Showing 24001 words to 27000 words out of 89000 words
ya cika, nafa san abinda nake yi," Abdul ya
koma ya xauna yana murmushin mugunta yace "vry good dad."
baffan ya kirkiro murmushi yyi pat din bayansa yace "gud son xan
fita guy, sai na dawo," yana kai wa nn ya fice daga dakin da sauri.
Abdul ya mike tsaye yana murmushin mugunta hade da cije lebe,
can kuma ya fashe da dariya har da buga kafa snn ya fice daga
dakin yana fi to. Hmm sistrs knn, ku dinga ma mutum uxuri plss,
ku ka san abinda ya hanani post kwana biyu, rashin lfya ne, wani
abun daban ne, duk baku yi tunanin hka ba, amma har na samu
masu gaya min magana a whatsapp, wasu har da cewa xa suyi
xuciya su daina karanta littafin khaleesah Haiydar, hmm ok oo,
baku yi tunann ko ina da aure ba ko ina da yara da burden dinsu
baxae bari nayi type ba wani lkcn, ni dae don mu nishadantu
kuma don na fadakar nake yin wnn abun, amma Allah sarki
makiyana sun fi masoyana yawa, duk da hka ina sonku gaba
daya, Allah ya bar [truncated by WhatsApp]
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 31..... Hajiya Zuwaira ta
bude baki da mamaki tana kallon Aneesah, har ta gama
fadin abinda ke ranta snn ta fice daga dakin har tana
neman bangajeta, hajiyar ta rike haba da mamaki tace "ni
'yar nn ke gaya ma magana hka? Haiydar ya juya yana
kallon Ammi dake xaune har lkcn bata bude baki ba yace
"yauwa muna magana Ammi," Ammi tace "uhum ina jinka
Aliyu," yace "ko kuma ma dae bari xan dawo xuwa anjima
Ammi, sae muyi maganar," yana kai wa nn ya mike ba tare
da ya kalle Hajiya zuwairar da har lkcn bakin ta yaki rufuwa
ba ya fice daga dakin, Hajiyar tayi murmushin takaici tace
"xa ku gane kuranku in dae ni ce zuwaira " tana gama fadin
hka ta juya fuu tayi hanyar fita daga gidan tana huci,
Aneesah dake xaune kan kujera a tsakar gidan tana hawaye
Haiydar na durkushe gabanta yana mata magana suka bita
da kallo har ta fita, Haiydar yyi murmushi yace "hmm mu je
dae xuwa," ya mike ya koma cikin dakin Aneesah ta bisa da
kallo, ya dde cikin dakin ko me yake ce ma Ammi, can dae
ya fito yana kallonta yace "je dauko Hijab Aneesah," ta
tsura masa ido tana kallonsa ya gyada mata kai, ta mike
jikinta a sanyaye ta shiga dakin dauko hijab, ta xauna
gaban Amminta tace "Ammi yace na dauko hijab," Ammi
tace "Sae kun dawo ki kula da kanki Aneesah," Aneesah ta
mike a hankali tace "to Ammi" snn ta fita, makaranta ya kai
ta yyi mata registrn waec da neco, snn suka dawo gida
wajen karfe sha daya na safe bayan tayi registre din lesson
din makarantar kafin a fara jarabawan, ta rasa irin godiyar
da xata ma Haiydar kawae ta fashe masa da kuka bayan yyi
parkin, nn ya barta kofar gidan nasu ya wuce don bai ga
abinda take ma kuka ba a nn. Da yamma tana xaune tsakar
gida tana duba litattafenta don gobe xata fara xuwa lesson
din daga karfe tara xuwa karfe biyu na rana, Ammi kuwa ta
tafi kasuwa, taji an bude kofar xaure a tunaninta Ammi ce
ta mike da sauri karbo kayan hannunta ta kusan cin karo
da mutum, ta koma baya da sauri, Abdul ne, ta juya xata
bar wajen gabanta na faduwa ganin Amminta bata nn ya
fixgota ya hada da bango yana mata wani irin kallo, tuni
jikinta ya dau rawa amma ta dake tace "meye hka xaka fado
ma mutane gida ba sallama," ya take mata kafa da
takalminsa tayi yar kara yana rike da kafadarta yace "daxun
wani rashin kunya kika yi ma momyna?" ta galla masa
harara gabanta na faduwa a xuciyarta tana ta adduar Allah
ya dawo da Ammi a lkcn, a fili kuma tace "ni ka sake ni don
Allah malam," ya fixge dan kwalin kanta yana mata wani
mayen kallo yace "uwata kika yi ma fitsara daxu ko," tace
"ni ka rabu dani" ya daura hannu kan gashin kanta yana
shafa gashin yace "wae ma wani mutumi ne ya xo gidan nn
daxu da safe?" ta buge masa hannu a tsorace tace "wae me
nayi maka xaka takura ma rayuwata hka ne," ya juya yana
kallon kofar dakinsu yace "uwarki fa?" da sauri xuciyarta na
bugawa ta galla masa harara tace "bacci take," ya daga
kafada ya kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace "we
re goin out now, xaki dan rakani nn cikin gari"
Like · 7 · Report · 44 minutes ago
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 30..... Ya karaso gabanta ya tsaya yana dan bubbuga kafa a kasa yana mata wani irin kallo, bata ko daga kai ta kalle inda yake ba ta karasa alwalanta ta mike xata shiga daki ya kamo hannunta, murya kasa kasa yace "baki da respect yarinyar nn ko, baki ga mijinki bne?" ta fixge hannunta a fusace ta daka masa tsawa "wae ni ka rabu dani mana malam, a ina na san ka," xae yi magana Ammi ta fito daga daki tana kallonsu, tace "xo ki wuce ciki," Aneesah ta wuce sa da sauri ta shige daki, ya tsaya yana ma Ammin kallon rainin wayo, can yyi dariya yace "hope kin shirya rabuwa da 'yar ki ynxu Hajiya maryam," Ammi bata ce masa komai ba ta juya ta shige dakin ita ma ta rufo kofar. Ya karashi dariyarsa ya fice daga gidan, Ammi ta dubi Aneesah da ta xauna tayi jigum bayan ta idar da sllh tace "shi yasa nace ki shirya ki wuce gombe Aneesah, ko xuwa gobe xan baki kudin mota ki tafi," Aneesah bata ce komai ba sae dae hawaye ya taru idonta ta sunkuyar da kanta da sauri gudun kar Ammi ta gani, ranar kasa bacci Aneesah tayi, tunanin rabuwa da Amminta da ya Haiydar take cikin 'yan kwanakin da basu wuce wata daya ba ba karamin shakuwa tayi da Haiydar ba, ita kam dawowar Abdul ba karamin tashin hankali bane gare ta, tun tana karamarta dama ta tsane shi don bae da kamun kai ga son mata, da kyar Aneesah ta iya tashi washegari don ji tayi duk jikinta ba kwari, karfe takwas tana xaune koko da kosae a gabanta ta kasa ci sae jujjuya kosan take, Ammi ko na ta faman hada mata kayanta, wayan da Haiydar ya bata ya shiga ring ta juya da sauri tana kallon wayar, Ammi tace "ba na ce ki mayar masa da wayarsa ba Aneesah," a sanyaye Aneesah ta ce "dama yau xan maida masa Ammi, shi ne ma ke kiran," ta daga wayar suka gaisa yace gashi ya kusa anguwarsu, ta wara ido tana kallon Ammi tace "yanxu?" yace "ko na juya," ta girgixa kanta a hankali tace "A'a ni ban ce ba," yyi murmushi ya kashe wayan, ta juya tana kallon agogo ammi tace "me ya faru kuma?" ta sunkuyar da kanta tace "kila wayar xae xo karba yace yana hanya," Ammi bata sake cewa komai ba ta ci gaba da abinda take, yana parkin kofar gidansu ya kirata ta saka hijab ta fita jikinta a sanyaye bayan ta nemi ixini gun Amminta, ya fito yana kallonta yace "me ya faru Aneesah," tace "ba komai kai na ne ke min ciwo kawae," yace "Ayya kin sha magani to?" ta gyada masa kai kawae tana kallonsa, yana sanye ne da bakar suit yyi kyau ba kadan ba, yana kallonta yace "Ammi fa," ta jingina jikin motar tace "tana ciki," wae jikin ne hka Aneesah," ya tambaya da damuwa, tace "A'a ae na sha magani," yace "to Allah ya sauwake, hope kin shirya kin ga aiki xan tafi," tace "na shirya me?" ya dan harareta yace "kin fasa xana waec din ne, registratn xa muje muyi," tayi shiru tana kallonsa a raunane tace "kaga gombe xan tafi yau fa," yace "gombe kuma, me xaki je yi a gombe," ta fara hawaye tace "Ammi ce tace na tafi," yyi shiru yana kallonta can yace "Ammi tana ciki," ta gyada masa kai kawae yace "can i go in," nn ma ta gyada masa kai ya shiga gidan tana biye da shi a baya, har daki ya shiga ya gaida Ammi ta amsa da fara'arta tana tambayarsa mutan gidan yace "duk lfya suke Ammi," Ammi tace "to madallah," ya danyi shiru snn yace "Ammi na xo ne xamuje registratn na waec tace min gombe xata tafi, don Allah Ammi ki bar ta ta xana exam dinta ko akwae abinda xata yi a can ne," Ammi ta girgixa kai tace "bbu Abinda xata yi a can Aliyu wajen kakata da ta rikeni xata ne, xuwan ta can xae fi mana kwanciyar hankali daga ni har itan," yace "sbda me Ammi," Ammi tayi shiru tana kallon Aneesar dake hawaye, xata yi magana taji an shigo gidan ana kwala mata kira, maryam, maryam, maryam, Ammi bata yi kkrin mikewa daga inda take ba jin muryar me kiran nata, matar baffa shehu ce, ta shigo dakin a fusace ta tsaya masu bakin kofa tana nuna su da dan yatsa, "wllh wllh ko ma uban me ku ka yi ma dana tun wuri kuje ku karya shi idan ba hka ba xa ku sha mamaki daga ke har 'yar ki, kaji mun talakokin banxa makwadaita, uban me Abdul dina xae yi da wnn shegiyar 'yar taki, wllh tun wuri ku koma wajen bokan da kuka je ya lalata aikin da yyi maku," Aneesah da ta kasa daure jin irin bakaken maganganun da matar baffanta ke gaya masu tace "ke wae ance maki kowa ma irin ki ne mai xuwa wajen boka, ko kuma uban me ma xanyi da dan naki da baki baki masa tarbiyar arxiki ba sae ta tsiya, kin xo kina ta ma mutane haushi uwa kare a gida, wllh na fi karfin dan ki Abdul, kuma da na auri Abdul gwara na aure mahaukaci mara hankali"
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 33.... Aneesah ce xaune kan tabarma a tsakar gida tana ta faman jujjuya littafin biology dake hannunta a sunan karatu, duk hankalinta baya jikinta, don rabon da taga Haiydar yau sati uku cif, kuma bai taba ddewa hka bae xo gidansu ba, snn bata san inda ta jefa wayar da ya bata ba ma Ammi na kitchen tana girkin dare da yake wajajen karfe biyar da rabi na yamma ne, ta mike a sanyaye jin kiran da Ammi ke mata ta karasa kitchen din, Ammi tace "ruwa xaki debo, kin dae san ba ruwa a gidan, na rasa wani irin karatu kike yi tun karfe uku," Aneesah bata ce kmai ba ta dauki bokitin ta juya xata bar gidan, Ammi ta kirata ta dawo tace "na'am Ammi," Ammi ta juyo tana kallnta tace "ki gaya min me ke damunki Aneesah duk kwanan nn na rasa gane maki, idan ma Aliyu ne ae addu'a xakiyi Allah yasa lfya Aneesah," ta gyada ma Ammi kai tana kkrin maida hawayen dake kkrin xubo mata ta juya ta bar gidan da sauri, har ta daura ruwan a ka bayan ta debo ta tuna warnin din Haiydar ta sauke a hankali ta rike a hannu ta kama hanyar gida, tana isa kofar gidansu ta ga mota a parke gabanta ya fadi, Allah yasa yayanta ne ta fadi a xuciyarta, ta tsaya tana kare ma motar kallo ganin bata taba ganin Haiydar da irin motar ba, Abdul ne ya fito kmr wani sarki yana mata wani irin kallo, ta ja dogon tsakin takaici ta dauki bokitin ruwanta xata shiga ciki yace "hey!" har ta shiga xauren ta fito don bata son ya shigo cikin gidan nasu yyi ma Ammi wlkncin da ya saba, yyi yar dariya yana kallon cikin idonta lkci daya yana takowa ixuwa gabanta, ita dae tana tsaye har ya karaso gabanta yace "Amaryata yane, me kike bukata, kinsan nn da asabar xaki xamo matata" tayi murmushin takaici ta ma rasa abinda xata ce masa, can ta tabe baki tace "yhu had beta wake up frm ur slumber," tana fadin hka ta ja tsaki ta juya xata shiga gidan ya fixgota, suna kallon juna, yyi murmushi mai sauti yace "we shall see 'yan mata, ina barristern naki" bata sake sauraransa ba ta shige gidan da sauri ranta a jagule, tun da suka fara exam sa ti uku knn kusan kullum sae Abdul ya xo mata da wnn maganar me tsoratata, tana shiga da ruwan hannunta bata sake komawa debo wani ba ta shige daki ta kwanta tana kuka a hankali, anya kuwa xata karasa waec din nn lfya kuwa, don ji tayi duk xams din ya fita ranta....
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 35..... Ya
karaso gabanta ya durkusa yana kallonta, har lkcn
bata dago ba idonta na kan littafinta, ya fixge
littafin yace "bby baki ganni bane?" tayi tsaki tace
"kai din bnxa me xan mka," tana fadin hka ta mike
tayi hanyar daki yyi murmushi yace "Ahaf ranar
asabar xan sauke maki wnn rawan kan ka tsiwar
dake damunki yarinya," yana fadin hka yyi dariya
ya fice daga gidan, Ammi ta mike xaune tana
kallon Aneesar da ta shigo dakin ta fashe da kuka
duk da tana jin duk abinda Abdul din yake fadi
tace "me ya faru Aneesah," cikin kuka tace "Ammi
ca fa yyi wae xuwa ranar asabar xan xama
matarsa ni bn gane me suke nufi da mu ba, kullum
ya xo gidan nn maganarsa knn fa Ammi," Ammi
tayi shiru tana kallonta can tace "ba gobe xaku
gama jarabawan ba," Aneesah ta gyada kai tana
hawaye, Ammi tace "to sae ki wuce gombe goben
kawae, bna son tashin hankali," a hankali tace "to
Ammi Neco fa" Ammi ta galla mata harara tace "ae
ba dole bane sae kinyi Neco," Aneesah tace "hka
ne," Ammi tace "don hka gobe kina dawowa daga
makarantar xaki wuce gombe," to kawae tace ma
Ammi ta kwanta jikinta a sanyaye, can kuma ta
juyo tana kallon Ammin tace "to Ammi ya Haydar
fa?" ba tare da Ammi ta kalleta ba tace "xan masa
bayani idan ya xo goben," Aneesah bata sake cewa
komai ba ta kulle idonta da xumar bacci, duk da
tasan ba barcin xata yi ba, ita dae taga rayuwa.
Abdul ya shigo falon Abbansa cikin gadara ya
xauna yana kallon iyayen nasa dake ta binsa da
kallo tun shigowarsa falon, yana shafa sajen dake
kwance luf luf a fuskarsa ya daga masu kafada
yana kallonsu ganin irin kallon da suka masa yace
"ya?" Hajiya zuwaira tayi murmushi tace "daga ina
hka Guy, tun tuni nake ta cigiyarka a gidan na kira
wayarka kuma baka daga ba," ya tabe baki yace
"naje gun local Amaryar nn tawa ce, ta ma bata
min rae kawae a bnxa, ni don dae kawae ina da
dalilin da yasa nake son ku aura min ita ne amma
wnn 'yar kauyen ba class dina bace wllh," baffa ya
dan sace kallon matar tasa ya ma rasa mai xae ce,
hajiya xuwaira ta kirkiro murmushi ta fara kame
kame "uhm, amm, guy ni kam na rasa dalilin da
kke son auren Aneesar nn, har karuwanci fa tayi
wllh, ni kar taje ma ta goga maka wani cutan ta
cuceni kasan kai daya Allah ya bamu, da xaka ji ta
nawa Abdul da......." ya mike a fusace cikin tsawa
yace "da xan ji ta naki me, ni fa ku bar gaya min
maganar bnxa, jibi fa dad yyi min alkawarin aura
min ita, xaki kawo min wnn maganr taki mara
ma'ana, ca nayi maki sonta nake yi dama to, ni
kadae nasan abinda na shirya a kanta don hka duk
wanda yace xae bata min plan dina wllh......" da
sauri baffa ya mike yana dan buga kafadarsa ciki
lallashi yace "cool down my guy, ynxu wa yace
mka baxa a aura maka ita ba, daxu baka ga
baffanka ibrahim ya xo ba dasu sambo, ai duk kan
maganar daurin auren ne, ka kwantar da
hankalinka insha'Allahu ranar juma'ah Aneesah
taka ce my son" Abdul yyi murmushi yace "gud
dad," snn yayi ma Hajiyar wani irin kallo ya fice
daga falon, Hajiya xuwaira ta fashe da kuka tana
salati tace "shknn na banu Alhaji, ynxu wnn
tsinanniyar yarinyar Abdul xae auro mana, to me
suka yi ma Abdul dina hka, kuma kafa san namiji
wawa ne duk irin tsanar da xae mata lkcin da xata
koya masa sonta ma ba sani xae yi ba, ni dae na
shiga uku ni zuwaira," baffa ya harde hannayensa
yana jijjiga kafa ransa a jagule, can ya mike shima
ya fice daga falon.. Haydar yyi parkin a hankali
yana hararan kofar shiga falon nasu kamr yyi masa
laifi, can yyi tsaki ya fito daga motar yyi hanyar
balcony a xuciyarsa yana cewa forsaken home knn,
ya shiga falon da sallamarsa yana kallon agogo,
yau satinsa uku rabonsa da gidan, suna xaune falo
gaba dayansu suna kallo, pretty ta taso da gudu
taxo ta rungumesa cike da farin cikin ganinsa, ya
shafa kanta yace "ykk bbyna," sumy da meenah
suka tabe baki a tare suka maida hankalinsu ga
kallon da suke yi, Hajiya ta taso da murnarta tana
masa sannu da xuwa, ya hade rai yana amsawa ba
tare da ya kalleta ba, yyi hanyar stairs pretty na
biye da shi yaji wani siririyar murya na masa
sannu da xuwa daga cikin falon, ya juya da sauri
yana kallonta, ya juyo yana kallon pretty yace "wnn
kuma fa," pretty tayi wani irin dariya can ciki tace
"ohon masu," bbu yabo bbu fallasa yace "yauwa,"
snn ya juya xae haura sama Hajiya ta dakatar da
shi, hka ake yi Haiydar baxa ka tsaya ku gaisa ba,
cikin fushi yace "to saninta nayi da xan tsaya mu
gaisa," Hajiyar ta tabe baki tace "to matar da na
xaba maka knn ko kaki ko kaso, ko shi Alhaji
usman bae maka bayani bne a can kanon, xaka
shigo kana cika kana babbatse ma mutane, ga ta
nn sunanta zeenah, 'yar gidan Aminiyata ce kuma
sae da na nemi shawara gun Alhaji usman shi ya
bani go ahead din yin komai, don hka nn da wata
daya ne bikinku tunda kai baka san ciwon kanka
ba, degree fa gareta nn da kke ganinta, kuma da ka
san irin mutanen dake nemanta da da gudu xaka
amince mata, daxun nn ta xo gaisheni nace ta bari
ta kwana kawae tunda na samu lbri gun Najeeb
cewar yau xaka dawo."
Like · Report · Just now
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
34.... Ba ita ta fito daga dakin ba sae
da aka kira maghrib shima ta dalilin
kiran da Ammi tayi mata ne, har lkcn
ammi na tsakar gidan xaune,
Aneesah tayi alwala ta koma ciki tayi
sallah, tana idar da sllh Ammi ta
kuma kiranta ta fito, Ammi tace "ki je
ga abincin ki can a kitchen ki dauka,
saura kiyi min irin na daxu wllh sae
na bata miki rae," Aneesah ta juya ta
koma cikin dakin tana cewa "ni sae
na