Showing 27001 words to 30000 words out of 40828 words

Chapter 10 - IKLAS BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Maman Noorul

21 Aug 2025

201

20 RAYHAN ya shigo yace"wiffy tashi muje gida"


Tashi tayi tace"toh bari in salami ummi"


Yace"toh ina mota"


Bayan ta sallami ummi ta fito ta shiga mota kallon idonta yayi yace"wiffy kinyi kuka ne?"


Tace"no dear daga barci na tashi"


Yace"toh"


Suna isa gida ta shiga kicin ta dafa musu abinci a falo suka ci bayan sun gama cin abinci yace"wiffy je kiyi alwala in jamu sallah"


Tace"toh"


Alwala sukayi sukayi sallah mangrib nan suka zauna har isha'i bayan sun idar ne


Tace"muje muyi wanka "


Zuwa sukayi suka yi wanka su na fitowa ta fara shafa shi cikin salo mai wuyar fasara


Dariya yayi yace" wiffy ashe kema kina so"


Tace"ai ka koya mun jaraba"


Nan dai suka koma duniyar ma'aurata bayan sun gama


IKLAS ta kalli fuskar shi tace"ina son ka,kuma ina son komai naka mijina,ina son inda kake jijjiga ni a gado"


Dariya yayi yace"ashe kema kin zama harija"


Tace"ba dole ba tunda bana son kishiya"


Tace"yauwa baby ina son tambayar ka in ba damuwa"


Yace"ina jin ki"


Tace"wai ya akayi nuratu ta mutu ne"


Yace"wajen haihuwar nawal"


Tace"ya zaga ji in akace maka kashe ta akayi"


Yace"gaskiya zan iya kashe koma waye"


Tace"toh ka kwantar da hankalin ka dan ni nan na ishe wacce ta kashe nuratu"


Kallon ta yayi cikin rashin fahimta yace"wiffy me kike nufi da hakane ko wani yace miki kashe ta akayi?"


Nan ta sanar da shi abin da zaliha ta fad'a mata shiru yayi idanun shi sunyi ja


Tace"gobe zan shigar da kara kotu"


Yace"what? Wallahi ba komai da zaki yi zata fa iya kashe ki kema"


Tace"dole ne in tsaya ma Wanda ta kashe dan a hukunta ta karka damu in ta kashe ni ai kwana ne ya kara"


Tureta yayi yace"ni kike fad'awa haka?wato so kike ki mutu kibar ni inda nuratu ta tafi ko?"


Rike me hanun tayi tace"habibi ba haka bane"


Wani ihu ya daka mata yace"toh yayane?"


Turata yayi ya bar d'akin


Bin shi tayi a matakala ta hango shi zaune yana kuka


Zama tayi ta had'e hanun shi tace"mijina abin alfahari na dan Allah ka fahimce ni,kana so Wanda ta kashe ma mata uwar yar ka ta tafi batare da an hukunta taba?koko kana so wanda ta kashe Wanda bata jiba bata gani ba zainab ta tafi batare da fuskanci hukunci ba?koko wace sanadiyar ta mutane hudu sukayi mata fyad'e su tafi a banza,inda Islam ne ya zaka ji?"da sauri ya kalleta yace"wiffy ni ban San fitina ne kuma bana son ratsa ki wallahi inaji a jikina zan ratsa wani nawa,


Dariya tayi tace"ba abinda zai faru inshaallah,ka kwantar da hankalin ka mijina ni nan zan hukunta duk wanda ya zalunce ka da yar mu"


Da sauri ya rungumeta yana kuka cikin sokana tace"wai mai yasa kake da sauri kuka ne sai ka ce mace"




Dariya yayi yace"ke ma kin San ni cikkeken namiji ne muje ciki na nuna miki"


Dariya tayi tace"ai nasan kai namiji ne a wanan harka"


Daki suka je aka soye




Washe gari ya raka ta kotu ta shiga da kara




Abida zaune rike da sammancin kotu


Tace...... .
















Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to Zainab Abubakar maitunbi


πŸ…Ώ6⃣3⃣&6⃣4⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Zaliha tace"kene barrister IKLAS umar faruq?"


Kallonta IKLAS tayi tace"eh"Islam ko mamaki ne ya kamata da gudu ta je ta kira ummi


Zama zaliha tayi tace"magana nike son na fad'a miki akan mutuwar nuratu"dai-dai nan ummi ta karaso falon tsayawa tana kallon ta


Islam tace"me kika ce?"


Tace"abinda kika ji"


Zaliha ta kalli IKLAS tace"suna na Zaliha ahmadu ni nurse ne a asibitin da Dr abida ke aiki,abinda ya faru shine ranar da RAYHAN ya kawo nuratu nine na kaita labour room,na je kiran Dr abida dan ita ke duty ranar nan ina bude kofa sai naji tana cewa"bata taba samanni komai zai zo mata cikin sauki ba"a farko ban fahimci abinda take nufi ba sai kawai nashiga ciki nace mata an kawo wata tana nakudata,tace toh inje gata nan zuwa da sauri na fita na koma labour room sai dai ina shiga na tarar da ita tana zubar jini,da sauri na fito na koma office d'in Dr abida dan sanar da ita abin da ke faruwa da nuratu sai dai ina shiga na gan ta tana waya tana kallon window dan ta bawa kofa baya,ji nayi tana cewa"a kawo mata allurar da zai kashe mutum amma bata son wanda zai kashe ta nan danna ta fison Wanda zai bi jikin ta a hankali dan gudun zargi


Jiki na rawa na bar jikin kofa sai dai cikin rashin sa'a ina sakin kofan yayi kara da gudu da na fito nazo wajen mijin nuratu dan sanar da shi,ina zuwa nace me zanyi magana da shi amma sai ya kore ni wai in barshi yana cikin tashin hankali baya son jin komai,nayi kokarin fahimtar dashi amma yaki sauraro na,na fito zan gudu naga wasu katti a gate nan na fahimci abida ta sa su kamo ni


Da gudu na dawo cikin asibiti d'akin da,nuratu take ciki na leka dai-dai nan abida ta Ciro alluran tayi mata ni kuma nayi video komai


Abida na jin motsi na ta wurgar da kwalbar alurar ta tafito dan duba kowaye ke leke niko samun wuri nayi ba lab'e tana fita nashiga na d'aukon kwalban alurar na gudu da shi ashe ta ganin


Nan tasa su biggi bina a boye dan ban san sun bini ba,cikin dare suka zo gidan mu suka kashe kanwata zainab suka kamo ni,rokan su na farayi amma said d'aya daga cikin su ya bada shawaran suyi min fyad'e,haka kuwa akayi su hud'u suka yi min fyad'e wanda sanardiyar haka tun ranan bana magana dan bana ma hayyaci kafin su kashe ni police suka zo jin karar motan police yasa su guduwa suka barni cikin jini


Makotan mu ne ya taimake ni kasancewar dama bani da kowa sai zainab dan dama mu marayu ne


Malam musa ne ya kaini kauyen su ya bani kulawa har na samu lafiya amma bana magana


Wata d'aya da suka wuce Allah yayi wa malam musa rasuwa shine nace bari na shigo gari niman RAYHAN shine ranan nan a cikin gari naga a nuna shari'ar ki a TV tundaga ranar nace sai nimo ki dan ke kad'ai ne zaki iya hukunta Abida"


Kasa magana tayi dan kuka da yaci karfinta,rungume ta IKLAS tayi itama kukan takeyi cikin kuka tace"yi shiru inshaallah zan sa kotu tayiwa ke da zainab da nuratu adalci ita kuma Abida sai ta fuskanci hukunci dai-dai da abinda ta aikata wanan alkawari ne"


Ummi ko kuka tausayin zaliha takeyi tace"wanan wani irin hasabibiya ce?"


Islam tace"anty karki raga mata"


Kallon zaliha IKLAS tayi tace"yanzu ina kwalbar alurar da videon?"


Zaliha tace"yana pause d'in na kafin inyi accident,amma tunda na farfado banga pause d'inba"


Da sauri Islam tace"yana wajena Abba ya bani in ajiye"


IKLAS tace"je ki d'auko"da gudu taje ta d'auko,suna bud'ewa sai ga kwalbar da memory card


Kallon Islam tayi tace"d'auko mana laptop"


Suna saka memory card suka shiga video nan suka kalli komai da ya faru Ranan


IKLAS tace"........
































Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.


Dedicated to my fans


πŸ…Ώ6⃣7⃣&6⃣8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Abida tace"dolene ma in kashe IKLAS"


Mugu yace"angama masoyiyata yau zan aikata lahira"


Tace"ah ah ba yanzu ba,so nike a sato mun ita,saboda bana so ta halalci zaman kotu,kaga inba ganta ba za ayi wasi da maganar,mu kuma bayan anyi wasi da maganan sai mu kashe ta"


Mugu yace"haka yayi,yanzu yaushene zaman kotun?"


Tace"nan da sati d'aya wato Monday 6-7-2019"


Yace"toh gobe zan sato ta"


Tace"na yarda da kai"


Washe gari minal ta kira IKLAS a waya dake kwance zazzabi tace "hello IKLAS kina kina?"


Da k'yar ta amsa da eh


Minal tace"ki zo ki same ni a asibiti yanzu angama bincike akan alurar da inda take aiki a jikin d'an adam lab attendant d'in mu zai miki bayani"


Tace"toh gani nan zuwa"


Da k'yar ta mike dai-dai nan RAYHAN ya fito daga bayi yana ganin ta tsaye yace"ya dai wiffy jikin ne"


Tace"da sauki"


Yace"toh yaya ne dear"


Kasa magana tayi dan miyau ne cike a bakin ta,san da ta je ta subar ta dawo


Tace"wallahi minal ne ta kirani in same ta asibiti akan magana binciken nan"


Yace"ba inda zaki dube ki fa baki da ishashen lafiya kike maganan zuwa wani wuri,akan wani banzan shari'a,nifa hankalina bai kwanta ba akan wanan abun"


Rufe me baki tayi tace"mijina bana son mu maimaita wanan maganan addu'a ka nike da bukata"


Yace"toh ai shikenan"


Tace"muje kayi min wanka toh"


Yace"ke ma kinsan in muka shiga sai na latsa dan wallahy bazan iya ganin ki ba kaya ba in hakura"


Tace"toh muje kayi inda kake so"


Dariya yayi yace"yarinyar nan na lura kwana biyu kin fiya jaraba"


Bayan awa d'aya RAYHAN ya shirya IKLAS cikin riga da zani atampa hijab yasa mata yace"muje in sauke ki"


A bakin asibiti RAYHAN ya sauke IKLAS yace"in kin gama ki kirani zan zo in d'auke ki"


Tace"toh"har zata fita ya rungumeta sosai tace"lafiya?"


Yace"wiffy wallahi gabana na fad'iwa ji nake kamar wani abu zai faru"


Tace"ka yawaita fad'i inalillahi wa ina ilahi rajiun,insha Allah komai zai zo da sauki"


Yace"nagode baby"murmushi tayi ta fita a motar sanda yagan shigarta asibiti ya bar guri cike da damuwa


IKLAS na shi direct office d'in minal tashiga


Minal tace" sannu da zuwa"


IKLAS tace"yauwa ya shirin biki"


Minal tace"lafiya"


IKLAS tace"minal muje waje warin asibitin nan na damu na"


Dariya tayi tace"hmmm ki kamu kenan"zaro ido IKLAS tayi tace"dame fa?"




Minal tace"ciki mana"


Tace"habadai sati biyu kawai zaki wani ce ciki ne dani"


Minal tace" ko ki yarda ko karki yarda ciki ne dake"


IKLAS tace"Allah ya kawu" tashi sukayi suka je lab nan lab attendant yayi mata bayani tare da bata result d'in,


Minal ne ta ansa suka fito office d'in minal suka koma


IKLAS tace"bari in kira shi yazo ya d'auke ki"


Kiran RAYHAN tayi tace"hello mijina kazo na gama"


Yace"sorry wiffy baki sun mun yawa a office ki bani nan da awa biyu"


Tace"no ba zan iya jira ba zazzabi nike ji ka bari kawai minal ta sauke ni"


Yace"toh sai na dawo ki lula da kanki"


Tace"toh"


Kallon minal tayi tace"minal sauke ni gida"


Minal tace"toh dama zan biya unguwar Ku in anshi d'inki"


Tashi sukayi suka bar office d'in




Minal na drivin suna fira minal tace"kin gan ni da shirme na manta da result d'inna a office"


IKLAS ta bud'e baki zata yi magana kawai sai ga wata mota ta shiga gaban su babu b'ata lokaci suka fito da IKLAS suka wurga ta mota sai ihu takeyi


Cikin tashin hankali ta fita a mota tana niman taimako


Cikin rudewa ta Ciro wayar ta ta kira Abdul ta fad'a me"


Yace"what ai na kike yanzu"


Kiran RAYHAN tayi ta fad'a me halin da ake Viki


RAYHAN dake tsaye yana bayani a mitin zama yayi kasa nan da nan ya fara zufa"


Abba da daddy suka kalli juna daddy ne ya karasa inda yake yace"son lafiya meke faruwa ne haka"


Kallon daddy yayi cikin rudewa yace"daddy sun sace mun ita wallahi sun tafi da IKLAS"


Daddy cikin rashin fahimta yace"su waye kuma saboda me?"




Yace"abida ne wallahi Abba dan Allah ka taimake ni"




Abu kamar wasa har akayi kwana biyar ba a gan IKLAS ba yan sanda ma suyi cigiya shiru Wanda sanadiyar haka aka kama Abida amma duk horo da akayi mata ansa d'aya ce batasan inda IKLAS take ba


RAYHAN ko abinci baya ci ko magana ba yayi said dai ya zauna kamar sabon kamu yayi ta magana yana cewa miyasa zaki yi mun haka?ki taimaka ki dawo gareni matata"


A yau a kayi kwana shida da b'atan IKLAS kuma gone ne shari'a,bikin minal kuma saura kwana shida,amm ba Wanda ya bi kan bikin


Zaliha ma kullum cikin kuka tace"da na sani da ban zo ba,laifi na ne wallahi"


Mamy ko hawan jinin ta San da ya tashi dan yanzu haka tana kwance a asibiti


Minal ne zaune tana tunani tace"dole ne IKLAS taje kotu gobe amma kafin haka ta faru dole nayi tunani irin nasu"


Mahmud ne ya fad'o mata a rai tace"yes shi kad'ai ne zai taimaka min tunda yanzu ya shiryu kuma nasan zai San inda take dan dashi aka had'a baki akayi mata sharri a Lagos


Tashi tayi ta d'au wayar ta bata fi


Bayan awa d'aya sai ga minal na magana da Mahmud


Tace"..........














Maman
, noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share


[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we the best among the rest.




πŸ…Ώ6⃣9⃣&7⃣0⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Minal ta kalli Mahmud dake zaune a wheel chair tace" an fa sace IKLAS"


Yace"what garin yaya?"


Nan ta kwashe komai ta fad'a me


Yace"wanan gaskiya ne dan abida ita kashe nuratu"


Minal tace"toh ya zayi yanzu"


Yace"bari in kira mai yin bincike yazo shi zai gaya mana mafita dan dolene IKLAS taje kotu gobe"


Bangaren IKLAS kuwa sun d'aure ta a wani daki da k'yar suke bata abinci tana ci ga zazzabi da ke damun ta"


Tunanin ta d'aya shine wani hali mijin ta ke ciki da tasan bashi da juriya abu kad'an ke sashi kuka a tace"Allah sarki mijina"


Bayan awa biyu yaron Mahmud mai bincike yazo


Mahmud yace"an gano inda aka kaita?"


Yace"eh mai gida tana bayan gari"


Minal tace"toh miye mafita kenan ko mu sanar da yan sands"


Yace"ah'ah bana jin haka mafitane domin ina zargin akwai d'an sanda mai yi musu aiki zai iya sanar da su kuma haka zai iya sa su kashe ta"


Mahmud yace"toh miye mafita ne?"


Yace"mafita d'aya ne a had'a baki da d'aya daga cikin su in akwai Wanda ka yarda dashi"


Mahmud yace"akwai"


Da sauri minal tace"waya?"


Yace"babsy"waya rshi ya d'auko ya kira shi yace"babsy ya dai "


Babsy yace"lafiya oga ka guje mu"


Mahmud ya mu hadu a guest house d'ina yanzu amma ban son kowa ya sani"


Yace"toh gani nan tahowa"


Bayan minti talatin babsy ya taho,nan dai suka gaya mai komai


Babsy yace"nawa za a bani"


Mahmud ya bashi cheque yace" ka cika ko nawa kake so kud'i ba Matsala bane"




Karba yayi yace"mafita d'aya ne"


Minal tace"muna jinka"


Yace"shine ki maye gurbin ya gobe ni zan San inda zanyi infito da ita ke kuka ki zauna a madadin ta dan ta samu zuwa kotu"


Mahmud yace"no baza mu sa ta a had'ari ba"


Babsy yace"toh gaskiya babu wata mafita sai wanan"


Minal tace"zan iya"


Mahmud yace"no kiyi tunani aure ki saura kwana shida"


Tace"mahmud IKLAS na bukatar taimako dan ciki ne da ita gashi ba lafiya da kagan halin da mijinta ke ciki da ka tausaya me"


Mahmud yace"ya kamata ki sanar da mijin kin"


Tace"no in na sanar da shi ba zai bari in je"


Kallonta babsy yayi yace"gobe kifito karfe 9:am




Haka kuwa akayi gari na wayewa minal ta shirya ta fita titi babsy ya dauketa zubawa su mugu maganin barci a abin sha,sai barci suke,


Suna isa suka tarar dasu suna barci a hankali babsy ya bude d'akin da IKLAS take


IKLAS na ganin minal tana so tayi magana babsy ya yasar shi a baki shhhhhhhhh




Shiru tayi da Sauri ya kwace ta yace"koyi sauri Ku canja kayar jikin Ku"fita yayi ya basu wuri cikin mintu biya suka sauya kayar su


IKLAS tace"minal me kike yi a nan"


Minal tace"ba lokacin bayani,kije ki tsayawa mutanen da aka zalunta a kotu saura minti 40 a zauna


Tace"ba in zani in da gaske ne mu gudu tare mana tunda sunyi barci"


Minal tace"da mun gudu zasu kashe zaliha dan tun jiya ba ganta ba kije ba lokaci"


Babsy ne ya shigo yace"muje in raka ki akwai mota a waje da zai kaiki kotu Islam zata same ki a kotu da kaya"


Kallon minal tayi tace"toh ita ya zayi da ita?"


Yace"da angama shari'a zan samo hanya kubutar da ita,Allah yasa karsu gane bake bane dan insu gane akwai matsala, amma minal bazan d'aure ki sosai ba incase in an samu matsala ki kare kanji,in kun ji shiru bayan shari"'a Ku zo da yan sands"




Rungumeta Minal tayi tace"in na mutu ki ce wa Abdul da iyaye na su yafe mun"


Kuka IKLAS tayi tace"gaskiya bazan iya barin ki a nan ba"


Babsy yace "mu je ba lokaci" da k'yar Minal tayi da IKLAS ta bi babsy


'Bangare RAYHAN ko














Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah




🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣1⃣&7⃣2⃣


Bismillahir Ramanir Rahim


'Bangaren RAYHAN ko sai abin da ya karu dan wuni yake yi yana kira sunan IKLAS nawal ma sai kuka take


Misallin karfe 9:40 IKLAS ta isa kotu sai dai bata da karfin jiki


Tana fitowa a kotu Islam ta karaso ta rungumeta


IKLAS tace"in mijina yake?"


Tace"yana gida ba lafiya"


Tace"kira shi ki ce ina nan"


Mahmud ne yayi gyran murya,sai a sanan ta lura dashi


Fad'iwar gaba had'e da mamaki ne ya kamata na ganin shi a keken guragu


Yace"ya jikin?"ko kallonshi batayi ba yace"ya kamata ki je ki shirya shari'a saura minti goma"


Kallon Islam tayi tace" meya had'a ki da wanan"


Murmushi Islam tayi ta bata labarin komai


Cikin jin kuya da nadama mahmud ya kalleta yace"ki yafe mun nasan nayi miki ba dai dai ba,kuma nayi miki alkawari ceto rayuwar minal yanzu ma nasa aje a nimo zaliha"


Tace"na yafe ma,Islam kirashi please"kiran RAYHAN Islam tayi ta fad'a me IKLAS na kotu


Ai da sauri ya tashi dan dama yana zaune ne a kasa yace"Allah nagode ma yace"ai babu shari'a da zatayi bana son in rasa ki kema"


A gurguje ta shirya cikin kayarta na lauyoyi


Ta fito tana shiga dai-dai alkali na cewa ina lauyan mai kara?"


Dariya Abida tayi a ranta tace"ai tana nan naure"


Jin muryan IKLAS tayi tace"gani ya mai shari'a"


Ai nan take gaban ta ya fad'i kallon

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login