Showing 111001 words to 114000 words out of 121890 words

Chapter 38 - DR KHALEEL Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

19353

ko baxae amsa ka ba ka gaishesa plss" ta karashe mgnr a sanyaye, nn ma shiru yyi snn yace "toh wife" tara da minti talatin da biyar suka isa gidan, har falon dad Ummi ta kai ta bayan sun gaisa, dad ya rage volume din news din da yake kallo ganinsu yace "sannu da xuwa, daga ina ku ke hka da daren nn" Ashnaah ta xauna kasa tace "daga gida muke Abba" dad yace "Ma'sha Allah, yi xaman ki kan kujera toh" tayi murmushi tace "A'a nn ya isa Abba ina yini?" Ya amsa mata yana murmushi, dai dai nn Khaleel ya shigo falon kansa a kasa ya durkusa ya gaida dad dinsa, ba tare da ya kallesa ba ya amsa, Khaleel ya Mike ya fita daga dakin, sun dde xaune da dad dake ta kallon news, can tace "Abba xa mu koma," Dad yace "baxa ku kwana nn ba, ae dare yyi" tayi murmushi tace "A'a tafiya xa mu yi Abba" yace "to shknn," mikewa tayi xata fita ya saida ta, ya dauka wayarsa ya kira Ummi, ba a dau lkci ba ta shigo, yace "ki bata sako na" Ummi tace "toh" snn suka fita dakin da Ashnaah bayan tayi masa gdya duk da bata san menene ba, dakin Ummi suka shiga, Khaleel dake xaune yana danna wayarsa ya dago kai yana kallonsu, Ummi ta bude ward robe dinta ta shiga fiddo ledoji dauke da kayan bbies masu tsada, Ashnaah ta dan komawa baya kanta a kasa, kaya ne masu yawan gskya kuma yawancinsu duk na waje ne, sae da momy ta gama fiddo su gaba daya snn ta kalli Ashnaah da ta kasa dago kae ta kalleta tace "gashi dad dinku ya siya maki" hawaye ne ya shiga sakkowa idonta ta kasa kallon ummin, a hnkli tace "na gode Ummi," Ummi tayi murmushi tace "aa ki je can ki masa gdya ba ni na siya maki ba" Ashnaah ta juya a sanyaye ta fita daga dakin ta koma falon dad ta durkusa har kasa hawaye na ci gaba da bin kuncinta tace "mun gods Abba, Allah ya kara budi" yyi murmushi yace "bbu komae dota" kasa tashi tayi ta bar dakin, a sanyaye tace "Abba ka yafe mana kuma" Dad yace "tashi ki je, Allah yyi maku albarka" mikewa tayi da kyar ta fice daga dakin, har suka koma gida Ashnaah bata daina kukan da take ba. Washegari litinin Karfe sha daya Najeeb ya shigo da sallama, Ashnaah ce xaune kadae falon rike da hisnul Muslim tana dubawa, ita kadae tasan abinda take ji tun tashin ta ranan amma taki barin Khaleel ya gane, wani ciwon bala'i bayanta da kwankwasonta ke mata, ta dauki hijab dinta ta sa suka gaisa tana kirkiran murmushi yace "Khaleel baya nn ne" tace "yace min yana xuwa ynxun nn, ya je pharmacy" Najeeb ya shafa kansa yace "OK, yauwa dama ina son wata mgna da ke Fateema" Ashnaah ta maida hnklinta tace "ina jin ka toh" ya dan yi shiru sae kuma yace "dama I only want to ask for ur forgiveness fateema, I caused everything yhu nd ur husband are goin through" Ashnaah tayi shiru tana kallonsa da confusion, ya gyada mata kai yace "yes! I wrote dat divorce content, sae dae in baki manta ba ke kika taba bukatan hka" hawaye ne ya cika idonta, a hnkli yace "na gaya ma Khaleel bae yrda ba don a tunaninsa baxan taba masa hka ba, amma ni ne nn na rubuta, da fatan xa ki gaya masa ki kuma rokan min shi ya yafe min" Ashnaah ta gyada masa kai a sanyaye tace "its OK" yyi murmushi ya mike yace "I will b on my way, ki gaida min shi idan ya dawo" kasa amsawa tayi ta dalilin wani axababben ciwo da mararta ya shiga yi mata, lkci daya bayanta da kugunta suka dauka su ma, Najeeb ya lura da halin da ta shiga lkci daya ya ce "ya dae?" Kasa basa amsa tayi, ta shiga yarfe hannu don axaba, ya dawo kusa da ita lkci daya ya gane labour ne ya xo mata, Ashnaah ta kasa daurewa ta fashe masa da kuka, ganin bbu wani alternative yasa ya dagota kawae ya ja ta suka fita daga falon da sauri, ba karamin daurewa tayi ba har suka isa motarsa ya bude bck seat ya taimaka mata ta shiga ya tada motar ya nufi asibitin dad din Ameesha da ita da sauri ganin nn ne kadae baxa a bata masu lkci ba, bbu bata lkcin kuwa aka karbeta aka nufi labour ward da ita, Ashnaah kam bata san inda kanta yake ba a lkcn nn, amma bbu abinda ke fitowa bakinta sae salati, can kuma tace ita ina Abbanta. Najeeb ya fice daga ward din ya Ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran Khaleel yana dagawa yace "ka taho clinic Khaleel, na je gida na samu fateema na labour" a rude Khaleel yace "wani asibitin" Najeeb ya gaya masa, a fusace yace "don me xaka kai ta wnn asibitin, gsya baka kyauta min ba Najeeb" Najeeb ya katse kiran ya nufi inda Ashnaah take don ganin halin da take ciki.
[8:51PM, 12/1/2016] A H💥: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
112.....
Khaleel na shigowa clinic din ya nufi labour ward hnklinsa a tashe ba tare da ya bi ta kan nurses din dake reception ba, suka ci karo da Najeeb, Najeeb ya rikosa yace "kana da nmbr Dad dinta?" Khaleel ya fixge hannunsa xae ci gaba da tafiya Najeeb ya fixgosa a fusace yace "da'lla ka saurareni malam" Khaleel yace "me xa ayi da shi" Najeeb yace "dad din Ameesha yace I shud ask yhu, yhu knw! she's just giving headache in there sae Abbanta take kira, just cal him kadda ta ja ma kanta da babies din cikinta wani harm" Khaleel ya dafe kansa ya juya xae shiga room din Najeeb ya kuma rikosa yace "Cool down man, she's OK ka bani nmbr dad dinta kawae" khaleel ya girgixa kai da kyar yace "bani da shi, I dnt have" yana kai wa nn ya kuma juyawa da sauri Najeeb ya kuma rikesa yace "ka kwantar da hnklin ka frnd xata sauka lfya idan Allah ya yrda, ko nmbr mum dinta gare ka ka bani kawae, we will get to her dad through d mum" khaleel ya fiddo wayarsa a sanyaye ya shiga neman layin mum din Ashnaah, Najeeb ne ya karba wayar ya ja sa suka fita xuwa haraban asibitin, bin sa kawae khaleel yake ba don yasan yana yi ba, bugu biyu momy ta daga, Najeeb ya gaisheta snn yace "em momy abokin mijin fateema ne, dama da Abba muke son mgna don Allah" momy da lkci daya hnklinta ya tashi ta dake tace "lfya?" Najeeb yace "lfya lau, Fateemar ce dae ke nakuda, kuma ta dage tana son ganin abbanta, don Allah ki masa mgna momy kar wani abun ya sameta, kila idan ta gansa xa ta samu nutsuwa, har Allah ya sauketa lfya" momy da gaba daya hnklinta ya gama tashi tace "toh bari in gaya masa, wani asibitin ne don Allah" Najeeb ya gaya mata asibitin, momy ta katse wayar hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri don xuwa gun mai gidan nata da ke falo, kasa ce mata komae Abba yyi yana kallonta can ya mike a hnkli ya dauki makullin motarsa yace "wani asibitin ne?" Momy ta gaya masa ya juya ya fice. Duk ynda khaleel ya so shiga labour ward ya ga Ashnaah kin barinsa dad din Ameesha yyi, wani doctor faruqh ya ja sa suka fita can haraban asibitin ya ajiye masa kujera yace "ka xauna nn plss kar ka kuma shigowa ko da reception ne, sae kace ba likita ba khaleel cool down plss Allah xae sauke matarka lfya kai ta mata addu'a kawae" Khaleel ya xauna ya dafe kansa dake sara masa bae ce komae ba, Likitan ya juya ya koma cikin asibitin, har Abban Ashnaah ya shigo asibitin Khaleel bae lura da shi ba, Abba na shiga reception Najeeb ya nufo sa da sauri yace "sannu da xuwa Abba, mu je ka ganta" bin sa kawae Abba ya shiga yi bae ce komae ba, dai dai bakin ward din suka hadu da dad din Ameesha ya fito da wani likita da ya tura ya kira masa Khaleel kawae ya xo ya sa hannu ayi mata cs don bae ga alamar xata iya haihuwa da kanta ba, yana kallon Abba yace "kai ne mahaifinta koh Alhaji?" Abba ya gyada masa kae kawae, dad din Ameesha ya koma cikin ward din ba a dau lkci ba ya fito yace "ka shiga ka ganta Alhaji," Abba ya tura kofan ya shiga Najeeb na biye da shi a baya, kasa karasawa ciki yyi yana kallon yar tasa, idonta rufe gam ta rike hannun Ameesha da ke ta tofa mata addu'a, bbu abinda ke fitowa bakinta sae salati in tayi tayi ta gaji sae kuma tace ina Abbanta ita a kira mata shi, nurses uku ne kanta da likita daya, Abba ya karaso ya dan duka kusa da ita yana kallonta yace "am here daughter," bude ido tayi da sauri lkci daya ta tsaida surutan da take ta shiga kkrin mikewa xaune ya dakatar da ita ya rike hannunta cikin nasa yace "kar ki damu fateema, yhu will b alryt in'sha Allah" ta kuma fashewa da kuka da kyar ta bude baki muryarta na rawa tace "don Allah don annabi ka yafe min Abbana" Abba ya girgixa mata kai a hnkli yace "na yafe maki da ddewa fateema, yhu will b alryt dota, kiyi ta addu'a" ta fashe da wani matsanancin kuka ta rike hannunsa gam muryarta na rawa tace "da gske Abbana" Kae kawae Abba ke iya gyada mata, ta saki salati tana girgixa ta dalilin wani axaba da take ji lkci daya ta shiga kkrin mikewa kuma, Abba ya mayar da ita shi ma ya shiga tofa mata addu'an, axaban da take ji bae sa ta rufe baki ba tace "Abba momyna fa ina take" Abba bae ce mata komae ba sae adduan da yake ta tofa mata yana rike da ita. Ba karamin wahala Ashnaah ta sha ba don har an fara shirin shiga da ita theatre ta sullubo santalelen danta ko minti daya ba ayi ba dan uwansa ya biyo sa, bbu abinda ke fitowa bakin ta sae salati tana rike da hannun Abbanta da ke kanta har lkcn idonta a runtse, a hnkli ta bude idanuwanta ta shiga kkrin bude baki da nufin yi ma abbanta mgna amma ta kasa, ya duka don jin me xata ce ya ga ta soma cika hannunsa daga nata a hnkli har ta sake gaba daya, lkci daya ya ga kmr komae na ta ya tsaya, a rude ya kamo hannunta yace "fateema" Ameesha da ke kallon duk abinda ya faru ta koma baya da sauri lkci daya ta juya masu baya ta runtse ido xuciyarta na bugawa, dad dinta ya taho da sauri yana kallon Ashnaah a sanyaye, Dr Faruqh ne yyi karfin halin dauko stethoscope ya dawo ya shiga duba ta, Najeeb ya ajiye yaron hannunsa ya karaso da sauri ganin ynda faruqh ya tsaya kmr gunki yana kallonta, fixge stethoscope din yyi ya shiga dubata, faruqh ya juya ya fice daga ward din kawae, Abba da gaba daya ya gama rudewa yace "plss ku gaya min wats wrong, wats wrong with my dota" Najeeb ya hade kansa da abun gado ya kasa dagowa.
Infact duk Wanda yasan chapter din nn yyi masa sugar ya taho mu kwashi shoki, lol, Wanda kuma yasan bae masa sugar ba toh I assure him dogon suma tayi. Masu kkrin hacking fcbk accnt dina kuma su rufamin asiri su yi hkuri bata mutu ba ehe, Lol.
I dedicate this page to Rukayya Usman Adam Allah bar min ke kawalli.
[8:52PM, 12/1/2016] A H💥: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
113.....
Najeeb ya mike da kyar idonsa ya kada yyi jajur ya juya xae fita daga dakin, Abba ya fixgosa hnkli tashe yace "na ce ku gaya min me ya sameta pls" hawaye ne suka sakko idon Najeeb yana kallon Abba, ya juya kawae ya fice daga ward din da sauri, Abba ya bi sa da kallo a sanyaye lkci daya ya xare glass din idonsa yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya juya yana kallonta yana girgixa kai ya nufe ta da sauri ya rike a rikice yana cewa "No! No! It can't be, y fateema, plss kar kiyi mana hka" hawaye suka shiga xubo masa shi ma ya hade kai da abun gadon har lkcn yana rike da ita, dad din Ameesha ya xare glass din idonsa shi ma idonsa ya kada ssae ya karaso kusa da Abba ya dago sa yace "dats nt the right thing to do now Alhaji," a hnkli ya kara da cewa "pray for ur dota" Abba ya rikosa a rude yana girgixa kai yace "are yhu tryn to tell me she's no more" dad din Ameesha bae ce komae ba, Abba ya kuma hade kae da gado yana hawaye ssae, Dad ya juya yana kallon Ameesha da ke durkushe sae rusa kuka take kmr ranta xae fita, ya karaso kusa da ita ya dagota, cikin rawar murya tace "dad she's gone" rungumeta yyi a hnkli yace "yes dota, yhu only pray for her now," ta kuma fashewa da wani matsanancin kukan da yafi da muryarta ta rawa tace "Khaleel...." Dad dinta ya dago kanta yana rarrashinta, Najeeb na fita daga asibitin Khaleel da ke xaune har lkcn a haraban hsptl ya mike da sauri ya nufo sa, da damuwa kmr xae masa kuka yace "plss frnd ka gaya min halin da ake ciki, how's my wife" Najeeb da ke ta ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya kallesa ba yace "da'alla malam ka rabu da ni, I've told yhu several times, she is OK" yana fadin hka ya fice daga gate gaba daya Khaleel ya bi sa da kallo, mancewa da warning din dad din Ameesha yyi ya nufi cikin asibitin da sauri, ko wacce nurse ya tambaya sae tace "she is OK dogon nakuda take" duk ya xama abun tausayi, ya ja gefe ya tsaya a reception din. Abba ya kusa minti goma kansa na kife kan gadon da Ashnaah ta ke har lkcn, Dad din Ameesha ya dago sa ya lulluba mata xanin gado yace "take heart Alhaji kar ka mance cewa kullum nafsin xa'ikatul maut, addu'a kawae xaka yi ma 'yar ka, mu ma idan ta mu ta xo Allah sa mu cika da imani" Abba da hawaye ya kasa tsaya masa bae ce komae ba ya ciro wayarsa da ke ring a aljihunsa, momy ce ke kiransa, ya mayar da wayar yana kallo. Ashnaah ya duka yana kallon Ashnaah hawaye ba sakko masa, a hnkli hawaye yace "Allah ya ji kan ki fateema ya yafe ma ki duk kurakuranki yyi maki rahama ya haskaka kabarin ki, ya raya abinda kika bari, na yafe maki duniya da lahira baki min komae ba fateema......" Kasa ci gaba yyi ta dalilin tokarewa da muryarsa yyi hawaye na ci gaba da sakko masa, dad din Ameesha ya dago sa yace "Ameen Alhaji, Allah yyi Mata rahama ya amshi shahadar ta" da kyar Abba yace "Ameen," snn ya ciro wayarsa jin momy na ta kiransa, ya fiddo handkerchief ya share fuskarsa ya daga kiran, daga daya bangaren momy tace "ta haihu ne Alhaji, wllh hnklina ya kasa kwanciya tun daxu" Abba da wasu sabbin hawayen suka xubo masa ya dake yace "ehh ta haihu Alhmdllh" cike da murna momy tace "Alhmdllh, me aka samu?" Abba ya juya yana kallon yaran da ke kwance nurses sun gama gyara su a hnkli yace "yan biyu ne duk maxa" ciki da jin ddi momy tace "Allah sarki, to ya fateemar?" Abba ya dan yi shiru a sanyaye sae kuma yace "Alhmdllh," momy tace "toh don Allah ka bata wayar" Abba ya girgixa kai da kyar yace "ni ina waje ne" momy tace "toh shknn, Ashfah ma bata jin ddi wllh amma na kira Mata likita ya xo har ya dubata ya mata allura, daxu muna kitchen ta yanke jiki ta fadi wllh ko minti talatin ba ayi ba ma ynxu, dama kuma tun jiya na lura bata jin ddi, kaga da mun xo" Abba da hawaye kawae yake ya daure yace "to sae na dawo" yana fadin hka ya katse wayar, bbu abinda Ameesha take har lkcn bn da kuka kmr ranta xae fita, dad dinta ya kamo hannunta ya share mata fuskar ta yace "maxa ki tafi office dina ki xauna, dnt say a word to any body" kae kawae take gyada masa a sanyaye har lkcn tana hawaye, ya kuma share mata fuska snn ta juya jiki ba kwari tana jan kafa ta fita daga ward din, Khaleel ta hango tayi saurin canxa hanya amma tuni ya ganta ya nufo ta da sauri, tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da tafiya da sauri da sauri, bin ta yyi shi ma da sauri har ya risketa ya rikota yace "wait Ameesha, don Allah ta haihu ne?" Ameesha ta ki juyowa ta dake tana ci gaba da tafiya ta ce "ehh ynxun nn ta haihu, sauri nake dad ya aike ni office" juyo da ita yyi da sauri yace "wait, don Allah is she OK" Shiru yyi yana kallonta ganin idanuwanta ynda suka kumbura, ta kirkiro murmushi tana gyada masa kai tace "yes she is OK, amma ta sha wahala ssae, ta ban tausayi" tana fadin hka tayi saurin juya masa baya ta dalilin hawayen da ya shiga taruwa idonta ta ci gaba da tafiya tace "bari in dauko abinda aka aikeni" Khaleel ya kuma bin ta ya juyo da ita hawayen da take mayar wa ya xubo mata lkci daya ta kasa daurewa ta fashe da kuka ssae, tsayawa kallonta yyi yana girgixa kae yace "no, no ki gaya min ina fateema ta, me ya faru" juyawa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login