Showing 39001 words to 40828 words out of 40828 words

Chapter 14 - IKLAS BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Maman Noorul

21 Aug 2025

202

tayi ta had'e kafafu


Bayan zaman ta da Minti biyar wayarta yayi kara Wanda alarm ne ta saks


D'agawa tayi tace"hello aisha ya kike?


Eh gobe zan shigo minna ai da yau na so zuwa amma dare yayi"


Shiru tayi na wani sakonni alamun tana jin abin da ake fad'a


Can kuma tace"wani aure ai aure na ya mutu,ai kin san tun muna school na tsani namiji mai dukar mace"


Kallonta yayi da sauri sai kuma ya basar


Tace"hmm ai dana fito zan koma wajen tsohon saurayi na"


Tashi yayi cike da kishi ya d'aga hanun zai mareta,ta rike hanun tace"haba ba girman ka bane malam,duk namiji mai dukar mace bai cika namiji ba,in dambe kake son yi sai kaje waje ka sami namiji irin ka Ku fafata"tsayawa yayi yana kallonta da mamaki tunani yake Islam ne ko dai wata ne"


Katse shi tayi da cewa"kuma na baka daga yau zuwa gobe da safe ka rubuta mun saki"


Cikin tashin hankali amma ya dake yace"meyasa zan sake ki"


Tace"saboda bana sonka"


Kallonta yayi yace"toh meyasa baki sona?"


Tace"saboda baka iya soyyaya ba,nagaji da rayuwa irin na dabbobi,shiyasa ka sake ni shi zai fi mana alkhairi"


Haurawa tayi ta barshi tsaye,zama yayi yana cewa"wallahi ba zan iya sakin ki ba,ina son ki ba zan iya rayuwa babu ke ba"


Itako bayan barin shi a falo d'akinta ta shiga ta kwanta a gado tace"ashe yana sona "domin ta gan tashin hankali karara a cikin idonshi


IKLAS ne zaune a falo tana cin indomie RAYHAN ya shigo ya ganta zaune yace" wiffy yau baza ayi welcoming d'ina bane?"


Tace"yi hakuri baby ka ya hana ni"


Yace"na lura kin fison babyn nan fiye dani ko"


Tace"ni na isa,toh bari in taso "tashi tayi taje ta rungumeshi


Tace"ina nawal?"


Yace"tana wajen ummi"


Tace"ummi dai bata son bamu nawal fa ni kuma ina bukatar ta"


Yace"ai gomma ta zauna can kar ta hana mu sakewa,wiffy muje ciki in gaida baby na in bashi ice cream"


Murmushi tayi tace"kai fa akwai son harka"


Misallin karfe 9:pm islam ta shiga kicin indomie ta dafa dai-dai bakinta ta zaune a centre rock ta fara ci


Yana saukowa ya kalli dining wayam yace"ina abinci na?"


Tace"ban dafa da kai ba"


Shiru yayi tana gamawa ta kai plate kicin ta fito ta haura sama direct d'akin ta,tashiga ta kulle


Shiko kasa barci yayi sai juyi yake yi fita yace"me yariyar nan ke nufi be?ni fa gaskiya ba zan iya bata hakuri ba" fita yayi hanya d'akinta murd'a kofa yayi ya jita a kulle


Yace"nashiga uku ashe da gaske take"


Washe gari misallin karfe 7:am na safe ya Islam ta shirya cikin gown d'in atamfa hijabi ta saka ta d'auki trolley ta kai falon ta haura kuma direct d'akin shi taje rike da biro da takarda a zaune ta same shi


Mikame takardar tayi


Yace"me zanyi dashi"


Tace "sakin zaka rubuta na rigada na hana kayana yana falo sauran za a turo mota"


Sake takarda yayi yace"........


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share


πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.




Na sadaukar da wanan page d'in zuwa ga masoyana abin alfari na ina jin dadin comment d'inku sosai Allah ya bar mu tare.ina yin Ku irin sosai d'in nan nagode da add'oin ku


πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


πŸ…Ώ9⃣9⃣
&
1⃣0⃣0⃣


Bismillahir Rahmani Rahim


Sake takarda yayi ta fad'i a kasa


Yace"haba matata,me yayi zafi haka"


Wani tsayi ya ziyarci zuciyarta for the first ya kirata da matan shi,a zahiri kuma ta fara kalle kalle


Tace"dawa kakeyi"


Yace"common da ke nike"


Tace"lallai yau za a duba kwakwalwar ka yaushe ka bani wanan matsayi"


Yace"baby please zauna mu dai-daita junan mu please my angel"


Tace"babu wani dai-daitawa tsakanin ni na da kai,ni dai takarda na zaka bani in je gida a aura mun mai sona "


Yace"toh mai zaki fad'awa Abba da ummi ki duba fa auren mu ko wata biyu beyi ba"


Tace"gaskiya mana"zaro ido yayi yace"gaskiya me?"


Tace "gaskiyar baka kula dani baka damu da damuwata ba,amfani na a wajen ka shine inyi maka girki da biya ma bukata amma ni baka damu da bukata ta ba,kuma zuwa kake yi mun kamar dabba babu wasa ko hira tsakanina da kai,bamu taba kwana d'aki d'aya da kai ba daka biya bukatar ficewa kakeyi nagaji gaskiya ka bani takarda na intafi"


Yace"yanzu baza ki ji kunyar fad'a masu irin wanan maganganun ba?"


Tace"kunyar me?ai iyaye na ne babu boye boye tsakanina dasu ko naji kunyar abba bazan ji na ummi ba,gomma na fad'a masu gomma in fad'i a halaka"


Shiru yayi a ranshi yace"bazan iya sakin ki ba Islam ba zan iya rayuwa babu ke ba"jin yayi shi yasa tace" kai fa nike jira bana son dare yayi mun a hanya,bari ma in tafi tunda naga baka da niyar yi min abin da na bukata,sai ka ji sammaci a kotu"


Kama hanya tayi zata fita ya rike mata hanun


Cikin tashin hakali yace"haba baby yi hakuri mana na tuba ki dubi condition d'inki mana"kallonshi tayi tace"wani condition?"


Yace"dear you are pregnant"


Tace"and so?"


Yace"toh ya zakiyi da baby na?"


Tace"ina haifo shi zan kawo maka d'anka ko yar ka inyi aure na"


Zaro ido yayi yace"yanzu har da jariri ma bazaki tausaya ma ba ko baki sona kiyi zaman yaran da zaki haifa mana"


Dariyar rainin hankali tayi tace"dama da wanan ake cutar mu da wani abu ya faru sai ka ji ance kayi zaman yara toh wallahi ba wani zaman yara da zanyi in sun girma zasu nime ni"


Da yaga dai da gaske take yi,rungumeta yayi ta fara kokari kwace kanta had'e bakin su yayi ya fara romancing d'inta


Har jikinta ya fara sanyi amma tana tuna abubuwan da yayi mata a ranta tace"ashe dama ya iya iskanci ne"


Ture shi tayi cikin mutuwar jiki yace"baby please ki saurare ni"


Tace"waye baby? If you think you can bribe me with pet names you are wasting your time you think this romance will work never,my mind is made up boy"


A ranshi yace"na shiga uku yau,bari dai in sauke girman kai in roke ta"


Yana ganin zata fita ya sha gaban ta yace"ki dubi girman Allah ki yafe mun matata wallahi ina son ki kamar raina bazan iya rayuwa babu ke ba please ki taimake ni,I will even be on my knees if you want me to,I promise to change to whatever you want"shiru tayi zata yi tafiya ya sunguna ya rike mata kafa"


Bayan sati biyu IKLAS ne zaune kujera RAYHAN na ja mata kafa


Yace"wiffy muje kicin muyi girki kigan dare nayi"


Tace"toh mijina"daukanta yayi kamar doli a kicin ya ajiye ta


Yace"toh me baby na zai ci yau"


Tace"fried platain"


Yace"OK let me make it for you"




'Bangaren mahmud kuwa anyi aiki cikin ikon Allah ya samu lafiya sai dai ba a sallame su ba Dan ana kan duba shi"




Mahmud ne zaune a gadon asibiti yace"baby"


Zaliha tace"na'am"


Yace" in two weeks time za a sallame mu,daga nan mu tafi dubai honey moon kafin mu koma gida ko"


Murmushi tayi tace"kullum dai maganan ka honey moon kamar Wanda ya auri cikekiyar budurwa"


B'ata rai yayi yace"bana hanaki maganan nan ba"


Tace"sorry"


Minal ko mulki take son ranta dan harta wanka sai Abdul yayi mata kafin ya tafi aiki inya dawo kuma ya sakeyi


Yau yana dawowa daga office yamm ganta kwance a falo


Kallonta yayi ya girgiza kai yace"tashi kije ki girka mana abinci"


Ya mutsa fuska tayi tace" zazzabi nikeji"


Yace"wallahi baki isa ba,kwana na nawa muna cin abinci waje nagaji ai ke likita ne kiyi maganin zazzabi mana"




Minal zatayi magana ya katseta da bani son musu


Tashi tayi ta guguni kallonta yayi harta shige kicin yace"dama nasan karya kike yi"




Cikin sati biyu sultan ya wahala dan duk inda yaso Islam ta saurare shi,ki tayi duk ya fita hankalinshi ko aiki baya zuwa,


Yau ma kamar kullum tana zaune a falo tana kallon film ya sauko gabanta ya zo ya sunguna


Yace" baby ki yafe mun please"


Ko kallon shi bata yi ba,ganin haka yasa yayi sauri had'e bakin su wuri guda


Romancing d'inta ya farayi had'e da bud'e zip d'inta fara wasa da nonuwanta yayi abin ka da mai cikin jaraba tuni ta fara ansa sakonin shi dama daurewa kawai takeyi kwana biyu nan


Ganin jikinta yayi sanyi yasa ya d'auketa zuwa d'akinshi ya kwantar ya cigaba da abin da yake yi


Bayan komai ya faru ya koma gafe yana mayar da numfashi"


Jawo ta yayi yace"baby nagode da kika yafe mun,na tuba wallahi please don't live me"


Shiru tayi bata ce komai ba yace"dear say something"


Tace"Allah ya yafe mana baki d'aya"


Yace"amin"




D'aukanta yayi ya kaita bayi yayi mata wanka


Bayan wata bakwai IKLAS ne zaune da katon cikin ta domin ta shiga wata tara


RAYHAN yace"tashi mujejan kafa"


Tace"no ba zan iya zuwa ba bayana na ciwo"




Yace"OK"




Bayan awa uku IKLAS ta fara nakuda ihu ta sake RAYHAN da ke kicin yana had'a masu abinci




Da sauri ya kashe gas ya fito yace"wiffy yaya ne"


Tace"please ka taimake ni mutuwa zanyi bayana da cikina ciwo"




Cikin sauri ya haura sama ya fito da jaka,kaiwa mota yayi ya dawo ya dauke ta sai asibiti




Bayan awa biyu ta haifo santalelen d'anta murna a wajen RAYHAN kamar ya haniye ta da yaron datayi motsi sai yace"ba dai masala ko"karshe sands ummi ta kore shi"


Baya sati d'aya akayi suna anci ansha yaro yaci sunan daddy amma za a ta Koran shi da Abba




Bayan su RAYHAN ya d'auko nawal dan yana son kan yaranshi ya hadu


Bayan haihuwa IKLAS da sati uku minal ta haifa baby girl ranan suna yariya taxi sunan umma Abdul maryam amma suna ce mata intesar




Zaliha ko Nada ciki wata hudu Islam ko wata bakwai kuma tana samu cikeken kulawa wajen sultan






Bayan shekara bakwai IKLAS ne zaune da minal har da Islam zaliha ma na nan a gidan ummi sai hira suke dan yanzu an zama manya mata yara ne a falo suna wasa


A yanzu IKLAS na da yara biyar maza uku mata biyu nawal ne cikon na shida


Minal yara hudu maza biyu mata biyu da sabon ciki


Islam yara uku duka maza




Zaliha yara biyu da tsohon ciki


Kallonsu IKLAS tayi tace"next week zamu tafi Paris honeymoon"


Harararta minal tayi tace"wani honeymoon sufai sufai daku"


IKLAS tace"waye ce miki soyyaya na sufa?"


Zaliha tace"toh wa zai rike miki yara"




Tace"gidan many zan kaisu"


Islam tace"gobe koma Kaduna fa"


Suna ciki hira RAYHAN ya shigo yace"wiffy tashi mu tafi gida"tashi ta yi taje ta sallami ummi su bar gidan da yaran su gwanin sha'awa




ALHAMDULILLAHi


Nan na kawo karshen wanan labari IKLAS inda nayi kuskure Allah ya yafe mun




Nagode da goyan bayan Ku matsoyana




NOTE:ban yarda wani ko wata ta canja mun labari ta kowani siga ba in haka ta fara Alllah ya isa ban yafe ba






Sai kun jini a littafina na gaba, Allah ya had'a fuskokin mu da alheri








Taku CE
Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u all
Pls share

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login