Showing 27001 words to 30000 words out of 30967 words
sanyi ƙalau sai yau taƙara tsorata da al'amarin su.
Aisha kuwa zafin ƙiyayyar su ce ta ƙara ta'azzara tinda ta zauna tayi tagumi taƙi kula kowa abun ya bata mamaki sosai duk da tasan irin baƙin halin Saifu batayi zaton hakan ba, gefe guda kuwa tausayin ABU ɗinta yayi mata maƙil.
Sai da kyar Nuriya ta samu ta lallaɓa ta.
a daren ranar ɗaurin auren ne Mahaifin ABU da Mahaifin Jose suka sake kawowa Abba ziyara bayan sun gaisa Abi yace, "to dai kar a gaji damu kamar munyi magana biyu"
Abba yace, "babu komai ai"
Mahaifin ABU yace, "Alhaji ɗana ne yace ya barwa ɗan uwansa ya auri Aisha wato Yusuf shine nima naga hakan ya dace domin kuwa Yusuf ɗin shi yafi dacewa da ita fiyeda kowa, dan haka idan babu damuwa dan Allah a mayar da auren kansa shi kuma ABU sai a aura masa Ruƙayya mun gama magana da iyayenta za'a ɗaura auren tare yanzu kawai izinin ka muke jira idan hakan babu damuwa"
Abba yace, "to Alhamdulillah duk ɗaya ne a wajena amma sai dai ina buƙatar jin ta bakin ta"
Abi yace, "ai hakan yana da kyau babu komai"
Abba yace, "to bari naje naji ko?"
Suka amsa sannan ya nufi cikin gida.
Koda Abba ya sanar mata abunda yafaru sai da takasa ɓoye farin cikinta haka kawai taji gaba ɗaya farin ciki ya lulluɓe ta.
Iya haka ma ya tabbatarwa Abba tafi son Yusuf ɗin akan ABU dan haka ya amsa maganar shima yana farin ciki.
Haka suka rabu cikin girmama juna da mutuntawa, yana shirin komawa ciki ne sai ga Dawood wujiga wujiga dashi, a gaban Abba ya zube a wahalce yace, "Abba ka temake ni karka aurar da Aisha ga wani ba ni ba wallahi mutuwa zanyi idan ban aureta ba, wallahi na tuba nayi nadama bazan kuma ba Abba wallahi na shiryu na faɗa masifa saboda Alhakin ta kaga Abba nima anyiwa ƴata fyaɗe har ta samu mutuwar rabin jiki matata ma ta gujeni ta gudu tabarni gashi yanzu banida shauki Abba ka temake ni karka ƙarasa rabani da farin ciki na nasan kanada tausayi nima ka tausaya min Abba"
Ko da kaɗan Abba beji alamar tausayin Dawood ba sai ma ransa da yayi mugun ɓaci, baya son sake sauraron wasu banzayen maganganun nasa dan haka ya zame yayi cikin gida kawai.
Saƙol Dawood ya tashi sanin baze saurare shi ba, yana tafiya yana kuka kamar ƙaramin yaro, haka ya koma ya tarar da ƴar tilon ƴarsa sai gunjin kuka take ita kaɗai a gida, tsugunnawa yayi a gabanta ya fashe da wani sabon kukan yana cewa, "na cuceki na cuci Aisha Allah baze barni ba, nasan ta dalilina akayi miki haka Bilkisu wallahi ni mugun mutum ne nayi nadamar haihuwa ta da akayi a duniya har narayu, tabbas da mutum yanada sani da be so zuwansa duniya ba indai yasan haka zata faru dashi"
(ni kuwa nace ka sani🤷🏽♀️ tinda kowa yasan ƙarshen mugu baya kyau, Allah ka tsare mana zukatan mu ka karemu da bin son ranmu🙏)
Khaalif saboda baƙin ciki da takaici ma barin gidan yayi ya koma dangin mahaifinsa dan baze iya jurar jin an shafa fatiha ba, sai yanzu ya gane me ake nufi da So lokacin da Allah ya jarrabe shi da sonta bayan tarwatsewar ƙudurin zuciyarsa, yanzu yasan me ake nufi damuwa da ya shige ta da gaske, sai yanzu ya gane me ake nufi da rasa Abunda kake so.
Idan aka gansa sai an tausaya masa saboda yadda yayi ranƙol dashi koda yaushe cikin damuwa da tunani yake.
Saif kuwa da alamun ya birkice ne dan hauka yakeyi sosai ko a gidan su ma be bari ba sai zazzaga bala'i yake ko gajiya bayayi kamar mahaukaci.
Aisha yau kwanan farin ciki tayi har sai da ta ƙagara gari ya waye saboda ƙaguwa da taji an ɗaura mata aure da Jose, su Nuriya sai tsokanarta suke sai dai tayi dariya kawai.
Washe gari da misalin goma da rabi na safiya aka ɗaura auren masu farin ciki sunayi masu baƙin sunayi.
(nikam nace Alhamdulillah na taya murna team Jose)
(Dan Allah kuyi haƙuri da wannan ba yawa, biki muke ina Aurar da ɗa😄 wannan ɗinma da kyar nayi kamar zanyi kuka😂)
*sannan ina me farin cikin sanar daku cewa zan cigaba da Littafin da na Ajiye na ɗora RINTSIN SO, wato SIHIRIN ƘAUNA da yardar Allah*
*INDO CE..*
[7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 29*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
da kallo ɗaya za a gane irin farin cikin da Aisha take ciki sai fara'a da walwala take kamar ba ita ba.
Da yamma aka ɗauke ta aka kaita gidan Umma, tarba ta mutunci ta samu daga kowane ɓangare dangin mahaifinsa da na mahaifiyar sa gaba ɗaya kowa murna yake da zuwan ta,
Duk abunda ake Jose be sani ba shi dai kawai yaga taron mutane maganin kar su dameshi ma sai yabar musu gidan yasan inda dare yayi masa.
zuwa dare ƴan kai amarya duk sun watse ya rage daga ita sai dangin Yusuf sauƙin ta ma dangin mahaifiyarsa duk ɗaya ne da na Mama sai dai Uba kawai suka haɗa amma duk da hakan tasan wasu daga cikin su,
Ita yanzu duk ba ta tasu take ba burinta kawai ta sanya Jose a idanunta amma taji ko labarinsa ba'ayi itama kuma bata tambaye su ba,
Tasha ƴan tayon kwana dan ƴan matan su Kiarat duk wajenta suka dawo suka tare sai da suka raba dare suna surutu kafin suyi bacci, ita dai sai murmushi take musu daga baya ma sai ta kwanta kamar tayi bacci sai dai ba baccin take ba har ma sai da suka rigata baccin.
Sai da tayi kwana biyu a gidan Umma lokacin taro ya tashi sannan Umma ta shiryata tsaff duka gidan suka nufi gidan Yusuf da Abi ya tanadar masa, acan suka tarar da Jose da Abi sai sokana yakewa Abin shi dai sai lallaɓa shi yakeyi.
Koda yaji sallamar su be bi takansu ba ya cigaba da ƴan surutunsa har sai da Kiara ta zauna kusa dashi tace masa Yaya Jose ga Ashshan ka mun kawo maka.
Binta yayi da ido kafin yace, "ke bana son raini fa"
Tace, " da gaske fa gata nan tareda Umma"
Da sauri ya miƙe ya nufi inda Umma take tsaye tana kallonsa cike da tausayawa, idanunta sai zubda ƙwalla suke, gefe guda kuwa farin cikin samuwar farin cikin ɗan nata kamar ya kashe ta.
Cikin rawar jiki ya ƙarasa ya tsaya a gabanta cikin son gazgatawa yace, "Umma?? da gaske KIARA take???"
Umma ta gyaɗa masa kai, a hankali ya matsa gaban Aisha yana ƙare mata kallo kafin yasa hannu ya zame mayafin da aka rufe mata fuska dashi, dogon numfashi yaja tareda sake waro idonsa akan fuskarta, cikin nutsuwa ta ɗago kai cike da ɗokin ganinsa itama ta zuba masa ido, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanunsu suka hautsinu juna yaƙara sakin baki yana kallonta har yanzu gani yake kamar ba gaskiya bane.
Hawayen da kai tsaye zata iya kiransu na farin ciki ne suka kwararo kan fuskarta tareda wani sassanyan murmushi. hannu yasa kan kumatunta ya shiga goge mata ƙwallar cikin wata rikitacciyar murya yace, "Ashshah!!!!! meyesa kike kuka????"
Girgiza masa kai tayi alamar "aa" tana so tayi magana amma takasa sai ma kuka ne ya ƙwace mata, da saurin ya rungume ta cikin kiɗima ya shiga bubbugar bayanta alamun rarrashi tareda tambayar abunda akai mata.
Mu'allim yace, "Yaya Jose naga kana harara ta bafa mune mukai mata laifi ba kaine da kanka"
Yayi magana yana dariya.
Murmushi Jose yayi gami da lumshe idonsa ya buɗe su sannan ya zubawa fuskarta ido lokaci ɗaya ya lula duniyar tunani, a hankali hawaye suka fara sintirin zubowa da sauri ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shashshekar kuka a hankali.
Sun ɗan kwashi lokaci a haka kafin Umma ta share ƙwallarta ta kamo hannunta tareda cewa, "bani ƴata nan da ba cewa kayi baka sonta ba.
badan yaso ba ya bari ta janye ta daga jikinsa, ya durƙusa kan guiwoyin sa cikin muryar kuka yace, "Umma wallahi Ina Sonta bazan kuma cewa hakan ba"
Umma tayi murmushi sannan tace, "na sani Yusuf shiyasa ma na kawota gareka a matsayin ta na matarka, yanzu amana ta dawo gareka Jose kayiwa Aisha adalci ka zauna da ita tsakani ga Allah ba cuta ba cutarwa"
Mu'allim ya dafa kafaɗarsa tareda cewa, "haba Yaya Jose ka dena kuka dan Allah lokacin sa ya wuce yanzu farin ciki ya kamata kayi"
Share ƙwallar yayi kafin ya miƙe, kusa da Abi ya zauna cikin farin ciki yace, "Abi nagode Allah yaƙara girma Allah ya jiƙan manyan ku"
Cike da ƙauna Abi ya rungumeshi yana amsawa da "amin"
Nasihohi sosai Umma da Abi harma da Mu'allim sukai musu kafin suka Rufe da Addu'o'i da fatan alkairi sannan suka barsu a gidan su biyu.
Kusan a tare Yusuf da Aisha suka sauke ajiyar zuciya lokacin da motar su Mu'allim tafara tafiya, hannunta ya riƙo tareda cewa, "Ashsha???"
Ɗago ido tayi ta kalleshi tareda sakar masa tattausan murmushi, shima murmushin yayi cikin sanyin murya yace, "Ashsha Allah yayi ke rabona ce, gashi kin dawo gareni"
Murmushi me sauti tayi tace, "Kalamillah!!! (Cewar Allah) ɗa ɗaya tilo da babu kamarsa, ina farin cikin kasancewa ta matarka Kalamillah"
Tinda ya zuba mata ido ko san ƙiftasu bayayi duk hankalinsa ya tafi akanta maganar da tayi ce tasashi sakin murmushi me sauti har sai da haƙoran sa suka bayyana ya lumshe ido tareda jan numfashi ya sauke"
Jan hannunsa ta shigayi tareda cewa, "mu koma ciki ko?"
Binta kawai yayi zoƙal zoƙal har sai da tace ya rufe gidan sannan ya rufe sukayi Addu'a sannan suka koma ciki,
Tana shirin wucewa sashinta ya dakatar da ita da cewa, "gaskiya tareda ni zaki kwana Ashshah"
Yadda yayi maganar a shagwaɓe sai sa ya bata dariya ta rausayar da kai tace, "to shikenan"
Hannunta ya kama gami da cewa, "riƙe ki zanyi karki gudu ki barni"
Tayi murmushi kafin tace, "Jose yanzu nifa mallakin ka ce har sai kace nagudu sannan zan gudu"
yace, "ai kuwa bazance ba"
Dariya kawai tayi bata sake magana ba har suka isa ɗakinsa, shi kuwa har yafara bata ƴan labarai"
A bakin gado ta zauna tareda cewa, "zaka ɗakko min kaya na?"
Shiru ya ɗanyi sannan yace, "aa bazanje ba sai dai ki raka ni"
Tace, "to meyesa??"
Yace, "wallahi kar naje zaki tafi ki bi Umma"
yadda yake maganar ma kawai ya isa tabbatar da ba wata cikakkiyar nutsuwa ce dashi ba, murmushi me cike da tausayawa tayi tace, "Muje na raka ka "
yace, "yauwa amma ki riƙe hannu na"
Miƙewa tayi ta kama hannun nasa gamm sannan tace, "to muje ko??"
suna tafiya yana bata labari har sukaje suka dawo, gurin shiga wanka ma sai da sukayi mujadala da kyar yabarta ta shiga ita kaɗai ya zauna a bakin ƙofa yana jiranta.
bayan sun ɗauro alwala suka gudanar da sallah .
Suna kammalawa ya janyo kwalba ze fara sha tayi saurin katse shi da cewa, "subhanallah Kalamillah me nake gani haka???!
..
a ɗan kunyace yace, "ɗan kaɗan zansha fa"
Matsowa tayi kusa dashi ta kwantar da kanta akan kafaɗarsa cikin nutsuwa tace, "ba irin wannan ne ya kamace ka ba, kaifa nasanka akwai sauƙin kai ga haƙuri haba Jose ɗina dan Allah kayi haƙuri da shan wannan abun nikam banaso, da fa ba haka kake ba meyesa yanzu kuma zaka koma haka?"
yayi ƙasa da ido kafin yace, "gobe fa?"
Tace, "idan bakasha yau ba kaga gobe ma zaka iya haƙura ai"
A wani irin sangarce yace, "kaiii???? gaskiya ban yarda ba gara nasha yanzu kinga goben ma sai na sha"
Sai yanzu ta fahimci hausar da tayi masa shine shi kuma ya baibaita abun, dariya tayi kafin tace, "ba haka nake nufi ba ina mufin goben ma zaka iya ƙin sha amma dai zakasha ƴar kaɗan"
Murmushi yayi cike da jindaɗi yace, "to na yarda, amma dai kinci abinci ko?"
da sauri tace, "na ci sosai kuwa"
Ya murmusa sannan yace, "to ai da dafa miki zanyi"
tace, "aa na ƙoshi bacci kawai zanyi"
Kafin yayi magana har tafara ƙoƙarin kwanciya, shima kwanciyar yayi tareda yimata matashin kai da damtsen hannunsa sai shafar kanta yake yana murmushi farin ciki yana ƙara lulluɓe zuciyarsa.
*INDO CE..*
[7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 30*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
*shafi na ƙarshe*
A gidan su ABU kuwa zaman lafiya suke sosai dukan su suna bawa juna kulawa dama Rookha a shirye take wa komai saboda shi dan haka ta shirya tsaf dan tarbarsa ta kowace siga ya zo mata, a nasa ɓangaren kuwa duk wata damuwarsa ya cireta ya ajiye a gefe sai ma roƙon Allah da yake da ya yaye masa Son Aisha, ana kwana ana tashi har nutsuwarsa tadawo dai-dai kuma hankalinsa ya koma kan Rookha.
Khaalif ne zaune yayi tagumi duk duniya ya rasa abinda yake masa daɗi jiyake kamar baze iya yafewa kansa ba saboda amanar soyayya da yaci yanzu ya tabbatar Aisha ta me rabo ce kuma tafi ƙarfinsa gashi wata sabuwar fitinar ma gaba ɗaya ya zurmawa son Nuriya yana cike da fargaba da tunanin yadda za ayi ta so shi dan kuwa yasan abunda ya damu Aisha itama ya dameta babu yadda za ayi kai tsaye ta amince dashi.
Saif kuwa gantalewar tasa kullum ƙara yawa take haka kawai ya zama wani mugun masifaffe shi kaɗai ma sai yayi ta zuba bala'i, rana tsaka kuwa aka wayi gari ya nemi ganinsa ya rasa dunɗum.
sai a lokacin ya gane girman kuskurem da ya aikata na na cutar da ABU ta hanyar makantar dashi da kuma haɗin kai da ya bayar wajen tarwatsa nutsuwar Jose gashi yau duk abunda ya shuka ya dawo kansa.
A fannin Haruna yaron Jose kuwa shima ya gama girba nashi makircin ya karɓi matsayin da yake hari na Jose kuma lamarin Allah lokaci guda aka gane ya haɗa hannu da Oga aka kamasu dukansu aka yankewa kowannen su hukunci daidai da abunda ya aikata.
Dawood tsanani iya tsanani yana cikinsa ya rasa gaba ya rasa baya bashida matemaki sai Allah shi kaɗai yake jigila da ƴarsa yake jinyarta gashi duk ɗawainiyar da yake wajen nema mata magani Allah be karya dokar abun ba beyi nasarar samuwar lafiyarta ba, duk ya rame yayi kanjau kamar ba shi ba.
Jose sai godiyar Allah Aisha tayi da gasken gasken wajen ganin ta shiga tsakaninsa da duk wata shiririta kuma tayi nasarar rabashi da shaye shayen da yakeyi kuma ya dawo Asalin Yusuf ɗinsa.
Suna zaune a falo suna hira cikin farin ciki da nishaɗi Mu'allim yayi sallama, amsawa yayi tareda faɗaɗa fara'arsa yace, "ƙaraso mana ƙanina"
Ƙarasawa yayi ya zauna kusa dashi bayan sun gaisa yace, "Yaya daman takardun komawarka aiki ne aka aiko ni dashi"
Da mamaki yace, "kuma ni Yusuf ɗin ba wani ba??"
Mu'allim yace, "ƙwarai Yaya"
Girgiza kai yayi yace, "bazanyi ba banaso"
maganin ma kar yaƙara wata maganar sai ya miƙe ze bar wajen Aisha tayi saurin dakatar dashi da cewa, "lokacin da kabar aikin kaine kasa kanka ne?? ko kuwa kasan hakan zata faru??"
Yace, "Maman Twins bazaki gane bane banason..."
Katse shi tayi da cewa, "basu kyauta ba kam, amma kai da kanka kasan dokar aikin ka, kayi haƙuri badan su ba dan Allah Ina son aikin"
Komawa yayi ya zauna kafin yace, "Mu'allim waye ya aiko ka?"
Yace, "waye kuwa idan ba iyayen mu ba? sune masu burin faranta mana a koda yaushe"
Jinjina kai yayi yace, "kace zan koma"
Cike da farin ciki Mu'allim yace, "Allah yayi maka jagora Yaya na"
Ya murmusa sannan suka amsa da "amin"
Khaalif bashi da zaɓin da ya wuce tinkarar Nuriya dan haka yayi kyakkyawar ɗamara yaje har gidan su, ai kuwa yasha ta sai da tayi masa wankin babban bargo sai da yayi kuka da idonsa amma hakan besa ta saurare shi ba.
Aisha tana kwance tayi matashin kai da damtsen Yusuf tana danne danne kiran Sayid ya shigo da sauri ta amsa tana kiran sunansa, bayan sun gaisa yace, "Aunty Aisha wallahi Yaya Khaalif ya zama abun tausayi Nuriya yake so kuma tace bata son shi tayi masa rashin mutunci a yanzu haka bashida lafiya, dan Allah ki shiga maganar kisa baki ko zata amince dan Allah ku yafe masa tinda har ya gane kuskurensa"
Shiru tayi tana tunani kafin tace, "Sayid sai anjima ko?"
Daga haka ta katse kiran tareda ajiye wayar a gefe tana sauke gwauron numfashi,
kallonta Yusuf yayi kafin yace, "meke faruwa da Khaalif ɗin?"
Cikin sanyi tace, "ƙanwar nan tawa Nuriya yake so shine tayi masa rashin mutunci abun ya taɓani sosai gaskiya"
Yusuf ya murmusa sannan yace, "karki damu Baiwar Allah