Showing 3001 words to 6000 words out of 30967 words
kasance bauɗaɗɗiya daga maganar iyayenta ba zaɓin mahaifina ne dan haka zan aureshi muyi haƙuri da duk yadda Allah ya ƙaddara mana mu karɓa hannu bibbiyu insha Allah wata rana zamu ga RIBAR HAƘURI rashinsa ba abunda yake amfana mana sai ɓacin rai mu jure har zuwa lokacin da ta Allah zata kasance"
Khaaalif yace, "banso jin wannan maganganun daga bakin ki ba Ayeeshah dama idan bamu haƙura ba babu yadda zamuyi amma fa dole na nunawa Saif taƙadarancin da yayi mana nashi kaɗan ne"
Cikin kuka tace, "Khaalif indai son gaskiya kake min bana so wata rigimar tsakanin ka da Saifu ka zuba masa ido kawai ina tsoron makircin sa, ka manta da batunsa kawai dan Allah"
Yace, "zan jarraba hakan"
Daga haka ya katse kiran yanajin kamar kansa zeyi tsawa saboda rugugin da yake.
Gaba ɗaya ya tsani kowa bama kamar ɗan uwansa da yake ganin shine wanda yafi shige masa gaba.
Wayarsa ya ɗauka ya kirashi suka yiwa juna tatasss kowa yaji a jikinsa, dan shima ABU idan aka taɓa shi ba haƙuri yau Khaalif ya kaishi ƙarshe dan haka sukayi kaca kaca.
Cikin kwana biyu Aisha ta manta da Saifu ta cigaba da gudanar da rayuwarta ba tareda la'akari da ta kusa aurensa ba.
hakan kuwa ba Ƙaramin zafafa Saif yaƙara yi ba yaso ace ta hukuntu da hakan da yayi mata sai yaga ko a jikinta, Hakan yasa yayi mugun ƙuduri kuma yafara shirin aiwatarwa.
Jose.
Tattare takardun da suke gabansa yayi ya watsar gefe ya ɗauki ƙafa ya ɗora akan ƙaramin tebur ɗin gabansa ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe ido.
Muryar Umma ce ta katse masa tunanin sa, "Jose baka da lafiya fa"
Da mamaki yace, "meke faruwa Umma?"
Umma tace, "cikin aikin ka yanzu akwai kuskure da kuskunda an sanar dani cewa ka zama mashiririci baka abunda ya kamata "
Yace, "Umma waye ya gaya miki wannan zancen??"
Tace, " yaron ka Haruna shine ya sanar dani hakan kuma har anfara tunanin ɗaukar mataki akan ka, banason hakan fa Jose kai da na sani me ƙoƙari da maida hankali akan aiki ya akai yanzu ka koma haka??"
Nazari ya ɗanyi kafin yace, "nima ina da irin wannan tambayoyin Umma akwai wanda yake bibiyar rayuwa ta akwai wanda yake son ganin na kasa kuma duk inda taje tazo an samu bara-gurbi a cikn yaran kusa dani, to waye Umma??"
Umma ta taɓe baki kafin tace, "babu wasu ƴan zille zille da zakai min bansan waye ba dan a yaran naka ma mutum nawa kawai na sani ?? ba dai zakace Haruna bane Jose dan shi yaron kirki ne"
Jinjina kai kawai yayi ba tareda yaƙara magana ba, amma abun yana ɗaure masa kai sosai duk ranar da ya haɗu da Aisha sai yaji ance wani abun, besan ya akai ma mutane suka san yafara soyayya ba mutanen ma kuma ba abokansa ko dangin sa ba gaba ɗaya abokan aikinsa sun san labarin komai yanzu duk motsin sa a idon duniya yake sai yaji ance ai yau kayi kaza to waye wannan da yake bambaɗar da sirrin sa kuwa??, Batun shiririta kuwa ya yarda dan kuwa yanzu duk wani aiki ma baya son jin ko labarin sa komai nashi yafi karkata ga Ashshah.
Yau ya shirya tsaf ya nufi gidan su ABU sai dai zuwan beyi masa daɗi ba saboda ya tarar da abokin nasa ba'a yanayi me daɗi ba jikinsa ne yayi sanyi salam, yau babu surutu ko hirar ma babu,
Matsawa yayi kusa dashi kafin yace, "meke faruwa ne wai??"
ABU yace, "ba komai bane"
Girgiza kai Jose yayi yace, " kuji wani bagwaren zance, ba haka kake ba fa, da an kalle ka za'a san baka cikin yanayi me daɗi da alamu ma kayi kuka amma ahakan kake cewa ba komai?? ai baze yuwu ba"
ABU yace, "idan na faɗa ma babu abunda hakan ze amfana maka sai ɓacin rai"
Jose yace, "na yarda komai yawan ɓacin ran da zanyi naji na kuma yarda, karka manta fa irin amintar dake tsakanin mu ABU babu wani abunda ze taso yasaka kuka kuma kayi tunanin be shafeni ba ka faɗa min duk da ni ba kowa bane amma ta yuwu ko akwai temakon da zan iya yi maka"
ABU ya ɗanyi murmushin ƙarfin hali sannan yace, "Khaalif ya dena ganin mutunci na ya raina ni duk saboda soyayya ta haɗamu guri ɗaya, yakasa tausaya min nima nakasa tausaya masa saboda muna jin duk bazamu iya ba, ina tsoron rasa Eeeahu Jose bansan yadda zanyi ha, kuma Khaalif ya gaya min akwai wani da take so bayan mu kuma narasa ko waye, kayi haƙuri fa abokina tin farko nakasa gaya maka ina son Aishan Mama sai yanzu da komai yaƙare min "
Wani mugun suman zaune Jose yayi sai ido da baki da ya buɗe yana kallon ABU wanda yake maganar sa da gaskiya kuma da yaƙini, zuciyarsa ta shiga tsalle a take zuffa tafara tsatstsafo masa jikinsa yayi sanyi ƙalau tin daga tsakiyar ka har tafin ƙafa
Da mamaki gami da firgici ABU yace, "Abokina?? meke faruwa??? naga kamar abun yazo maka ba daɗi"
Har yanzu Jose yakasa magana sai dai wasu zafafan hawaye da suka ciko idonsa suke ƙoƙarin samun damar gangarowa.
ABU da zuwa yanzu ya gama diriricewa yace, "Jose kar dai kaima kana son Eeeshu?? kayi magana dan Allah ka faɗa min gaskiya abokina kar ka ɓoye min komai"
a hankali ya gyaɗa masa kai alamar hakane,
Zumbur ABU ya tashi daga zauna yafara zarya a cikin ɗakin da kyar da kyar yake jan numfashi yana saukewa saboda nauyin da zuciyarsa tayi kamar an ɗora masa dutse.
Ƙasa Jose yayi da kai tareda lumshe ido hakan ya bawa hawayen damar zubowa, cikin sanyi da kuma sarewa yace, "ka yafe min saboda naso wadda kake so ABU tabbas da nasan kana son Aisha da na hani kaina daga sa rai gareta da na danni zuciyata da haƙura da tunanin ta, A RASHIN SANI son Aisha yayi min mugun kamu ABU kuma nima nakasa gaya maka, ka dena damuwa haka, babu amfanin amintar dake tsakanin mu indai har bazan iya haƙura da farin cikina na samar da naka ba, ina maka fatan nasara a cikin su, na bar maka Aisha abokina ina so ka haɗa da SOYAYYATA da taka guri ɗaya domin nema mata farin ciki, akwai ƙalu bale a rayuwarta ina so ka zamo mata katanga da duk wata damuwa abokina dan Allah kar kace min aa ka amince da buƙata ta ni nayi niyya kuma na janye maka domin a cikin mutane ukun da Aisha take so ina ɗaya daga cikin su"
Dawowa ABU yayi kusa dashi ya zauna girgiza kai yayi gami da cewa, "aa karka jefa kanka cikin matsala saboda ni ni na haƙura Jose"
Jose ya karyar da kai sannan yace, "uhmm dama nasan sai kayi gardama, daga yau ka rubuta ka ajiye babu ni babu Aisha nayi maka alƙawarin fita harkarta zan manta da ita nashimfiɗa sabuwar rayuwa, bayan haka ko meye yafaru dani kasa a ranka daga Allah ne ba daga kai ko ni ko Aisha ba, ina maka fatan nasara kuma ina so ya kasance kaine Gwarzon su iya haka zakai min shine abunda zanji daɗi, daga yau kuma anan gurin labarin ya sauya daga RINTSIN SO ya koma SADAUKARWAR SO na sadaukar da soyayyata gareka abokina"
Kuka ne ya kufcewa ABU wanda yakasa banbance ko na mene, Jose beyi ƙoƙarin dakatar dashi ba dan kuwa shima hawaye yake, sai bayan ɗan wani lokaci sannan ABU yace, "nagode abokina bansan da wane baki zan iya gode maka ba Allah ne kawai ze baka ladan abunda kai min"
Jose yace, "karka ƙara sa damuwa a lamarin ka dan damuwa tana kawo matsaltsalu gare mu kayi ƙoƙarin kare lafiyar ka"
Be bari yayi wani zance ba yafara ƙoƙarin jansa da surutu, sun ɗan daɗe suna hira kafin Jose ya tashi tafiya gida, Allah ne kawai yasan iya raɗaɗi da azabar da yake ciki amma duk ya danne saboda ƙarfafawa abokinsa guiwa sai da yafara tafiya yaƙara tabbatarwa kansa a hargitse yake, azababben ciwon da kansa yake masa ƙara ƙaruwa yake ga jiri jiri da yake ɗibarsa ga tarin ƙuncin da yakeji a zuciyarsa, lokacin har yafara ganin duhu duhu, sauri sauri yake dan ya isa gida kamar daga sama yaga wani me mashin ya shiga gabansa, da sauri yayi gefe da motar shima me mashin ɗin yayi gefen da yayi, me mashin ɗin yafara yin wasa da hankalinsa har ya ida ruɗar dashi, garin ƙoƙarin kauce masa yana dawowa ɗaya hannun sukayi wata kyakkyawar arangama da wani me tifar ɗebo yashi, ji kake kantsam,
Kafin mutane su farga tini me tifar ya gudu dan dama gefe yasa masa ya daka, asalin abunda ya haddasa hakan ma kuɗi aka biyasu daga shi har me mashin ɗin da yafara wasa da hankalinsa har ta kai ga haka.
*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 17*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
waya direban tifar ya cira ya turawa Haruna yaron Jose kira ya sanar dashi ya aiwatar da abunda ya sa shi.
Haruna ya murmusa cikin farin ciki da jindaɗi shima ya kira Saif basu wani magantu ba Haruna ya faɗa masa abunda yafaru duk shirin da sukayi yayi.
Shima Saif Yaji daɗin hakan sosai lokaci guda yaji hankalinsa ya kwanta komai ya lafa ya rage wata matsalar.
Haruna ya kira Ogansa bayan ya ɗaga yace, "Sai Oga kafi ƙarfin kayi sai dai ayi maka, kana daga gefe ka haɗa gwaramar da aka kawar maka da maƙiyin ka cikin sauƙi, Saifu yasa an haɗawa Jose haɗari a yanzu haka ba lallai yana raye ba ko ya rayu ba lallai yayi tsawon rai ba, shima ya kashe tashi matsalar muma ya kashe mana, na tsani ganin Jose shine ya hana ni zama babba kawai aka ɗorashi da tini fa nine ogan sa amma yayi min kaka gida dan haka ya wajabta akaina na kawar dashi na hau kan matsayi na"
Oga yayi wata shegiyar dariya kafin yace, "bansan wane irin kyauta zan maka ba saboda wannan kyakkyawan albushir naka, yanzu na samu damar da zanyi komai kaima ka samu taka damar, amfanin Saif yaƙare garemu ina tunanin, dan haka ka fita harkarsa kawai tin kafin ya gano asalin karatun"
Haruna yace, "Shikenan Oga yadda kace haka za ai babu me yi maka musu Oga"
Da haka sukayi sallama dukansu suna farin cikin an kawar musu da Jose.
Saif
Murmushi ya saki na gayya kafin yace, "saura kai ABU na sallami Jose ɗin yanzu nasan dole yayi nakastuwar da da kanta ma zatace bata son sa, to irin wannan hukuncin ne ya dace da ABU Khaalif kuwa a haka zan cigaba da tafiyar dashi har zuwa lokacin da ze faɗa ramin"
Aisha tana zaune suna ɗan hira da Mama jefi jefi dan kuwa nutsuwarta duk ta tafi gurin tunane tunane, kiran Rookha ne ya shigo ta tashi ta nufi ɗaki tana amsa sallamar da Rookha take mata, cikin sanyi suka gama gaisawa kafin Rookha tace, "Aisha na haƙura da soyayyar ABU na gaji da azabtuwar da nake na haƙura, ba ta ni yake ba hankalin sa baya kaina be damu da Tarin yawan son da nake masa ba, narasa ya zanyi dashi sai a yanzu na yanke hukuncin haƙura dashi dan ba ni yake so ba"
Taƙarasa maganar tana kuka.
Kan kujera Aisha ta zauna cikin kaɗuwa tace, "Rookha??"
Katse ta tayi da cewa, "Aisha ABU ke yake so meyesa zaki tambaye ni bayan kin fini sanin halin da muke ciki gaba ɗaya koda na aureshi bazan samu kwanciyar hankali ba dan haka na haƙura, kawai abunda banji daɗi ba da kika ɓoye min tsakanin ku tin farko, ni kaina na sani ABU baya sona nice nafara son sa kuma be taɓa gaya min yana sona ba dan haka bana ganin laifin ki, kuma shima bashi da laifi nice babbar me laifin da nafara son sa ba tareda bincike ko nazari akan abunda ze je yazo ba, ina miki fatan alkairi a rayuwa Aisha nima ina yiwa kaina fatan samun mafi alkairi ga rayuwata"
daga haka ta tsinke kiran, rintse ido Aisha tayi da ƙarfi gami da cije gefen leɓenta wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska, tabbas bata kyautawa kanta ba sai dai babu yadda ta iya dan ba yin kanta bane.
Cikin tashin hankali mutane suka taru a wajen suka fara ƙoƙarin nema masa temakon gaggawa kai tsaye asibiti suka wuce dashi, baya motsi kamar babu rai a jikinsa kuma gashi babu inda yayi ko ƙwartane sai dai kamar gawa haka yake.
Dandanan likitoci suka taru akansa suka fara ƙoƙarin bashi temako sai dai basu ga alamun ze tashi ba gashi dai zuciyar sa tana bugawa.
Ƙoƙarin neman wani nasa da za'a sanarwa aka farayi cikin sa'a sukayi arangama da lambar Mu'Allim ƙaninsa kai tsaye suka kirashi suka sanar dashi, shi kuwa be sanarwa kowa ba ya nufi asibitin hankali tashe, karo yayi da Dr Muktar yace masa ya biyo shi ofishin sa dan haka ya bishi.
Ruwa ya miƙa masa tareda cewa, "ga ruwa kasha Mu'Allim"
"Nagode" kawai ya iya cewa sannan ya ɗan kurɓi ruwan yaƙara bin Dr Muktar da kallon tuhuma, cikin sanyi yace, "Dr yaya na fa?? meke faruwa dashi?"
Dr Muktar yace, "aa karka fa wani damu yanzu lafiyarsa tana tareda shi insha Allah dan haka ina son sanar da kai ne ko kuma baka shawara akan cewa kar a sanarwa kowa rashin lafiyarsa kasancewar sa Jami'in sirri"
Mu'allim yace, "hakane shiyasa nima ko iyayen mu ban sanarwa ba, ni yanzu ba wannan ne damuwata ba meye ya same shi????"
Jinjina kai Dr Muktar yayi kafin yace, "to maganar gaskiya akwai wata ƙudura ta Allah a rayuwar Jose dan kuwa babu abunda ya same shi duk da irin wannan iftila in da ya faɗa amma sai dai ya samu buguwa sosai, yanzu firgicin da nake ciki kawai ace kansa yayi buguwar da ze manta da rayuwarsa ta baya ko kuma ya samu wata illar amma hakan ma Allah ze kiyaye babu abunda ze faru karka damu, amma fa har yanzu ya faɗa suma har yanzu be dawo ba muna nan dai muna ƙara bincike akai domin gano ina ne inda yafi buguwa dan magance matsalar dan haka ina so ka kwantar da hankalin ka"
Numfashi Mu'Allim ya sauke sannan yace, "Nagode Dr to amma ya akai ya samu haɗarin ma wai??"
Dr yace, "eh to gaskiya ina tunanin sai dai ka nemi yaransa ko kuma abokan aikinsa sai suyi maka bincike domin gano inda bakin zaren yake, amma yanzu karka sanarwa kowa idan ance ina yake ma kawai ka sanar dasu cewa yayi tafiyar gaggawa har dangin ku ma ina tunanin faɗa musu hakan shine mafita"
Jinjina kai kawai Mu'Allim yayi yana godewa Allah.
Dr yace, "wani hanzari ba gudu ba Mu'Allim maganar gaskiya akwai matsalar zuciya a tattare da ɗan uwan ka, da alamu ya shiga wani abu na firgici da damuwa kafin ya faɗa wannan yanayin yana da damuwa sosai wadda idan abun yazo da matsala ze iya zamo masa ciwon zuciya ma kuma me matuƙar illa, idan an samu lafiyar sa yanzu ƙoƙarin da zaka farayi kenan na yaƙi da damuwarsa "
Sosai jikin Mu'allim yayi sanyi ko uffan kasa cewa Dr yayi sai tashi da yayi ya fice.
sai washe gari Allah ya bashi ikon farkawa sai dai ba um ba um um sai bin mutane da ido da yakeyi.
Mu'allim ne ya kalleshi cikin tausayawa yace, "Yaya Jose meke damunka haka dan Allah"
Murmushin ƙarfin hali yayi da kyar yayi magana irin ta marasa lafiya yace, "Umma ta"
Mu,allim yace, "zata zo nan ba da daɗewa ba amma ka faɗa min me yafaru da kai"
Girgiza kai yayi alamar baze faɗa ba hakan yasa Mu,allim yaja bakinsa ya tsuke dan yasan halin kayan sa.
Ba a wani ɓata lokaci me yawa ba Umma ta iso cikin sanyin jiki ta matsa kusa dashi kamar zatayi kuka tace, "ya jikin Jose??"
ya gyaɗa kai tareda cewa, "da sauƙi Umma"
Tace, "Jose meke damunka ne?? ƙanin ka ya gaya min kana da damuwa menene damuwar??"
Girgiza kai yayi kafin yace, "Umma damuwar akan soyayya ne kuma ta wuce tinda na riga na sadaukar da ita wa abokina ABU kuma bana so ku gaya masa banida