet mai had'e da bathroom, gaskiya anyi komai cikin tsari dan kuwa ginin yayi kyau sosai haka kuma labulaye sai da aka sakama kowan ne d'aki, kujerun khadija masu matukar kyau ne Ahmad ya zuba mata, amma d'akin Mama babu abinda aka saka mata sai cafet wanda ya mamaye d'akin.

Sai d'akin Aminu daga gadon shi sai wajan ajiyar kayan shi.

Gyara ya kammalu harma ya fad'i randa zasu tare.

*****

Zaune yake akan kujerar shi dake cikin ofis d'in shi, waya ce a hannun shi sai murmushi kawai yake zab gawa har wani lumshe idanun shi ya keyi da alama ba k'aramin jin dad'in wayar ya keba.

"Please babyna kibar kukan haka nan in dai ba so kike in kasa duba marasa lafiya ba, yanzu zan duba wani amma idan na gama zan kiraki kinji ko?"

"Ok bye-bye.."

Yanke wayar tayi tare da murmushi duk da cewa ba wani dad'in jikinta take jiba domin kuwa wani irin murd'awa takeji cikin ta na mata kamar za tayo amai.

**

Ba tare da yayi mishi kallon sani ba ya fara tambayar shi abinda ke da munshi, mamaki ya hana mutumin magana kamin ya d'ore yace,

"Oh nikam gani na keyi kamar yaron k'anina wanda yarasu IRO?!"

Wani kallon zama kai bayani Ahmad d'in yayi mishi kamin yace,

"Allah ko?!"

Cigaba yayi da rubutun shi kamin yace,

"Zaka iya tafiya wasu su shigo idan baka da abunda ke damun ka."

Da sauri mutumin ya fara bashi hakuri kamin yayi mai baya nin damuwar shi, magunguna ya rubuta mishi kamin yace.

"Insun k'are zaka iya dawowa domin muga yana yin jikin naka, zaka iya tafiya."

Tsabar kallon daya kema Ahmad din ne yasa shi cin karo da kofar office d'in, cikin tashin hankali ya fice har wani sassarfa ya keyi ya kosa ya k'arasa wajan babban yaronshi daya rako shi,

"Rikeni zubairu rikeni zubairu ashe wannan yaron me sunan baba na wajan marigayi ne likitan wallahi shine..."

Shi kan shi wanda aka kira da zubairun sai da yayi mamaki kuma ya tab'a zuwa ganin likita yaga Ahmad d'in amma sam be gane shi ba domin rabon Ahmad d'in da garinsu tun rasuwar mahaifinshi da yaje so d'aya suka yi mishi wulakanci be kuma komawa ba.

Hannun uban ya kama kamin yace,

"Allah ya kyauta to kawuce muje wajan maganin inga idan kud'ina zasu isa na siya maka."

Wani murmishin takaici yayi bayan tsohon ya b'acema ganin shi tabbas ada ya manta yanada wasu dangi daga mahaifinshi sai dai ayau da yaga tsohon nan ya tuno komai daya manta yayi kuma kokarin ganin ya sharesu aran shi.

*****

Sukuku haka ya koma gida, damuwa fal cikin ranshi sama-sama suka gaisa da Maman ya wuce d'akin da yake nasu shida khadijan, sai dai yana shiga ya taddata tana ta amai tuni ta gama galabaita.

"Innalillahi."

Ya furta da karfi kamin ya rungumeta jikin shi be damu da aman dake jikin taba.

Shigar da ita yayi ban d'akin dake d'akin ya gyara mata jikinta kamin ya kwantar da ita ya fara gyaran wajan, sannan ya shiga yayi wanka. koda ya fito tuni tai barci dan haka jikinta kawai ya tab'a sannan ya bar d'akin ta wuce d'akin Mama.

"Mama naga baba salisu yau yaje asibiti."

"Allah sarki ya suke suna lafiya ko?"

Beyi mamakin jin hakan daga gare taba domin tuni ya san cewa mahaifiyar shi macece me kawaici da kauda kai tare da yafiya. haushi yaji dan haka be kuma maganar ba sai ma maganar khadija daya sako mata,

"Mama baby fa amai ta keyi dana shiga d'akin amma dai yanzu tayi barci."

A rud'e ta kalleshi kamin tace,

"Subhanillahi dama naga yau kamar bata jin dad'i girkin ma ni nayi, Allah ya bata lafiya amma dan Allah babana ka dubata idan ciki ne sai kafara hakuri kadda amai-maita irin wancan karan."

Sauke kanshi k'asa yayi yana cin abinin shi sabida kunya, ya jima bece komai ba kamin yace,

"Kun gama had'a kayan ko? sabida daga dare zuwa safiyar gobe nake so mukoma can sabida an kusa bikin yusuf d'in bana so in takura shi sai insa ai mishi gyare-gyaren inda muka b'ata duk da dai naga babu abinda gidan yayi."

"Eh hakan yayi aima ya kyauta wallahi Allah ya saka da alkhairi ni tun jiyama na gama kintsa komai harna Aminu, sai dai ko d'akin ku."

"A'a canma yanzu zan shirya kamin ta tashi daga barcin tace ita zata yi.."

"To Allah yayi albarka ya kara bud'i me amfani."

"Amin Mama na gode."

******

"Wallahi da gaske nake muku yaron Habiba na gani yayi kud'i ya zama babban mutun daga gani ya tara abin duniya yaron nan."

D'alha wanda ke zaune abin duniya yada meshi yace musu,

"Yanda za ayi kawai mu shirya ranar asabar muje gidan nasu sai muce kawai dama zumunci muka zoyi kunga sai mugani idan arzikin nasu ne."

Innarsu wacce girma ya kama sosai tace,

"lallai baku da kunya har kai wannan yaron yanxu nan har kuna da idanun da zaku kalli iyalin iro da sunan zumunci? lallai kuna tare da dana sani."

Banza suka yi mata da kudirin zasuje su gani kota halin k'ak'ane.

****

Motsin shi taji ya ta sheta saida ta wanko bakinta sannan ya tema kamata ta zauna kamin yace,

"Babyna ya jikin naki? Tashi muje in ga fitsarinki kinji ko? yi hakuri me kike so kici? gaya mun na shirya mana kayan mu zuwa gobe zamu koma namu gidan angama komai sai naje na samo miki abinda kike so bayan kinyi fitsari na aunaki."











*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/8, 10:40 PM] ‪+234 816 846 7910‬: *💗DR.AHMAD💗*

39

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by Dota *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*I*nnalillahi haba khadijatu toh kuma menene na kuka? kiyi hakuri kinji dama haka ne kowa ce mace da kalar yadda take yin natq laulayin, kiyi shiru kinji ina ke miki ciwo yanzu?"

"Mama babu inda kemin ciwo, kawai dai banijin dad'i ne."

"Toh Allah ya baki lafiya ai kuma yanzu ke dajin dai-dai sai dai idan Allah ya saukeki lafiya sannu."

A bincin su aminu ya jera musu kamin ya fice gidan su khadija sabida sam be san zaman gidan sabida babu abokan wasa amma gidan su khadija akwai.

Cin karo ya kusa yi da ita tafito daga toilet daga ita sai karamin tawul wanda iyakar shi cinyoyinta had'iyar miyau yayi jikake k'uttt kamin ya nufeta yana murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban ya sakalata jikin shi tare da cewa,

"Babyna kin k'ara kyau da cika wallahi cikin nan yayi matukar yi miki kyau."

k'okarin zame jikinta ta keyi daga jikin shi shi kuma tuni ya fara sunsunarta yana lumshe idanuwa sabida kamshin sabulun da tayi amfani dashi, daurewa tayi ta biye mishi sabida tasan yayi hakurima sabida yanda yake da zalama tasan sam beda hakuri amma gashi yayi wajan kwana biyar sabida rashin lafiyar da tayi.

Kusan babu kalar shirmen da bemata ba sabida tsabar gigicewar da yayi, jiyayi kamar ranar ya fara saninta sabida irin samun nutsuwar da yayi akanta jikinta yayi zam-zam ta k'ara armashi har ya kasa gane farkon yinshi da na yanzu.

Cikin sanyin murya ya fara mata magana yayin da hannun shi ke cigaba da yawo ajikinta,

"Babyna kin gaji ko?"

"Uhumm..!"

Kawai ta iya cewa sabida gajiyar da tayi.

Ganin tayi shiru yasa shi cigaba da lalubarta da alama sake yi zai yi sabida ba karamin dad'i yajiba yanzu saima ji yayi kamar ya tsokano ma kanshi buk'atarta.

Cigaba da murzarta yayi har saida yaji ta sakar mishi kukan ta gaji sannan ya saura mata tare da rungumeta ajikin shi yana d'an jijjigata jikin shi saida yaga tayi lamo tana sauke nunfashi sannan ya tashi a hankali yana cewa,

"Bari in had'a mana ruwan wanka kinji ko..?!"

Tare suka yo wankan su har lokacin bebar lakud'ar jikinta ba ita ko kasala sai dai kawai tabishi da manyan idanuwan ta farare kal.

****

Sun jima tsaye kofar gidan suna jiran ganin yaron da zasu aika cikin gidan domin sam basu yadda da cewa wai wannan gidan nasu Ahmad bane, domin cikin suma akwai wa in da basu yarda da cewa Ahmad d'in likita bane.

Cikin ikon Allah saiga malam Mamuda zai shiga gidan domin tunda suka tare bezo yayi musu Allah ya sanya alkhairi ba, shine yaga yau tunda asabar ce yasan duk suna gida bari yaje.

Saida sukai kallon-kallon tsakaninsu kamin malam Mamudan ya mika musu hannu sukai musabaha domin shi yaga basu da niyyar bashi hannun da alama dai mamaki ne ya kusa kashe su.

"Kushigo mana kuzo mushiga ai sunanan ciki yau hutun karshen mako har Dr d'in ma nasan yana nan ciki."

Cikin sanyin jiki suka bi bayan shi, yayin da idanunsu keta yawo acikin gidan domin ba wata k'arya aka tsaraba agidan ammafa bak'aramin kyau yayi ba musamman da har yanzu yake kamshin sabon fenti.

Zaune suka taddasu d'akin Maman Ahmad na kusa da Maman shi yayin da khadija ke kwance acinyar Maman Ahmad d'in na mata matsar kafafu ita kuma Maman nata shafar gashin kanta tuni ita tayi barcinta sukuma hira kawai suke abunsu bazaka tab'a gane cewar suruka akewa wannan gatan ba.

"Sannu da zuwa Ahmad d'in da Maman kema malam Mamuda kamin idanun su ya sauka akan wa inda ke bayan shi.

Fuskar Maman babu wata damuwa sai dai tuni ta Ahmad ta canza dan haka komawa yayi kawai ya zauna tare da gyarama khadijan kafafunta wa inda ya sauke daga jikin shi yanzu.

Malam salisu ne ya fara magana cikin alhini da karayar zuciya yace,

"Dama mun zone domin muyi zumunci tunda kun yaddar damu sai kace ba jinin kuba."

Wani mugun kallon takaici Ahmad yayi mishi kamin yace cikin gadara,

"Ahh zumuncifa kace malam? kanaso kuyi shari'a da zumunci a gaban Allah kenan tunda har zaka iya zuwa wajan mu da sunan wai zumunci, koda yake kila ka manta irin korar dabbobin da kukai mana tare da yanke duk wata alaka datake tsakanin mu? kamanta ranar da ka dinga kiranmu da shegu karnuka kuma lalatattu dan kawai munje sada zumunci daku? ka manta ranar da kace mu d'auka bamu da sauran dangi acikin garin charanci sabida kun ruga kun ya femu? kun manta ranar da kuka tasani nida kanina kuka dinga tsine mana albarka da zagin cin mutunci ga mahafiyar mu kuma a gaban idanun mu?

Kamanta ranar da kake furta cewa kune kuka kashe mana mahaifi kuma kani agareku sabida kawai beyi muku d'in kunan daya saba mukuba?

Kun manta kace duk ranar da muka sake waiwayar charanci lallai sai kunyi sanadin ajalina musamman ni danake babba?
a hakan kuke tunanin zamu kuma waiwayarku harmu sada zumuncin?"

Ckin matukar sanyin murya ya furta,

"Ina yawan zuwa charanci ba tare da sanin kuba haka ma Mama sabida inaso inga ko zuciyarku ta sauya kunfara son mu, sai dai kash! kullum baku da aiki saina binmu da mugun kalaima na b'atanci da lalacewa, idan ban manta ba ko wata hudu da suka shige ankama yaronku musa yayima wata yarinya ciki, me kace a ranar? cewa kayi inama me sunan babane aka samu da laifin nan.
sabida haka kunga wannan ya nuna musu malam Mamuda wanda ya zabga tagumin mamaki da tsoran halin mutanen ya hanashi ko motsin kirki, Ahmad yaci gaba, to wannan shine uba agaremu nida k'anina bamu da kowa saishi shine ya tsaya mana haihuwar mune kawai beyi ba sannan daga karshe kun san gatan da yayi min wanda Ku kuka kekashe kuka kasa yimin? nasan baku saniba to wannan d'iyarshi ce ya aura min kamar yadda kukemin fatan inyima yaran mutane ciki to hakan be faruba sabida ya bani d'iyar shi tun kamin ta mallaki hankalin kanta, yanzu haka cikina ne na halal a cikin jikinta kuma ban tab'a shaye-shaye ba kamar yadda kuke min fata, ni _AHMAD BANI DA SAURAN WATA ALAKA DAKU_, dan haka kuyi gaggawar barin gidan nan kamin in had'aku da hukuma."

"Kai Ahmad gidan ku, nace kajiko gidan ku, nace iyayen naka zaka kai ga hukuma dan iya shege to inji kafara kaga yanda zanyi dakai..."

Cewar malam Mamuda da yayi karfin halin yin maganar, itako Mama ai kuka kawai take yi sabida jitai komai ya dawo mata sabo sannan bata tab'a tunanin shi Ahmad d'in ya rike abubuwan da suka faruba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login