Showing 6001 words to 9000 words out of 30967 words

Chapter 3 - RINTSIN SO Book 2 Free Hausa Novel

Unknown   

11 Nov 2024

1172

lafiya dan Allah"

Zama Umma tayi a gefen sa da mamaki tace, "kana sane da abunda kake faɗa kuwa?? kana nufin ABU ma yana son Aisha??"

Be bata amsa ba sai cewa da yayi , "Umma dan Allah ki kira Mama ki gaya mata banida lafiya"


Umma tace, "to saboda me kuma? ka tayar mata da hankali haka kawai ko me??"

Yace, "Umma ki gane dan Allah wallahi ina son ganin Aisha ne ganin ƙarshe nake so nayi mata nasan idan kika faɗawa Mama zata zo duba ni"


Cikin tausayawa Umma tace, "shikenan Yusuf Allah ya baka lafiya "

Yace, "Umma na ma warke fa kawai dama na bugu ne sosai shiyasa duk jikina yake min ciwo ina tunanin fa ƙugu na ya sauka daga kan layi magana ma da kyar nakeyi Umma amma fa duk hakan ba wani abun damuwa bane, ni banso ma na rayu ba naso ace na mutu na bawa wanda basa son ganina sararin duniyar, Allah ne kawai yasan me yake nufi dani da yasa na rayu amma ina ji a jikina na gama ingantacciyar rayuwa wadda zan shiga yanzu bazata kasance me kyau ba"

Yaƙarasa maganar yana zubda ƙwalla, shafar kansa Umma tayi cikin sigar rarrashi tace, "be zama lallai abunda zuciya take saƙawa ba shine abunda ze faru ko yake faruwa a zahiriyya bana so ka dinga irin wannan furucin domin baki kaifi gareshi, kayi mana fatan Alkairi domin ko meye ya sameka mu ya shafa ba kai ba, ka dena kukan nan addu'a itace maganin duk wata damuwa da ta sako mu gaba mu fauwala wa Allah lamuran mu shine yafi kowa sanin halin da muke ciki kuma babu wani ɗan adam da ze dauwama cikin baƙim ciki ko ƙunci dole sauƙi ze zo daga Allah, ka cigaba da addu'a karka gaza da yinta domin ba'a gajiya idan kayi kana ganin batai maka amfani tanan ba to zaka ga tayi maka amfani ta inda baka taɓa zato ba bama lallai kasan tayi maka amfanin ba sai kayi dogon tunani, ka dena kuka domin shi kuka alamar rauni ce Kuma ni Yusuf ɗina jarumi ne ba rago ba"

Hannunta ya riƙe gam tareda rintse idanunsa da suke masa zafi da kyar ya ƙwaƙulo murmushi ya ɗora akan fuskarsa sannan yace, "Umma na dena kema karki damu kanki kinji Ummata kisa a ranki komai yafaru dani Allah ne ya tsara hakan ga rayuwa ta"

Sai a lokacin hawaye suka kwaranyo kan fuskarta tayi saurin zame hannunta ta tashi daga gurin ta juya masa baya cikin muryar da bata fita sosai tace, "ban damu ba Jose ina fatan alkairi gareka a duk inda kake"

Daga haka ta fice daga ɗakin dan gudun yin kuka a gabansa.











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 18*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*







suna zaune suna kallo itada Sayid suna rigima akan remote wayar Mama tafara ƙara, sakar masa tayi tana cewa, "maza ka cinye idan ka tashi, ni bari na kaiwa Mama waya Allah yasa ma muji ance Anti Zulaihat ce ta haihu"

Kafin taƙarasa ya rigata saurin ɗauke wayar yana dariya yace, "da yardar Allah sai satin aurenki zata haihu ni kuma ni zan kai mata wayar kinga anfi ƙarfinki kenan dole ki zauna ki kalli Arewa"

Kansa tayi da nufin ƙwatar wayar sai yatashi da gudu yayi waje itama ta taka masa baya, sai da ya riga ya miƙawa Mama sannan ta ƙaraso tana numfarfashi, harara kawai ta zuba masa sannan ta maida hankalinta kan Mama, jin ta zuba salati ne yasa ta zaro ido tana kallonta, tana sauke wayar ta jefa mata tambayar "me yake faruwa?"

Mama tace, "oo ikon Allah kenan, kana taka Allah na tashi Yusuf Jose ne yayi haɗari yanzu ma haka suna asibiti abun kamar almara"

rarassss zuciyarta ta buga firgitar da tayi tasa ta sarƙe da yawunta ta ƙware aikuwa tafara tari me tsananin zafi takawa tayi da nufin barin gurin amma takasa saboda wani irin tangaɗi da take can ta tsinci kanta a jikin bango lokacin har tafara ganin duhu gashi tarin ba dena shi tayi ba, dishi dishi take iya ji da ganin Sayid da Mama da suka taru akanta ruwa ma Mama ke miƙo mata amma azaba ta hana ta amsa, lokaci ɗaya ta jigata matuƙa ta fita daga hayyacinta idanunta sunyi jajir sun ƙara firfitowa indai kana da zuciyar imani kayi mata kallo ɗaya sai ka tausaya mata, su Mama duk sun ruɗe sun rasa yadda zasuyi gashi da alamu duk maganar ma da sukeyi bata jinsu, ta ɓata lokaci cikin wannan yanayin kafin ta fashe da wani azababben kuka me matuƙar zafi da raɗaɗi"

cikin sanyi Mama tace, "Aisha sannu maza kisha ruwa ki dena kukan kinji ko??"

Girgiza kai tayi alamar "aa" ƙoƙarin tashi tafarayi Mama ta temaka mata da bi bango ta isa ɗaki wayarta ta ɗauka tafara neman lambarsa amma taji a kashe, wani sabon kukan taƙara buɗewa tashin hankalin ta yaƙara ninkuwa a yanzu bata da buri ko muradin da ya wuce tayi tozali dashi taga halin da yake ciki hankalinta ze fi kwanciya, iya rarrashin duniya anyi amma taƙi dena kuka dan dole suka rabu da ita ta cigaba da yin kayanta har zuwa lokacin da ta gaji ta dena sai sauke huci da ajiyar zuciya, Bata dena kiran lambarsa ba amma duk da hakan taƙi tafiya.

Khaalif yana shigowa Mama ta sanar masa zataje asibiti da daddare duba Jose.
tinda Aisha taji haka ta fitar da rai da samun nutsuwa koda sunje da ita, daren kuwa yanayi Khaalif yace babu amfanin zuwa da yara asibiti dan haka ta zauna ta kula da gida ita kuwa Mama ta yarda, baƙin ciki kamar ya kasheta ji take inama zata iya ta rufeshi da duka sai dai hakan baze amfana mata komai ba dan abun takaici kuma yace baza a je da ita ba kuma an tafi da Sayid sai kace shi ba yaron bane,

duk mutanen da suke wajen ba ta tasu yake ba ido kawai yake
bazawa ko ze ganta amma ko me kama da ita be gani ba wata sabuwar damuwar ce taƙara harba masa mashi dandanan yayi ƙasa da ido magana ma ya dena yiwa kowa sai dai alama da kai"

Sayid ne ya matso kusa dashi ya miƙa masa takarda tareda cewa, "saƙon Anti Aisha bata samu zuwa ba"

cikin sauri ya Karɓa ya warware ta yafara karantawa, " kasancewar Mama baza ta zo da Shahid ba yasa ta barni a gida domin kula dashi amma karka damu gobe zan zo ko ta wane hali ne, idan ban ganka ba bazan iya shan iska me daɗi ba, ina fatan dai jikinka da sauƙi ba kamar yadda nake tunani ba na shiga firgici sosai gashi an hanani ganinka"

murmushi ya saki tareda shafar kansa sai a lokacin yaji ɗan sanyi sanyi, "waye ze hanaki ganina ma idan Ba Khaalif ba??" ya jefawa kansa tambaya, wayar Mu'Allim dake kusa dashi ya ɗauka ya tura mata saƙo kamar haka, "tinda kin ɗorawa Mama laifin ba komai Allah ya kaimu goben ina fatan dai kar wani abu ya dameki ina lafiya naji sauƙi sosai koma nace komai yazo da sauƙi kar hakan yasa ki shiga damuwar da zata jawo min matsala kisa a ranki lafiyata ƙalau kuma zaki tabbatar da hakan idan kinzo gobe idan kinga na faɗa ba daidai ba to ina jiran ki hukuntani"

Murmushi ta saki da taga saƙon ta mayar masa da amsa da cewa, "duk da ban tabbata ba amma naji daɗin jin hakan ko ba komai nasan saƙo na ya iso gareka Allah ya ƙara maka lafiya"

a daren ranar da zazzaɓi ta kwana amma da gari ya waye sai tayi kamar ba ita ba saboda tana son fita kuma idan tabari Mama ta gane bata da lafiya babu yadda za ayi ta barta ta fita"

Cikin baƙar doguwar riga ta shirya ta yafa baƙin mayafi batayi kwalliya ba dan dama ba damunta tayi ba kanta a ƙasa tace, "Mama zan tafi aiki Maman Nabia tace nazo"

Ido Mama ta zuba mata tana nazartar yanayinta kafin tace, "kuma shine baki faɗa min da wuri ba??"

Ƙara yin ƙasa tayi da kai kafin tace, "Mama ai yau ta sanar dani hakan kuma yana da kyau naje dan tace akwai aiki da yawa"

Jinjina kai Mama tayi tace, "Allah ya tsare ki kula sosai fa"

Ta amsa da "amin" ta fice cikin sauri sauri, tayi babbar sa'a batayi gamo da kowa ba,
Lambar Mu'Allim ta nema dan ya sanar da ita inda zataje kai tsaye,
ya sanar da ita sun koma gida ma ya rigime musu dole aka taitayeshi akai gida dashi,
Ita hakan daɗi yayi mata dan haka ta nufi gidan nasu.

cikin sakin fuska Umma ta tare ta bayan sun gaisa ta rakata ɗakin da yake, yana kishingiɗe bakin gado Kiarat tana zaune a ƙasa ƙoƙarin lallaɓa shi take yaci abinci amma yayi banza da ita ko kallonta ma yaƙi yi bare tasa ran ze saurari abincin.

Da sallama ta shiga ɗakin kanta a ƙasa Kiyarat ta amsa cikin fara'a tace, "ga Anti ga Anti zo kisa baki ko ze ci abincin nan yanzu Yaya Jose yafi yara murɗewa wallahi yanzu baya son cin abinci"

Fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Kiyarat sannu da ƙoƙari ai kinyi ma idan da nice ni zan cinye abincin na cewa Umma yacinye tinda ba yaro bane"

Kiarat tayi dariya tareda cewa, "ai kuwa wallahi kin kawo shawara da alamu sai yasha duka ma ze dawo dai-dai"

Ido Aisha ta zaro tana cewa, "laa ila Kiarat nifa da wasa nake haba ke kam yanzu ai kamar jariri haka yake sai da rarrashi amma me yakawo zancen duka?? har kinsa ma na tsorata"

Kiarat ta kwashe da dariya tayi hanyar waje tana cewa, "Anti Aisha kece fa kika fara kawo aidiyar"

fitar da tayi ne ya bata damar ƙarasawa kusa dashi ido ta zuba masa cikin tausayawa tace, "Jose?? ya jikinka"


Tattausan murmushi ya sakar mata tareda cewa, "naji sauƙi sosai ki zauna mana"

Zaman tayi a gefensa tana ƙara binsa da ido zatayi magana yayi saurin katse ta da cewa, "ina tunanin ki sai ga ki kinzo da wuri ma ba kamar yadda nayi tunani ba yanzu Kiarat yar raini take cewa na ma dena tunanin ki ba zaki zo yanzu ba"

Ƴar dariya tayi kafin tace, "ai Kiarat akwai ta da son wasa ooh kenan? abunda ta faɗa maka ne yasa ka ƙi cin abinci??"

murmushi yayi yace, "ba ni kaɗai ne nake buƙatar abincin ba ai kema kina buƙatan dan nasan baki ci komai ba tinda kika tashi"

Cikin zaro ido tace, "kaii? ya akai ka sani"

Shiru ya ɗanyi yana kallonta sannan yace, "nasan hakan ƙaramin aiki ne gareki to yanzu bismillah zauna ki ci ko nayi miki ɗura"

Turo baki tayi gaba kafin tace, "aa gaskiya nifa dubiya nazo kuma sai na ɓuge da cin abincin mara lafiya to ba dani ba, ka zauna ka ci naka kawai"

Girgiza kai yayi yace, " nima kuwa bazanci ba"

Miƙewa tayi ta zubo masa abincin ta dawo ta zauna ta wani haɗe fuska kamar gaske a dake tace, "idan bazaka iya ci da kanka ba buɗe bakin"

"iyee?? zarra zaki min??"

Tace, "eh ai naga alamun hakan"

Murmusawa yayi gami da lumshe ido sannan yace, "tinda na ganki ma sai naji na ƙoshi"

Zare masa ido tayi tareda cewa, "wai wasa nake maka?? maza ka karɓa ka ci ko kuma na tashi nai tafiyata"

Da sauri yace, "aa zanci"

Miƙa masa tayi ya karɓa yafara ci yana ɓata rai kamar me cin magani, ba wani da yawa ya ci ba ya ajiye ya janyo ruwa ya ɗan kurɓa sannan yayi wurgi da robar.
Kallonsa tayi baki a sake ta buɗe baki zatayi magana yayi sauri ɗora hannunsa kan nata cikin wani irin salo me ɗauke wutar kai, hakan yasa ta haɗiye maganar ta ƙara warara masa ido, kallon ido cikin ido suka shiga yiwa juna har na tsawon lokaci be gaji ba sai da tafara neman nutsuwarta ta rasa sannan tayi saurin sauke kallonta ƙasa gami da lumshe ido ta sauke ƴar ajiyar zuciya"

Cikin wata sanyayyar murya yace, "Ashshah nayi miki laifi fa, ba tareda na sanar dake ba na barwa amini na soyayyarki, kinsan alfarmar da nake so kiyi min??"

Girgiza kai tayi cikin sanyin da jikinta yayi. ɗan cije leɓensa yayi saboda wani irin zugi da yaji zuciyarsa tanayi, dannewa yayi ta yadda bazata gane ba yace, "dani da ABU duk abu ɗaya ne ina so ki ninka masa son da kike masa ki haɗa da nawa hakan ne kawai ze sani farin ciki a koda yaushe, kar kiji babu daɗi ko kuma ki fahimci hakan abai-bai Abubakar ya fini buƙatar ki Ashshah yana sonki so me tsanani wannan ne karo na farko da yake son wani abu kuma yake sa ran samu ina son ganin farin cikinsa kuma kece wannan farin cikin nasa dan Allah kar kice min aa"


Tinda yafara maganar take kallonsa har ya kai ƙarshe, murmushin da takasa gane na farin ciki ne ko baƙin ciki ya suɓuce mata, tace, "nayi farin ciki kasancewar ka jajirtaccen aboki kuma na ƙwarai, naji daɗi da kayi hakan domin farin cikin abokin ka bazan taɓa so matsala ta shiga tsakanin ku saboda ni ba ka tseratar dani daga wannan tafarkin ina maka godiya Jose, amma abunda yake damuna shine aurena da Saif lokaci koda yaushe ƙara zuwa yake kasan me ya rage yanzu? be wuce sati biyu ba ina cikin matuƙar damuwa Jo amma babu yadda na iya dole na na aureshi"

Taƙarasa maganar tana kuka kashirɓan.
Duk yadda yake daurewa yana cijewa sai da hawayensa suka samu damar zubowa, ya rasa ma ta ina ze fara rarrashinta gashi kukan take da gaske sai yaji zuciyarsa tana ƙara ƙonuwa dan kuwa ya tabbatar kukan nata yana da alaƙa da abubuwa da yawa ba iya maganar ce ta kawo shi ba tausayinta yaƙara ɗarsuwa a ransa zuciyarsa taƙara yin rauni, janyo ta yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana ɗan bubbugar bayanta alamun rarrashi.

Cikin sanyi yace, "kiyi shiru Ashsha dan Allah kiyi haƙuri akan kuskuren da nayi miki bada son raina nayi hakan ba ba kuma dan bana sonki bane bazan iya so wa kaina abunda bazan iya so wa ɗan uwa na ba ni me haƙura da komai ne na barwa ABU koda hakan ze jawo silar mutuwata dan shi wani tsagi ne na rayuwata, kukan nan naki yana ƙona zuciyata sosai dan Allah ki dena"

Tana so ta dena ɗin amma takasa saboda ya riga ya gama cin ƙarfinta sai da kyar ta samu ta rage ƙarfinsa amma duk da haka bata dena ba.

share nasa hawayen yayi yana ƙoƙarin yin magana muryar Abi ta katse shi "wacece wannan kuma Jose??"

Sunkuyar da kai yayi yana ɗan murmushi a shagwaɓe yace, "Abi harna ɗanji kunya"

Abi yace, "na shigo ne da nufin ganinka amma na ganka tareda wata dole na dasa alamar tambaya amma kai komai sai ka saka shi da wasa da alama sunan kakannin ka gareni ko??"

ƴar dariya yayi yace, "Aisha ce ƴar gidan Ɗan Gaske"


Jinjina kai yayi yace, " to meye alaƙarka da ita kuma??"

Yace, "ƙanwata ce fa Abi"


zeyi magana Umma ta katse shi da cewa, "ƴar ƙanwata ce Aisha kenan bayan alaƙa ta jini ma akwai alaƙar soyayya tsakanin su"

Da mamaki Abi yace, "amma meyesa baku sanar dani ba?? da kun faɗa min ai da abun bazeyi girma haka ba ma zanje na samu Ɗan Gasken muyi magana"











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 19*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*








Umma tace, "baka nan ne shiyasa baka sani ba amma ai yanzu komai ya wuce dan ya riga ya haƙura saboda ɗan uwansa yana sonta"

Da kallo Abi ya bishi cikin mamaki da kuma tausayawa,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login