Showing 84001 words to 87000 words out of 121890 words

Chapter 29 - DR KHALEEL Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

19358

da ya gama hadawa ya dauko don yi mata, da kyar ya samu yyi mata don ta basa wahala ssae, ya rungumeta yana lallashinta ta gaji da kukan tayi shiru don kanta daga karshe bacci ya dauketa.




[10:54AM, 11/25/2016] AH💫: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
95.....
Mikewa Khaleel yyi bayan ya lullube ta ya koma can
gefen gado ya xauna ya dafe kansa yana tunanin
kiran da Dad dinsa yyi masa na gaggawa, juyawa
yyi yana kallon Ashnaah, can ya Mike yana kallon
agogo ya ga uku da rabi ya dauki car key dinsa ya
fice daga dakin don xuwa amsa kiran dad din nasa
don ya san baxata tashi ba a lkcn, ana kiran sllhn
La'asar ya isa gidan, sae da ya fara shiga masallaci
yyi sllhn snn ya shiga gida, Ummi na kitchen da
rukayya suna girki, ya shiga kitchen din ya gaida
umminsa, ta amsa masa ba tare da ta kallesa ba,
jikinsa yyi sanyi jin irin amsawar da Ummi tayi
masa, yana kallon rukayya yace "Abba fa?" Rukayya
tace "yana falonsa" a sanyaye Khaleel ya nufi falon
dad dinsa a Sama yyi sallama ya shiga, xaune ya
sami dad din nasa da amininsa sae kawunsa, ya
nemi kasa daga gefen kawunsa ya xauna ya gaishe
su kansa a kasa, Kawunsa kadae ne ya amsa, Dad
dinsa ya mike yana masa mugun kallo yace "me na
gaya maka kwanaki Khaleel" shiru Khaleel yyi bae
ce komae ba, ya daka masa tsawa yace "are yhu
daft?" Khaleel ya dago a hnkli yana kallonsa still
bae ce komae ba, Dad yyi murmushin takaici yace
"har ni xaka dinga ja ma ana biyo wa har gida ana
ci ma mutunci ko Khaleel," sunkuyar da kai Khaleel
yyi kawae, Kawunsa yace "wae yarinyar nn ita kadae
ce mace a duniya Ibrahim, yau ko da ace baka
saketa ba baxa ka iya rabuwa da ita ba ko dan
tijaran da mahaifanta ke ma ubanka?" Dad yace "to
bari ka ji khaleel wllh daga yau ka kara nuna kasan
yarinyar nn ba ni ba kai har abada, maxa maxa ka
sallameta ta koma inda ta fito idan ba hka ba ka ga
bacin raina, na haneka da kara interact da ita bbu
kai ba ita, na raba ka da yar matsiyatan nn daga
yau ta je can ta karata, kuma duk inda xa mu shiga
ka amsa cikin da ke jikinta na ka ne bn yafe maka
ba, tashi ka ban waje malam" Khaleel da tun fara
mgnr Dad dinsa xufa ke karyo masa ya dago kai da
kyar yana kallon dad din nasa da idanuwansa da
suka kada, Alhaji mukhtar ya daka masa tsawa yace
"uban me kke jira mister man, c'mon get lost"
hawaye ne suka shiga sakko masa da kyar yana
girgixa kai yace "Dad ni bn saketa ba wllh matata
ce har ynxu, kayi hkuri dad I can't deny her
pregnancy" bae rufe baki ba dad ya sauke masa
mari, tunda yake a iya saninsa Dad dinsa bae taba
marin sa ba sae ranan, Khaleel ya kasa dago kansa
cikin tsawa dad yace "har ni xaka bude baki kana
gaya ma wnn mgnr? to wllh Khaleel I mean my
wordz idan har baka rabu da yar marasu mutuncin
nn ba bbu ni bbu kai, shari'a fa ubanta yace xae yi
da mu," Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye
yace "kayi hkuri Dad idan nace xan guje ta ban san
halin da xata shiga ba, kuma ni ina son matata,
forgive me dad" kallonsa duk suka tsaya yi da
mmki, dad yyi murmushin takaici yace "hka kace
koh?" Khaleel bae ce komae ba har lkcn yana rike
da kansa, dad yace "gud, bani dukka makullan
gidajena dake hannunka da documents dina,"
Khaleel ya gyada kai da kyar yace "toh" snn ya mike
ya fice daga falon duk suka bi sa da kallo da
mugun mmki, gida Khaleel ya koma, har lkcin
Ashnaah bata tashi ba ya dauki duk kaddaran dad
dinsa dake hannunsa a dakinsa, snn ya fito ya samu
mai gadinsa ya basa cheque din dubu hamsin yace
ya ja jari ya sallamesa don xae rufe gidan ne sanin
gidan dad dinsa ne ba nasa ba, abubuwan da yasan
xae bukata ya kwashe a dakinsa ya kai cikin mota,
snn ya dawo dakin ya shiga tada Ashnaah a hnkli,
bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata
murmushi yace "srry na tashe ki koh?" Dagota yyi
ya dauki hijab dinta ya sa Mata snn suka fito ya
kulle gidan, ita dae bin sa kawae take don jiri ne ke
dibanta, mota ya bude mata ta shiga ya kulle snn ya
xaga ya shiga motar ya fice daga gidan ya fito ya
kulle gate din ta waje don har mai gadin ya wuce
snn ya koma motan ya shiga ya tada ya nufi
gidansu, bacci Ashnaah take daga xaunen da take
cikin motar ko da ya isa kofar gidansu, hkn ya basa
daman fita ya nufi cikin gidansu ya haura sama
xuwa falon dad dinsa, ynda ya barsu hka ya same
su, ya isa gaban dad dinsa ya duka da ladabi ya
ajiye masa makullan hannunsa da takardu snn a
sanyaye yace "kayi hkuri dad" yana fadin hka ya
mike ya fice daga falon, ya shiga dakin umminsa ya
sameta xaune tayi jigum, nn da nn ya ji hawaye na
neman xubo masa, ya isa gabanta ya durkusa a
hnkli yace "kiyi hkuri ummina," ta girgixa masa kai
tace "bbu komae Son, Allah ya Baka ikon rike
matarka da gskya" yace "Ameen ummina" mikewa
yyi yace "sae mun yi waya Ummi" snn ya juya ya
fice daga dakin, ya fita xuwa inda yyi parkin a waje,
har lkcn bacci Ashnaah take, ya shiga motar ya tada
ya nufi hotel da ita, don duk kudinsa bae taba
tunanin siyan gida dai dai da rana daya ba sanin
mahaifinsa na da gidaje fiye da shidda kuma duk
shi ke rike da su.




[10:54AM, 11/25/2016] AH💫: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 96..... A hnkli Khaleel ya
shiga tada Ashnaah a cikin mota bayan ya shiga hotel din yyi
masu bookn din daki ya fito, Ashnaah ta bude ido tana kallonsa,
da ganinta kasan bacci ne ssae a idonta, ya kamo hannunta yace
"Cum on wife mu je ki kwanta, I knw yhu need rest" da
taimakonsa ta fito daga motar ta shiga bin haraban hotel din
kawae da kallo, snn ta juya tana kallonsa, murmushi ya sakar
mata ya nufi entrance din shiga hotel din yana rike da hannunta
har lkcn, bin sa kawae take har suka shiga hotel din ya haura
sama da ita, room din da aka bashi suka nufa ya tura kofar dakin
suka shiga, hijab din jikinta ya cire mata ya shimfida kan neat
bedsheet din da ke kan gadon dakin snn yace ta kwanta tayi
baccinta, bbu musu ta kwanta shi kuma ya fita don shigo da
abubuwan da yasan xa su bukata, ko da ya dawo har ta koma
bacci, ya ajiye jakar hannunsa ya xauna gefen gadon a sanyaye ya
dafe kansa da yyi masa nauyi yana tunanin abun yi ynxu, yes
yana da 4.5 mlln a acc ynxu wat is he suppose to do, idan yace
xae siya gida there will b nothin left he knw, to da me xae kula da
ita da bbyn da ke cikinta idan ya siya gidan, yes sae ya nemi aiki
to meet up their needs nd demands idan ya siya gidan ynxu, kmr
wnda ya tuno abu ya girgixa kai a hnkli ya lumshe ido yace "No!
lookn 4 job is a kinda hell ynxu, dafe kansa ya kuma yi a
xuciyarsa yace "its better I rent an apartment, yes 5 to 6 hndrd
thousand I guess" shiru yyi yana tunanin shawaran da ya ba kansa
na karshe, ajiyar xuciya ya sauke ganin hkn kadae ne abun yi
ynxu, wayarsa dake gefensa ya shiga ring ya daga da sauri ya sa
cylnt don kar ya tada Ashnaah, ya ga Najeeb ne ke kiransa, da
kmr baxae daga ba don wani mugun haushinsa yake ji, sae kuma
ya daga yace "ya aka yi?" Daga daya bangaren Najeeb yace "kana
gida ne? Gani nn xuwa ynxu." Khaleel yace "bana gida ina Zaria,
Akwae matsala ne?" Najeeb yace "of course no dan bakar mgna,
kawae naga kwana biyu bamu hadu bne" Khaleel yace "ina Zaria
ynxu, sae na dawo." Najeeb yace "ok ka kirani idan ka dawo"
Khaleel yace "OK" snn ya katse kiran ya ajiye wayarsa tare da jan
tsaki, ko kadan baya bukatan taimakon kowa a ynxu dae. Mikewa
yyi ya fita don siyo mata abinda xata ci kafin ta tashi duk da
yasan ba abincin ma take ci ba, wani supermarket ya tafi ya siyo
kayan tea ya dawo snn ya siya abinci a eatry din dake cikin hotel
din ya haura sama, xaune ya sameta kasan dakin ta hade kai da
gwiwa, ya karaso ya durkusa gabanta a hnkli yace "me ya faru
wife" ta dago kai tana kallonsa da kyar tace "amae nake ji,"
dagota yyi yace "mu je kiyi toh" kmr xata yi kuka tace "ya ki
fitowa" xaunar da ita yyi gefen gado ya ce "idan kin ci abinci xae
fito, ga abinci nn na siyo maki ki ci kadan sae kiyi aman" haransa
tayi sae kuma ta saka kuka irin ta shagwaba, yyi shiru yana
kallonta lkci daya yyi murmushi ya rungumota a hnkli yana shafa
bayanta yace "to ya kike son in maki wife" lamo tayi a jikinsa bata
ce komae ba, ya dago kanta yana kallon cikin idonta yace "to xa
ki sha tea?" Ta make kafada alamar A'a, murmushi ya kuma yi
yace "to me xa ki ci?" Kmr xata yi kuka tace "ni amae nake ji"
mikewa yyi ya dauko ledan abincin da ya siyo ya dawo gabanta ta
mike da sauri ta bar wajen don ko ganin abincin bata son yi, can
karshen gadon ta koma ta xauna, ya ajiye abincin ya bi ta ya
xauna gefenta yace "toh xa ki sha kunu?" Juyawa tayi tana
kallonsa tayi shiru kmr me naxari snn ta gyada masa kai da sauri,
wayarsa ya dauka, ya shiga neman layin Zeenat, har ya mance
rabon da suyi waya, duk da da can ma ita ke kiransa ba shi ke
kiranta ba, bugu daya ta dauka, suka gaisa tace "ka mance da ni
ko doctor" Khaleel yace "A'a ban mance ki ba, ya mutanen
gidan?" Zeenat tace "duk suna lfya, ya su Fateema da khadija"
Khaleel yace "suna lfya, kina kd ne?" Tace "ehh ina nn" juyawa yyi
yana kallon Ashnaah da ta hade rae tana kallonsa, ya mike ya fice
daga dakin, sae bayan da ya fita yace "favour daya nake son kiyi
min Zeenat" tace "na me fa Dr" Khaleel yace "kunu xa ki dama
min plss idan bbu takura" da mmki Zeenat tace "kunu?" Yace
"yeah pls" tace "to shknn office xan kawo maka?" Khaleel yace
"No idan kin gama ki kirani kawae xan xo in amsa" tace "to shknn
xan yi ynxu" yace "am grateful, ki hada min da ruwan xafi a flask
plss" tace "OK bbu matsala" ya kuma yi mata gdya, snn ya katse
wayar ya dawo dakin, karasowa yyi kan gado ya xauna gefen
Ashnaah ganin ynda ta wani hade rae ta juya baya yace "me ya
faru wife?" Kmr jira take "ta fashe da kuka tace "ina ruwanka," ya
dan yi shiru snn yace "Allah ya ba ki hkuri wife" kmr ya kara
tunxurata ta kuma rushewa da kuka, yyi murmushi ya mike jin ana
kiraye kirayen sllhn magrib ya nufi bathroom, mikewa tayi da sauri
ta nufi inda ya ajiye wayarsa ta dauka ta shiga call log don ganin
da wnda ya gama waya, ajiye wayar tayi a sanyaye ganin Zeenat,
ta koma inda take ta xauna duk gaba daya sae ta nemi aman da
take ji ta rasa. Ko da ya fito kallo daya yyi mata ya fita daga dakin
don xuwa masallaci, kasa tafiya masallacin yyi ya dawo dakin ya
sameta ta sakko kasa ta hade kai da gwiwa tana kuka, ya karaso
kusa da ita yana murmushi ya durkusa gabanta ya dagota a hnkli
yace "I only belong to yhu wife, no one else but yhu" xaunawa yyi
a hnkli ya jawota jikinsa yana murmushi.





[10:54AM, 11/25/2016] AH💫: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
97.....
Khaleel ya dago kanta yana kallon manyan idanuwanta murya can kasa yace "let me go nd pray wife" sunkuyar da idonta tayi bata ce komai ba ya mike ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin snn ita ma ta mike tsaye da nufin shiga bathroom tayi alwala taji baxata iya ba ta koma gefen gado ta kwanta, da kyar ta iya mikewa daga karshe ta shiga bayin tayi alwala ta fito ta dauki darduman da ta gani a dakin, har Khaleel ya shigo dakin bata idar da sllhn da take ba don duk sae da ta rama sallolin da ake binta, tana idarwa tayi kwanciyarta kan darduman don jiri kawae take gani, Khaleel ya dawo inda take yana kallonta yace "sannu wife" dauke kanta tayi bata ce komae ba, wayarsa dake hannunsa yyi vibrate ya daga tare da sallama, daga daya bangaren Zeenat tace "Na gama ya Khaleel" Khaleel yace "OK to gani nn tahowa" ajiye wayar yyi yana kallon Ashnaah yace "bari in je in dawo ynxu wife" Ashnaah ta mike xaune da sauri ta hade rae tace "ni xan bi ka" yace "to mu tafi" kasa tashi tayi daga xaunen da take, shi dae kallonta kawae yake, can yyi murmushi ya dagota ya dauki hijab dinta ya sa mata snn ya kama hannunta suka fita daga dakin ya rufe kofar, sae da suka bar haraban hotel din Ashnaah tace "me yasa ka kawo ni Motel?" Khaleel yyi shiru kmr baxae bata amsa ba sae kuma a sanyaye yace "gobe xa mu tafi gida," kallonsa kawae Ashnaah ke yi bata dae ce komae ba, bakwae da rabi suka isa kofar gidansu Zeenat, Khaleel ya dauki waya ya kirata yace gashi ya xo, ba a dau lkci ba ta fito rike da babban leda me dauke da flasks biyu, Khaleel ya fita ya sameta suka gaisa kuma snn ta mika masa ya karba yyi mata gdya yace "xo ku gaisa da Fateema tare mu ke" Zeenat tace "OK" snn ta nufi motar, Khaleel ya bude mata, da fara'arta ta gaida Ashnaah, bbu yabo bbu fallasa Ashnaah ta amsa mata, Zeenat tayi masu sae da safe snn ta koma ciki, Khaleel ya tada motar yana kallon Ashnaah da mood dinta ya gama canxawa, reverse yyi suka bar anguwan, sae a snn yace "y dat face wife" Ashnaah ta dauke kanta kawae, wani bank taga yyi parkin yace "ina xuwa" bata tankasa ba ya fita ya nufi gun atm machine, ba a dau lkci ba ya dawo suka bar gun ya nufi wani boutique nn ma yyi parkin yana kallonta yace "ina xuwa wife" nn ma bata ce komae ba ya fita, ya kusa minti sha biyar a ciki snn ya fito, duk ta gaji gun kwanciya kawae take nema ga amae dake damunta ssae, back seat ya bude ya xuba ledojin hannunsa snn ya xaga ya shiga driver seat yana kallonta yace "ki yi hkuri wife kin gaji ko" tada motar yyi suka bar wajen. Yana gama parkin cikin hotel din ya fito ya bude mata motar ya kamo hannunta ta fito ya ji jikinta yyi xafi, da damuwa yace "ina ke maki ciwo ynxu" durkusawa yaga tana neman yi don bata jin xata iya tsayuwa, ya dagota xae dauketa ta girgixa kai da sauri tace "A'a ni bna so" kyaleta yyi yace "to mu shiga" ta shiga binsa a baya kanta na juya mata, dai dai stairs ta kasa ci gaba da tafiyar ta durkushe wajen, Khaleel ya dagota ya dauketa kawae ya karasa dakinsu da ita, kwantar da ita yyi kan gado, ta mike xaune murya can kasa tace "wanka xanyi" ya mike ya shiga bayin dakin, ko da ya fito kwance ya sameta, da taimakon sa ta cire rigar jikinta ta bar ves da skirt din jikinta, snn ta mike ya dauki towel dinsa ya mika mata ta shiga bathroom din da sauri, ruwan dumi ta samu ya tanadar mata da sabulunsa me ddin kamshi ga shower gel, a daddafe ta gama wankan ta daura towel amma ta kasa fitowa, hka kawae taji tana kunyansa ga shi bata shigo da hijab ba, ta fi minti biyar jingine jikin bango daga karshe ta ji tana neman faduwa ta fito rike da kayan da ta cire, bata samesa cikin dakin ba, ta ji ddi ssae ta isa inda hijab dinta yake da sauri ta dauka ta sa, kayan bacci ta gani a ajiye gefen gadon da turarurruka, ta tsaya kallon kayan snn ta karasa ta daga red silky gown din ta ga har da undies, kallon gown din kawae take, iyakar sa tasan baxae wuce cinya ba, gashi yyi mugun haduwa, ta tabe baki ta dauki under wear din ta koma bayi ta sa snn ta fito, tayi niyyar sllhn isha amma ta ji baxata iya ba hkn yasa tayi kwanciyarta har lkcn tana daure da tawul sae hijab a jikinta, ko minti biyar ba ta yi da kwanciya ba Khaleel ya shigo, ya ajiye abubuwan hannunsa ya karaso yana kallonta yace "tashi in xuba maki kunun ki sha" bae jira me xata ce ba ya fiddo wani sabon cup snn ya bude flask din kunun ya xuba mata da taimakon sa ta sauko daga kan gadon ya mika mata kunun, ba musu ta karba tana kallon kunun, a hnkli ta kai cup din bakinta ta shiga sha don bbu xafi ssai, har sae da ta kusa rabi snn ta ajiye cup din tana goge bakinta, yace "kin koshi?" Kai ta gyada masa yace "aa dan kara kadan wife" girgixa Kai tayi ta shiga kkrin mikewa ya rikota yace "kadan fa xa ki kara" kuka ta sakar masa irin ta shagwaba, ya rungumota da sauri yace "A'a yi hkuri wife" kwantar da ita yyi ya dauki sauran ya shanye snn ya fiddo magungunanta ya dawo gefenta ya xauna yana kallonta xae yi mgna wayarsa da ke aljihunsa ya shiga vibrate, ya ciro yana kallon screen din ya ga umminsa ce ke kiransa, ya daga kiran, yyi mata sallama suka gaisa, Ummi tace "ya jikin fateemar?" Yace "da sauki Ummi" tace "ba ta mu gaisa idan tana kusa" kallon Ashnaah yyi ya mika mata wayar yace "ga shi ku gaisa da Ummi," ta mike xaune ta jingina jikin gadon ta karbi wayar tare da yin sallama, Ummi tace "ya jikin fateema? Kina cin abinci dae koh?" Ashnaah ta gyada mata kai tace "ina ci Ummi" Ummi tace "to Allah ya sauwake, ba shi wayan" Ashnaah tayi mata gdya snn ta mika masa wayar, Ummi tace "kuna ina ne ynxu Khaleel" Khaleel ya dan yi shiru snn a hnkli yace "muna gidan wani frnd dina ne Ummi" Ummi tace "kana ji na koh?" Yace "ina ji Ummi" tace "gobe dad

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login