Showing 1 words to 3000 words out of 121890 words

Chapter 1 - DR KHALEEL Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

16458

[10/14, 3:25 PM] ‪+234 806 484 7850‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
1.....
A hankali yake cin fruit Salad din dake gabansa kansa a sunkuye yana murmushin nan nasa mae kyau da ya kai ga har ana iya ganin dimples dinsa, ya girgixa kai snn ya dago yana kallon matashiyar matar dake xaune kan kujerar dake kallon nasa fuskarta a daure ta kafa masa ido tana kallo, murmushi ya kuma yi mai sauti xae yi magana ta rigasa a fusace tace "ohh ga mahaukaciya na magana ko Khaleel, ni ce ma na xama abun dariyarka knn" ya dan marairaice ya ajiye fork din hannunsa yace "ba hka bane Mum, kiyi hkuri," ya dan shafa kansa da damuwa yace "kinsan komai fa lkci ne mum, kawae su Ummi da Abba sun kasa gane hkn ne, sun ki fahimtar abinda nake nufi am just bored of all dis...." shafa kansa ya kuma yi har lkcn fuskarsa na dauke da damuwa yana kallon Small mum din tasa, sallamar da aka yi yasa duk suka maida hankalinsu ga bakin kofa tare da amsa sallamar, mikewa mum tayi ganin baki tayi da fara'arta tana masu sannu da xuwa suka karaso cikin falon aka shiga gaggaisawa, Khaleel ya mike yana kallon Small mum din tasa yace "to mumy sae na kuma dawowa ko xuwa gobe" tace "a'a ka dae dawo xuwa anjima da daddare bamu gama magana ba" yyi murmushi yace "in'sha Allah mum" bowl din fruit Salad din da ya ci ya dauka xae kai kitchen tace "a'a ka bar shi kawae xa a kwashe" yace "No bari in kai mum" ya nufi kitchen da bowl din ya ajiya snn ya fito yyi ma bakin sallama ya fice daga falon yana kallon agogon hannunsa, gun motarsa ya nufa yana tafe yana satan kallon wata bishiya dake dauke da fararen kujerun roba da table a karkashinta ya ga ko wa inda ya gani daxu gurin suna nan ko sun bar wajen, suna xaune ko har lkcn su biyu kmr ynda ya samesu da ya shigo, sae dae wnn karan ba hira suke ba daya na danna wayarta daya kuma na waya ne, hada ido suka yi da warce ke danna waya don ita ma satan kallon nasa take, ya dauke kansa da sauri, ita ko kallon me wayar tayi tana 'yar dariya tace "dubi gantalalle neman gaisuwata yake" da sauri tayi pretend tace "lahh Ya Khaleel yaushe ka xo" juyawa yyi yana kallonta duk da yasan taga shigowarsa daxu bbu yabo bbu fallasa yace "kin ban sako ne" ta dan yatsine fuska tace "No kawae nayi mamakin ganin ka a gidanmu ne yau, coz ba saba xuwa kayi ba, any way ina yini" ya watsa mata wani mugun kallo ya bude motarsa ya shige yyi horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, dariya ta saki tana kallon kawarta da ta kasa ci gaba da wayan da take ta rakasa da kallo har ta daina hango motarsa mai gadi ya rufe gate din, can ta maida kallonta ga kawarta dake ta faman dariya ta sauke ajiyar xuciya tace "gaskiya gayen nn ya hadu Meenah, ni dae hka kawae naji yana burgeni," Meenah tayi ma kawarta ta wani irin kallo tace "shi Khaleel din ke burgeki? Tabdi da kinsan halinsa da baxa ki ce komai ba wllh! wnn mugun dan rainin hankalin, ae ni tun da na taso kallon arziki bae taba hada mu ba kin dae ga dan uwana ne, ki bari xan baki lbrin ko waye shi salma, kin taba ganin wani cousin dina ya shigo gidan nn ban gaishesa ba, kuma kin dae san ni da son xumunci Salma, tunda har ki ka ga Khaleel ya shigo gidanmu ban gaida sa ba na dauke kai kiyi shiru kawae" Salma tace "haba abun ya ban mmki wllh, to Allah shi kyauta, ni dae mu shiga ciki in yi ma Momy sallama in kama hanyar gida kafin Mama ta fara kirana" Meenah tace "haba tun da wuri hka, to ki bari bakinta su tafi mana, nasan ba dde wa xa su yi ba" Salma ta harare ta tace "lallai kam da yake ke a gidan ku kike ba shiyasa xaki ce in jira bakin da ban san ranan tafiyarsu ba su wuce" mikewa salma tayi ta nufi cikin gida, Meenah ta mike tana dariya ta bita suka shiga falon a tare. Barkan Ku da Sallah sisterz.
[10/14, 3:25 PM] ‪+234 806 484 7850‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 2...... Karfe tara da rabi na dare Khaleel ya gama parkin din motarsa a parkin space din dake cikin gidansu dake G.R.A kaduna, ya bude motar ya fito yana kallon motar dad dinsa ko ba a gaya masa ba yasan ya dawo, ya nufi balconyn da xae sada sa da kofar shiga babban falon gidan, can ciki yyi sallama ya shiga falon ya tarda kanwarsa Rukayya kwance tana kallo, ta mike xaune ganinsa tace "sannu da dawowa ya Khaleel" ba tare da ya kalleta ba yace "sannu" snn ya nufi stairs, dad dinsa suka kusan cin karo da ya ja baya da sauri tare da dan ritsinawa ya gaishesa, bbu yabo bbu fallasa mahaifin nasa ya amsa snn yace "ina nemanka a falona" dad dinsa na fadin hka ya juya ya koma xuwa falonsa, Khaleel ya share wata xufa dake keto masa a goshi ya shafa kansa snn ya shiga haurawa saman a sanyaye, dakin mum dinsa ya nufa tana xaune gefen gadonta tana waya, mai aiki na yayyanka mata fruits a faranti, ya nemi gefenta ya xauna har ta gama, tana kallonsa tace "sae ynxu son" ya dan marairaice mata yace "ummi don Allah ki raka ni gun abba wae yana kirana" tayi masa wani irin kallo tace "sae na raka ka? Ashe ko baxa ka je ba" ya ciro handkerchief ya share fuskarsa bae ce komai ba ya mike ya fita daga dakin ya nufi falon Abbansa, xaune ya tarda Abban nasa yana shan coffee, ya xauna kasan carpet din dake tsakiyar falon ba tare da ya kallesa ba yace "Abba gani"Abban nasa ya ajiya kofin hannunsa yace "ka gama play din hide nd seek din dani Khaleel" Khaleel ya dan yi murmushi ba tare da ya shirya ba yace "wllh ba hka bane Abba aiki ne yyi min yawa a clinic" ummi ce ta turo kofan falon ta shigo, Khaleel yaji ddin ganinta ta nemi gefen mai gidan nata ta xauna.
[10/14, 3:26 PM] ‪+234 806 484 7850‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 3..... A hankali Khaleel ya daga kai yana kallon Abbansa ganin shirun yyi yawa, kallonsa ya ga Abba na yi, hkn yasa ya dukar da kansa kuma, Abba ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace "me kke nufi da mu Khaleel?" kasa cewa komai Khaleel yyi har lkcin kansa na kasa, Abba ya maida kallonsa ga TVn dake ta aiki a falon yace "shknn, dat clearly shows dat raina mu kawae kayi, don hka ni na yanke shawarar hada ka da either Meenah ko Maryam, ka je kayi shawara ka xabi daya cikinsu, nd bet me, dat wont take a lng tym, ka tashi ka bamu waje" kasa ko da kwakkwaran Motsi Khaleel yyi daga inda yake a durkushe, komae nasa ya tsaya cak, da kyar ya shiga share xufar dake keto masa a fuska ya daga kai yana kallon Mum dinsa da ko kadan bae ga alaman hkn ya dameta ba, sunayen wa inda Abba ya ambato masa suka shiga yawo a kansa, wae Meenah ko Maryam, ji yyi kmr ya saka ma iyayen nasa kuka, Muryar Abba ya ji a tsakiyar kansa yana cewa "nace ka tashi ka bamu waje" dago kansa yyi da sauri ya marairaice murya yana kallon iyayen nasa yace "don Allah don annabi kayi hkuri Abba wllh ni duk bana son su, na maka alkawarin nn da wata daya kacal xan gabato maku da matar da xan aura plss Abbana consider me, nasan na maku laifi" ya karashe mgnr kmr xae yi kuka, Abba na masa mugun kallo yace "ka raina ma kan ka hankali ba mu ba, common get out my frnd" juyawa yyi da sauri yana kallon Mum dinsa, idonsa ya kada yyi jajur cikin rawan murya ya fara mata mgna "ummi don Allah ki sa baki...." harara ta watsa masa tace "da knn ba ynxu ba" dafe kansa yyi xuciyarsa na tafarfasa, ae shi da ya aure wa in nan yaran da abba ya ambato masa gwara ya mutu ba aure, dat aside ma shi ko kadan bae son auren xumunci kallon arxiki baya hada sa da yaran yan uwan iyayensa gaba daya duk baya sake masu, goge Fuskarsa yyi da handkerchief a nutse yana kallon Abbansa ya fara magana "Abba i knw na maku laifi, plss ku yi hkuri ku yafe min, na kuma maku alkawarin nan da wata daya xan....." tsawa Abba ya daka masa yace "Enough Malam, tashi ka ban waje" Khaleel bae kuma cewa komai ba ya mike da kyar ya juya ya fice daga falon. Karfe sha daya da rabi Ummi ta shigo dakin Khaleel, yana kwance ya kafa ma Ac ido da ganinsa kasan abun duniya ya ishesa, ummi ta karaso ta xauna gefensa tana kallonsa ya mike xaune yace "ummina kin ga abinda Abba ke shirin min ko" Ummi tace "to ae kai ka ja ma kan ka Khaleel, tun yaushe muke bin ka kana kakkaucewa ka maida mu yara" komawa yyi ya kwanta bae kuma cewa komai ba, sarai tasan halin dan nata da abun da ke iya faruwa kafin gobe in ya kwana cikin tashin hankalin nn da yake ciki, hkn yasa tace "ka kwantar da hankalinka son, na shawo mana kan Abba amma fa da kyar, ya kuma baka wata dayan da kace don hka kafin lkcn ka gabato matar, kar ka kuma ban kunya kasan ni bana son abinda xae taba min kai son" mikewa Khaleel yyi ya rungume ummin tasa cike da jin ddi ya shiga mata godiya, ta shafa kansa tana murmushi ta sa masa albarka snn ta mike yyi mata sae da safe ta fita xuwa dakinta. Kasa bacci Khaleel yyi daren ranan duk da hankalinsa ya kwanta, amma damuwarsa daya ta inda xae fara nemo matar da xae gabato ma parent dinsa ynxu, ta ina xae fara wnn jan aikin, tunanin hkn na mugun tada masa hankali.
[10/14, 3:26 PM] ‪+234 806 484 7850‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
4.....
. A hanxarce Khaleel ya gama shirinsa cikin bakar suit da wando da farar T-Shirt sae neck tie ash colour, dakin Umminsa ya nufa ya sameta xaune gaban madubi tana gyara gashinta, yace "ummina xan tafi" Ummi na kallonsa tace "baka yi breakfast ba" ya kalli agogon hannunsa yace "idan naje office xan yi ummi, sae na fara xuwa cikin gari an duba min motata" Ummi tace "ba john ya kai shekaranjiya an gyara ba" ya girgixa mata kai yace "a'a it's still nt ok, xan je da kaina ynxu" Ummi tace "ikon Allah, to shi kadae ne motar ka Khaleel ka dauki wata mana in ya so ko anjima sae john ya maidata" yace "No xan tafi da ita ynxu Ummi na fi son in je da kai na" Ummi tace "to Allah ya tsare" ya nufi kofa xae fita yace "Ameen ummina sae na dawo" tace "to a dawo lfya" a stairs suka hadu da Rukayya tace "yaya baka yi breakfast ba" yace "eh sauri nake sae na je office" tace "to yaya ka ajiye ni ni ma sch xan tafi ynxu" yace "cikin gari na nufa ynxu" yana kai wa nn ya sauka ya nufi kofar fita daga falon, ta bi sa da kallo snn ta dan tabe baki ta nufi dakin ummi. Karfe takwas da kusan rabi Khaleel ya iso cikin gari, ya mika ma engineers din motarsa snn ya nemi kujerah ya xauna tare da fiddo wayarsa yana dannawa to while away time. Tafe take tana bincike jakar dake sakale a kafadarta alaman tana neman abu, cak ta tsaya ta wara ido hade da bude baki ta saki salati tana kallon cikin jakar, hkn ya ja hankalin Khaleel dake xaune har lkcn yana danna waya, juyawa tayi ta bi layin da ta fito daga da kallo, can ta dan tabe baki hade da tsaki ta xuge jakar ta kuma sakala sa a kafadarta da kyau snn ta ci gaba da tafiyarta da takunta mai jan hankali, sanye take da riga da skirt ta atamfa orange colour mae ratsin ash da brown, hijabin jikinta ma orange ne ya wuce gwiwa da kadan, hka ma takalmin kafarta orange ne, jakar hannunta kadae ne brown, da ganinta kasan makaranta xa ta, Khaleel ya bi ta da kallo har ta isa bakin titi snn yyi tsaki ya ci gaba da duba wayarsa, tsaye tayi bakin titin alamar tana jiran abun hawa, ba a Kuma dau lkci ba ta samu ta hau suka bar gurin, kmr ance Khaleel ya juya ya ga wasu fararen takardu a kasa dai dai inda ta tsaya, ya mike ya nufi gurin ya duka ya kwashe takardun har uku yana kallonsu, reciept ya gani da admission letter sae handout na physics, ya girgixa kai hade da tsaki da kmr xae wurgar da su sae kuma ya fasa ya linkesu ya koma ya xauna da xumar ya ba kanikawan idan sun ganta su bata, cikin minti sha biyar aka gama yi ma motarsa abinda ya kamata, ya basu kudi duk da basu bukaci hkn ba snn ya shige motarsa ya kama hanyar office cikin hanxari don ya makara. Tana xaune a class ta sa Chemistry text buk dinta a gaba kmr me karatu taji an rankwasheta, ta juya da sauri kuma a fusace don taga waye, ta wani hade rae tace "bana son irin wasan nn Aisha" Aisha ta xauna tace "Allah ya baki hkuri" sauran kawayen nata ma xaunawa suka yi suna kallonta, Ummi tace "wae me ya faru ne Ashnaah yau duk you re nt ur self" tayi masu wani irin kallo tace "dole ku ce am nt my self tunda ba reciept dinku bane ya fadi" Maryam tace "au wae shi yasa kika xama hka, ba mun ce maki xaki gani ba kila ma a gida kika xubar" tsaki Ashnaah tayi tace "eh naji xan gani a gida ku rabu dani" Bilkisu ta mike ta bar wajen Nafisa ta bi bayanta, Ashnaah ta bi su da harara, snn tace "bari in ta murna na xubar da reciept dina" tana kai wa nn ta mike ita ma ta fice daga class din, Ummi tace "da'alla mu rabu da ita mu muka xubar mata" mikewa su ma suka yi suka bar class din.
[10/14, 3:26 PM] ‪+234 806 484 7850‬: ~Dr Khaleel By Khaleesat Haiydar
5.....
Khaleel ne xaune office dinsa ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa lumshe, maganganun umminsa ne ke masa yawo a ka, tunanin ta Inda xae fara neman mata kawae yake, ko kadan shi kam matan kaduna ba su masa ba, basa burgesa, bude office dinsa da aka yi ya sa ya gyara xamansa da sauri ya bude ido ya ga wani isasshen ne xae shigo masa office ba knocking, ta rufe kofar bayan ta shigo, ya wani hade rae yana kallonta, da ma yasan baxae wuce ita ba, bae jira jin me xata ce ba a nutse yace "get out" ta dan marairaice masa tace "ka ga fa files na kawo maka Sir" ya kuma hade rae yace "ki bar min office nace" ajiye files din hannunta tayi nn da nn idonta ya kada, ta juya xata fita, murya can kasa yace "Ameesha" ta juya tana kallonsa sae ga hawaye, ya mike tsaye ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta, sae ta sakar masa kuka, dafa kafadarta yyi ya dago kanta yana goge mata hawayen idonta a hankali yace "am sorry" gyada masa kai tayi hawaye na ci gaba da xuba a fuskarta tace "Abbana yace in kawo maka files" tana fadin haka ta juya ta Fita daga office din tare da kullo masa kofarsa, komawa yyi ya xauna ya lumshe idonsa duk abun duniya sun ishesa. Bayan minti goma da fitan Ameesha aka kwankwasa masa kofa, ya tura file din gabansa bayan kmr minti daya yace "come in" wata nurse ta shigo rike da file a hannunta ta gaishesa cike da ladabi snn tace "Dr patient xaka duba, kuma Emergency ne, yace "don me xaki kawo min baki kai ma Dr Umar ba, ni din engine ne?" Tace "No sir suna Theatre ne, Oga ne yace in kawo maka" tsaki yyi ta ajiye masa file din ta Fita, ba a dau lkci ba nurse din ta dawo da patient din ya daga kai yana kallon yarinyar da baxa ta wuce sha takwas ba, bbu abinda take sae kuka tana rike da cikinta, ya dan yi tsaki Mara sauti ya jawo file dinta ya bude yana dubawa, nurse din ta juya ta Fita, yace "ke malama ba kuka xa ki min ba amsa min duk tambayoyina xa ki," shiru tayi tana goge hawayen fuskarta tana kallonsa, jin ynda tayi shiru lkci daya yasa ya daga kai yana kallonta, ta sunkuyar da kanta da sauri, cire farin glass din idonsa yyi ya sake fuska ya dan sassauta murya yace "daurewa xa ki yi Zeenat and tel me wat ur prblm, look at me" ta daga idonta da ya rine don kuka tana kallonsa, ya sakar mata murmushi snn ya shiga yi mata tambayoyi tana basa amsa. Karfe hudu da rabi Ashnaah ta shigo gida ta jefar da Jakarta nan bakin kofa ba tare da ta kalli inna dake tuka tuwo tsakar gidan ba ta Shige falo, inna ta tabe baki tace "aniyar ki ta bi ki yarinya, kuma ba ni kika wurga ma jaka ba, Adamu kika jefa ma" Ashnaah ta fito tace "kin fara ko inna ni dae fa ki dinga kyaleni, kina ganin na batar da takardun makaranta na gaba daya duk ban gani ba" inna ta mike da sauri ta dafe kirjinta tace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login