Showing 30001 words to 30967 words out of 30967 words

Chapter 11 - RINTSIN SO Book 2 Free Hausa Novel

Unknown   

11 Nov 2024

1166

har hauka nayi na dawo nai hankali saboda sonki kuma gashi Allah yayi na mallake ki kinga kuwa idan dai rabonsa ce to fa dolenta tasa ce, kinsan ya za'ayi??"

ta Girgiza kai alamar "aa"

Yace, "kira mana ita a waya mu bata baki nasan zata sakko, kuma kinsan ƙanin nawa ba baya bane tinda har yayi nasarar sace zuciyar Zinariyar kinga kuwa ai itama cikin sauƙi zata faɗa"

Murmushi Aisha tayi sannan tace, "shikenan"

Sai da tayi kira uku sannan ta ɗauka bayan ta kusan katsewa, Aisha tace, "haka duniyar ta zama?? wai muna ta taku amma ba ta tamu kuke ba meye rayuwar ne har zanyi kira uku manya manya ba'a ɗauka ba ko nima laifin Khaalif ne ya shafeni??"


ɗan Murmushi tayi tace, "haba dai wallahi bana kusa ne ya gidan ya ɗan namu?"


Aisha tace, "waye yace miki namiji zan haifa ne?? har kinsa uban ɗan yafara wani yashe baki kamar wani me tallan makilin to ƴan biyu zan haifa kuma duk mata ɗaya me sunan Mama ɗaya me sunan Umma kin gane ko???"

dariya Yusuf yayi tareda cewa, "insha Allahu namiji zaki haifa min"

Nuriya tace, "ato ina dalili haihuwar fari ta haifa maka mata wallahi karka yarda kwana kaɗan zakaji an fara kawo maka sirikai daga haka sai kaji ana Kaka Kaka"

Dariya sukayi sosai kafin yace, "na ɗauki wannan zigar taki kuwa Nuriya?"

Tace, "af zauna kallon ruwa kwaɗo yai maka ƙafa to Allah dai ya raba lafiya ni kam zanga me za'a haifa"

Yayi saurin cewa, "ƴan biyu duk maza"

Nuriya tace, "to Allah ya baka"


Aisha tace, "kinga malama ba wannan ba tukunna ina dalilin ki na sassabawa Khaalif ɗina rashin mutunci"

Murmushin takaici tayi tace, "kiji ƴar iska wani Khaalif ɗinki nayi masa ɗin bana son harkar rashin amana kinsani"

Aisha tace, "to amma madam kinsani sarai yanzu Khaalif ya canja kinga kuwa da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu kinga kinsa shi rashin lafiya"

Zatayi magana Yusuf Jose ya dakatar da ita da cewa, "aaaa ba haka akeyi ba Nuriya itafa rayuwa tana son afuwa da masu afuwa idan mukayi haƙuri muka manta da baya mukai ƙoƙarin gyara gaba sai kiga Allah yayi mana temako rayuwar tayi mana daɗi, kiyi haƙuri komai ai ya wuce ki yafe masa"

ta buɗi baki zatayi magana Aisha ma ta ƙara tarar numfashinta, sai da sukayi mata nasihu masu ratsa jiki sosai har suka tabbatar tayi sanyi sannan sukayi sallama.

Suna gama wayar ta shiga turawa Khaalif kira, jikinsa har ɓari yake wajen ɗagawa amma sai yakasa magana. sai da taja shi da surutu sannan ya warware yana ɗan taya ta.
Tin daga lokacin take kiransa da ya gane cewa ta dawo gareshi farin cikinsa kasa ɓoyuwa yayi yanzu bashida zancen da ya Wuce Nuriya kullum baitinsa kenan,
Sunyi sabo da shaƙuwa sosai da sosai.


ana kwana ana tashi har magana tayi ƙarfi komai ya kankama aka tsayarda lokacin auren Khaalif Mohammad da Nuriya.

yau Aisha ta tashi ba lafiya har ta kaiga asibiti bayan wani lokaci ma'aikatan asibitin suka sanarwa Yusuf cewar an samu ƴan tagwaye mace da namiji amma sun koma dukansu macen bata zo da rai ba namijin kuma daga baya ya koma.

Sosai jikinsa yayi sanyi liƙiss
Allah kenan me yadda yaso gashi dai ya basu ƴan biyun da suke ta muradi kuma ya karɓi abunsa.

Bayan wasu lokuta aka sallemata daga asibitin ta samu lafiya sosai tayi tangargar.


Haka suka koma rayuwarsu cikin farin ciki da walwala bayan wasu watanni taƙara samun wani cikin, sai fatan Allah ya raba lafiya.


Rookha ma ta samu ƴarta mace santaleliya taci sunan Aisha ana kiranta Humaira.



Tana zaune ta miƙe ƙafa sai ciye ciye da gwaguye gwaguye take itace goruba itace gyaɗa itace aya.
Yusuf ne yayi sallama ta amsa tana murmushi tace, "barka da dawowa"


Yace, "yauwa, kina nan kina cin ko?"
Tayi dariya gami da cewa, "kyautar da Allah ya baka ce ta kawo hakan"

Dariya yayi yace, "to Allah ya raba lafiya kuma ya bamu masu albarka"

Ta amsa da "amin"


Bayan wani ɗan lokaci ta haihu lafiya ƙalau ta samu namiji shi kuma yaci sunan ABU Abubakar.

Ansha murna da farin ciki ta ko ina ALHAMDULILLAH .








*Alhamdulillah. anan na kawo ƙarshen littafi na me suna RINTSIN SO na godewa Allah da yabani ikon farashi lafiya kuma na gamashi lafiya kuma ina roƙon yafiyarsa a dukkan kuskure na a ciki.*


*ina godiya sosai masoyana ina fatan ganin so da ƙaunar ku a littafina na gaba da nayi waja waja da basirata wajen tsara muku shi wato DOGON YARO* inkiya *(JANCY)* *Naira 300 Ne Kacal Ba Yawa, Sai Na Jiku.*


*KU BIYO NI A CIKIN LITTAFIN (SIHIRIN ƘAUNA) DOMIN JIN MEKE ƘUNSHE A CIKIN WANNAN SALON SHI KUMA KYAUTA NE BA KO SISI KAWAI ƘAUNA CE TASA NA TSARA KUMA NA RUBUTA MUKU SHI*


Sunayen littafai na. Sirrin Ƙeta A Jini Ɗaya Tajmahaal paid book Ib Ɗan Wanka Rintsin So tareda Sihirin Ƙauna da nake kan rubutawa sai Dogon Yaro.





*Jinjina gareki Ummu Sulaim ina godiya da yabawa da irin ƙoƙarin ki Allah ya saka da Alkairi*

*Waziriya ta wato Salmaaji kema taki dabance Allah yabar kyakkyawar ƙauna*


*sauran masoyana musamman Group 1 abun alfaharina Allah ya ƙara zumunci, bazan iya zayyana sunayen ku ba amma tabbas kuna raina*














*INDO CE..*

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login