Showing 30001 words to 33000 words out of 141906 words

Chapter 11 - Ta Fita Zakka Part 2

10 Oct 2024

4141

cikin kwabarta na gida hamida ta rakata gidansu Hanne.
A bakin shashen Hajiya suka ga Haj.Uwa tunda taji zuwan Amina ta kasa zama tana ganinsu ta washe baki Tana fadin"Ga Amina Amarya..!
Sai kunya ya kama Amina ta Dukar dakai tana gaisheta
Hannu taja tana Fadin"Au bazaki shiga Shashena mu gaisa ba..?
Yar"uwarki ma Umaima bata da lafiya jiya ko barci bamu yi ba..!
Amina tace"Allah sarki bansani ba..!
Hamida tace"Mun manta ne bamu Fada miki ba..Jiya kwana tayi ihu mallam da su ya Akilu suka kwana suna mata karatu..!
Amina taji Tsausayi ya kamata sosai Ta kalli Hamida tana fadin"muje na Dubata Hamida..!
Da Sauri Hajiya Uwa tace"ai ita sun shigo sun dubata da Safe..Ke dai muje Diyata Amaryan Umaru Faruqu..!
Tafada tana jan Amina Hamida sai bata bisu ba tunda taga kamar Haj.uwa ta fi son Amina ita kadai.
Sai ta juya ita ta shige Shashen Hajiya babba.

Kafa kafa Haj uwani ta dinga yi da Amina har shashenta kai tsaye kuma har Dakin da Umaima ke kwance tana barcin Wahala duk ta kara ramewa sai Dogon wuya Amina ta kalleta Cikin Tsausayinta tace"Allah ya bata lafiya..!
Haj Uwani ta kalli Umaima sai ta fara Sharan kwallah kafin tace"Wlh ciwon nan na Umai ya fara damuna Sa"o'inta duk suna Dakunansu har da ku ma kannen bayanta ita ko kalli Halin Datake ciki..!
Amina tace"sai hakuri Allah ya bata lafiya..bari na tafi..!
Haj Uwa tace"Bazaki tafi ba sai kin sha wani abu muje..!
Ta kaita har falo ta zaunar da ita kan kujera tana fadin"Umaru dai ana Madina ko..?
Amina tace"Uhm..!
Daganan bata kara mgana ba mamaki abun ke bata Duk da Tasan Hajiya uwa bata da matsala ammh bata janta ajiki kamar na yau sai kawai taji bata yarda da ita ba.
Tana nan zaune sai gata ta fito da Jug da kofi ta kawo gaban Amina ta ja Center table ta dora lokaci Daya tana Fadin"Lemon kankana nayi tun Safe kinganshi nan yayi sanyi zaki ji Dadinsa Amina..!
Amina ta yi kasake tana kallonta ganin haka yasa ta Zauna gefenta tana Fadin"Kada ki damu nan Umaru ke karyawa indai yana gari dagashi har matansa abinci shashena basu da Shamaki dashi..!
Amina dai batace komwi ba ta Dauka ta Tsiyaya kadan Ta Daga kofin takai Bakinta Hj.uwa na kallonta zuciyarta Cike da Farinciki zata aiwatar da Tsarinta Cikin Sauki kamar yadda ta Saba.!
Amina acikin ranta taji bazata sha wannan abun ba,ba domin tana Zarginta ba sai domin cikinta ya cika sannan in ta fada mata bazata yarda ba Sai dai kamar an kwato bakinta Ta Furta.
Bismilallahi..!
Sannan ta Kurba kadan Haj.Uwa taji kamar an sakata acikin Aljannah Ta Bude zatayi mgana kenan Kukan Umaima ya katseta tatashi da gudu tatafi Dakin tana cema Amina tana zuwa..!
Tana shigewa Amina ta Dawo da na bakinta wanda bata gama Hadiye ba jin wani makaki a makogwaronta waige waige ta farayi ganin Haj.Uwa bata fito ba yasa tatashi Sadaf Sadaf ta shiga Kitchen dinta ta Juyesa a wajen wanke wanke taga yana wani yauki mamaki ya kamata da sauri ta Bisa da Ruwa ya wuce sannan ta samu ruwa ta Kuskure bakinta ta koma Falo da Sauri ta ijiye kofin ta zauna kenan sai gata fito Idonta kan kofin tana ganinsa ba komai ta wani Saki ajiyar rai kafin ma ta zauna Amina ta mike tana cemata zata tafi Cikin Murna da Cikar Burinta tace"To shikenan Aminatu Sai na shigo shashen Hajiyar..!
Harda Dari biyar ta bama Amina tace bazata karba ba ta matsa mata ta karba Amina ta fice cikin mamaki sannan uwa uba kuma Makogwaronta bai yi mata Dadi ba Tunda tasha wannan lemon
Tana Fita Haj.Uwa ta Daga Kofin kafin ta Sheke da wata Dariya a Fili ta Furta"Kema kin Hau keken beran kamar yadda na Dora na bayanki..!
Sai ta wani Saki shewa Duniya Sabuwa..burinta ya kusa cika Nazeem Sauransa wattani kadan ya gama makaranta Uzairu kuma ya gama Degree dinsa na farko Services ma yake shirin tafiya ta fara Hango kanta a matakin datake Wahala Shekaru masu yawa.
Abunda bata sani ba Kafin nata Tsarin Ta manta Allah ma da nashi..?
To nashi ya riga nata sannan abunda Allah ya rubuta shi zai faru wannan gudan jinin sai ya fito Duniya wannan Cewarsa ne..!
Amina haka taje Shashen Hajiya ba cikin natsuwarta ba cikinta nata Juya mata sai dai bata cema kowa komai ba suka gaisa da Hajiya tana ta Tambayanta ko ba matsala tace mata eh Dakin su hanne suka shige suna Hira Amina ta kasa natsuwa sai da ta shiga Tiolet ta dinga Tura Hannunta Cikin baki sai da ta samu Wannan dan Lemon daya shiga Cikinta ya fito harda Abincin data ci sai da ta Amayar dashi tayi sauri ta wanke wajen ta fito su hanne suna chan suna Hira basu ji karan Kakwazon aman nata ba.
Sai alokacin ta samu salama.
Allah yayi ikon sa Ko tasha wannan nganin bazai zauna acikinta ba sai ya fita saboda ba koda yaushe kake aikata abu kaci nasara ba daga Lokacin daka fara Hango nasara Daga lokacin kila Lokacin bayyanan wasu abubuwan ne.
La"asar nayi suka shirya suka tafi islamiya irin su mariya sai kallon Amina? suke domin Sa"adatu ta Fesa musu Amina ta auri yayansu mijin Anty Sakina to sanin Halin Amina Shiyaasa ba wanda ya Tareta da mganar har aka tashi.
Suna Dawowa gida Amina taso ta Tsaya wai taga Aba da Mallam Hajiya tace maza ta wuce idi ya maidata gida Mallam yana Hadeja sun je bude wani masallaci ba yanzu zai dawo ba shi da Aba Dole Amina taje tayima mamanmu sallama ko mangariba agidan ta tayi ta sai kunci take yi.
Aranar dai bata Hadu da Sakina ba sai Washegari da Idi ya maidota da yammah ta ganta afilo suka kalli juna kasa kasa kowacce ta kauda kanta bata Damu da abinci ba, tana ciko Cikinta Kafin ta Dawo da Safe kuma Tea kadai tashe sha watarana ma haka take Tafiya.
Asatin nan kaf haka Rayuwar Amina ta cigaba da gudana kudin hannunta sai da ta gama kashe ma su hanne gbadaya sannan Hankalinta ya kwanta Ranar jumma'a daga makaranta bata koma gida ba Ta jira sai da Mallam da Aba suka Dawo ta gaisheshesu Aba sai mamakin Amina yake a idonsa yaga kamar ta kara mishi girma sannan tayi hankali Kadan Mallam kuma kamar ya maidata Ciki saboda so Shiyasa bata koma gida ba sai Ranar Lahadi da yammah Mallam yace tayi kwana Biyu saboda Har da Hajiya bata so ba Ammh Tunda mallam ya saka baki shikenan.

Jafar kuwa sam ya manta da Kudin wayar da Danmallam ya barmasa ya siya ma Amina sai da Umar din yaji Shuru ya kirasa sannan ya Tuna Hakuri ya basa aranar bayan ya Dawo Daga wajen aiki ya biya ya siyama Amina waya karama Nokia sai washegari ya siya mata layi yayi mata Rigister sannan yazo ya kawoma Hajiya wayar Tunda Aminar na makaranta Hajiya ita har ta ma manta da Batun wayar sanda ya kawo mata Cikin wardrope dinta ta saka wayar sai kuma Allah ya mantar da ita har Amina ta dawo ba ta bata ba.

Wajen kwana Hudu da Jafar ya sanar ma da Danmallam ya siya waya ya kaima Hajiya ta bama Amina sannan ya Turama sa Layin Aminar sai dai tun Washegarin ranar yake ta faman kiran wayar a kashe sai ya fara Tunanin kodai Hajiya bata bama Amina wayar bane.?
Shi kuma ya kasa Hakuri ya rasa meke Damunsa Daidai da rana Daya Tunda ya Dawo madina Zuciyarsa bata manta Amina ba.
Wannan yarinyar daya ke kira kazama Kwaila itace ya kasa mantawa da ita ko Sakina da suka Dade tare baya jin nauyi da wani Damuwa da ita akan yadda yake ji kan Amina wani al"amari ne da Ubangiji ya barma kansa sani abu Daya ya sani yana matukar son yaji muryanta sannan yaji lafiyanta baya fatan ace yau yabar baya da kura.
Sannnan yarinyar itace ya Hada Abu mai muhimmanci da ita abunda bai Taba Hasaahen zai iya Faruwa Tsakaninsa da ita ba..
Abunda bai sani ba Addu"an Hajiya da Mallam ne Allah ya amsa sannan Addu"ar yaya ce Allah ya amsa ya Amintar da Ruhin Amina da Umaru waje Daya..Aminci na har Abada..!







*Janafty*
[10/19, 6:19 PM] +234 810 431 4972: *TFZB2008*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Amina tana rakube a falo tsoro duk ya cikata tunda Danmallam ya fita take duban idon su hanne ammh har Dare ya fara shiga ana gabda kiran sallar mangariba bata gansu ba Tsoronta Allah kada Dare yayi basu zo ba bazata iya kwana ita kadai ba Tana jin tsoro.
Tana zaune kan kujera a rakube saman kujera tana fiki fiki da ido,kamar mara gaskiya ko kwakwaran motsi bata yarda tayi ba, saboda tsoro,Saboda yanayin Datake ciki yasa ko karan Bude get bata ji ba sai ihun kiran sunanta da Hanne da Hamida suke mata kamar daga sama haka taji tana kyalla ido kawai taga Hanne da Hamida da kaya niki niki a Hannunsu,bata san sadda ta Diro daga kan kujera ba duk da yanayin Datake ciki bai sa ta tsaya ba Cikin Farin ciki da murnan da Rabonta da tayi har ta manta ta fada Jikin Hanne Tana Fadin"Oyoyo..oyoyo..!
Haka take fada sai hawaye sharr kafin ta Saki hanne ta Rumgume Hamida tana Fadin"Nayi kewarku..Nayi kewarku ba adadi Hanne da Hamida..!
Ta fada tana sharan kwallah suma sai da kwallar ta kawo musu suka kara Rumgumeta suna fadin muma mun yi matukar kewarki Amina.
Hannunsu taja tana fadin su kariso mana Bakinta yaki Rufuwa Saboda Murna basu Tsaya a falo ba sai Dakin Data kan gadon suka yada Zango Hanne da Hamida suna ta bin Gidan da Dakin da kallo.
Amina Murna yasa ta rasa me zata basu kallonsu tayi tana fadin"Kuna jin yunwa.?
Ga Abincin chan da ya danmallan ya siyomin kafin ya tafi zaku ci na Dauko muku..?
Binta kawai suke da kallo har ta Fice sai gata ta Dawo da shi a Hannunta Hade da maltina,tana shigowa Hamida tace"Mufa mun koshi Sai dai anjima..!
Amina ta Dago tana fadin"Hanne kema bazaki ci ba..?
Hanne tace"Mun ci abinci agida..Sannan ni ba abincin siya zan ci ba girkin Amarya Amina zan ci..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"ai sai ki ci abinci bayan matar gidan ta Kulle Kitchen dinta ta tafi bansan inda taje ba..!
Hamida ta zaro ido kafin tace"Bangane ba..?
Hanne ta karbe da cewa"Naji Hajiya na Fada ammh inaga ya Danmallam ya mata mgana ga keys din gidan gabadaya na wajen Hajiya tace nazo miki dashi..!
Amina ta tabe baki batayi mgana ba, Hamida da Hanne sai binta suke da kallon kurillah Amina sai ta Tsargu ta balla musu harara kafin tace"Wai kallon fa na miye..?
Hamida ta kalli Hanne suka Tsintsire da Dariya Amina sai ta sha kuni Tana Fadin"Bana son munafunci hanne da Hamida..!
Hamida tace"Ba wani gulma munga kinga sauya ne Amina kin rame sannan kinyi wani sanyi kamar bake ba..Eye Amarya Amaryan Ya danmallam to ya amarcin ne da Dadi ko ba Dadi..?
Amina sai Hararanta take yi kafin tace"Sai dai ango..Sannan ba Amarci ba amaro..!
Gabadayansu suka saka Dariya Farimciki ya cika Amina bakinta yaki Rufuwa Hanne ce tabi Dakin da kallo kafin tace"Dakin waye wannan hala..?
Amina tace"Na Sarood ne..!
Hamida tace"To ba kayanta a Dakin ne..?
Amina tace"Dillah kun isheni ko bari ma na Tambayi mutanen gida baku yi ba..Hamida shegen son jin kwakwaf to da kayanta zaki ganni aciki ne..?
Hamida na Dariya tace"Allah ya baki Hakuri Daga tambaya..!
Amina ta mata banza ta zauna kusa da Hanne tana Fadin"Hanne ya su Hajiya da Baba mallam..ke kuma Hamida yasu Mamanmu da Aba ina Jawaad su ya Zeenatu sun san an kawo ni nan..?
Ta fada a marairaice kamar zatayi kuka Hanne ta tura mata Ledan Hannunta tana fadin"Kowa lafiya..Ga Sakon hajiya tace mu kawo miki Sannan tana gaisheki sosai..!
Hamida ma tace"Mamanmu ma na gaisheki Aba da Jawaad duk suna lafiya sannan kowa yaji kina gidan ya Danmallam sunce duk a gaisheki..!
Sai Amina ta jawo leda ta fara fito da kaya bakinta yaki Rufuwa Fadi take yi Duk ni kadai wannan..?
Tana Daga kaya da Hijaban tana fadin"Wannan nasan aikin baba mallam ne..!
Ta daga su yaji da kayan da Hajiya ta Hadamata tace"Wannan kuma na Hajiya ne..!
Hanne tace"Kamar kin sani ta kasa sukuni komai sai tace na Amina ne..!
Amina sai hawayen Farinciki Fadi take nagode nagode sosai Kafin ta kalli Hamida tana fadin"Hamida ina abun Dadin da mamanmu ta bada ki kawo min bana son wasa fitomin dashu kafin raina ya bci..!
Tafada tana mikamata Hannu Har da shan kuni.
Hamida sai taji wani iri ta kasa mgana Domin ita dai mamanmu bata bata komai ta kawoma Aminar ba Hanne ce ta ceceta ta Dauko mata Turaran? wutan da mamanmu ta bata ta Saka ma Amina a Hannu tana fadin"Ga shi in ji mamanmu..!
Amina ta karba tana jin Dadi tace"Kai nagode sosai nayi kewarta sosai Allah Sarki mamanmu..!
Haka take ta fada suna Binta da kallo Sai da tagama gani duka sannan zata kwashi kayan ta maida a ledan Hamida ta hanata ta karba tana fadin"Bari na jera miki Cikin Kwabarki..!
Amima tace"Wayyo Anty Hamida i miss u..!
Ta fada tana Rumgumeta Hamida ta kwace jikinta tana fadin"Ni sakeni..Dole kiyi missing dina anan bamai miki nasani..!
Amina tace"Wlh kuwa kamar kinsani..Ya Danmallam ne in yayi mun masifarsa nake dan ninkewa shi baya son ganin Datti..
Hanne tace"Tab baki san kyamkyamin ya danmallam bane baya shiri da kazami sam Amina sai a Rage son jiki..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"In an ki fa..!?
Hanne ta mike tana Dariya tace"Sai a Daku..Don Wlh keda megidan ne ba ruwana.!
Jin haka yasa Amina tayi shuru su kuma suna mata Dariya Hamida ta Bude Wardrope din taganshi Tsab Cikin mamaki ta juyo tana kallon Amina kafin tace"Amina kece yau da gyaran kayanki..Lalle aure dabam ne..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Bani na gyara ba shi ya gyara ni fa tunda nazo gidan nan ban saki jikina ba sai yau dana ganku..!

Atare Hamida Da Hanne suka Hada baki wajen fadin"Shiwa..?
Amina ta kallesu kafun ta ce"Bansani ba..!
Lokaci Daya tana juya musu ido Dariya suka kwashemata da shi Hamida tace"Soyayya ruwan zuma ka sha ka bama masoyi..!
Amina taki cewa komai ta kyalesu suna ta mata iskanci Hanne ta taya Hamida suka gyara ma Amina kayanta suka jera nasu suma da suka zo dashi suka tsinke da labarin makarantar su da Amina sai dai ta tambayi wance da wance sai jin Dadi take yi Amina ta Dauka Aminene ta tafi kenan sai ta gane cewa har yanzu Aminene na nan Rayuwa ce ta sakata tayi sanyi nan da nan kewar makaranta ya kamata Cikin Jin Dadi tace"Ai ranar monday nima zan koma in ji ya Danmallam..!
Hanne tace"Naji yana fadama Hajiya.!
Hamida tace'Yauwa gwara ki Dawo Wlh daga Unity har islamiya ba Dadi baki Amina..!.
Amina tace"Nima bakusan yadda nake kuka in na tunaku bane kamar in yi Tsalle in gani agida..!
Hamida tace"Wlh muma Hajiya take Lallabamu da mallam in sukaga muna kuka ko mun Damu Saboda baki nan..!
Hira ce kawai ta Tsinke kamar bakin su bazai gaji ba Daga Dakin Amina Kitchen sukaje suka Bude Hanne ta Sassaka ma Amina su Samosa da danbun namanta a Fridge kar ya lalace suka kuma jera maltinan aciki Duk da akwai lemuka kala kala aciki Sannan suka Diba samosan Hamida ta soya musu.
Sai alokacin sukaje sukayi sallar mangariba Amina kamar an bata Kujeran Hajji Saboda murna yau gata ga Hanne ga hamida
Bayan sun idar da salla su ka koma Falo sukaci Takeway din nan suka hada da samosa suka kuma sha Tea suka Dora da maltina ransu Fes gashi akwai Wuta basu Dauke ba Amina bata manta da shan mganinta ba bayan sun yi sallar isha"i ta Dauko Zata sha su Hamida suka tambayeta tace tayi Zazzabi ne basu matsa mata ba Tunda daman sunga ta rame kadan sai suka yar da da mganarta..
Afalo suka baje suna Hira Hanne ta kuna kallo gabadaya Tasoshin na wa"azi ne dana addini Ta kashe ta Dawo ta zauna tana fadin"Na manta gidan ustazai ne nan ba"a kallo..!
Hamida ta yi Dariya kafin tace"Ko agidanku ai ba kallon kike ba..!
Amina tace"Gulma da iyayin Hanne mana..ku wai ina Sa"adatu ne..?
Hanne tace"Tana nan mun manta da mun mata mgana mun zo da ita..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"Wlh da kuwa daga ke har ita ba matsiyaciyar da zata shigomin gida..!
Hanne ta Bude baki ita da Hamida kafin su kalli juna su hada baki suna Fadin"Uhm masu gida da miji..ammh nan ana kuka ana ba"a so..!
Ashe dai ana son ya Danmallam din..!.Hanne ta karishe Fada tana Dariya Amina ta karkace baki tace"Allah ya isa Tsakanina daku..Kuma Wlh wuta..!
Suka karisa mata da bal bal..!
Suna Dariya ta tashi tana jefansu da filon Kujera tana fadin"Munafukai kawai..!
Sai da suka gaji suka koma suka zauna Hamida tace"Wato Hanne Halin mutum zanen dutse Amina ko ta Sauya akwai wasu hallayanta da Har Abada bazata sauya su ba..!
Hanne tace"Kamar Taurin kai da Tsiwa da Fada..!
Amina ta kallesu ta harare su batayi mgana ita kanta ta zata ta koma Ruwan sanyi ammh Sanadin zuwansu yasa ta Fahimci Aminene bata Mutu ba Doguwar suma tayi ta Fara Farfadowa yanzu.
Sai kusan goma na Dare suka je suka kwanta achan dim ma wata Hirar suka Dasa tuna irin abubuwan da sukayi suke yi suna Dariya Amina in ta Fara Dariyan mugunta har da Hawaye yau gata ga Hanne da Hamida suna kwance waje Daya Amina ce a Tsakiya Hamida tace"Wai har yanzu baki daina shegen tsoron nan ba..Ke in ba kin kwakwume mutum ba bakya iya barci..?
Hanne tace"Ga ya danmallam sai ta Rika kwantamai abaya in suna barci..!
Amima ta balla musu harara kafin ta juya ta yi Daidai hannunta kan Cikin Hanne kafanta kan kafafun Hamida suna Tureta tana kara Dorawa Dole suka gaji suka kyaleta Daga haka sukayi addu"an barci suka kwanta.
Dayake sun riga sun saba da tashin asuba kiran sallar farko suka tashi suka yi alwala sukayi Raka"atul Fijir sukayi sallah sannan suka koma barci su Hanne an samu waje sai goma na Safe suka tashi suka shiga Kitchen sune har store sai da suka Bude babu abunda babu na kayan abinci kamar ma ba"a Dade da Zuba su.
dankalin Turawa Amina tace su soya da kwai haka kuwa akayi Hamida ta Fere Dankalin ita da Amina Hanne

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login