Showing 27001 words to 30000 words out of 141906 words

Chapter 10 - Ta Fita Zakka Part 2

10 Oct 2024

4142

ya Dade bata taba amfani dashi ba tamikama hanne domin bata taba Zaton Sa"idu yayi zencen ya bata kudi da Hajiya ba. ganin suna ta Murna yasa batace komai ba gwara Hamidan taje ta gano wani irin Halin da Amina ke Ciki don ta tabbata Sakina bazata mata wasa ba ita fa a gayyas gida yanzu ya Rage daga ita sai mijinta Jawaad yanzu in Aba ya Dawo yadaina zuwa saboda samunsa tayi tajamai kunni yaro kuma da Tsoro ko Aba ya Dawo ko ya kirasa daya zo sai yace yana da Homework sai ya tafi hakan yafi ma Mamammu Duniyarta take so taci ita kadai bata san Takura.









*Janafty*
[10/19, 6:19 PM] +234 810 431 4972: *TFZB2009*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Hamida da Hanne cikin rawan jiki suka gyara komai Hanne ta share falo ta goge shi tas hamida kuma ta kintsa Kitchen din ta wanke kwanukan da suka bata ta goge kitchen lokacin har an fara sallar mangariba a masallatai yasa suka wuce dakin da Amina take suka isketa Ta fara salla,suma alwalan suka Dauro suka zo suka jera da Amina suka tada salla har suka idar Amina bata musu mgana ba suma ganinta cikin wannan yanayin yasa suka mata shuru.
Tana ganinsu suna hada kaya sai ranta ya kara baci Haka kurum take jin wani zafin zuciya wanda ko a baya ba irinsa take ji ba tasan dai tana Saurin Hasala ammh Bata da Saurin Harzuka kamar na yanzu sai ta Danganta haka da Tafiyar su Hanne Abunda bata sani ba wannan zafin zuciyar da aka kara mata ne maimakon tayi shi ga wanda akayi Domin sa sai ya kuskuremai Bashi a kusa da ita sai abun zai tsaya ga wanda ke kusa da ita da kuma wanda ke bata mata rai a kusa.
Sallar da tayi ne ma yasa taji dan Dama Dama ammh ranta yagama baci da abunda Sakina tayi mata yau ji take yi daman ta Tabata da sunan daambe da ta gane bata da wayau a yadda take jin kanta da karfi sai sun kwashi yan kallo domin karfin jikinta ya Dawo sannan ta warke kasanta ma batajin wani ciwo ruwan zafi da mgangunar nan sun tainaka mata wajen dawowa da ita Daidai shiyasa ko su Hanne basu Fahimci komai ba tota ina ma zasu gane..?
Amina ta fi su Budewar ido kan irin abubuwan nan saboda ita tana karance karancen Littafan hausa su kuma fa dukum ne su basu riga sun san wasu abubuwan kamar yadda ta sani ba.
Suna cikin Hada kayan ne suka ji knooking daga kofar falon Amina ta Dago tana kallonsu hanne ma ta kalleta kafin ta mike tana fadin"Ina ga Idi ne..!
Ba jimawa sai ga shi ta dawo tana Fadin"Shine Hamida..Hajiya tace maza maza ya Daukomu gobe akwai makaranta..!
Hamida batace komai ba ta Zura Hijabinta haka Hanne suka Dauki Ledan kayansu Hamida ta kalli Amina Dake Zaune tana kallonsu tace"Amina mu zamu tafi..
Amina tayi kamar bata ji su ba kuka taji yana neman tasomata Hanne ce Cikin karfin hali tace"Kiyi hakuri ai gobe zamu biyo mu Dauke ki..Ki shirya da wuri..!
Hamida da Hanne suma karfin hali suke kada su yi kuka ganin yadda Amina Tayi ganin ta musu banza yasa Hanne taja Hannun Hamida suka Fice Daga Dakin Amina na ganin haka ta mike Zaraf ta biyosu falon tana Fadin"Yanzu wai tafiya zaku yi..?
Ku bari gobe mana basai mu tafi makarantar tare ba..!
Hanne tace"To ai uniform din mu na gida kuma kinga Hajiya ce ta aiko a Daukemu..!
Amina bata kara mgana ba kawai ta Juya ta koma Dakinta ta Zauna gefen gado sai kuka wiwi kamar wacce aka Daketa Tana jin karan Bude get tasan su Hanne sun tafi kawai sai ta kwanta Saman Cafet ta cigaba da kukanta kuka mai Cin rai rabin kukan na kewa ne da Zaman kadaici rabin kukam kuma na kuncin zuciyar da ta rasa Dalilinsa wani Kululune ya Tsaya mata? arai yaki wucewa tana Tunanin in tayi kuka zata samu sauki.

Sakina kuwa ko da ta shiga Dakinta ko gani batayi Ranta ya gama baci tana Tunanin karamar yarinya kazama kamar Amina ce zata tsaya tana Zaginta Lalle sai ta gane bata da wayau Zata Kira Habibi ta Fadamai Rashin kunyar Amina sai ya Dauki mataki akanta domin ita bazata iya Zama da ita haka ba Allah nagani.
Wayarta ta Dauka ta kira Lambarsa ta Saudiya ta shiga sau biyu bai Dauka ba ta Duba Lokaci bakwai Saura na Dare su achan zai zama tara da wani abu kenan bai isa ya kwanta ba Duk da Tun da ya tafi sai jiya ta kirasa suka gaisa bai tsawaita mganar ba yace mata yana Aji ne in ya koma gida zai kirata kuma bai kara kiranta ba.
Ganin bai Dauka ba Sarood ta kira ita kan ta Dauka suka gaisa take tambayanta Habibi ta sanar da ita baya nan ya tafi Cikin gari masallaci Har yanzu bai shigo ba.
Sakina ta gyara zama tana cema Sarood? ta rokar mata Umar don Allah ya zo ya Dauketa yaki komawa da ita Madina Sarood tace mata kawai zata mai mgana da haka suka rabu Sakinar ta Lura kamar Sarood din bata son Wata Doguwar magana da ita tana sota kawomata Labarin Amina sai tayi Saurin Dakile mganar da cewa Tana girki ne kada ya kone..
Abunda bata sani ba ita kanta Sarood din tunda ya Dawo sama sama suke domin daman kafin su tafi sun yi Rigimar tahowa tun Tarkon da Sakina ta Hadama mata ita kuma ta Fada har sai da Mahaifinta ya shiga mganar To kishi da kuma takaicin abunda ke Faruwa Tsakaninamsu ya Rufemata ido gani take yi yana chan yana jin Dadinsa da Sakina da Amaryansa ita kuma ya barta anan ita bata ga Tsuntsun ba ga Tarko shiyasa taso ta Biyosa batare da sanin ko iyayanta nata ba Sai dai kalmar daya fadamata na sai tazo ne ya bata tsoro yasa ta fasa zuwa Tasan Halinsa kaifi Daya ne.
To kwana Hudu Tsakani ya Dawo Tunda ya Dawo ta sakamai Rigimar ita bazata yarda ba, da gangan yake yi Ba wai bazai iya kadaicewa da ita bane meyasa shi da Sakina Lafiya kuma gashi har yayi amarya itama tasan ai lafiya kalau meyasa sai itane bazai iya Raba ba .
Alokacin akwai gajiya tare da shi,Shiyasa bai biyemata ba sannan kuma ta wani Fannin tana da gaskiya ta wani Fanni kuma bata dashi Saboda ai ba Laifinsa bane sai da yace su sanar da manya mganar in da cutarwa tace taji ta gani sai kuma Daga baya ta Bullo da wata mgana Ba domin ma Su din ba su cika yarda da Sihiri ba, da haka yasan zatace Duk da shima lamarin ya bashi mamaki ammh bai Taba Zargin wani ba ga Allah kadai ya Dogara shiyasa yake Neman waraka daga garesa..!

******

Amina batayi wani barcin kirki ba Saboda kuncin zuciya sannan ta dinga Tsorata acikin barcinta da Daddare barcinta sai ya zama sama sama ne tasan a gida bata iya barci sai acikin mutane ammh Tsoronta bakai na yanzu ba ko ya ta kwanta ta fara barci sai taji kamar ana Tabata sai ta Tashi a Firgice daganan sai kuka in tayi addu"a ne ta koma sai barcin nata yadan yi Tsayi.
Yau da wuri tatashi ga rashin barci sannan tasa ka Komawa makaranta aranta yau din tayi wankanta sannan tayi sallar asuba Saboda zumudi Amina ko Karyawa bata tsaya tayi ba ta Saka Uniform dinta dake goge Daman Hamida tun agida ta goge mata ta fito da Jakar makarantar data Islamiya ta tura ta islamiyar da Hijabin cikin jakarta saboda chan zata zauna sai sun dawo daga islamiyar yammah Ta saka Safa da Takalminta ko Falo bata fita ba kuma bata ji motsin Sakina ba.
Tun bakwai na Safe ta gama shiryawa tana zaman jiran su Hanne cikin kudin da Danmallam ya bata ta Dauki Dubu Daya yau zasu ci su sha ita dasu Hanne su Sa"adatu kuma Sai dai suga anayi yan bakinciki.
Har takwas saura sai ta fara Tunanin ko dai sun tafi ne sun barta ayadda tayi Shirin zuwa makaranta yau sai ta kama gabanta don bazata fasa ba Kamar daga sama taji Hon din mota dayake motar tasu akwai kara bata gama Tantancewa ba taji Muryan Hanne na Kiranta tayi Zaraf ta Fito Daga Dakinta bayan ta kulle kofar Hanne na ganinta ta washe baki Tana Fadin"Amina Aminene ikon Allah..!
Amina tayi Fari da ido kafin tace"Kwarai ba dai ta mutum ba sai ta Allah wlh..kainuwa Dashen Allah .!
Hanne tayi Dariya kafin ta kalli jakar Amina Datake neman rinjayanta tace"Meye kika sako ajakar ko Abun Dadi ne na amare..?
Tafada sanda suka fice Daga Falon Amina tace"Uban na Amaren ne..Hijabin islamiya ne da Jakata..!
Hanne tace"Kin ga kuwa Sai da Hajiya tace na Tuna miki kada ki manta..!
Amina tace"Ina zan manta..yarda na kosa na ganni a makaranta..!
Hanne na Dariya yace"Yau watarana Amina na murna zata makaranta..!
Amina ta murguda mata baki kafin tace"Yau Litini to munafuka..!
Hanne na Dariya suka fita Daga gidan Dayake Idin bai shigo get ba Tunda suka fito yan motar suka sako ido suna bin Amina da kallo musamman Sa"adatu.
Amina na shiga motar Idi kawai ta gaisar banda su Akilu da suka wani kame agaba Zubairu ne yace"Amina ba gaisuwa..?
Wani kallon Tara saura kwata tayi mai kafin ta Dauke kanta Akilu yace"Kaima da wata mgana..So kake ta raina ka.
Ta karo iskanci mana tana ganin ta matar ya Danmallam..!
Tana jinsu ta musu banza kusa da Hamida ta zauna tana fadin"Baki ganni bane ko kimin oyoyo..!
Hamida tace"Tunda kika shigo nake washe miki baki kikayi kamar baki ganni ba..!
Ta Rumgume Hamida tana fadin"Sorry ban lura ba..Wata ke min kallon banza na maida mata..
Ta fada tana Hararan Sa"adatu Dake kallonta Daga sama har kasa Sabeeha kanwarta ce tace"Ya Amina daman gidan Anty Sakina kika dawo..?
Amina tace"Eh Sabeeha baki sani ba..?
Yarinya ta girgiza kai kafin tace"Shiyasa bana ganinki..!
Sa"adatu ne ta Harari kanwarta Shiyasa tayi shuru Hanne kusa da Sa"adatu ta zauna Amina ta kalleta Cikin mamaki kafin tayi ma Hamida rada tana fadin"Hanne fa munafuka ce..Dubeta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ita adole mai yar"uwa..!
Hamidai dai Dariya tayi batace komai ba.
Har suka isa makaranta Amina bata kara ma Hanne mgana ba da aka Sauke su ma ana Assamble ne Hanne na ma Amina mgana tayi kamar bata jita ba ta Nufi Zainab isa Dake Faman Daga mata Hannu Amina bakinta yaki Rufuwa ganinta a makaranta ashe ma karatun wani Lokaci zuwansa Rahma ne sai da aka kaita wannan kurkukun gidan nan ta san da haka.
Ba dadewa aka gama Assamble din suka Tafi aji yan ajin su Amina sai mata ya jiki suke saboda Rashin Lafiya su Hanne suka ce tayi Saboda Hajiya ta gargade su kada su sake suce aure tayi har Sa"adatu sai da ta kira ta ja mata kunne.
Gabadaya Amina sai taji ta kamar a aljannah ta saki jikinta sosai ana tashi Break taje ajinsu Hanne ta ta jasu Shagon makaranta ta siya musu banza ta siya musu wofi Hamida ke Fadin"Amina ina kika samu kudi haka.?
Amina ta Kalleta tana shan Nutrimilk din data siya tace"Mijina..!.
Tafada Cikin gatse Hamida da Hanne suka kalli juna kafin su Tsintsire Da Dariya Hanne tace"masu miji..To tunda ya bar mana kudi zamu ci mu sha ko Hamida..!?
Suka tafa atare suna Dariya Amina tace"Kuma kika bama sa"adatu abuna Alah ya isa Hanne..!
Hanne tace"kai wannan kiyayyar Dake Tsakaninki da Sa"adatu bansan irinta ba..!
Amina ta wuce fuu tana fadin"Kika dai bata in na yafe Allah tsinan kin ji ma na fada miki..!
Daga haka ta koma ajinsu ta siya ma zainab maltina ta bata,Daman sun fi Shakuwa tun Jss1 tana juran Jidalin Amina Sa"adatu na shigowa Amina sai da ta kalleta sannan ta ga Nutri dinta tana sha aranta tace bakinciki kan sai dai ya kasheki Amina kam tafi karfinki haka kurum ita Amina bata kaunar sa"adatu kuma hakan ya samo asali ne da yadda ta Tsani Anty Amarya.
Sai biyu da rabi Idi yaje ya Dauko su suka koma gida mota na Tsayawa Amina ta Dira sai gida Hamida da Hanne suka bita da kallo Akilu ya rike baki yana fadin"Ya dammallam dai an Hadasa da kwaila..!
Shi da zubairu sai Dariya suke yi.
Amina da gudu ta shiga gida tana Kiran sunan mamanmu da Karfi da Jawaad taci karo ya fito daga Kitchen yana shan ruwa yana ganinta ya jefar da Kofin hannunsa ya Nufeta yana Fadin"Yaya Amina oyoyo.!
Amina ta jefar da Jaka ta Cafeshi Taso ta Dagasa sama ne taji yafi karfinta ta Sauke shi tana fadin"Jawaad din yaya ya kara girma..!
Cike da Tsantsan murnan yaga yar"uwansa yace"Ya Amina ina ta kuka da baki nan ina ta cema Aba ya kaini wajenki yace ba yanzu ba..!
Sai Amina taji kwalla ta taso mata ta Kama Jawaad ta Rumgume cikin wani yanayi take fadin"Watarana zaka zo inda nike kaji jawaaad..!
Kai ya gyada mata ita kuma tace"Daga yau kullum zaka dinga ganina kaji ko..?
Baki ya washe yana fadin"Da gaske..?
Jakarta ta Dauko ta Zage ta fito da sweets din data siyamai ta bashi ya amsa yana ta Tsalle tana Dago kanta suka Hada ido da mamanmu da tunda ta shigo da Kwakwazo ta jita tana kuryan Daki tana Faman Lissafim kudin da Aba ya bata yau da Safe na siyan Turaranta Datace mai ya kare ba gaddama ya tambayeta kudin tace mai 10k ya ciro ya bata,ita kam yanzu bata cikin wani bakinciki Burinta ya cika in ma bai cika ba kadan ya Rage mata.
Alokacin da Amina ke mgana da Jawaad hararansu take yi tana Tsine musu acikin ranta in ma tana da wata Damuwa sune su Jaleela suna gidan auransu sai su Dade basu zo ba Jawaad ne da Jafar? wanda har yanzu Ta kasa shan gabansa ta Lura shima a Tsaye yake ammh zai yi Laushi Tunda Sa"idu yayi Laushi Amina Datake murnan ta Rabu da ita kuma sai gata Koda yake daman Ai Jiya ta shiga wajen Hajiya gyara kanta Tunda Hamida ta Dawo ta bata Labarin sha tara na arzikin da mallam da Hajiya suka Hadama Amina sai taji ta muzanta kafin Hajiya ta fara Dora zargin akanta yasa ta shiga tana mata kame kamen bata san da zuwansu Hamida ba shiyasa bata siya mata komai ba ammh Zata? siya mata su humra ta kai mata da kanta kudi ne bashi a Hannunta shiyasa.
Hajiya babba bata kawo komai aranta ba sai ta nuna ma Mamanmu bakomai kada ta Damu Amina bata bukatar komai yanzu to anan nema Hajiyar ke fadamata Tsarin Amina zata koma makaranta sannan nan zata Dinga wuni sai yammah in sun Taso islamiya sai idi ya maidata gida.

Amina na hada ido da Mamanmu tayi Falati da Jakarta ta Nufeta cikin murna tana fadin"Oyoyo mamammu..!
Itama ganin haka sai ta saki Ranta Bakinta har kunne ta Rike Amina ta rumgumeta tana fadin"Oyoyo yata Amina..Nayi kewarki..!
Amina tace"Nima haka mamanmu..kullum sai nayi kuka in na Tuna daku ina Aba..!
Ta fada tana Sakin mamanmu Daidai Lokacin da Hamida ta shigo.
Mamanmu tace"Aba dinku yana Lafiya Amina ya bakon waje..?
Hamida ta fadamin irin Dibar albarkar da Shegiyar Sakinar nan tayi muku..Nidai ki Daina kulata kada ta nakasamin ke baki kaita karfi ba..!
Amina tayi Dariya kafin tace"Haba mamanmu ita din banza..?Wlj ba cika baki ba ni Amina Aminene nafi karfinta wlh ta taba nin watarana Tagani..Sai ta raina kanta..!
Mamanmu ta saki baki tana kallon Amina kawai gabanta na Faduwa ashe bakinta bai mutu ba jiya da Hamida ke fada mata ta sha mamaki ta Kira Anty Amarya sukayi mgana tace kokarinta Daya Umar yazo ya tafi da Sakina sai Amina taci iskancinta ita kadai Mamanmu tace tabbas..!

Hamida ita ta Dauke ma Amina Jaka takai Dakinsu Mamanmu kuma ta shiga kitchen ta Debo mata abiinci da ruwa,Ta sakata gaba kamar ta bata a baki sai Dukan ruwan cikinta take yi ko zata ji wani abu Hamida Dakin su ta shige Tayi sallah ta Debo abinci dama ta shigo Dakin da suke korarta Mamanmu tayi saboda tana so sai taji yanayin zaman Amina da Danmallam kafin ya koma Madina.
Shiyasa Amina na cin abincinta Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Ni ko Amina Allah yasa Danmallam dai kafin ya koma bai miki komai ba ko..?
Gaban Amina ya fadi ta Dakata da cin abinci ta Dago tana kallon mamanmu Cikin mamaki ita tunaninta ko ta Fahimci abunda ya shiga Tsakaninsu ne yasa cikin sauri tace"Name ne mamammu..?
Ni babu abunda yayi min..!
Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Yauwa Allah yasa ma baya shiga Harkanki..!
Amina tace"To ina ruwana dasu..!
Ni har ya tafi ma ban gansa ba..!
Ya cika fada haka yayi tamin masifa ranar da muka tafi Daganan..!

Mamanmu taji Dadin haka yasa tace"To ai kin gani irin wannan abun na Gudar miki yasa naso araba wannan auran kika ki bani Dama..!
Amina tace"Bakomai Mamanmu hajiya da Mallam sun wuce komai a wajenmu..Sannan ni nayi alkwarin Aba bazai kara bacin rai saboda ni ba..!

Mamanmu tayi shuru tana kallon Amina kafin tace"Hakane kuma ammh ki Daina tankama Sakina Da shi din ne dai da nace ki yi tamai Fitsara har ya gaji ya sako min ke na aura miki mai sonki Aminullah..!
Amina tayi Tsai tana kallonta sai taji bata ji Dadi ba datace a asakota Saki fa ba Kyau ance sai al'arshin Allah ya girgiza sannan ita karan Hauka ya Cijeta? da zata ma ya Danmallam rashin kunya sai dai Sakinar itace Daidai da ita.
Daganan bata kara mgana ba Mamanmu kuma sai janta take da Labari Amina ba domin Rokon Umar ta Boyema mamammu komai ba,,sai saboda Tana jin kunyarta da Tunanin in taji abunda ya faru zata yi mata Fada kila ma ranta ya baci shiyasa bata gayamata ba..
Ita kuma mamanmu adole Allah zatayi ma wayau batasan bakin Alkalami ya riga ya bushe ba,Haduwar jini ta Haifar da gudan jinin da zai yi Sanadiyar Fallasan duka sirrukansu.

Amina sai da taci ta koshi tayi sallah kan gadonta ta fada tana Fadin"Nayi kewarka gado na..!
Take fada tana Shafa gadon Hamida na kallonta kafin tace"Sai a Daukesa akai miki chan..!
Amina tace"Da naji dadi kuwa..!
Hamida ce tace"Hajiya sai da tambayeki fa Amina..!
Amina ta mike Tana fadin"Bari na shiga..!
Uniform dinta ta cire ta sauya dana gida akwai wasu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login