Showing 12001 words to 15000 words out of 30967 words

Chapter 5 - RINTSIN SO Book 2 Free Hausa Novel

Unknown   

11 Nov 2024

1171

mata tayi nata guri.
Kallon kofin tayi taƙara sakin murmushi a zahiri tace, "su kuma ana ta kai suna ta kaya sai kace ance musu zaman auren zanje yi, aikin banza yanzu mutane duk basu da tausayi wallahi, zaki ga na shanye ne wallahi zubar dashi zanyi"

Bata gama surutan ba wayarta ta katseta, sai da zuciyarta ta buga ganin Kiran Khaalif Mohammad dan yanzu tsoronsa takeji, jiki na rawa ta amsa dan idan bata ɗauka ɗin ba ma wata rigimar ce, Cikin sanyi tace, "Assalamu alaikum Khaalif??"











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 20*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*








tashi Mama tayi ta bar ɗakin cikin sanyin jiki abun yayi mata yawa ga ɗan da yanzu bashida kowa sai Allah sai su ya makance ga itama Aisha koda yaushe ƙara fita take daga hayyacin ta.

ABU Umma ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama cikin rawar baki tace, "ɗan nan wannan wane irin baƙin labari ne??"

Abul Abbas ne ya katse ta da cewa, "Umma ai kinfi kowa sani tinda ke kika aikata"

Kafin ya gama rife baki tace, "na shiga uku na lalace Abul ni kuma?? to wallahi tallahi ban aikata ba wallahi ba ni bace"

Rai ɓace Abul Abbas yace, "dama ai babu yadda za ayi ki amsa Umma bansan meye abunda bawan Allahn nan ya tare miki ba a rayuwa duk irin izayar da kikai masa hakan be isa ba sai kin nakasta shi wace irin mummunar zuciya ce wannan Umma?? tabbas badan kin haife ne ba da na ɗauki tsatstsauran mataki akanki wanda bama shi kaɗai ba babu wanda zaki iya cutarwa ko ba mutum bane, amma babu komai duniya ce yadda kika yiwa ɗan wani wata rana za a yiwa naki ko meye ya faru akanmu karkiyi tunanin ƙaddara ce kece kika jawo mana kuma Allah zeyi mana sakayya"

Yaƙarasa maganar cikin kukan baƙin ciki.

Fashewa tayi da kuka harda ɗora hannu aka tana jujjuya kai tareda cewa, "Wallahil azimu ban aikata ba Abubakari ka yafe min dan Allah wallahi nasan na cutar da kai amma nasan ba nice na makanta ka ba wallahi dan Allah karku ƙullace ni ƴaƴan nan amma ko meye ma baƙin halina shine ya jawo min gashi yau na taka sahun da ba nawa ba wayyo Allah ni Sakina yau naga ta kaina"

cikin zafi Abul Abbas ya ɗago zeyi magana ABU yayi saurin dakatar dashi da cewa, "ya isa haka Abbasu, ka manta cewa ita ɗin mahaifiyar ka ce?? bance kar na ƙara jin wannan kalamin daga bakinka ba??"

Cikin kuka yace, "yaya ina baƙin cikin kasancewa ta ɗa gareta dama na mutu tin kafin ta haife ni tabbas da na huta da takaicin duniya dani da kai da ƙannen mu fa duk ƴaƴa ne amma ta fifita mu akanka meye banbancin mu?? ta zalumce ka duk hakan be isa ba, badan kanada dogon kwana ba na tabbata da tini ta kashe ka amma ka tsalle duk wannan siraɗin rayuwar har ka girma ka zama wani hakan be sa ta ƙyale ka ba taga kafi ƙarfin ta shine ta maida kai haka ita ba abun yarda bace nasan zata aikata fin hakan ma"

Da sauri tace, "Abubakar Abbas ku gafarce ni dan Allah wallahi kuskuren baya ne yake bibiya ta amma yanzu ban aikata masa haka ba Abbas wallahi ba ni bace amma nasan bazaku yarda ba saboda banida hali me kyau na zalumci kaina "

Cikin dauriya ABU yace, "Umma zafin zuci ne yasa Abbas yake irin wannan maganar amma ba da gaske yake ba, karki damu kanki ni nasan bazaki aikata min hakan ba ki dena kuka dan Allah"

Cikin hanzari tace, "nagode ɗan nan ko a yanzu kai min rana wallahi ni azzaluma ce na cuci kaina nima Ban taɓa tunani faruwar hakan ba abun ya girgizani wallahi bani bace ka yafe min Abubakar nasan duniya ma bazata barni ba bare lahira ka yafe min ɗan nan"

Share hawayen sa yayi tareda jinjina kai yace, "Umma ki yarda na fa yafe miki kuma nasan ba kece ba banaso ki cigaba da damuwa koda Abbas ze ƙara cewa wani abun"

Tace, "wallahi zan jure ko meye ze faɗa dan nasan nayi, wannan ne kawai ban aikata ba kuma nayi baƙin ciki nayi baƙar nadama ABU in Allah ya yarda nabar mugun halina yanzu zan gyara rayuwata na dena zalumtar ka"


Aisha abun kamar da wasa tana jin zazzaɓi kamar ba na gaske ba sai ya zama na gasken kuka take na fitar hankali yayin da jikinta yake tsuma yayi zafi ɗau ga wani mugun ciwon kai da ya tirsaso ta yake mata barazana, har wunin ranar yafaru ya ƙare bata cewa kowa uffan ba sai aikin kuka Abinci kuwa ko tunaninsa batayi bare tasa ran zata




yau Mama ta shirya zuwa dubashi dan taga halin da yake ciki babu yadda Aisha batayi ba akan su tafi tare amma taƙi Khaalif kuwa dama shine ɗan hannunta bata son laifinsa haka ko me yafaɗa hawa take ta zauna musamman idan akan Aisha ne dan haka ta murzawa idonta toka tace baza taje da ita ba dole ta haƙura.

Tinda ta shiga ɗaki ta kulle ta nemi guri ta zauna ta haɗe kai da guiwa bata da aikin da ya wuce tayi kuka ta share ƙwallar sai tunane tunane da sukai mata yawa ga tarin damuwa, ita kanta a yanzu tasan bata da lafiya"

Tana zaune ta ji sallamar Khaalif takaici ne yaƙara lulluɓe ta, kai tsaye ɗakin ya nufa har ya ya isa inda take bata ɗago ba da sunan tasan ya shigo, ƙare mata kallo yayi kafin ya murmusa sannan yace, "Ayeesha kiyi haƙuri fa nakasa jurar hakan ne shiyasa nace Mama kar taje dake"

cikin ɓacin rai tace, "me kuma zaka gaya min?? bana son jin komai dan Allah kayi shiru da bakin ka"

Karyar da kai yayi kafin yace, "meye na ɓacin rai kuma bayan kece kika jawo faruwar hakan, kin sani ina kishin ki sosai kuma ina sonki so mara misaltuwa amma baki damu dani ba kan yadda kika damu dasu mamakin suman da kikai saboda ABU ya makance sai da ya hanani bacci fa, dan na hanaki zuwa duba Jose shikenan sai da kowa ya ɗanɗana ɓacin rai saboda kema ranki ya ɓaci kuma duk da hakan sai da kikaje, duk meye hakan yake nufi?? bakya sona ko Ayeeshah??"

Kuka ta shiga razgawa cike da tausayin kanta ji take inama zata iya ta rufeshi da duka ranta in yayi dubu ya gama ɓaci ta rasa meyesa baya tausayinta baya sassauta mata kodan mugun halin da take ciki"

Ɗan murmushi yayi yace, "bana jindaɗin kukan nan naki amma ke kuma shine zaɓin ki, ki dena wahalar da kanki kawai kisa a ranki nine mijin da zaki aura bayan ni kuma ko waye to fa babu zaman lafiya bare kwanciyar hankali wannan kawai nake so ki dinga tunawa dan haka ki dena sa kanki a damuwa, tin yanzu gashi kin gani da idon ki nasan dai da hankalin ki bazaki auri makaho ba haka kuma bazaki auri mahaukaci kuma ɗan shaye-shaye ba"

A matuƙar razane ta ɗago tana kallon sa da idanunta da suka gama fita daga hayyacin su cikin tsananin firgici take masa kallon neman ƙarin bayani.

Gira ya ɗaga mata tareda cewa, "ƙwarai nasan zakiji abun a bauɗe, nasan kinsan dai Saif yana ta'ammali da ƙwayoyi to ba wannan ne abun damuwar ba domin nasan ba son Saif kike ba, wanda kika so ɗin kuma kike masa kallon me hankali shine yanzu ya zama mahaukaci kuma ya zama mashayin giya kinsan waye ?? Jose kenan yanzu hakan ma baya gidan su ya zama gantali daɗi aikinsa ma suna gab da korar sa saboda ya haukace ba'a hayyacinsa yake ba gashi kuma ɗayan ya makance yanzu kinga babu wanda ya rage miki sai Khaalif Moh... wanda bakyaso ɗin"

lokaci ɗaya jikinta yaƙara rikicewa tsoro da razani suka bayyano, cikin rawar baki tace, "Jose ɗina ya haukace kake cewa?? kasan kuwa me kake faɗe Moh... anya kuwa ba kaine ka haukace ba?? a hayyacin ka kake kuwa??"

ƙasa yayi da kai yana murmushi yace, "Ayeeesha Ayeesha wallahi kina burgeni ina dai kinji abunda na faɗa?? to ki tabbatar dan kinsan bazan miki ƙarya ba"

da sauri tace, "indai hakane kuwa a yanzu banida zaɓin da ya wuce su biyun ka dena tunani dan sun zama haka zan guje su tausayin su yasa nake jin kamar nayi hauka tabbas da ana auren maza biyu da na auri Yusuf da Abubakar ban zamo irin matan da suke gudun masoyan su ba dan wata jarrabawa ta faɗa kansu, bazan taɓa dena son su ba idan kuwa kunyi wannan tunanin to kun yaudari kanku zan cigaba da neman zaɓin Allah kuma indai ya kasance ɗayan su ne mijina to zan aureshi ba tareda nayi duba da halin da suke ciki ba, nayiwa kaina tabbacin ABU ya makance ne ta dalilin soyayya ta a wannan tafarkin ne aka nakastar dashi kuma Allah zeyi mana sakayya duk wanda ya zalumce mu Allah baze barshi ba Khaalif ka bar bin son zuciyarka kaji tausayina ka tausayawa ɗan uwanka son zuciya baya kai mutum hanya me kyau bana son ka faɗa wani yanayi saboda son zuciyar ka Khaalif ka dena Khaalif ɗina karka zama mutumin banza dan Allah"

Ta ƙarasa maganar tana ƙara fashewa da wani sabon kukan.

Ido ya zuba mata har wani lokaci sannan ya tashi ya nufi hanyar fita har ya kusa ƙofa ya juyo yace, "ban zamo yadda kike tunani ba amma dama nayi miki kashedi karki bari na rikiɗa na zama wani daban ba Khaalif ɗinki ba Ayeeesha yanzu banajin tausayin kowa akanki maganar gaskiya idona ya rufe ina ganin ma nafi ɗan uwana makanta saboda sonki, kuma bazan karaya ba Allah shine yasan daidai tayuwu duk abunda kike tunani ba lallai ya yuwu ba kwatsam zaki iya wayar gari kiga na zama mijinki ni kuma wannan shine mafarki na kuma shine cikar muradin Khaalif Mohammad"


Daga haka yayi waje yabarta da sakakken baki tana kallonsa maganganunsa suka shiga yimata yawo a tunanin ta, kamar mahaukaciya haka takejin ta saboda yadda duk tunanin ta ya wargatse zuciyarta take ƙuna da raɗaɗi, ga ƙululun baƙin ciki da yayi mata tsaye a maƙoshi, tabbas badan tasan hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma tana tsoron hukuncin da itama ta shiga sahun su ta kashe kanta ta huta da zafin duniya, yanzu ta tabbatar bata shigo duniyar a sa'a"

Bata haƙura da tambayar Mama akan zataje duba ABU ba amma maganganun Khaalif sun sa Mama tayi kunnen ta shegu da ita.

yau tana zaune bayan ta gama kuka ta gaji wayarta tafara ƙara, cikin sauri ta ɗauka gami da yin sallama, ABU ya amsa sannan ya cigaba da cewa, "kina lafiya dai ko?"


Wani gwauron numfashi ta sauke sannan ta gyaɗa kai kamar yana ganinta takasa cewa uffan.

Cigaba yayi da cewa, "Eeeshu kiyi magana mana dan Allah ABU ne ko baki ganeni bane?? na matsu naji lafiyarki dan bana cikin nutsuwata har yanzu"

Sai da ta haɗiyi wani ƙullutu sannan tace, "Ya ABU lafiya ta ba itace abun damuwa ba kana cikin irin wannan halin karka damu kanka akaina dan Allah bana so ka sawa kanka wata damuwar bayan taka, ina lafiya kuma ina tareda kai a koda yaushe duk da an hanani ganinka amma addu'a ta nasan tana bibiyarka Allah yasan da kai kuma ze yaye maka karkayi tunanin a haka zaka dauwama duk me son ganin kukan ka in Allah ya yarda sai ka gagareshi"











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 22*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*







murmushi yayi tareda cewa, "ya akai kike wani saurin kiran sunana??"

Ƙasa tayi da kai sannan tace, "ba komai"

Yace, "Amarya kenan, shikenan nima ba wani abu zance miki ba wata dama ce kawai zan baki shiyasa na kiraki idan kina so fa amma"

Tace, "ina jinka Allah yasa zata amsu"

Murmusawa yayi yace, "wannan kuma abunda ya shafe ki ne, kina sona ko??"

Tace, "eh"

Yace, "idan har da gaske ne to ki shirya gobe zamu bar gida, amma fa sai kin amince, babu amfanin ki zauna kina ɓata lokacin ki a banza kinsan ko maza sun ƙare bazaki zauna da Saif ba ko?? to ina ganin tin kafin a ɗaura auren kawai ki bi ni"

Shiru tayi tana tunani kafin tace, "kayi haƙuri Khaalif Moh.. ina sonka amma bazan iya yin abunda kake so ba a wannan ƙadamin, bazan iya saɓawa iyaye na akan son zuciyar mu ba, shi Abba babu ruwansa ko me na aikata laifin ze ƙare ne akan Mama ta batasan irin wainar da muke soyawa ba batasan halin da muke ciki ba haka laifin da mukayi ze rataya a wuyanta bazan iya zalimtar ta ba Khaalif Moh.. ba wai dan bana sonka bane ya kamata ka fahimce ni dan Allah"

Taƙarasa magana tana shirin fashewa da kuka.

Jinjina kai yayi sannan yace, "zaɓi me kyau Ayeeshah kije kiyi auren ki keda Saif sai kuma ku jirayi abunda ze biyo baya"

tace, "ko a yanzu jiran hukuncin ka nake Khaalif na yarda da ko menene amma bazanyi wannan kasadar ba zan auri Saif"

Yace, "bance fa karki aureshi ba Allah ya sanya alkairi, kuma ki fito yanzun nan ina jiranki idan baki zo ba kuma kinsan kwanan zancen"

Kafin ya gama magana ta miƙe jikinta har rawa yake cikin sauri tace, "gani nan zuwa"...

Murmusawa yayi sannan ya ajiye wayar.

Surar kofin da Anti Maimuna ta kawo mata tayi ta kundume a cikin hijab dinta sannan tayo waje dashi tana fakar idonsa ta zubar dashi tayi wurgi da kofin sannan ta cigaba da tafiya, tana fita ƙofar gidan tayi katari dashi ya tsira mata ido kamar me shirin haɗiye ta da sauri tayi ƙasa da kai tana wasa da yatsunta.

Daf da ita ya matso sannan yace, "ga mota can je ki shiga salin alin"

Bata tsaya gardama ba ta nufi inda motar take gidan gaba ya buɗe mata tayi masa banza ta shiga baya, murmusawa yayi sannan ya shiga yafara janta, tin batayi magana ba har tagaji tace, "wai ina zaka kaini Khaalif??"

Yace, "kasshh irinku ne bakwa cin ribar zance baki bari kin gani ba ai kika fara tambaya, ba komai bane ba fa kawai irin yadda Jose yakeyi nima shi zanyi yau ko shi kaɗaine yake da matsayin ɗaukarki a mota? kodan shi ɗan masu dashi ne?? ni kuwa kinga iyaye na ma sun mutu"

Cikin sanyi tace, "ba haka bane ba fa ka fahimce ni mana Khaalif ka rufamin asiri karka cutar dani ko kayi abunda zaka ƙuntaci iyaye na, ka mayar dani gida dan Allah"

Kai tsaye yace, "Ayeeshah aurefa zakiyi zaki auri wani ta yaya ni kuma hankalina ze kwanta "

Shiru tayi masa har sai da yaje inda yake son tsayawa sannan ya tsayar da motar ya fito ya koma baya, cikin zaro ido take kallonsa yayin da bugun zuciyarta yake ƙara ƙaruwa baki na rawa ta kira sunan sa "Khaalif!!!!!"

Cikin wata narkakkiyar murya ya amsa mata da cewa, "Ayeesha nah!!!!"

Saurin sauke kanta tayi zuwa ƙasa har cikin ranta tsoro ya dirar mata tayi shiru tana tsammanin abunda ze ce, Gefe guda kuwa wutar so gami da tausayinsa sai azalzalarta suke"

Tana cikin tunani taji yasa hannu ya ɗago haɓarta yana cewa, "kin kasa haɗa ido dani fa Ayeeshah"

Sai a lokacin ta ware idanunta a cikin nasa lokaci ɗaya taƙara lulawa duniyar tunani wanda ya jawo zubar hawayenta, lallai ta yarda duniyar abai-bai tazo mata dama haka rayuwa take idan Allah yaso sai ya wadataka da komai sai kuma ya tauyeka ta wani gurin ko kuma ka samu silar ƙuntata a dalilin da baka zata ba to ita tata ƙaddarar ɗa namiji ne bata da wani ciwo ko damuwar da ta wuce namiji shine yafara nakasta ta sannan basu haƙura ba kowa ya ɗora idonsa akanta farmaki yake

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login