Showing 63001 words to 66000 words out of 141906 words

Chapter 22 - Ta Fita Zakka Part 2

10 Oct 2024

4176

gidanta mallam yace Tunda taji Sauki ta koma Gidanta ta Jira Mijinta Dole ta tattara tatafi ammh Sai da ta roki mallam ya bata Sa"adatu tatafi da ita sai yace sai dai Tatafi da Sabeeha tunda ta gama primary zata shiga Jss1 kafin a sakata to da Sabeehan ta koma bayan mallaminsu ya Kira Anty Amarya ta koma wajensa ta Zubaimai kudi ya bata wani kullin mgani yace Sakina ta sha da Ruwan Zafi duk abunda Uwani ta bata taci ko ta sha Zatayi amansa ko Tayi kashinsa Domin ya tabbatar ma da Anty Amarya wani abu ne Aka bama Sakina taci acikinta..
Haka kuwa akayi ranar data sha mganin kwana tayi tana Zagayawa har safe ta Kira Anty ta Sanar da ita Tana jin haka Cikin farimciki tace in Sha Allahu nasara tasu ce.
Tsakaninta da Haj Uwa kuma ko mgana basa yi sai agaban idon da bai san tsakaninsu ba kamar mallam da Hajiya da Suke Dauka bata san boyayyin Fuskokinsu ba..Ammh in suka hadu su Biyu su harari juna sannan kuma kowacce ta wuce tana ikirarin sai taga bayan yar"uwanta.

*****

Achan Madina kuwa Danmallam dai da Sarood balarabiya suna ta gwangwajen amarcin su sosai fa ya Saki jiki yana Morewa Saboda ai ya Dade Rabonsa da mace tun Kan Amina wannan kuma ai ya Daukesa a matsayin Rabo ne shiyasa daya samu wannan Damar yake ta amfana da ita Domin Daman Daurewa kawai yake yi Yana fama da azumin Litini da alhamis saboda kariya da Tsare kansan.
Ita kanta Sarood din sai alokacin tasan ta yi aure sai kuma ayanzu tasan tana kishin Mijinta ada kamar bata Damu da kishin Sakina ba ammh yanzu da tasan waye Umar sai taji har Sakina ma tana matsanancin kishi da ita ballatana Amina datafi Tsayamata arai ganin itace yarinya sannan kuma Amarya.
Sosai take ta shagwabanta shi kuma yana lallabata Dalilin haka ne ma yasa har yau bai kira Amina ba Saboda ai sun yi mgana da Hajiya washegarin Ranar data koma Gumel a wayar Nazir Saboda ya cika alkwari yaje ya kwana Daya Ranar Litini da Safe ya hau Jirgi ya koma hankalinsa ya kwanta daya ga Hajiya lafiyanta kalau Cikin koshin Lafiya.
Da farko kafin Bullowan Cikin jikin Amina har ya fara Cuku cukun nema mata Takardan Zama madina sannan har sun yi shawara da Aliyu kan zai shigar da Takardan kan zai karbi Gidan malamai na makaranta Saboda gidansa yayi musu kadan sai ya saka Amina an??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a Cikin makaranta,Sai kuma ga wannan al"amarin da hajiya tace ya Dakatar da komai Shiyasa ya dan Samu Sauki ya fara shirin Tahowa saboda Sakina sannan uwa uba Amina yana son yazo ya ganta Tunda ya tafi bai fi sau hudu sukayi mgana ta waya ba sannan Sakina duk sanda sukayi mgana ta Dinga mai kuka keman tana fadin yazo ya tafi da ita Tsausayinta yake ji ganin halin Datake Ciki yasa yayi mata alkawarin zai zo nan da wata Biyu zai zo sai su koma Tare Umra yake so yayi shiyasa ya Dakata da Tafiyar Sannan Sarood ma tayi Damara sai taje kuma in yace bazai je da ita yayi rashin adalci ko Iyayanta sai sun ga rashin adalcinsa...!
Tunda suka yi mgana da Hajiya tace kada ya sanar ma kowa ko Aliyu bai Fadama komai ba yadai Fadamai laluran nan tasa Allah ya basa waraka da Taimakon shawarwarin mallam Daganan kuma sun ma Dade basu yi mgana ba daya kirasa sai ya Fara mai Tsiyan ya barsa ne yaci amarcinsa da yar Balarabiyarsa Danmallam Tsaki kawai yake yi da Dariya domin ba karya yana fa shan amarci.
Sai da Amina tayi kwana Goma A Abuja sannan ya nemi wayarta da lambar da Jafar ya Dade da Turomai sai kuma ya kara jin wayar a kashe bai ji Dadi ba in yace Amina bata aransa yayi karya abubuwa ne suka sha mai kai sannan da Tazaran Dake Tsakaninsa da ita da rashin shakuwa da kuma Basu wani saba da juna ba.
Aisha ya kira kawai saboda ko ya Kira Hajiya bata kusa da Amina.
Daman duka kannensa suna kiransa awaya suna gaisheshi lokaci bayan Lokaci Haka suke basu yar da tarbiyan gidan mallam ba ko da yayyinsu basa kusa dashi suna Kiransu a waya suna Zumunci dasu Lokacin Ba'rin Sakina sun ta Kiransa suna mai Jaje.
Lokacin da yake tambayan Aisha mganar yaji wayar Amina akashe ya Aisha tace bata sani ba ammh Zata tambayi Aminar taji tunda ita tama manta da mganar wayar sannan batama Taba ganin Aminar da wayar ba.
Yace to ta fadama Amina yana son mgana da ita ta kuna wayarta Ya Aisha ta amsa da insha Allahu zata Fada mata ya tambayeta ya jikin Aminar..?
Ta sanar dashi lafiyanta kalau sai godiya Zazzabin Dare dai take fama dashi sai amai sannan bata iya cin kowani abinci sai Tea sai Kuma wainar Fulawa,Komai Taci baya Zama sai ta Amayar dashi sai yaji Tausayinta gata yarinya ga shi ya Dora mata nauyi sun yi mgana da ya Aisha sosai ya sanar da ita suje asibiti tace eh Usman ne yace ta bari ya Dawo yaje Kaduna wani aiki Da haka suka rabu..
Suna gama wayar Aisha ta nufi Dakin Yakaka tana shiga ta iske Amina Zaune saman Cafet tayi Daidai tana cin wainar Fulamai mai manja da Saude mai aikinta tayi mata Tun Safe bata ci komai ba Tea din ma yau taki sha ita sai Wainar Fulawa Shine Yakaka tace Saude tayi mata Wainar Fulawan har Sauden tana Dakin ne suna ta Hira Yakaka na basu labarin Cikin kakan su Usman har ta Haihu kanwa ne abincinta sai da bakinta ya Lashe saboda Cin kanwa tana Fadama Amina ta godema Allah tayi ma Ciki mai kyau tunda batayi mugun laulayi ba sannan ta iya shan Tea da Cin wainar Fulawar tayi kyan ma Laulayi.
Amina sai cin abunta take yi tana Dangwala yaji tana Sanye Cikin Bakar Doguwar riga cikin kayan ya Aisha ne da ta bata take sakawa tunda kayanta sun Daina Shigarta Cikin fa Kiba kawai da Budewa yake saka Amina ta bari ne Usman ya dawo su je asibiti da kasuwa ta siyo ma Aminar Dogayen Riguna tunda duk ta bata na wajen nata sannan sun ma Aminar karanci.

Shiga Dakin tayi da Sallama Suka amsa mata,Saude tama mgana tace taje Kitchen ta Dora Girkin Rana Ta amsa da Toh ta fice sai da ta fita sannan ya Aisha ta kalli yakaka tana Fadin"Yakaka sannu da Hira..!
Tana Dariya tace"Yauwa Sannu Aisha..Hala har kin kwanta Hirarmu ta, tada ke..?
Aisha tace"A"a Wlh ina ta gyare gyare ne ma Yakaka ban ji ma Hirarku ba..!
Yakaka tace"Au ho..Ai ina nan ina ma Takwarata Tsiya ina fadin ta godema Allah tayi Ciki mai kyau ba laulayi sannan ta na cin abincin Zamaninmu ni lokacin da nayi Cikin Gaddafi har na Haihu kanwa ce abincina..!
Ya Aisha ta jinjina kai tana fadin"Kanwa..?
Taba..Yakaka kin sha wahala..!
Ta yi Dariya kafin tace"Ai Darajan Uwa ta Daban ce Aisha..Allah dai ya bama kowa nashi kema ina miki addu"an Allah ya baki naki Aisha ita Aminatu ai tana mai kyau ma Kinga banda aman da take yi to sai Zazzabin Daren dana ce miki tana Faama dashi..!
Ya Aisha tace"Eh zamu je asibiti taga Likita ma yakaka in Usman ya Dawo..!
Ta jinjina kai kafin tace"Hakan yana Dakyau..Allah ya Dawo dashi lafiya..!
Suka amsa da Ameen harda Amina Data gama ci ta Kora da ruwa ta koma Tana Sauke Numfashi.
Ya Aisha ta kalleta tana Fadin"Amina ina wayar da Hajiya ta baki da Zata tafi..?
Amina ta Dafe Cikinta daya Fara Fitowa ta yamutsa Fuska kafin tace"To ina na sani..?
Tunda ta bani chan Dakin na wurgar da ita..!
Ya Aisha ta hararrta tana Fadin"To daman don ki ijiye Aka baki wayar..?
Kefa kina da sarkaci bayan ma jidalinki wani Lokaci..!
Amina ta kalleta kafin ta Tura baki ya Aisha tace"Tashi muje ki Daukomin ita na saka miki chaji tunda Daman Hajiya tace Sabuwa ce..Mijin ki ya Kirani yace yana son mgana Dake in fada miki ki kunna wayar hannunki..!
Amina ta kalleta Shekeke kafin tace"Mijina kuma..?
Ya Aisha tace"Eh ko ba mijin naki bane..?
Amina ta Hura Hanci kafin tace"Ina Laifin kice yaya danmallan..?
Ya Aisha tace"Ni yayana ne ke kuma Mijin ki ne..karyan iskanci kike yi bakin ki ya Bude yanzu ko..?
Amina ta Yi fari da ido kafin ta bata rai Lokaci Daya tana Fadin"To ni yaushe rabon daya nemeni?
Ko tawayar Hajiya yaushe da Rabon Daya Kira yace abani..!

Tafada tana bata rai saboda Tsakani ga Allah tana jin takaicin hakan wato bai Damu da ita ba..?
Ya Aisha ta rike baki Tana Fadin"Au Daman kina jiran sai ya nemeki ne..?
tab kina da aiki kada ki manta wata matar garesa achan sannan anan ma yana da Sakina mu masu mu kadai muna Kula da Mazajenmu ballatana ke mai Kishiyoyi har biyu.?
To ki rage wannan Sakarcin naki ko ba Haka ba Yakaka..?
Yakaka ta gyara Zama Tana Fadin"Au to gayamata dai ai ni nan Tunda naji yarinyar nan da Zama da kishiyoyi har Biyu nace Zama bai ganni ba..Tana Haihuwa Gyaran yan maiduguri zan
Mata wanda ba su biyu ko su Uku ne itace ta Hudu sai ta fita Zakka..Ai mu masu sunan mu ba Borori bane..Muna da Tasiri sannan wlh badai mutum ba Sai ta Allah..
Amina na Dariya Ita da ya Aisha wacce tace"To ai Kirarin ta kenan Yakaka Aminene badai ta Mutum ba sai ta Allah..!
Yakaka tace"Ai Gaskiya ne..Ke kwantar da Hankalin ki yar nan har nan Zai zo yana mana yar murna sai mun Wahalar dashi ammh dai kafin nan tashi maza ki Dauko wayar ajonata in ta Cika sai ki kirasa ai mune akasansa ba komai in min nemesa muma watarana Zai nememu ko don Darajan wannan abun da ke Tare Dake in ya manta Dake don Kaniyarsa ai bazai manta da wannan aikin Daya kunsamiki ba..!

Amina sai ta kasa mgana kunya ya kamata ya Aisha kuma ta Fice sum sum tana Dariya Dole Amina ta mike tabi bayanta suka shiga Dakin atare ta Dauko wayar nan Gefen katifa inda ta Watsar da ita Aisha ta karba ta Bude ta a kwali ta jona mata achaji Tana ta mata Fada fadi take"Wlh ijiye wannan Jidalin naki Zaki yi agefe wajen bautar aure ba wannan ake Bukata ba..ki iya Kissa da Kisisinan rike miji..Ni ban ma jin balarabiyar nan Sakinar ce mai ido a Tsakar ka..Kema ki Samu ki Zama mace awajensa..!
Amina dai batace komai ba aranta Tace ai so ma suke ya Sakeni baki sani ba.
Afili kuma batayi mgana ba Saboda abun ya fado mata arai duk da Tana kokarin Cire abun aranta ammh kuma har Abada bazai taba Fita ba..
Har ya Aisha ta gama fadanta ta fita batace komai gefen katifa ta koma ta Zauna tayi tagumi in ta Tuna kalaman mamanmu na kashe mata uwa sai taji ta tsaneta kamar tayi tsuntsuwa ta ganta agabanta ta Chaka mata wuka har sai? ta Daina Numfashi.
Sannan ga kewar yaya aranta ga kuma Rashin samun wanda Zata Fadamawa baalle ta samu sauki ta kwanta akan jikinsa tayi kukan abunda ke ranta.
Haka ta Dinga kuka ita kadai ta Share Hawayenta ta sulale nan saman katifar ta kwanta ta na maida Numfashi har barci ya kwasheta bata Sani ba sai Wajen Biyu na rana ta Farka shima Ya Aisha ce ta tada ita tayi sallah Sai da tayi wanka tayi salla Ta maida Doguwar rigar jikinta ta koma Dakin yakaka ta Haye gadon ta kwanta tana jin yakaka Dake zaune a saman Cafet tana goga goranta tana Korafin ta rage yawan barci mai Ciki da zirga Zirga aka santa tana jinta ta kara Dunkule kanta Cikin Filo aranta tana fadin Yakaka ba kisan irin barcin dana ke ji bane ita dai sama sama ta dinga jin yakaka dagachan kuma barci ya sake Daukanta la"sar nayi yakaka tatasheta tace ta tashi tayi salla ta Daina kuma barcin la"asar.
Fadi take"Ke bake kadai ba..Ki rika barci har yamma tayi in kina son Lafiyanki da abunda ke Cikin ki sai kin kiyaye wasu abubuwan ku yaran yanzu komai Cikin gata kuke yi mu alokacin da in kina da Ciki ko barcin sai kin Ragesa har na Dare bama na yammah ba..!
Amina dai batace komai ba ta Fada Tiolet ta Dauro alwala tazo tayi sallar tayi addu"a domin ta daina Sakaci da addu",an kamar baya da kuruciya yake Dauke mata hankali.
Tana Idarwa ta Dauko Sauran wainar Fulawanta ta Sake ci tana ci tana jan yaji Yakaka na kallinta tana Girgiza kai fadi take"Ki Sautata ma kanki Cin yaji nan wajen haihuwa nake jiyemiki basir ya taso miki..!
Amina tace"Au daman yana Tasowa ne..!?
Yakaka tace"Zaki sani ne in kika shiga Dakim Haihuwa..!
Amina Dariya kawai tayi sai ga Ya Aisha ta shigo tana Fadin"Amina wayar ta Cika na kunna miki..Rike ta Hannunki na Fadama ya Danmallam Zai kiraki yace..!
Ta Fada tana mika mata wayar ta karba tana Tura baki ya Aisha ta Dunguremata kai Tana Fadin"Kinsan Allah ki fita Daga idonaa Amina na Rufe..!
Zamu zo mu Tsara abubuwan da Zaki rika koya fanni girki da gayu dasauran abubuwa sannan har karatu Zamu rika yi,ga yakaka nan na san ban da matsala zata koya miki Dubarun Zaman duniya..!
Yakaka tace"Ai ita Duniya basai an koya maka Dubarunta ba..Ita ke koya maka yin Hankali da ita..barni da ita ai muna Tare har Madina in tayi ba Daidai ba tasha rankwashi..!

Amina tace"Tab wazai bisa madinan..?
Ya Aisha tace"Yakaka kina jinta ko..!?
Tace"Yi tafiyarki barni da yar nema..!
Bata lambar mijin nata ta Kirasa da kanta..!
Ya Aisha tace"Munyi mgana yanzu yace zai kirata..!
Yakaka ta amsa da Toh fita Aisha tayi ta barta da yakaka sai Fada take mata ta shiga bata labarin irin yadda tayi gwagwamarya agidan kakan su Usman Cikin mata Biyu har sai mijinsu ya rasu ana ta Kishi da ita Amina dai tayi bakam tana jinta kafin tace"Yakaka in ka hadu da masu asiri fa suna zuwa gidan Boka..?
Yakaka tace"To Sai me..,?
Ai akwai su duniya ta lalace sai ka koma gefe ka rike Allah ka sa aranka Bawa bai isa yayi maka abunda Allah bai maka ba..yar nan rike gaskiya ki rike Allah ko min Dadewa gaskiyanki Zata bayyana sannan Allah baya barin Azzalumi da sannnu hakki zai bayyana .!
Kai ta jinjina domin ta gamsu da mganar Yakaka suna Cikin hirar ne Taji karar wayar dake gefenta da Farko ta Firgita sai da Yakaka tace mata wayar tace sannan hankalinta ya kwanta Mikewa yakaka tayi da Go ranta ta fice tana Fadin"Mgana mai Dadi kuma ban da Tura masa wannan bakin..Ki ce sabuwar amaryansa tana gaishesa .!
Ta fice ta bar Amina da waya a Hannunta sai da ta Katse sai kuma ya Sake kira tabi jerin lambobin da kallo bata Nigeria bane,Daukan wayar tayi Domin sak irin ta yaya ce tasan yanayinta tana Daga Kiran taji Sanyayyar Muryansa yana mata sallama sai taji kamar an kwara mata Ruwan sanyi ko"ina na jikinta yayi Sanyi har Bakinta ma yayi nauyi ta kasa amsa mai sai da ya maimaita sannan ta iya amsa murya shake Cikin Haibansa yace"Amina ya jikin ki..?
Tura baki tayi kamar yana ganinta kafin tace"Ni ai lafiyata kalau..!
Gemunsa ya sosa kujeran Office dinsa tana Dan juyawa dashi,yace"To ko ya nauyin jiki zan ce..?
Amina sai taji kunya ta kasa mgana cikin wani yanayi yace"Nayi ta Kiranki ban samu ba tunda Hajiya tace min ta baki wayar..!
Uhm kawai tace ya Cigaba da Fadin"Amina kinga lamarin Ubangiji ko..?
Wannan rabon Dake Tsakanin mu shine silar Faruwar duk abunda ya Faru..!
Amina tayi shuru batayi mgana ba shims shurun yayi kafin yace"Ba inda ke miki ciwo ko..?
Amima sai taji wani Rauni ya shigeta kafin tace"Eh..!
Cikin Rudewa yace"Eh kuma..?
To ina ke miki ciwo..?
Amina kai Tsaye tace"Menene mgani in an yi ma mutun sihiri sannan ta wata hanya Zai gane an yi masa..?
Umar yaji mamakin mganarta Cikin mamakin yace"Amina waye akayi ma Sihiri..?
Cikin wani yanayi Amina tace"Ni ce..!
Baki ya Bude kamar tana ganinsa Cikin mamaki yace"Ke kuma..?
Ta ce"Eh..!
Sai kuma kawai ta Fashemai da kuka Har da Sheshsheka Saboda Dacin abun na taso mata lokaci Daya Rauninta na bayanna.
Danmallan jikinsa yayi sanyi Cikin wani yanayi yake fadin"Kinga Amina..bar kuka nan yimin bayani yadda zan gane..!
Ina ko jinsa batayi sai faman kuka take yi Dagacin kukan datake yi Daga karkashin Zuciyarta ne kansa ya Dafe Cikin wani yanayi duk da yasan yarinyar akwai kukan banza har da na siyarwa sai dai jin kalamanta da wannan kukan datake yi tabbatar wani ya faru wanda kedamunta acikinta kuma ta kasa fadamawa kowa..!
Cikin sigar lallashi yake fadin"kiyi hakuri ki daina kuka sanar dani abunda ke faruwa..!
Sai taji muryansa kamar wani waraka ne ga matsalanta yasa tace mai cikin kuka"ban taba Fada ma kowa ba sai kai..Wlh duk abunda Zan fada maka ba karya bane ya Dannallam..!
Da Sauri yace"Eh naji bazan Fada ma kowa ba taimakeni kibar wannan kukan saboda yanayin Dakike Ciki..!
Amina ta share Hawaye tana jan majina tace"Yaya..Yaya. !
Ta fada sai kuma ta kara sakamai kuka Umar ya shiga wani yanayin Tashin hankali da jin kukanta Cikin mamaki yace"Yaya. ?
Amina tace"Eh yaya ba mutuwa tayi ba Kasheta MAMANMU tayi..!
Ta fada tana matse bakinta kada kukanta ya kara fitowa yana Zaune ne sai da ya mike Cikin wani yanayi a Muryansa yace"Yaya ba mutuwa tayi ba kuma..?
Mamanmu ta kasheta..?
Amina ta amsa mai da Eh Cikin kuka Umar ya katseta Cikin Muryansa da kaifi yace"Ki bar wannan kukan yimin bayani sosai yadda Zan gane..!
Amina sai kawai taji ta yarda Data Fadama Danmallam abunda taji ko zai Daina Damunta aranta ko Zata Samu Saukin abunda take ji..
Cikin kuka ta fara Fadamai komai Tun farkon wayar da taji Anty Amarya nayi a ranar da Hajiya tace zata tare da kuma Ranar da Ta kama mamanmu tana mgana da duka mganganunta,Sai dai ta Boye sunan Hajiya Uwa tunda bata san meye Tsakaninsu ba..
Amina ta sharbe hawaye tana Fadin"Da kunbina naji suna waya ya Danmallan..Da kunnina naji mamanmu na Fadin malaminta ta saka ya kashe mana uwa Saboda ta Samu Aba yadda take so Sannan da kunnena naji tana Fadamin Ba ni taso na ZAMA haka ba ya Jafar taso ya lalace da kunnina naji Tana Fadin Bazan haihu Dakai ba Sai Sakina sannan sukace har Abada sai dai aurena Dakai ya kare a gantali..Zuciyata tana min Zafi tun Ranar da naji haka..nayi kukan rashin Uwa Ya Danmallam bansan Dadinta ba Duka Mamanmu ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login