Showing 18001 words to 21000 words out of 30967 words
baki daku ba ko?? dan banyi miki lahani ba shine zaki dinga kawo min maganar banza"
Girgiza kai tayi kafin tace, "ai Saif ka zama mutum, tin bakasan kanka ba tsohon nawa ya raine ka ya baka tarbiya amma saboda ba ɗan kirki bane kai duk ka watsar da ita, wai yau gashi kaine kake korar ƴarsa daga cikin gidan ka kamar kaga mugun abu saboda ya riga yayi maka komai, Saif duniya ce da kai da wadda ta kawo ku duniya da ƴan uwanka duk sai kunga sakaiya Allah baze barku ba Saif kuma na gode ko babu komai yanzu ka bani damar auren wanda nake so"
Kafin yayi wata magana tafara tafiya, kawai yaja tsaki ya koma cikin gidan sa sai huci yake, a duk tunanin sa ba abunda yake yawo illa ta cuce shi tagama dashi.
Tana cikin tafiyar ne mota ta tsaya a gabanta har zata wuce taji ya cukume ta ya tura a motar bata san ko waye ba batasan irin halin sa ba dan haka tayi shiru har suka isa inda yake son zuwa yace ta fito sannan ta fito.
har lokacin bata yarda bazeyi mata komai ba sai dai bata da zaɓin da ya wuce yimasa ladabin kunama dan kuwa daga shi sai ita a gidan ko yankata yayi har ya soya ya cinye wani be sani ba.
yana murmushi yace, "Aisha in faɗa miki gaskiya ?? ke ba macece wadda ake samu a gama gari ba,
Kuma ke macece wadda duk wani lafiyayyen namiji in ya ɗora idonsa akanki sai yaji ya ƙyasa, ke ƴar baiwa ce fa"
Murmushin ƙarfin hali tayi masa kafin tace, "nagode"
Takowa yayi ya matso inda take ya zauna kusa da ita yana fuskantar ta idanu ya zuba mata kamar tsohon maye sai wani murmushi yake me manufofi da yawa.
ita dai kanta yana ƙasa dan kuwa a tsorace take.
Muryarsa ce ta katse mata tunanin ta, "idan na tuna daren farkon mu sai naji shauki ya ɗebe ni A'isha jinake dama za'a kuma"
Cikin takaici tace, "ai za'a kuma ɗin amma ba da kai ba"
Dariya yayi yace, "shikenan na yarda ba dani ɗin ba amma koma waye ai nine na nuna masa hanya"
Takaici be barta tayi magana ba sai ɗan murmushi da takeyi wanda ita kaɗai tasan manufarsa sai Allah.
Yace, "tashi kije kiyi wanka"
kai tsaye tace, "bazanyi ba"
Murmusawa yayi yace, "ohhh A'isha har yau baki canja ba, gardama ga tarin zurfin ciki gaskiya kina burgeni"
Tace, "idan da na canja ai da tuni labarin ma ya canja"
Yace, "kuma fa hakane amma dai kiyi abunda nace"
Tace, "nifa bazanyi ba, akan me zanyi wanka a gida dagani sai kai??, kana ma hauka"
be tsaya jin zancen ba ya sungume ta ya ɗorata a kafaɗa ya nufi ɗakin wanka da ita, mutsil mutsil ta shigayi tana ƙoƙarin ƙwacewa amma takasa har sai da ya kaita sannan ya direta, ya kalle ta a dake yace, "zaki cire kayan da kanki ko kuwa na cire da kaina??"
Da sauri tace, "dan Allah kayi Yaya Dawood zanyi wankan ma da kaina"
Wani shu'umin murmushi ne ya buwayi fuskarsa har cikin ransa maganar ta ratsa shi be taɓa tsammanin akwai ranar da zata zo Aisha taƙara kiransa da Yaya ba shiyasa yaji abun kamar a mafarki, gefe guda kuwa yana mamakin yadda har take iya yimasa murmushi yau bayan idan ta ganshi kamar taga shaiɗan amma yau gashi ta saki jiki dashi, beyi tunanin komai ba dan kuwa idonsa ya rufe haka kawai tinda ya ɗakko ta yakejin wani irin shauki har ma ya kasa yi mata kashedi ta hanyar azabtarwar da yace ze bi mata da farko.
Muryarta wadda take ƙara bauɗar da tunaninsa ce ta sarƙaƙa cikin kunnen sa, da yake lallaɓa shi take cikin sigar rarrashi tace, "dan Allah ka fita zanyi wankan karka ƙara shigowa kuma"
yace, "na yarda kuma kiyi sauri dan nasan kina tareda ni bazan juri zama ni kaɗai ba"
Kai ta gyaɗa masa tana murmushi, yana juya baya ta doka masa harara me taken ZALLAR ƘIYAYYA.
Sai da ta tabbatar ta garƙame ƙofa sannan tafara wankan tanayi tana kuka sauƙin ta ma dai da ruwan ɗumi yadda take shan jiki da ruwan sanyi ne da ta ɗanɗana ta"
Yana nan zaune ta fito sai raɓe raɓe take cikin sanyi tace, "na fito"
Kallonta yayi sama da ƙasa kafin yace, "kuma shine kika ɗauki kayan da kika cire kika mayar dan shirme??"
Tace, "kaga malam bana son iskanci nan fa ba gidan ubana bane ina naga wasu kayan"
Yana dariya yace, "A'isha nine ɗan iskan ko?? kodan yau banyi miki iskancin bane yasa kika samu bakin magana?"
sai a lokacin ta tuno da irin halinsa na rashin imani gudun kar a kuma yasa tace "kayi haƙuri" sannan taja baki ta tsuke.
bata ankara ba sai ganinsa tayi a gabanta yana binta da kallo yana murmushi yace, "A'isha makullin sirrina gaskiya naga ƙoƙarin ki da kika kasa gayawa kowa, to amma yanzu kinga Saif ya jawo mana dama abunda naso gaya miki tin farko shine bana son sunana ya fito duk gumurzun da za'ayi idan kikace nine kinsani ke zaki kwana a ciki dan idan nace banyi ba babu me cewa dole nayi"
Ƙasa tayi da kai tana murmushi tace, "Dawood Yayan Saif gaskiya kun more wajen tarwatsa farin cikina da kai da ƙanin ka, to amma ba komai indai akan wannan ne karka wani tashi kanka tsaye, duk tsawon shekarun da aka ɗauka ko mahaifiyata bata san anyi ba bare wani kaga kuwa babu dalilin da ze sa yanzu na faɗa"
Yace, "wow A'isha gaskiya kin iya riƙon amana irin ku wahala kuke a zamanin nan"
*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 24*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
yaƙara da cewa, "har yanzu ƙara kyau kike amma kin ɗanyi baƙi ba kamar lokacin da kina yarinya ba da fa kamar a taɓa jini ya fito haka kike"
Zamewa tayi zuwa gefe tana cewa, "zafin duniya ma kaɗai ya isheni bare kuma kasan wani idan yana girma kamannin sa suna ƙara fitowa sai kaga ya canja launi"
Yace, "hakane kuma"
Wasu kaya ya miƙo mata yana cewa, "maza ki canja kaya"
Karɓa tayi tareda nufar hanyar ɗakin wanka, da ido ya rakata har ta ɓacewa ganinsa sannan ya saki murmushi tareda cewa, "A'isha manyan gari"
yana nan zaune ta fito ta tsaya akansa ba tareda ta kalleshi ba tace, "gida zan tafi"
Yayi kamar be ji ba sai da taƙara cewa, "nace ka kaini gida ko?"
Ido ya zuba mata har tsawon wani lokaci kafin yace, "anan zaki kwana"
A zabure tace, "me????"
Sarawar da kanta yayi ne yasa tayi saurin sakin maganar ta rintse ido gami da cije leɓenta, sai da ya sassauta sannan tace, "Dan Allah Dawood karka ƙara cutar dani ka maidani gidan mu, ka fita daga rayuwata ko na samu sassauci, nayi maka alƙawarin bazan faɗawa kowa abunda yafaru ba ko a wane matsayi aka ɗaukeni zan yarda amma dan Allah karka ƙara cutar dani"
wata ƴar dariya yayi sannan yace, "na yarda bazaki faɗawa kowa ba yakamata kema ki yarda bazanyi miki komai ba indai ba ke kika amince ba, amma fa anan zaki kwana bazan kaiki gida da daren ba"
Sanin ba kaitan zeyi ba yasa ta koma ta zauna ta buga tagumi.
sai da ya gama abunda zeyi sannan ya kalleta tace, "tashi muje ki kwanta"
Bata tsaya yimasa gardama ba ta bi bayansa wani ɗan madai-daicin ɗaki me ɗauke da matsakaicin gado ya kaita sannan yace, "duk abunda zaki iya buƙata akwaishi a ɗakin, sai da safe ko??"
Gyaɗa kai tayi idonta a ƙasa. yace, " bazaki ce min komai ba??"
Shirun taƙarayi dan kuwa bata san abunda zatace masa ba hasalima ta ƙagu ya tafi yabata guri dan ba ƙaunar ganinsa take ba.
Ɗan murmushi yayi kafin yace, "shikenan sai da safe naga kamar kina jin bacci sosai"
be jira me zatace ba ya fice, sai da ta sauke ƴar ajiyar zuciya sannan taƙarasa kan gadon ta zauna a gefen sa ta shiga ƙarewa ɗakin kallo har wani lokaci kafin taja tsaki, tareda zullumi da adda'a a bakinta ta haura kan gadon ta kwanta gami da lumshe idonta tana jiran zuwan bacci, tin tana sa ran ze ɗauke ta har ra dena saboda tunane tunane da suka durfafeta ga idonta sun ƙeƙashe babu alamun bacci a tattare dasu sai zafi da zugi kawai suke, fargaba da tsoron abunda ze faru kuwa sunyi cunkuss a zuciyarta hakan ya haifar mata da buguwar zuciya akai akai wanda yasa jikinta ya ɗauko tsuma, ta daɗe cikin wannan yanayin tana shan azaba kafin zuciyarta tayi rauni har kuka ya samu damar kufce mata hawayenta suka zuba, sai a lokacin ta ɗanji damar zugin da takeji sai dai kanta da ya cigaba da tsala ciwo, ta daɗe tana kukan sannan bacci me cike da mafarkai munana yayi ɗaukar shaho da ita, batafi minti ashirin ba tafarka bayan wani lokaci taƙara komawa, haka tayi baccin guntu guntu sai ƴan mafarkai da tunani da take faman yi, sai gab da Assubhu sannan bacci me nauyi ya ɗauketa.
lokacin Sallah yanayi kuwa Dawood yazo ya tashe ta a cewar sa tayi Sallah ko takansa bata bi ba ta nufi inda take tunanin ɗakin wanka ne ta ɗauro alwala ta fito lokacin shi kuma ya fita hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, tayi sallarta cikin nutsuwa tareda roƙon Allah sassauci.
Sai da tayi addu'o'i sosai sannan ta koma bacci, ba ita ta farka ba sai tara da minti arba'in da biyu 09:42 sannan ta tashi a razane tana wuri wuri da ido ai kuwa idonta ya sauka akan Dawood da yake zaune a gefenta yana ƙare mata kallo kamar wanda yaga baƙuwar halitta, ashe dai mafarkin da tayi gaskiya ne banbancin kawai a iya kallonta ya tsaya be taɓa ta ba.
Yadda ta zazzaro masa ido ya tabbatar masa a firgice ta tashi ya sakar mata murmushi sannsn yace, "Barka da safiya ƙanwata A'isha ina fatan lafiya kika tashi"
da kai ta amsa masa da "e" cikin ranta kuwa cewa take azzalumi ko meye damuwarsa da lafiyata bayan ya rabani da ita?"
Katse ta yayi da cewa, "na haɗa miki ruwan wanka kiyi ki fito kiyi kari"
Bata tanka masa ba ta zame tayi ƙasa har ta fito daga wankan yana nan zaune, zama tayi a gefen gado tayi zugummm ba um ba um um,.
Abincin karin ya ya dire mata sannan ya koma ya harɗe, da taƙi ci sai da taga yayi da gaske sannan ta ci saboda tsoron abunda ze biyo baya.
Sai kusan Azhar sannan ya ɗakko mota yace ta shiga ya maida ita gida tayi kukan tayi magiyar har tagaji ta dena ta zuba masa ido.
Da har ƙofar gida ze kaita sai da ta dage bata so sannan ya haƙura ya direta a bakin layinsu bayan ya ƙara jaddada mata kar yaji ta ambaci sunan sa a cikin labarinta, hakanan ta amsa masa sannan ya barta ta tafi, bugun zuciyarta ƙara gudu yake a duk takun da tayi da sunan ta nufi gidan.
tana yin sallama sukayi ido huɗu da Mama ta bi ta da kallon mamaki da tambaya.
Ƙasa tayi da kai a ciki ciki tace, "sannun ku" daga haka ta wuce ta nufi ɗakinta.
Mama da ta daskare a zaune tace, "Aisha????? kina cikin hayyacin ki kuwa???"
Aunty Maimuna ta jinjina kai tareda cewa, "tabɗi jam Aisha ya zamu ganki anan yanzu kuwa bayan kamata yayi ace kina gidan mijinki"
Duk da ba kallonsu take ba amma tasan duk idanun su suna kanta kuma jiran amsarta suke, Rintse ido tayi da ƙarfi a ƙagauce tace, "ya sakeni saki uku".
Mama kasa magana tayi sai sauran mutanen da suke gurin me salati tanayi me ƙara jefo wata tambayar tanayi.
Aunty Zuhailat tace, "iskanci ne ko ƙuruciya yake damunki Aisha?? akan wane dalili zaki zo mana da irin wannan banzan zancen??"
Tace, "Aunty Zulaihat wallahi Saifu ya sakeni ga takardar ma a hannu na"
Inna lillahi wa inna ilaihirraji un shine kalmar da Anti Zulaihat ta faɗa cikin rawar jiki da firgici,
Aisha kuwa wuce tayi ta nufi ɗaki har taje ƙofa Mama ta dawo da ita da cewa, "zo nan dan ubanki Aisha"
Dawowa tayi idonta a ƙasa tayi tsaye tana sauraren su, Cikin kuka Mama tace, "yanzu Allah ya rufa miki asiri ya rufamin shine zaki kashe aurenki?? Saif dai nasan bashi da wata matsala ko meye yafaru daga ke ne, maza ki gaya min wace tsiyar kika shuka"
Gyara tsayuwa tayi gami da cewa, "ku tambaye shi mana shi da yai sakin"
Mama takasa cewa komai sai sharar Ƙwallah, Cikin ɓacin rai Anti Maimuna tace, "bazamu tambaye shi ba ke zamu tambaya"
Tace, "aikuwa zaku mutu bakuji ba"
Tana rufe baki Anti Zulaihart tayi kanta da duka sai da ƙyar mutane suka dakatar da ita aka bata baki sai kuma ta fashe da kuka.
Aisha kuwa gefe ta koma ta cigaba da ƙasa ƙasa da ido yanzu kukan ma har ta kai matakin da takejin baza ta iyayinsa ba zuciyarta ta bushe.
Mama tace, "ku ƙyaleta idan ubanta yazo sai ta gaya masa tinda shine maɗaurin auren nata"
Bata tanka ba kawai ta wuce ta shige ɗaki, wata ƙanwar Abban su wadda suke Ɗan wa da ɗan ƙani ta tashi ta bi bayanta, da yake akwai tsugul da son nuna iyawa ta raɓa kusa da ita cikin sigar lallami tace, "Aisha kinga ran mahaifiyar ki ya ɓaci kije ki bata haƙuri koda bazaki gaya mata abunda yafaru ba, amma kinyi ƙememe da ido ko hawaye bakyayi ai dole ace kece da laifin kije ki bata haƙuri kinji ko?? kar ta gayawa Abban ku ya ɗauki tsatstsauran mataki fa"
A faɗace Aisha tace, "yaaa isa hakaa!! har shekara nawa zan ɗiba inayiwa ɗa namiji kuka??? bazanyi ba ɗin haƙurin ma bazan bayar ba tinda idan na faɗa ma ba abunda ze ragu ko ya ƙaru dan haka kar a ƙara yimin zancen banza na ɗebi tsawon lokaci ina kokawa saboda namiji yau ɗaya dan na samu hutu shine za'a takura min?? ki fita tin ina ganin mutuncin ki ki bani guri"
Kamar munafukar kaza haka ta summ summ jikinta har rawa yake ta bi iska ta fice daga ɗakin...
Waya Mama tasa aka kira Abba aka sanar dashi ai kuwa sai gashi ya dawo shima tin kafin ya dawo ya zabaro Saifu bayan dawowarsa kaɗan sai ga Saif ɗin.
Aisha kuwa tanajin su tayi kamar bataji ba, Abba ne ya fara yambayar Saif ba,asi ai kuwa ya zayyana masa abunda yafaru tin jiya"
Shiru yayi yana nazari sannan yasa a nemo masa ita a gefe ta tsakure tana jiran abunda ze ce, sai da ya ɗanyi gyaran murya sannan yace, "kinji abunda ta faɗa ko??" ta gyaɗa kai, yace, "to hakane" tace, "eh amma fa karya ƙara cewa ina neman maza dan ba aikina kenan ba"
Cikin fushi Abba yace, "bayan tin jiya ya sakeke kuma ina kika kwana?? wannan ma kaɗai ya isa shedar abunda yafaɗa, Subhanallahi Aisha wannan rayuwar kika zaɓawa kanki?? A uzu billah"
Saif yace, "gata nan dai ana ganin kamar su kaɗai ne masu tarbiya duk dangi ashe kura ce a lulluɓe da fatar akuya, ku tambaye ta waye wanda take zuwa gurinsa dan ni an daɗe ana sanar dani akwai wani namiji da take zuwa gurinsa, kuma ko waye sai munyi shari'a dashi"
Cikin ƙunar rai Mama tace, "ka tambaye ta Alhaji ni ta ɓatawa suna ta zibarwa da mutunci dan nice uwa mace, ko meye yafaru ni za"a fara hari dan haka ta gaya mana da yaushe ta zama haka da yaushe ta watsar da tarbiyar da muka bata?? ta gaya min waye wanda ya lalata ta wallahi sai dai duniya tarabani dashi dan ni ƴa ta nasan ba karuwa bace sai dai in wanine yaja ra'ayin ta"
Cikin tsawa Abba yace, "zaki goyi bayan ta ko??? gashi ƙiri ƙiri kina ji kina gani zaki ce ba haka ba?? ta gaya min ma jiya gidan ubanwa ta kwana"
Shiru tayi dan kuwa tana matuƙar tsoron Dawood babu yadda za"ayi tace a gidansa ta kwana.
Abba yace, "zakiyi magana ko kuwa sai na fara dukanki??"
Tace, "Abba wallahi kawai zargina ake amma ni bana haka wallahi kunji na rantse"
Saif yace, "ƙarya fa take munafuka ai na firgita da lamarin yarinyar nan azzaluma ni ai ta gama cutata kuma bazan yafe ba duk ma abunda na kashe dan aurenta sai an biyani"
Abba ya jinjina kai kafin yace, "daga nan zuwa gobe ki gaya min waye idan ba haka ba ranki ze ɓaci, ku kuma ku sa ido akanta karta ƙarayin wani gurin"
Mama ta share ƙwallah gami da cewa, "to"
Komawa tayi ɗaki ta zauna sai fici fici take da idanu.
Nuriya da take ta kuka ta kalleta cike da damuwa tace, "Aisha wannan wane irin baƙin labari ne?? neman maza kike???"
Murmusawa tayi kafin tace, "ba nice na nemeshi ba shine ya nemeni Nuriya, kasancewar ki amintacciya