Showing 66001 words to 69000 words out of 141906 words

Chapter 23 - Ta Fita Zakka Part 2

10 Oct 2024

4164

nesanta dashi ya Zanyi..? Abun na Damuna Zuciyata zafi take min kamar Zan mutu. !
Ta karishe fada Cikin kuka Danmallam Zufa kawai yake yi kansa na juyawa Mamaki da Dimuwa da al"ajabi sun kamasa ya kame awaje daya salati kawai yake maimaitawa acikin Ransa kafin ya samu yar natsuwa Cikin Wani irin Sauti yace"AMINA..!Kin tabbatar da mganar da kika Fadamin..?
Amina ta kara fashewa da kuka Tana Fadin"Wlh in nayi maka karya Allah ya..!
Da Sauri ya Katseta da Fadin"Amina ba kyau irin wannan rantsuwan ba kyau..!
Sai yaji yama kasa mgana Saboda mamakin abunda yaji,Amina kuka ta Cigaba da yi kamar ranta zai Fita yana jinta ya kasa mgana sai chan yace"Kin Sanar da Hajiya ne..?
Saboda yana tunanin kodai Hajiya ta sani ne Data Dauki wannan matakin sai Amina tace bata Fadama kowa ba...kansa ya Daure Tunaninsa ba Lokaci Daya bane yana Bukatar natsuwa Cikin lallashi yace"Ki daina kuka..Sannan ki cire damuwa aranki..Zan yi Bincike a barayina in dai mganar ki gaskiya ne akwai yuyuwar kowa yaji labarin nan,Alkawari Zaki min zaki Daina Tunani da Damuwa bakin gayamin ba .?
Da yardan Allah komai zai zama Daidai kada ki damu..!
Amina ta koma sheshshekan kuka tana Fadin"Haka mamanmu ZAta kashe mana uwa a banza kenan ya Danmallam..?
Kai ya girgiza kafin yace"Ai hakkin Rai ma bazai barta ba Amina..In ma da Gaske ne Allah bazai barta ba sai ya Wulakantata aduniya..Sannan ai Allah ya nuna musu basu isa ba..Suna nasu ne Allah shi kuma yayi nashi..Amina Kina da juna Biyu wannan kadai ya isa kisan Allah ne Kadai mai yi alokacin da yaso a kuma Sanda yaso..!
Amina taji jikinta yayi sanyi ammh bata bar kuka ba shi kuma ya tattaro Jarumtarsa yana ta bata baki da lallashinta Shima kenan datake da shekaru ya shiga wannan Halin balle ita mai karancin shekaru kamar Amina..?
Dakyar ya samu Amina ta bar kuka shi Tunaninsa ma kada Damuwar ta Haifar da Matsala ga abunda ke Cikinta sai da ya tabbatar da ya lallasheta tare da alkawarin komai zai zama Daidai ya karishe da Fadin"Zan zo Gida watan gobe..In nazo sai mu Sake zama muyi mganar musan yadda zamu bullo ma lamarin ni dai ki daina Damuwa Sannan kada ki Fadamawa kowa..!
Amina ta gyada kai kafin tace"Zaka zo nan ne..?
Wajena..?
Yace"Eh zan zo na ganki naga yadda Kika koma in kuma ga yadda Cikina ya zauna ajikinki !
Sai kunya ta kama Amina ta kasa mgana shi ma bai wani Damu ba,baya Cikin natsuwarsa Daganan ya mata sallama ya katse kiran.
Zagayen office dinsa ya farayi kansa ya Dafe ya shiga Tunanin mganganun Amina bai san mamanmu a boye ba sai dan Zahirinta Daya sani kadan ana Fadin Kirkinta,ko abakin yaya yasha jin haka Sannan shi bai da wani Sakewa da ita iyakarsa su gaisa sannan ita kanta Anty Amarya gaisuwa ce Tsakaninsu har gwara itama sukan yi Doguwar mgana Sanadin Sakina Sai dai kuma ya fara jiyo kamshin gaskiya kan mganar Amina Duba da Yaya ance Lafiyalau ta kwanta sai gawa duk da ita Mutuwa ko da Ciwo ko ba Ciwo sai an tafi..!
Ammh Amina yarinya ce ba yadda Zata Zauna ta Tsara mgana haka in ba ji tayi ba Sannan ya tuna yadda Sakina tada hankalinta kan Auran sa da Amina da kuma Matsalan data Faru tsakaninsa da Sarood Aliyu ya fara Hangomai Lamarin a matsayin Shihiri ammh bai yarda ba sai da Mallam ya sanar dashi Cikin Hikima har ga Allah bai zargi Sakina ba ammh kuma yanzu Dayaji wannan mganar sai ya shiga kokonta ya tuna Bakin kishi Sakina da Burinta ita ta Samu Ciki ta Haihu har wani Lokacin ya Dinga mata Fadan ta roki mafi alheri..
Bawai ya yarda da mganar Amina Duka bane sai dai kuma ya shiga Rudi da kokwanto agidansu ake wannan Tsantsan jahilcin da mugunta har da kashe rai..!
Indai ko gaskiya ne Anty Amarya da mamanmu Allah bazai barsu ba sannan sai ya nuna musu basu isa su raba auran da Allah ya kulla da kansa ba.
Cikin tashin Hankali ya kira jafar a waya yana Tambayansa Amina na karya?.. tunda sun fisa sanin yarintar ta shi ba mazauni banw baisan komai kan Rayuwarsu ba.
Ya jafar ya fara fada yana Fadin"Hala iskancinta ta maka..? Ai Amina sai Allah..Wlh ya Danmallan ka daina Sake mata ne. !
Cikin haushinsa yace"Tambayata zaka bani amsa ko zaka Tsaya kana gayamin abunda zan yi da matata ne..?
Saj jafar ya rike baki yana yar Dariya kafin yace"Amina bata da Halin karya..Bata da kumbiya kumbiya ita Free take abunta bata da Tsoro sannan tana da kafiya da Taurin kai yadda kasan zuciyan kafuran farko bantaba ganin wanda duka baya Sata tayi Laushi ba sai Amina..Ko zaka kasheta sai tayi mgana sannan abunda yake gaskiya take fada
Bansanta da karya ba gaskiya..Sai dai Rashin kunya da tsiwa da Tonen fada da Yawon tsiya..!
Danmallam ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya Datse kiransa ya jafar afili yace"Ko son Amina ya Danmallam ya fara ne..?
Dariya yayi kafin yace"Tab..bai Fada hannu na gari ba..Amina ai jidali ce..!
Danmallam kuwa suna gama mgana ya saki Huci Amina tana da gaskiya wani abu na Faruwa sannan ya Fara ZArgin Hajiya tasan wani abu shiyasa ta hana Amina ta zauna a gumel sannan kuma ta hana kowa yasan da Cikin jikinta tabbas ya hasaso wani abu..
Sai dai koma menene ya kamata yaje Negaria yaga Amina su yi mgana sosai sannan yaga ta ina zai Bullo ma al"amarin da ke faruwa agidansu karkashin Tarbiyan mallam..?
Lalle ana Zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka..Zuciyarsa ne taji ta Bude da duka mganar Amina da Tsausayinta da bai taba jiba ba..Dole ya tafi gida cikin watanan mai Shiga abubuwa Dadama suna Bukatar yaje ya gabatar dasu tukunnah..!








*Janafty*
[10/19, 6:19 PM] +234 810 431 4972: *TFZB2016*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*


Hajiya Shashenta ta koma cikin wani yanayi,yanayin da take ciki tun Lokacin dataji wayar uwani da kanwarta,wani irin dakiya da kwarin gwiwa tare da yakinin babu wani mai yi sai Allah ne suka shigeta.
Ta samu sukuni da sukayi mgana ta Fahimta da mallam yanzu zata jira har ya Kira shi Usman din mijin Aishar duk da tasan ba matsala Aisha kuma sai sun isa goben zata mata bayani haka kurum taji Hankalinta ya kwanta da Aishar saboda tana da bambamcin Hallayar da sauran sannan Halinta kamar Halin Danmallam ne, bata da Hayaniya ballatana yawan surutu.
Ta yi ta leka Amina tagani ko tatashi bata tashi ba sai wajen sha biyun rana Data Sake lekata ta ga ta tashi Hajiya da kanta ta shiga Tiolet ta Hada mata Ruwan wanka ta taimaka mata ta shiga tayi wanka bayan ta fito ita ta Dauko mata wata Doguwar riga ta saka Duk ta rame ta wuya idanuwanta sun kumbura kadan Saboda kuka.
Tea Hajiya ta sake hado mata da sauran Doyar da suka karya dashi da Safe,Kadan Amina taci Doyar Tea din ta Shanye duka domin cikin jikinta na son shan Tea musamman ma Dayake akwai madara aciki.
Sai da Hajiya ta barta ta natsu sannan ta Dawo domin tayi mgana da ita Amina na Zaune Saman Cafet ta jingina da gadon Hanne tana maida numfashi Lokacin da Hajiya ta Sake shigowa Amina kuka take yi domin bata Zaman mintina goma bata tuna da Yaya ba da irin yadda mamanmu ta Dai'dai'ta Rayuwarsu.
Tana ganin Hajiya sai tayi Dubara ta share Hawayenta,Bata sani ba Hajiyar ta gani ammh sai tayi Tunanin Sabida yanayin datake Ciki Domin abubuwa sun faru ne duka Tsammanin abunda basu yi Tsammani ba dukkansu.
Gabanta Hajiya ta Zauna ta Tankwashe kafa Amina tana kokarin gyara Zamanta Hajiya ta Dakatar da ita da fadin"A"a mamah yi zamanki..!
Kanta ta maida kasa domin kunyar Hajiya take ji.
Hajiya ta kalli Amina Lokaci Daya ta Kira sunanta ta amsa jin muryan Hajiya Daga gani mganace a bakinta.

Hajiya ta cigaba da fadin"Amina ina so kiyi hakuri ki kuma Dauki Rayuwa yadda tazo miki. domin bawa bai isa ya Zabama kansa wata Rayuwa ba illah wacce Allah ya Zaba masa..!
Amina dai batace komai ba Hajiya ta kara Gyara Zamanta tacigaba da Fadin"Ina so na fada miki..Gobe zamu Tafi Abuja gidan Aisha chan zaki Zauna kiyi Renon Cikin ki Zuwa wani Lokacin..!
Amina ta Dago da mamaki tana kallon Hajiya kafin tace"Hajiya gidan yaya Aisha..?
Hajiya ta gyada kai kafin tace"Nan Amina nasan zaki yi ta mamakin meyasa haka..?
Ina da Dalilina Amina akan hakan Dayasa bazaki zauna anan ba..Sannan bana so kowa yasan da mganar Cikin ki Mamah ko Hanne da Hamida ne kada ki Fadama kowa sannan shima Batun Tafiyarki ban ce ki sanar dasu ba..In na Dawo goben Daga kai ki Zan musu bayani bana son koken koken nan naku..!
Kiyi hakuri Jarabawarki bazaki yi ta yanzu ba sai in kin haihu nayi miki alkawarin karatu zaki yi shi har sai kin gaji..Danmallam ma bazai taba Tauye miki Hakki ba..!
Amina sai ta fara Tunanin ko Hajiya tasan wani abu ne kan mamanmu da Anty Amarya..?
Sai dai bata ga wani alama ba,Ita yanzu zata iya yin komai Saboda Cikin jikinta sannan Zatayi komai Saboda Tonama mamanmu asiri da Anty Amarya kuma Cikin jikinta ne makami shiyasa bayanin Hajiya bai Dameta ba Hawaye suka kawo Idanuwanta in ta tuna Shekarun data kwashe bata san Dadi da muhimmancin Uwa ba,Gashi yanzu tana Cikin wani Siradi,Siradin da uwa ce kadai Zata tallafamata sai dai ina Mamanmu ta yanke wannan abun Saboda son zuciyrta da kuma Mugunta da zalunci.
Ganin Tana Hawaye Yasa Hajiya tayi Tunanin Rabuwa da su hanne da karatunta yasa ta saka Hannu ta Rumgumo Amina kan kafadarta Tana Lallashinta Lokaci Daya tana Fadin"Kiyi hakuri Amina..ki daina kuka na dan Lokaci ne watarana sai Labari..!
Amina na Shesshekan kuka tace"Hajiya ba ina kukan hukuncin ki bane..
Ina kukan rashin yaya ne..ayau bata a Duniya ina jin matukar kewarta..!
Hajiya Tsausayinta ya kamata ta Dagota tana share mata Hawaye lokci Daya Tana fadin"In kin Tunata ki mata addu"a kin ji ko..?.Sannan in kin ji kewarta ki tuna Dani Domin tamkar Uwa nake gareki ina nan Saboda ke Amina ni ba Uwar Umar nake ba Har Abada ni ina matsayin mahaifiya gareki ne nayi kuma alkawarin Kareki da yardan Allah ke da abunda ke Cikin ki..!
Tana Fada tana share mata Hawaye wasu na Bulbulowa Hajiya fadi take"ki daina kuka nasan zaki ji Dadin Zama da Aisha na dan Lokaci ne Zaki Dawo in Lokacin hakan yayi.!
Amina ta gyada kai tana Fadin"Hajiya ke da mallam nasan har Abada bazaku kai ni inda Zan cutu ba..Sannan duk abunda kuka Zartan kan Rayuwata ina maraba dashi..Na yarda da Hukunci ku kuma Insha Allahu Zaki Sameni mai Bin Umarninki..!
Hajiya taji Dadin haka ta Dinga shafa kan Amina ta saka mata albarka kafin ta mike tana fadin"Kayan ki duk suna gida ko..?
Amina tace"Eh akwai wasu anan hajiya..!
Hajiya tace"To ai ba kaya da yawa Zaki Diba ba nan gaba ma kadan zasu yi miki. Sai ta Dinka miki wasu achan kawai..!
Har Hajiya ta Fice Daga Dakin Amina bata kara mgana ba,wani irin Dakiya ne da Taurin zuciya ke shiganta da kwarin gwiwan da bata san tana Dashi ba Duk da tasan zatayi kewar su hanne da makaranta ammh Gaskiyan Hajiya ne datace na dan Lokaci ne watarana sai labari.
Daya da wani abu na rana su Hanne suka Dawo sun ji dadin ganin Amina taji Sauki basu damu da yanayinta ba sun Dauka saboda bata da Lafiya ne ita kuwa kallon su kawai take yi Tana Tunanin sai dai suga Hajiya ta Dawo ita kadai zasu yi kewarta kamar yadda itama Zatayi kewarsu Hamida kuma Tsausayinta take ji domin in ta kalletasa sai taji kuka ya taso mata ya Zataji in taji Abunda mahaifiyarta take aikatawa..? Bazasu iya Daukan wannan abun ba su take Tsausayi domin ba d'an da zai so uwarsa ta kasance bata gari ba abun akwai taba Zuciya ammh Dolen wata watarana Allah ya Tona musu asiri kamar yadda ya Fara Tona musu awajenta.
Kamar sun san Amina zata koma wani wajen Ranar wuni sukayi tare ko Hamida bata ko leka gida ba suna Tare har Dare,Da mallam ya shigo har Shashen Hajiya ya Dubata ya Dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka..Allah ya Saukeki lafiya ya kareki mamana..!
Ta amsa kanta na kasa kafin ya Sake fadin"Kina tsorata Cikin barcin ki har yanzu ko kin bari..?
Amina tace"Yayi sauki baba..!
Malam ya jin jina kai yana Fadin"Zai bari gabadaya ki Dage sosai ki Daina kwanciya ba alwala sannan ki Rike addu"o"in nan da yawaita karatun Qur"ani..!
Amina ta amsa da toh ya Dade yana mata Nasiha kafin ya fita,Dakin Hajiya ya shiga sukayi mgana ya Fadamata ya Kira Usman mijin Aisha yace ba wata matsala sannan bayama gida yana Lagos,Daganan sukayi mgana sama sama kafin ya fice Daman shi da Aba suka shigo shima ya shiga ya gaida Amina bai Dade ba shima ya fita Amina bata Damu ba Sai ma wani Tsausayinsa Daya kamata Mace tatasa shi gaba da makircinta.
Mallam nan ya bar Aba Hajiya tamai mganar Zata kai Amina gidan D'aya Daga Cikin yaran nan tadan koyi wasu abubuwa tunda ga yanayin yarintarta bata koyi wasu abubuwa ba sannan nan da Lokaci kadan Danmallan zai zo ya tafi da ita madina..
Aba bai Tambayi ina Za"a kai Amina ba Sai kawai yabi Hajiya da godiya yana komawa gida ya Fadama mamanmu yadda sukayi da Hajiya anan nema take jin Amina bata da lafiya Mamanmu dataji haka shewa ta Saki aranta tace auran da Zai kare a gantali ne za"a je koyon zama da Miji..!?
Shiyasa kwata kwata bata Damu ba,ita Atunaninta Wahalar da kai kawai Hajiya take yi ammh Amina da Umar ai sai hange Daga nesa ammh a fili sai ta nuna Tasauyawanta da cewa da Safe zata shiga ta gaida Ameenan kafin su tafi ko aranta bata Damu da Sanin ina Hajiya zata kai Aminar ba wannan baya gabanta yanzu.
Adaran Hajiya Ta kira Aisha tace gobe tana nan tafe Aisha taji mganar kamar Daga sama murna ta Cikata Dayake Usman din bai riga ya Kirata ya Fadamata ba Hajiya ta rigasa sai taga kamar ta zama mai sa"a domin Hajiya basa zuwa gidan mutum hakanan sai da babban Dalili ammh ita yau gata Hajiya Zata zo gidanta Murnan ta ya kasa Boyuwa suna gama mgana da Hajiya ta tafi Dakin kakar mijinta Dake zaune tare Dasu da suke Kira Yakaka ta sanar da ita Hajiyarsu na tafe gobe.
Har gari ya waye su hanne basu san komai ba da Safen dai Hajiya tace ma Hanne zasu fita da Amina su shirya su tafi hadda sukace to basu yi wani tunani ba, sai sukayi Zaton Ko asibiti zasu koma basu damu ba.
Ammh Sanda suke shirin tafiya Amina na kwance na kallon Hamida na shiryawa ta fito wanka aran Amina tana tunanin Hajiya zata zame ma Hamida uwa kamar yadda ta Zame mata uwa,Idonta ya kawo ruwa in ta Tuna zatayi nesa dasu saurin share Hawayenta tayi ta kira sunan Hamida bata Damu data waigo ba ta amsa mata.
Amina tace"Hamida don Allah ki kula da Jawaad..!
Hamida sai da ta saka Rigar wata atamfar dake jikinta sannan ta Juyo jin abunda Aminar tace da yanayinta yasa Cikin mamaki tace"Wasiya kika fara bari ne Aminene .!?
Amina tayi Mirmishi tace"Eh mana kinsan Rayuwa haka ta gada..muna tafe ne bamu san muna tafiya da mutuwarmu ba .!
Hamida ta fara Dariya tana Fadin"Lalle Amina ta fara Tunanin mutuwa..Hanne tazo kiji..Hanne. !
Ta shiga kwalama Hanne kira sai gata ta Dawo da Faratin kayan karinsu tana Fadin"Kiran me kike min hamida kamar kin bani ajiya..?
Hamida na Dariya tace"Amina ce ta fara barin wasiyya..!
Hanne ta ijiye abun hannunta saman Cafet tana kallon Amina Lokaci Daya tace"Topa ta fara Tunanin mutuwa ne..?
Ko azara"ilu ta gani..?
Ta fada tana yar Dariya Amina ta balla musu harara tana fadin"Bansani ba. kufa yan iska ne baku san abun arziki ba.!
Hamida tace"Mu ko ke ne bamu san abun arziki ba..?
Ke Amina uban wa ya kaiki maida abun arziki na fada ma. !
Hanne ta Zauna tana Fadin"Ki zauna mu karya hamida kada mu makara..Amina inaga asibiti zasu koma da Hajiya. !
Hamida tace"Shiyasa ta fara barin wasiyya kenan. !
Duk tana jinsu batace musu komai ba illah tasowa da tayi tace su karya Tare harda Jawaad daya shigo yanzu gabadayansu suka karya suna yi suna Hira Amina tana tunanin shine na karshe Zaman su tare Indomie ne sai soyayyan kwai da Tea Amina kwan taci ya taso mata da zuciya sai da tayi Amai ta koma ta kwanta tana maida Numfashi su Hanne na mata sannu da Zasu tafi haka taji kamar ta Bisu har suka fice tana musu bye bye suka fita Suna Dariyanta wai Amina ciwo yasa ta fara Tunanin mutuwa
Basu san cewa Amina Zatayi nisa da su na wani dan Lokaci ba..suna fita ta Fashe da kuka sai da tagaji tatashi ta rarrafa tayi wanka sai a yanzu da aka Tabbatar tana da Ciki take jin wani Sauye Sauye ajikinta na masu juna Biyu.
Ta shirya Cikin Riga da zani na kayan da Hajiya ta Dinka musu ita da Hanne da Hamida abunda yasa ma rigar tayi mata daman tun farko dinki yayi mata yawa saboda Sizes din Hamida aka mata kuma tun Lokacin ba"a rage kayan ba Ta yi shirinta da wuri ne Sabida Hajiya tace da wuri zasu tafi Tunda ita ayau din zata Dawo.
Yan kayanta Dake nan kawai ta Hada kala uku sai Azakar da addu"o"in da mallam ya Rubuta mata' sai mangunanta,wasu kayan nata suna gidan Aba wasu kuma suna gidan ya Danmallam bata kwaso duka ba,Zama ta yi kawai tayi Tagumi tana Tunanin yadda Sabuwar rayuwa zata Bude mata ita da abunda ke Cikinta tana tunani tana Hawaye sai ga Hajiya ta shigo tayi saurin goge hawayenta saboda kada ta gani ashe ta gani sai bata nuna mata ba
Kallonta tayi tana Fadin"Mamah kin gama shiryawan .?
Amina kanta na kasa tace"Eh Hajiya ina kwana..?
Hajiya ta amsa tana fadin"To kin kar ya kuwa..?
Ta gyada mata kai tana Fadin"Eh hajiya..Tare da su hanne muka karya. !
Juyawa tayi ta Fice tana Fadin"To bari Idi ya dawo kai su makaranta sai mu wuce..!
Fitan ta ba Dadewa ta Leko tace ma Amina ta fito Dogon Hijabinta ta Saka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login