Showing 96001 words to 99000 words out of 121890 words

Chapter 33 - DR KHALEEL Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

19352

ita, ina ta san ni ko kuma na Santa, kawae ta xo wajen ka ta wani ce ta xo gaishe ni" fashewa da kuka tayi, Khaleel ya danne dariyarsa yace "Haba bby meye abun kuka a nn, ba sae in bar gidan ba idan ta gama gaishe ki ta yi wucewarta" Ashnaah ta galla masa harara ya mike yana dariya ya fita, bin sa tayi da kallo lkci daya ta ji haushin kanta, share hawayen fuskarta ta shiga yi a hnkli, y will she show she cares dat much abou him, he is d cause of everythin she is goin through, me yasa son sa ya shigeta lkci daya bayan duk wahalan da ta sha a hannunsa, girgixa kai tayi ta tura wainan gabanta cike da jin haushin kanta, dae dae nn Zeenat ta shigo dakin da sallama rike da flask a hannunta da ledan fruit, Ashnaah ta sunkuyar da kai da sauri, Zeenat ta karaso gabanta tana murmushi tace "sannu Fateema, ya jikin" Ashnaah ta kasa yi mata abinda tayi niya, ta dago kanta ta dan kirkiri murmushi tace "da sauki, Alhmdllh," Zeenat ta ce "toh Allah ya kara lfya, ga kunu na yo maki" Ashnaah tace "to ngdd Allah ya saka da alkhairi" Mintin Zeenat goma a dakin ta mike tace "xa ta koma" Ashnaah ta kuma yi mata gdya snn tace bari ta rakata falo, duk ynda Zeenat ta so tayi xamanta ta bar rakiyan kn yadda Ashnaah ta yi suka sauko har falo, Zeenat na kallon Rukayya dake kallo a falon tace "doctor fa Rukayya?" Rukayya tace "ya fita wllh" Ashnaah na jin hka ta juya ta nufi sama, Zeenat tace "to idan ya dawo ki ce masa na tafi" Rukayya tace to, snn suka yi sallama ta fita, sae a snn hnklin Ashnaah ya kwanta ta koma sama, Karfe biyu saura Rukayya tayi ma yayanta da Ashnaah sallama ta wuce gida. Da yamma Karfe hudu da rabi Khaleel ya sa Ashnaah ta shirya suka tafi can gidansu tun da Abbansa na Abuja. Suna gidan har kusan Karfe shidda sae ga Abba ya dawo daga Abuja, ba karamin tashi hnklin khaleel yyi ba don bae taba xaton dawowan dad din nasa a lkcn ba, toh da wani idon ma xae kalli mahaifin nasa, da ma bae shigo da motarsa cikin gidan bne, ita kanta Ummi bata so dawowan mai gidan nata ba a lkcn sanin ita kanta sae ranta ya baci, ae kam hka ya faru don ko da ta je yi masa sannu da xuwa shareta yyi, ta bar masa dakinsa kawae, tana dawowa bedroom dinta Khaleel da ke xaune ya rike kansa ya mike da sauri yace "Ummi xa mu tafi" Ummi ya galla masa harara tace "tana baccin xa ku tafi" ya juya yana kallon Ashnaah da ke bacci tun shigowar su gidan, a hnkli yace "tashin ta xan yi Ummi" Ummi tace "bbu inda xa ku sae ta tashi" kasa mata musu yyi ya koma ya xauna, ita kuma ta ci gaba da abinda take, a hnkli yace "xan iya xuwa gaida dad Ummi" girgixa masa kai tayi ba tare da ta kallesa ba tace "A'a kar ka je" bae kuma ce mata komae ba har aka kira sllhn Magrib snn ya mike ya shiga bathroom dinta yyi alwala ya ce ya tafi masallaci, Khaleel bae nufi masallacin da yasan xae hadu da dad dinsa ba, kuma ana idar da sllh ya dawo gida don ma kar su hadu bakin gate. Da kyar ya iya cin shinkafar da Ummi tayi masa ranan bayan ya dawo daga sllhn isha, Karfe takwas da kusan rabi Ashnaah ta tashi, Ummi ta kawo mata kunun da tayi mata, ta mike ta nufi bayi ta kuskure bakinta snn ta dawo ta dauki kunun tana sha, Karfe tara Khaleel ya shiga dakin rukayya yace ta duba masa falo ko dad na nn don xa su koma gida ne, ta dawo tace baya falo, komawa dakin umminsa yyi yace da ita xa su wuce gida, Ashnaah ta Mike ta dauki hijab din da Rukayya ta bata ta sa snn suka yi ma Ummi sae da safe, Ummi tayi masu Allah ya kiyaye suka fita daga dakin tana gaba yana biye da ita a baya, ido hudu Khaleel yyi da dad dinsa da sakkowansa falon knn yana cin fruit a kan centre table, Khaleel ya dauke kansa da sauri ya kasa ci gaba da tafiyar ya tsaya stairs din karshe, Ashnaah ta juya tana kallonsa, ita ma jikinta yyi sanyi, ta karasa falon a sanyaye ta isa inda dad din yake ta durkusa kasa ta gaishesa kanta a sunkuye, dago kai yyi yana kallonta, ya ajiye fork din hannunsa yana dan murmushi yace "lfya lau, kun xo lfya?" Ta dago Kai tace "lfya lau Abba," dad yace "to madallah, ashe kuna ciki nayi xaton kun tafi ne" ta girgixa kai tace "ba mu tafi ba" Dad yace "to yyi kyau, ya jikin naki?" Tace "da sauki Abba" yace "to Allah ya sauwake, ko xa ki ci kankanan ne in dibar maki" tayi murmushi tace "Aa nagode Abba" dad yace "A'a bari a debar maki dae" murmushi ta kuma yi bata ce komae ba don sae taji kankanan ya bata sha'awa, dad ya dauki wani plate ya shiga deban mata kankanan snn ya sa mata toothpick ya mika mata, a kunyace ta karba tare da yi masa gdya, yace "tashi ki koma kujera toh" kin tashi tayi ta shiga cin fruit din nn inda take, sae ta ji ina ma Abbanta ne hka, tunanin hka ya sa kwalla ya taru a idonta.






[10:55AM, 11/25/2016] AH💫: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 106..... Juyawa Khaleel yyi ya bar sa wajen a tsaye ya koma kan kujera ya xauna, Najeeb ya runtse ido ya bude yana girgixa kai lkci daya ya share gumin da ke karyo masa ya dawo gefen Khaleel yana kallonsa boldly yace "wat if I claim being the one dat wrote dat divorce content?" Khaleel ya dago ido yana kallonsa, can yyi tsaki ya girgixa kai hade da tabe baki yace "go ahead mana, if yhu think dat will make yhu get her, u will only end up ruining matters, dat is addin salt to injury" Khaleel yyi murmushin da bae yi niyya ba yana kallon abokin nasa, lallai ya yrda Najeeb ya rikice kan Ashfah, Najeeb ya fuxa iska yace "it sound meaningless nd annoying ryt?" Mikewa Khaleel yyi yace "ka ga ka tafi gida ka bar min hauka a nn don Allah, in ka dawo nml koh xuwa anjima da daddare sae ka dawo let get a soln" Khaleel na kai wa nn ya dauki wayarsa ya nufi sama, Najeeb ya bi sa da kallo jikinsa yyi sanyi ssae, ya dafe kansa, yes! yasan no matter wat Khaleel baxae taba yrda shi ya rubuta takardan da ya tarwatse farin cikinsa ba ko jikinsa xae xama kunnuwa ne gaba daya, but hw is he goin to proof dat to him. Karfe takwas da rabi na dare Najeeb ya dawo gidan, Khaleel na kwance falo kan doguwar kujera yana kallon kwallo, yana ganinsa ya mike xaune, Najeeb ya karaso ya xauna yana kallonsa, Khaleel yace "kae da nace ana magrib ka xo malam, to gashi har sun yi bacci har fa nayi mata mgna daxu ta amince xata saurareka" Najeeb kwalalo ido yace "don Allah Khaleel, wllh daga clinic nake shi yasa bn xo da wuri ba, plss ka tashe ta mana" Khaleel yace "A'a ka dae xo gobe da safe xae fi" Najeeb yyi shiru bae ce komae ba, ba don ransa ya so ba ya mike yyi masa sallama ya fice, Khaleel ya bi sa da kallo har ya fita snn yyi dariya. Mikewa Khaleel yyi ya nufi sama yyi sallama ya shiga dakin da su Ashnaah su ke, Ashfah ce xaune kan darduma tana shafa'i da wutr, Ashnaah kuma tana bayi tana wanka, Khaleel ya rasa gane Ashnaah ce xaune kan darduman ko ba ita ba don hijab din Ashnaahr ce, ya dae yi assure din kansa ita ce, tsaye yyi bakin kofa yana jiran ta idar, dae dae nn Ashnaah ta fito daga wanka daure da towel, kallo daya yyi mata ya juya da sauri tare da cewa "oh srry sister" ya fice daga dakin, Ashnaah ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Ashfah na idar da sllh tace "wae ba kin fi ni tsayi ba da haske" Ashnaah dake dariya har lkcn tace "gane min hanya, ko da yake mu ryt frm tym ba a iya banbance mu" Hijab Ashnaah ta sa tace ma yar uwarta tana xuwa snn ta fita, falo ta samesa xaune, ta kuma fashewa da dariya, ya mike yana kallonta da mmki, ta karaso tace "daga ynxu idan kana son sanin wacece fateema tsayin mu kawae xaka kalla," Khaleel ya sauke ajiyar xuciya ya jawota jikinsa yace "OK wife" xaunawa yyi kan kujera ya xaunar da ita kan kafarsa ta shiga kkrin mikewa da sauri ya rungumeta yace "kin ga kin dan fara samun sauki ynxu ko wife, bbyn nn nawa na son ki dayawa baya son wahalar da ke, just a month nd two wk fa yhu re gettin beta," Ashnaah ta galla masa harara tace "ko ba better ba, don kawae ina daurewa koh," kmr xata masa kuka ta karashe mgnr, Khaleel ya shiga kkrin cire hijab din jikinta a hnkli yace "to yi hkuri bbyna yhu re nt gettin beta" ta xaro ido ta rike da sauri tace "tawul kadae ne fa jikina" sake mata hijab din yyi ya shiga dagawa daga kasa a hnkli yana kallon santala santalan kafafuwanta, ya lumshe ido ya daura lips dinsa kan wuyanta murya can kasa kmr me rada yace "wife ki dan tausaya min yau mana, I i need yhu badly" Ashnaah ta hade rae ta fara kkrin tashi daga kafarsa ya rikota da sauri a hnkli yace "to kiyi hkuri wife, I won't again na bari" Karfe sha daya Ashfah ta ishe Ashnaah ta fi gun mijinta ta bar ta ta fara jin bacci, da kyar Ashnaah ta fita daga dakin ba dan ta so ba da sunan xata dawo idan tayi masa sae da safe. Dakin da tasan xata samesa ta shiga, kwance ta samesa yyi rub da ciki kan gado idonsa lumshe kmr me bacci





~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
107.....
Ashnaah ta karaso gefensa ta xauna tana kallonsa tace "re yhu sleepn" a hnkli ya bude manyan idonsa da suka sauya kala yana kallonta, ta mike tace "came to say gudnt" shiru yyi bae ce komae ba har lkcn idonsa na kanta, hade rae tayi ganin hka ta juya xata bar dakin ya mike xaune ya rikota da sauri ya dawo da ita ya xaunar gefensa, cikin wata kasalalliyar murya yace "am srry wife, me kika ce?" Kmr xata yi kuka tace "ba ka ma ji abinda nace ba koh" lumshe ido yyi ya rungumota a hnkli yace "wllh bn ji ba bby" shiru tayi bata ce komae ba kanta na kirjinsa, sun kusa minti goma a hka can dae ta dago tana kallon agogo ta ga sha daya ya kusa, ta shiga kkrin mikewa tace "xan tafi in kwanta sae da safe" kin saketa yyi, tace "don Allah ka kyaleni in je in kwanta" da kyar ya iya bude baki yace "baki tausayina ko wife?" Ta xaro ido xata yi mgna ya saka bakinsa cikin nata, ssae ta tsorata kmr ranan ya fara kiss dinta, ta fara neman kwace kanta amma ta kasa, hkn yasa ta sakar masa kuka jikinta na bari tana cewa ya bata so, Khaleel bae sarara mata ba duk da ynda ya ga ta rude daren nn har sae da ya kai ga cimma burinsa, bbu abinda take sae aikin kuka tana neman tashi ta bar masa dakin amma ya ki saketa, wani mugun haushinsa kawae take ji a lkcn duk da ta dan sha wahala amma ba kmr na farko ba, bbu irin lallashin da bae mata ba amma kamar 'da da tunxurata yake, ta gaji da kukan wajen Karfe daya bacci ya dauketa, can wajen Karfe uku ta farka ta Mike xaune da kyar ta dalilin xaxxabi da ke jikinta ga wani tashin xuciya da ta ke ji, kkrin sauka daga kan gadon ta shiga yi ya rikota da sauri ta fixge hannunta da karfi ta sauka, gabanta ya shiga faduwa tana tsoron kadda ta kasa tafiya yau ma, amma sae ta ji bata ji xafi ba, ta fice daga dakin da sauri, kasa shiga dakinta tayi ta nufi downstairs don ta ga akwae bayi, nn tayi wankan ta ta fito ta sa hijab xata koma dakinta, xaune ta gansa a falon, ta kauda kai da sauri ta nufi sama ya mike ya bi ta, kuka ta saki ta ki ci gaba da tafiyan, tsayawa yyi inda yake, cikin kuka tace "ni wllh ka kyaleni bana so" shiru yyi yana kallonta, a hnkli yace "kiyi hkuri wife, am srry" juyawa tayi ta haura sama da sauri, tana shiga dakin ta kwanta gefen yar uwarta nn da nn bacci ya dauketa.
Washegari da safe Ashfah ta gama shirin tafiya wae tana da lecture, don takaici Ashnaah da ke kwance ga xaxxabin da ya sa ta gaba ga ciwon mara bata ko kalleta ba bare ta tanka mata, Ashfah ta karaso gefen gadon tace "kin ji sister, xan tafi" ba tare da Ashnaah ta kalleta ba tace "Allah ya tsare" Ashfah ta mike tace "Ameen, Allah ya kara lfya sae mun yi waya" Ashnaah bata tanka ta ba har ta fice, Ashfah tayi murmushi kawae ta sauka downstairs abun ta, falo ta samu Khaleel, ta karaso cikin falon tace "sae anjima ni xan tafi" Khaleel ya daga kai yana kallonta yace "da safe hka sister, baki yi breakfast ba ae" Ashfah tace "bana breakfast da safe sae eleven, ina da lecture ne" Khaleel ya mike yace "OK, bari in dauko makulli in ajiye ki" tace "A'a wlh ka bar shi xan samu napep idan na fita" bae saurareta ba ya nufi sama ya dauko makullin motarsa ya shiga bedroom da Ashnaah take, xaune ya sameta tsakiyar gado ta hade kai da gwiwa tana kuka, ya karaso kusa da ita yana kallonta bata jira me xae ce ba ta mike ta shige bayi ta kulle kofar, ya dan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin, a hanya yake ce ma Ashfah ta bar Ashnaah tana ta kuka, Ashfah tayi murmushi tace "wae baxan tafi ba ga shi yau Abbanmu xae dawo, kuma bae san na tafi ko ina ba" Khaleel yace "gskya ne" har kofar gidansu ya ajiye ta ya bata dubu biyar tare da cewa ta gaida masa momy ta karba da kyar snn ta shiga gida yyi reverse ya bar anguwar, a tare suka yi parkin da Najeeb a kofar gida, Khaleel ya rike kai yana dariya har Najeeb ya fito daga motarsa snn shi ma ya fito, Najeeb yace "Allah ya sa sun tashi" Khaleel ya fashe da dariya yace "ynzun nn na mayar da ita gida, ko karyawa ta ki yi wae tana da lecture, lkci daya mood din Najeeb ya canxa yace "ya xa ka min hka Khaleel?" Khaleel yace "its nt my fault frnd" juyawa Najeeb yyi ya shige motarsa ya fixgeta a guje ya bar anguwar Khaleel ya bi sa da kallo yana murmushi. Washegari Asabar ba tare da Najeeb ya Bari Khaleel ya sa ni ba ya lallaba abokanan dad dinsa shi ma ya bisu xuwa can gidansu Ashnaah don ganin Abbanta, Abba na gida a lkcn, as usual da fara'arsa ya tare su snn suka gabatar masa da abinda ya kawo su kan cewa sun xo neman auren Ashfah, Abba ya dan yi shiru snn yana kallon Najeeb yace "ita ta ce ka turo koh?" Najeeb ya girgixa kai da sauri yacec"A'a Dad, hasalima ni bata taba kulani ba wllh shi yasa na ce bari in xo neman ixini a gida" Abokanan dad din nasa suka tsaya kallonsa da mmki don ba hka ya fadi masu ba, Ca yyi yarinyar tace ya turo manyansa in ji babanta, Abba ya dan yi murmushi yace "gskya ne" maida dubansa yyi ga bakin nasa yace "to xancen gskya 'ya ta karatu take ynxu, kuma sae ta gama xan bada aurenta kuyi hkuri dob Allah, kae in kaga kana sonta xaka iya jiran ta gama, saura mata shekara uku idan Allah ya yrda" mikewa abokan dad din Najeeb suka yi kowa ransa a bace, bbu wani kwakkwaran sallama suka fice daga falon, Najeeb kam kasa tashi yyi, ya marairaice ma Abban yace "wllh dad xan bari tayi karatunta baxan hanata ba" Abba yace "to ni bnyi niyar aurar da ita ynxu ba sae nn da shekara uku," mikewa Najeeb yyi jiki ba kwari yyi masa sallama ya fita daga falon.





108......
Dayz went by followed by month, wasa wasa yau cikin Ashnaah ya cika wata shidda da sati biyu cif ynxu kam bbu wani laulayi sae nauyin da tayi, tayi garau abunta cikinta ya fito ssae but bata da kwanciyar hnkli kullum cikin tunani da xubda hawaye take, hkn yasa bata kumari, bbu abinda ke sa Khaleel farin ciki sae idan ya tuna cikin yan biyunsa Ashnaah ke dauke da, sae dae har lkcn bbu wani improvement daga parent dinsu maxa gaba daya barin ma Ashnaah, duk da dad din Khaleel baya nuna mata komae yana mata kmr ynda xae yi ma Rukayya kuma yana tausayinta, Khaleel kam baya samun fuskarsa, amma duk da hka bae hanasa shigowa gidansa ba, har lkcn gidan Al-ameen suke xaune, lkci lkci Al-ameen din ya kan kawo masu xiyara da Maryam, ko mgnr neman aiki Khaleel baya yi duk da ynda frnds dinsa na arxiki suka damu ko wannensu na kkrin ganin yyi masa hanyar samun aiki amma Khaleel bae damu ba don har lkcn kwalinsa na gun dad dinsa, lkci lkci Najeeb kan kawo masu ziyara kuma yana taimakon abokin nasa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login