Showing 15001 words to 18000 words out of 30967 words

Chapter 6 - RINTSIN SO Book 2 Free Hausa Novel

Unknown   

11 Nov 2024

1168

kaiwa.

Iskar da ya hura mata ne yasa taja numfashi tareda sauke kallonta ƙasa, cikin sanyi tace, "Khaalif bana so a neme ni a rasani dan Allah mu koma gida yanzu idon kowa akaina yake su kansu sun fara dasa alamar tambaya akaina yanzu basu yarda dani har yanzu hankalin Mamata be kwanta ba da bakinta tafaɗa bazata nutsu ba har sai ta kawar dani daga gabanta, ni kuwa wace irin ƴa ce haka"

Ta ƙarasa maganar tana cije baki dan hana kukanta kufcewa.

Khaalif ya tsira mata ido na wani lokaci kafin yace, "zamu koma mana"

magiya ta shiga zuba masa amma yayi banza da ita daga baya ma sai ya ciri wayarsa ya shiga dannawa yayi banza da lamarinta.


Zuwa yanzu tagama kaiwa maƙura musamman da ta duba lokaci taga yadda suka kwashi lokaci me yawa batasan lokacin da ta fashe da kuka ba.

Murmusawa yayi gami da kashe wayar tasa ya saka a aljihu sannan ya matso kusa da ita, hannunsa ya jefa cikin tafin hannunta a hankali yace, "ki dena kuka fa Ayeeshah na wannan ba abun zafi bane fa"

Ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da kuka da iya ƙarfinta, janyota yayi cikin kulawa yayi mata masauki a ƙirjinsa cikin sigar rarrashi ya shiga bubbugar bayanta amma takasa dena kukan, abun yafara hawar masa kai cikin nutsuwa ya kai bakinsa saitin nata ya shiga sumbatar ta cikin wani irin yanayi da ya tsinci kansa a ciki yanayi yana lumshe gami da sauke sassanyar ajiyar zuciya,
Aisha kuwa wata wahaltacciyar ajiyar zuciya ta sauke gami da rintse ido tin abun baya mata daɗi har ta saki jikin taƙara lafewa a jikinsa.

Sun ɗebi lokaci cikin wannan yanayin kafin ya dakata kallon fuskarta yayi cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa yace, "kiyi haƙuri Ayeesha yau nazo miki da baƙon lamari nima ba haka naso ba kawai na tsinci kaina ne cikin wannan halin, meyesa bazaki aureni ba Ayeeshah na???"

tinda suka haɗa ido sau ɗaya ta rufe idonta dan in tanada kunya bazata iya ƙara haɗa ido dashi a wannan lokacin ba, ƙoƙarin zamewa tafarayi daga jikinsa amma yaƙi bata damar hakan sai ma cigaba yayi da cewa, "naso a ɗaura min aure dake a ranar jumu'ar nan kafin lokacin da aka sa aurenki da Saif amma ya riga ya tarwatsa duk shiri na da alamun ya gano me nake nufi, amma ba kome za'a haɗu wata rana ai, nidai abu ɗaya nake so kiyi min hankalinmu ya kwanta mu duka"

Gyaɗa kai tayi alamar tana sauraronsa, yace, "karki bari Saif ya taɓa min komai a jikinki hakan ne ze sa mu fi nutsuwa bayan haka kuma kinsan hankalina baze iya ɗauka ba"

Cikin tausayin kanta tayi saurin amsa masa da, "to amma dan Allah ka maidani gida"

yace, "to shikenan ko?"

Kai kawai ta iya gyaɗa masa dan lokacin bacci yafara fizgarta kafin yayi wani yunƙuri bacci ya saɓeta hakan yasa ya gyara mata zama don tafi jin daɗin baccin.

bayan wasu mintuna kamar da wasa ta farka ta jita a jikin mutum tayi saurin buɗe ido sukayi ido huɗu dashi take duk abunda yafaru ta shiga dawo mata saurin rintse ido tana tana furta "Astagfirullah" cikin sauri ta zame jikinta ta matsa gefe,
Shu'umin murmushin nasa yayi kafin yace, "kin tashi kenan??"

Kamar zata fashe da kuka tace, "Khaalif meyesa baka maidani gida ba??"

Yace, "kin danne ni tayaya zan iya jan motar kinsani dai ko a mafarki bazan iya tashinki a bacci ba"

Bata ce masa komai ba dan ta lura neman zance da neman dalili kawai yake.

Tin a ƙofar gida Sayid yake sanar da ita sai nemanta ake zuciyarta na dukan tara tara haka ta shiga gidan sai sauke ido ƙasa take gaba ɗaya ita kanta ta tsargu da kanta duk ta kasa sakin jiki musamman idan ta tuna ɓelesin da sukayi sai taji takaici yaƙara kamata, har mamakin yadda Khaalif yayi tasiri akanta take musamman kwanakin nan idan layi ya shata yace kar a tsallaka tofa ta barshi kenan"

Aunty Zulaihat ce ta maka mata harara gami da watso mata tambayar "daga ina kike??"

Ba tareda ta kallesu ba tace, "daga gidan su Surayya"

Anti Maimuna tace, "a layin nan inane inda bamu tambaya ba kuma duk ance bakya nan har gidan su Surayyan"

Sayid yayi saurin cewa, "amma dai Mamansu cewa tayi sun tafi wani guri itada Surayya amma bata faɗi inda sukaje ba"

sai da ta sauke ajiyar zuciya saboda daɗin maganar Sayid da taji tayi gaba tana cewa, "na rakata haɗo kayan kwalliya ne"

Maida hankali sukayi kan Sayid suna tambayarsa dalilin da yasa be gaya musu hakan tin wuri ba kawai yace ya manta ne dole suka ja baki suka tsuke.


Tana zaune ta buga tagumi tana abunda ta saba wato tunani Sayid ya shigo ya zauna kusa da ita sai haɗe rai yake, cikin fushi yace, "yanzu Anti Aisha kin kyauta kenan?? kin tafi gantali keda Yaya Khaalif gashi sai nemanki ake ke bakya gudun ɓacin rai ne wai?? keda zaki auri wani ina ke ina wani banda neman fitinar ki"

Cikin sanyi tace, "Sayid Khaalif!! ina tsoron fushinsa wallahi"


Kai tsaye yace, "fushin nasa na banza? duk Tsananin fushin sa ya kai ya ɓacin ran iyayenki ne??"

Tace, "kai Sayid so fa ba ƙarya bane do Allah karka takura min da zancen shashashan Saifun nan dan shi ban ɗauke shi namiji ba ka gane??"


Yace, "na dai gaya miki ai kuma gaskiya ce idan kinji ilaiki idan bakiji ba ilaiki"

Banza tayi masa sai ma harara da ta bishi da ita taja tsaki.


yau ta kasance ranar ɗaurin auren Saif da Aisha gidan ya cika maƙil sai kai kawo akeyi.

Tin safiyar Allah take kuka kamar wadda ta rasa iyayenta, Nuriya ce ta miƙo mata wayarta tana cewa, " gashi an kira ki"

Karɓa tayi ta duba tana ganin ABU ne tayi saurin karawa a kunne.

Cikin farin ciki yace, "Alhamdulillah Eeeshu na samu lafiya"

murmushi ne ya buwayi fuskarta ta zaro ido tareda cewa, "Da gaske????"

Yace, "da gaske ba da wasa ba haka kawai naga nafara gani nima kaina kamar a mafarki nakeji"

saboda farin ciki bakinta yaƙi rufuwa ga murmushi ga hawayen farin ciki duk a lokaci ɗaya,
share ƙwallar tayi kafin tace, "nagodewa Allah nikam nayi farin ciki mara misaltuwa tabbas naji daɗi Ya ABU Allah yaƙara maka lafiya ya kare ka da dukkan wani sharri"

Ya amsa da "amin" sannan ya cigaba da cewa, "Eeeshu Khaalif Mohammad ya sanar dani yau ne ɗaurin aurenki ina miki fatan alkairi a duk inda kika shiga"


Murmushi tayi tace, "nagode sosai"

Yayi murmushin farin ciki kafin yace, "Rookha tazo kuwa??"

Tace, "nima banji daɗin rashin zuwanta ba amma babu yadda na iya dan kuwa yanzu bata son ganina ko jin labari na ma saboda na rabata da abunda take so"

Yace, "Allah sarki ai ba laifin ki bane"

Aisha tace, "ka kirata kaji lafiyarta ka sanar mata yanzu ka samu lafiya nasan zatayi farin ciki sosai"

Yace, "zanyi ƙoƙarin hakan"

Murmushi tayi tace, "sai anjima ko?"


Yace, "eh amma dai ina fatan duk abunda Khaalif yayi miki be sa kin dena son sa ba ko??"

Lumshe ido tayi sannan tace, "koda kaɗan banji hakan ba"

Yace, "nagode Eeeshu sai yanzu na gane wautar da nayi da na tauyewa ɗan uwa na farin cikin sa ban kyauta ba gaskiya banji daɗi ba gashi yanzu ya tsane ni nayi matuƙar dana sanin ƙin sakar masa da nayi tin farko, ko a yanzu gani yake duk nine na jawo ya rasa ki"

Tace, "hmm dan dai be sani bane amma ko yanzun ma ba wai ya rasanin bane, amma fa karka damu kanka akan wannan indai Khaalif ne ze sakko ne dan fushin sa baya ɗorewa"

Yace, "ina fatan hakan Allah yasa karya ƙullace ni har gaba gaba"

Tace, "amin"

Da haka sukayi sallama ta ajiye wayar sai fara'a take, Nuriya ce ta kalle ta tace, "Ya ABU ya samu lafiya na tayaki murna"

Tace, "nagode Nuriya gaskiya zan kasance cikin farin ciki a wannan ranar samuwar lafiyarsa ta wanke duk wani ɓacin rai nawa"


Nuriya tace, "to Khaalif fa dan yanzu shine abun ji"

Murmushi tayi kafin tace, "Nuriya yau za'a kaini gidan Saifu amma gobe i warhaka ina gidan ubana"


Cikin zaro ido Nuriya tace, "saboda me wai meye yake baki ƙwarin guiwa haka ne??? kashe shi zakiyi??"

Tace, "rufani ki sayani ina ni ina kisan rai??? ke dai ki jira kawai zakiji"



Da misalin ƙarfe ɗaya 01:00 na dare, Aisha cikin rashin sanin madafa take tafiya ga wani jiri da yake ɗibarta tana tafiya tana haɗa hanya, kamar daga sama taga mota ta tsaya a gabanta bata tsaya tunanin komai ba tayi gaba zata wuce, hannunta yaja ya tura ta a motar sannan ya jata da mugun gudu.


Kai tsaye wani madai-dai-cin gida ya kaita har zuwa lokacin batasan ko Waye ba kawai dai tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido,
Sai da ya kunna hasken ɗakin sannan ta gansa cikin zaro ido take kallonsa cikin rawar baki tace, "Dawood kaine?????"

yace, "nine mana A'isha dama nasan hakan zata faru ne shiyasa na kasance a yankin ina jiran zuwan ki, gaskiya ƙanina yayi rashi kai tsaye zan iya kiran sa mutum mara sa'a"


A tsorace tace, "meyesa zaka ƙara shigowa rayuwata kuma?? abunda kaine be ishe ka ba ko me?? meyesa?? me zakayi min???"


Yayi dariya tareda cewa, "haba ƙanwata abun ba na zafi bane ba fa ki nutsu mana yanzu a daren nan ina zaki dosa?? ni bazan miki komai ba kawai zan kora miki wasu bayanai ne"











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 23*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*








da Azhar aka ɗaura auren Saif da Aisha bayan anyi sallar Jumu'at kowa shagalinsa yakeyi amma banda ita da Nuriya dan kuwa Nuriya ta damu da damuwarta sosai hakan yasa itama bata farin ciki.

shirun da tayi tana tunani ne yasa Nuriya cewa, "Aisha tunanin me kike ne haka??"

Ta ɗan murmusa kafin tace, "Khaalif Mohh..."

Murmushin takaici Nuriya tayi kafin tace, "zancen banza da wofi bayan an aura miki wancan shashashan kuma?? kodan bari nai miki uzuri dan SO BA ƘARYA BANE"

tace, "hmm.. ai kin gama magana kuma, ba fa zan dena tunanin Khaalif ba Nuriya dan bansan halin da yake ciki ba tin jiya baya gida kuma lambarsa ma bata tafiya nikuma hankalina nema yake ya kasa jurar hakan dama sai dai kui min uzuri indai akan Khaalif ne na kasa sarrafa kaina gashi sai yanzu nakejin ina ƙara son sa wallahi"

Nuriya tace, "Allah yayi miki maganin damuwar ki hakan kawai shi zan iya cewa"

Ta amsa da "amin"

tin yamma da sauran rana aka ɗauke ta aka kaita gidan Saif aka dangwarar tayi kukan tayi kukan har ta gaji, sai da akayi da gaske sannan aka ɓanɓare ta daga jikin Mama aka tafi da ita,
Zuwa dare gidan ya ɗaɗe ba kowa sai ita kamar tsohuwar mayya.

Tana zaune can ƙuryar gado ta haɗe kai da guiwa sai fizgar numfashi take tana saukewa saboda azababben kukan da tasha ga kanta da ya dasa ciwo kamar ya rabe biyu ga tunane tunane da fargaba sun yi mata cunkusss.
Saif ne yayi sallama a ɗakin, ko motsawa batayi ba da sunan taji motsin mutum.

ƙare mata kallo yayi tass sannan ya saki murmushi aransa yace, "shikenan fa ƙarya ta ƙare Aisha gaki kin shiga hannu"

A zahiri kuwa cewa, "yayi sannu da gida Amarsu".

Har lokacin bata motsa ba sai ma takaici da baƙin ciki da suka ƙara turnuƙo mata.

be ƙara cewa uffan ba yayi waje bayan wani lokaci ya dawo tareda ledoji ya zube sannan ya kalleta yace, "wai har yanzu kina nan?? taso ki ci abinci, kuka baya magani sai dai ya kawo cuta ya zakiyi tinda Allah ya haɗa babu wanda ya isa ya raba, dan haka haƙuri ne ta kama ki dan nan gidan bautar aure ne"

Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalleshi ta kauda kai kafin tace, "bana buƙatar komai da zaka kwashe su ma da yafi, na riga na ci a gidan da ba na bautar aure ba"

Yayi dariya yace, "Aisha kenan ƙarfin hali da tsaurin ido to ba komai baa tilasta mutum"

Banza tayi kamar bata jishi ba, haka ya cigaba da ƴan surutansa duk tayi masa banza har abun yafara ɓata masa rai dan haka ya tattara ta ya watsar daga ƙarshe ma bar mata ɗakin yayi"

tin tana zaune har tagaji ta zame ta kwanta saboda gajiyar Da tayi tana kwanciya bata ja lokaci me tsayi ba bacci ya sungume ta, kamar mara gata haka take baccin a wahalce.

Saif kuwa sai da ya gama shaye shayen sa sannan ya nufo ɗakin kai tsaye kan gadon ya nufa ya zauna kusa da ita ya ƙare mata kallo kafin yayi murmushi, janyo ta yayi zuwa jikinsa saboda farin cikin da yake bakinsa ma yaƙi rufuwa, ba dan komai yake farin ciki ba sai dan ya sa mugunta a ransa ya ɗau aniyar nuna mata iyakatar ta tareda fansar duk wahalar da ya sha akanta.

Cikin bacci tafara jin baƙon al'amari duk da tanada nauyin bacci amma indai za'a taɓa ta to fa zata tashi bare kuma anyi mata me dalilin, cikin matuƙar razani ta farka ido warwaje take kallonsa, zuciyarta ta buga cikin ranta tafara neman tsari dashi dan daga ganin yadda idanunsa suka canja tasan sai da yasha mugayen ƙwayoyi har da na ƙeta dan ta tabbata yayi ƙazamin shiri akanta,
Cikin ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata tafara ƙoƙarin ƙwatar kanta.
da yake ƙarfin ba ɗaya bane takasa saboda yadda yaƙara yimata dabaibayi,
Fashewa tayi da kuka kawai dan bata da abunyi wanda ya wuce shi cikin ranta kuwa ta dage wajen kai kukanta ga Allah tareda neman temakon sa.

bayan wani lokaci ya ture ta daga jikinsa jikinsa har rawa yake saboda jaraba ga ɓacin rai ga kuma ƙwayoyin da ya bankaɗa suna masa aiki, a fasace yace, "dama abunda ake faɗa akanki duk gaskiya ne ko?? ashe dama da gaske bin maza kike munafuka?? bazaki gaya min gaskiya ba"

Ita kuwa ganin ta tsira yasa tayi saurin direwa daga gadon tana murtsike idanunta da suka gaji da koke koken nata, cikin bushewar zuciya tace, "ba nice nake binsu ba su suke bina"

Inda take yayi yana ƙara cewa, "ni zaki yiwa hauka ? bazaki gaya min inda kikai budurcin ki ba? dama an daɗe ana gaya min gaskiya naƙi yarda ashe duk da gaske ne, bazaki bani amsa ta ba sai na ɓallaki"

Ba tareda ta kalleshi ba tace, "kai ni fa duk wannan maganganun banza ne ƙarya ce kawai"

Wata kyakkyawar mangara ya bata har sai da bakinta yafara jini sai da ta ɗauki ɗan lokaci bata ƙara wani motsin kirki ba saboda azabar da ta ratsa ta, kafin tayi maganar ma ya shaƙe mata wuya cikin hargagi yake cewa, "bazaki faɗa min ba?? kuma ki sani sai na ɗau fansar duk abunda nayi wallahi kuma bazan zauna da ke ba na aureki kuma ban samu abunda nake so ba ai baze yuwu ba, ki gaya min waye ɗan iskan naki ko kuma na saɓawa tunanin ki yanzu"

Kai kawai take iya girgiza masa takasa maganar saboda shaƙeta da yayi, sai da ya tabbatar ta jigata sannan ya sake ta sai da yayi mata tsala tsalan maruka guda uku a jere sannan yaƙara jefa mata tambayar"

kuka take na fitar hayyaci da ƙyar ta iya cewa, "gaskiya nake gaya maka wallahi ni bana abunda kace, kawai dai da ina yarinya ne.."

Yace, "akai uban me???"

cikin azabar da take sha tace, "fyaɗe yayi min"

Kukane yaƙara cin ƙarfinta hakan yasa sauran maganar ta maƙale, baji ba gani haka Saif yafara dukanta cikin rashin tausayi da rashin imani, sai da ya tabbatar yayi mata jan duka sannan ya kama hannunta ya jata kamar akuya yayi waje da ita ya watsa ta.

Duk irin magiyar da roƙonsa da takeyi akan ya barta sai gobe yayi kunnen ta shegu, sai ma cewa da yayi "kije tsohon banzan da ya yaudare ni ya bani ke a haka ya tambaye ki ki bashi amsar inda kika barbaɗar da mutuncin ki, kuma na sakeki saki uku ki jira ma na kawo miki takarda dan ya tabbatar ni bazan zauna da mace irin ki ba"

Yayi fuuu ya shiga cikin gidan ya fito ya miƙa mata takarda tareda cewa, "gashi nan na sake ki sai kije ki cigaba da yawon barbaɗin"

Cikin kuka tace, "Saif ko ni ba ƴar uwarka bace ban cancanci wannan hukuncin ba da daddaren nan ina zan tafi? ka barni na kwana dan Allah in yaso gobe da wuri sai na tafi"

Yace, "ki kwanar min a gida??

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login