Showing 6001 words to 9000 words out of 89000 words

Chapter 3 - ANEESAH Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

3123

take a gidan don har marinta Hajiyar nayi, ga wani muguwar tsana da babbar 'yarta meenah ke mata duk tabi ta sa mata ido a gidan da tayi mistake daya ta dinga yayyafa mata masifa knn tana xagi, ita dae Aneesa sae dae ta sunkuyar da kai don sun hanata hada ido da su, ko kuma ta durkusa, duk irin abubuwan da take fuskanta a gidan kin gaya ma Amminta tayi, kullum cikin pretend take duk da irin muguwar raman da tayi, fatanta ita dae kawae tayi wata biyu tana aiki ta tara kudin waec dinta tayi gaba, amma da ta karbi kudi karshen wata matsalar gida ke karar dashi don wani lkcn ma sae su kwana hka basu ci komai ba, sae dae Ammi ta tura yusuf makwabta yaci abinci, hkn yasa ta ji ta fara hkura da karatun ma kawae, indae ta hka xasu dinga samun abinda xasu kai baki, kuma duk da irin walakancin da taga akeyi da abinci a gidan da take aiki ko sau daya bata taba debowa tace xata kawo gida ba, don itama wani lkcin da yunwa take yini a gidan sae ta dawo gida xata ci tunda ba bata suka yi ba ita kuma bata daukan abinda ba a bata ba, da hajiyar ce ma ta lura da hka duk da walakanci da gadaranta ta kan tambayeta ita ta ci abincin idan sun ci sun yi kat da 'ya yanta, sae tace mata aa don ko dan dana masu abinci bata yi idan ta gama girka masu, hkn yasa Hajiyar ta ware mata wani plate daban wae idan ta xuba ma kowa har maigadi da karen dake bayan gidan ita ma sae ta xuba nata, Aneesah tayi mata godiya ta mike ta bar wajen. Ran da Aneesah ta cika wata biyu da sati daya a gidan tana kitchen tana wanke wanke Hajiyar ta kwado mata kira "Aneesah," idan tana kwala mata kira sae ka rantse kace ita ta rada mata sunan, Aneesah ta taho da sauri ta durkushe gabanta tace "Na'am Hajiya," Hajiyar ta galla mata harara tace "da kina jina mahaukaciya kika yi min bnxa," Aneesah ta girgixa kai tace "kiyi hkuri Hajiya na bude famfo ne shiyasa banji ba," hajiyar ta daka mata tsawa "da yake kunnenki na ciwo ne ko 'yar walakanci," Aneesah tayi shiru bata ce komai ba, hajiyar tace "tashi ki ban waje raina ya daina baci shegiya kawae, anjima kya ji abinda xan gaya maki idan xuciyata ta huce," Aneesah ta mike a sanyaye ta bar wajen hawaye cike idonta, tana barin wajen meenah tace "wllh na tsani yarinyar nn mum, bata fa yi kama da 'yar aiki ba, ni ban ma yarda da ita ba kila wllh aikota gidan nn akayi ko kuma plan aka yi da ita, ji ta fa kyakkyawa gata fara, ni ban ga alamar ta taba aiki ba ma," sumy tace "ke dae bari kawae, kinga fa jiya da nake ta kallonta na kalli naga bbu abinda xaki nuna mata sae hasken bleachn," meenah ta mike a fusace tace "kika ce me, to ke din an ce maki kyau gare ki, wllh 'yar aikin nn tafi ki kyau sau dubu."
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 11...... Wani gigitattcen mari Hajiya ta kai mata tana ball da ita a fusace, "don uwarki ke dabbar wace gari ce, baki da hankali ne xaki bata masa jiki hka da drink muguwa kawai," shi ko Haiydar mikewa yyi da sauri ya bar wajen ya haye sama, kuka ta dinga yi tana ba hajiyar hakuri tana cewa bata sani ba, amma hkn bae sa matar nn ta kyaleta ba, don marinta ta dinga yi son ranta, har ta gaji snn cikin tsawa tace "bace ki ban waje mahaukaciya kawae," da kyar Aneesah ta bar falon tana ganin jiri, a daddafe ta shiga kitchen ta jingina jikin fridge ta dinga kuka a hankali, ganin tsayuwar baxae mata ba yasa ta bude kofa ta shiga garden ta xauna ta hade kanta da gwiwa tana ci gaba da kukan takaici, wnn wace irin bakar rayuwace ita kam, ta kai minti kusan sha biyar a wajen tana ta aikin kuka, taji an dafa kafadarta a hankali, ta dago a tsorace taga wanene, xuciyarta ya kusan shigewa cikinta ganin ko waye, ya xauna gefenta yana kallonta ta matsa a tsorace tare da kkrin mikewa ta bar wajen ya rikota, a gigice ta tura hannunsa tace "nashiga uku, malam ka rufa min asiri don Allah don annabi ina rokanka," ya ki sakinta a hankali yace "to xauna kiji abinda xan ce," ta shiga waige waige a tsorace tace "kayi hkuri nace don Allah," ya wara mata manyan idanunsa yace "sae kin fara saurarata," ta sulale kasa gefensa don yaki sakinta har lkcin, hawaye na bin kuncinta tace "bka ma Allah knn" ya girgixa mata kai a hankali yace "ina yi masa," snn ya ciro handkercheif ya dafe kanta da hannunsa ya shiga goge mata hawayen fuskarta ta kauda fuskar da sauri xata mike tsaye, yyi saurin matsowa kusa da ita ya sakale hannunsa a wuyanta ya ci gaba da goge mata fuskar, ta tsorata sosai don tunda take ba a taba mata hka ba, ta fara kkrin kwace kanta tana cewa "nashiga uku meye hka malam," muryar Hajiya suka ji a kitchen tana cewa pretty wae ina Haiydar ya shiga ne, tace "momy nima shi nake nema har ynxu yaki bamu tsarabar mu fa, ita kuma wnn yarinyar taki taxo ta ba mutane abinci har worm din cikina sun fara cinye min fatar cikin " Hajiyar ta kwala mata kira da karfi "Aneesah!" Aneesah ta turasa da karfi muryarta na rawa tace "innalillahi, wayyo Allahna ka rufa min asiri don ya rasulillahi," ya saketa ya mike da sauri ya xaga yyi hanyar garage, ita ma ta mike da sauri ta bude kofar kitchen ta shiga suka kusan cin karo da Hajiyar...
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~ANEESAH~ By Khaleesah Haiydar
9......
Aneesah ta gama shiri karfe shidda da rabi xata bar gida, Ammi dake xaune kan darduma har lkcn ta bi ta da kallo da mamaki "kina da hankali kuwa Aneesah, ina xaki da sassafen nn hka," Aneesah ta xauna gaban Amminta tana kallonta tace "ae nayi maki bayani Ammi, xasu yi baki ne yau, xan masu girki da dan yawa shine tace naxo da wuri," Ammi ta harareta tace "shine ko karfe bakwae bai karasa ba xaki fita, ina laifin ki bari karfe bakwan,ko fa karyawa baki yi ba " Aneesah tace "A'a Ammi ynxu xan wuce, da wuri bakin xasu iso ne fa," Ammi tace "to ki sha kokon kafin ki tafi," Aneesah tace "ohh Ammina ni bana jin yunwa idan naje can ma ai suna bani wllh," ba dan ran Ammi ya so ba ta bata kudin mota tayi mata Allah ya kiyaye snn ta bar gidan ta kama hanyar gidan aikinta. Ko da ta isa gidan duk bacci suke basu tashi ba, ta danyi share share da goge gogenta tayi mopping ko ina, snn ta hada masu breakfst kafin su tashi ta jera kan dininn, tukunna ta fara girke-girken da aka lissafa mata jiya da yake akwae kayan cefanen gaba daya a fridge. Ba ita ta gama girkin ba sae kusan karfe sha daya don ma gas biyu ta kunna, da electric cooker, ko da ta gama sae da ta fara gyara dinning din da suka yi breakfst ta kwashe duk kwanukan, ta gaisar da yan gidan gaba daya, snn ta fara jera sabon girkin da ta yi a dinning din, ta saka ginger drink din a fridge yyi sanyi, tana goge gogen kitchen taji sun fito gaba daya su ukun sun hade cikin kananan kaya suna ta murna xa su je dauko yayansu a Airport, Hajiyar ta rakasu har bakin mota suka ce da kansu xasuyi driving basa son driver ya jasu, tayi masu Allah ya kiyaye ta shigo gidan tana kwala ma Aneesah kira, Aneesah ta fito da sauri ta durkusa gabanta tace "na'am Hajiya gani," "kiyi maxa kije ki gyara masa bedroom dinsa ki canxa bedsheet,ki tabbatar ko ina yyi fes snn ki shiga nawa bedroom din ki gyara " Aneesah tace "to Hajiya," snn ta mike ta bar wajen ta hau sama ta shiga yin aikin da ta sa ta. Cikin awa daya ta gama komai ta sauko downstairs, Hajiyar na falonta tana waya, tana shiga kitchen taji shigowar motarsu, pretty ta shigo da gudu tana dariya ta dinga kwala ma momynsu kira wae taxo taga yayansu, Hajiyar ta fito da sauri suka hade dae-dae bakin kofa ta rungume dan nata cike da farin ciki da murna tace "waw my son ya hanya," shi ko ya hade rae "don Allah ku bar ni naji da gajiya na mana mum, su kuma wa innan sun tashi sun kwashi jiki sun bi ni Airport kamr wasu mahaukata " meenah ta dan tabe baki tace "dan ma ka samu ana farin cikin dawowarka, wllh momy tun a airport yake ta gwasale mu sai kace dole, ni da nasani ma da baxan je ba," ya juya yana kallonta yace "to uwar waye yace da ki xo din munafuka, kin tashi kin yi shiga kmr mai shirin tsallaka wuta kin bini airport, wae ma ban hana ku sa irin wa in nan kayan ba, har da ke ko Zainab," ya fadi yana kallon pretty, sumy ta tabe baki ta dan yi tsaki ta haye sama hka ma meenah da ta shiga gunguni, pretty tace "kayi hkuri yayana," Hajiyar ta hade rae ita ma "kaga matsalata da kai knn Haiydar ba dawowarka ba takura ma 'ya yana, gskya baxa mu shirya ba wnn karan, kawae bbu ruwanka ka sa masu ido duk me kaga suna yi," yace "Allah ya baku hkuri," snn ya haye sama pretty ta bi shi a baya, Hajiyar ma ta bi sa ganin kmr ransa ne ya bace, duk wnn abunda suke Aneesah na jinsu, sae abun ma ya bata dariya, a xuciyarta tace "Allah ya kyauta da irin wnn familyn, don tun da taxo gidan ita kam bata taba ganin mai sllh cikinsu ba, sae dae Hajiyar ita ma idan lkci ya wuce, ita ko dama bata isa tayi a cikin gidan ba sae dae taje garden.
14 mins · Khaleesat Haiydar...
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: Aneesah.... By Khaleesah Haiydar 10.... Bayan minti Ashirin Aneesah na xaune cikin garden, don bbu aikin da xata yi a lkcn sae kuma xuwa anjima, da yake akwae kofa ta kitchen da xae sada ka da garden din tanan ta bi ta fita, Hajiya taji tana kwada mata kira ta shigo gidan da sauri ta durkusa daga bakin kofar kitchen din tace "gani Hajiya," ta galla mata Harara tace "gidan ubanwa kika shiga nke ta faman ihu kmr makogwarona xae fito?" ta sunkuyar da kai tace "kiyi hkuri Hajiya ina daga waje ne," ta daka mata tsawa "da'allah tashi ki ban waje muguwar yarinya kawae nasan kasheni kawae kike son yi abinda na haifa ma basu kasheni ba shegiya kawae," Aneesah ta mike a sanyaye xata bar falon sae a lkcn ta kula gaba dayansu har yayan nasu ma na falon, su sumy da meenah suka tuntsire da dariya suka dinga yi, shi dae hankalinsa na kan laptop, pretty na jikinsa tana kallon abinda yake yi, Hajiyar ta kara da cewa "kuma idan kinga dama ki dauko ma son dina ginger drink a fridge," ta juya ta shige kitchen din da sauri, sae a snn ya dago kai yana yatsine fuska yace "ita ce ta hada drink din mum?" Hajiyar tace "eh ita ce ta hada, ta iya sosae son, snn tana da tsafta shi yasa ma nace tayi," ya gyada kai yace "tab! Ku bar shi kawae bna sha, ynxu momy fisabilillahi mai yaran nn suke da sae wata 'yar aiki can xata hada min abinda xan ci, wae meyasa ku ke hka ne mum, meye amfaninsu idan basu yi a nn ba ina xasu je su yi, knn kuna nufin ita ce ma tayi min girkin da xan ci," Hajiyar tace "kayi hkuri son, naga basu iya bne, shi yasa na sa ta tayi maka, amma ai ba komai sae na tashi da kaina na yi maka ynxun nan," yace "A'a ku barshi kawae bana so, ngd" Aneesah na tsaye a kitchen duk tana jinsu gabanta ya shiga faduwa, ga hawayen da yaki tsaya mata, to ynxu kai masu gingern xata yi ko bari xata yi, jin bbu wanda ya sake cewa komai ne yasa ta daura drink din a faranti da cup ta dauko ta fito falon a sanyaye ta tsaya daga bayan kujera a hankali tace "na kai dinning ne Hajiya ko nn xan kawo," hajiyar ta watsa mata wani mugun kallo tace "ke kurma ce lkcn da yace bae ciki da harkan kaxanta," ta dago kanta a raunane tana kallonsa ga hawayen da ya taru a idonta suna shirin gangarowa hkn yasa cikin idonta ya dinga kyalli gabanta yyi mugun faduwa dai-dai lkcn da shima ya dago kansa ya sauke manyan idanuwansa kan nata, da sauri ta kauda kanta ta juya xata shiga kitchen din, da sauri taji yace "momy ta kawo xan sha am vry thirsty," murya can ciki yyi maganar, Hajiyar ta sake kwado mata kira ta dawo, tace "ki kawo masa drink din, ya ya iya tunda yana so," ta tako a hankali ta shigo falon ta durkushe gabansa ta ajiye trayn, har lkcn kallonta yake yana son kara kallon cikin idonta amma taki bari su hada ido kuma, ta mike xata bar wajen hajiyar ta daka mata tsawa "ke wacce irin dabba ce, brain dinki bai baki cewar xuba masa a cup din xakiyi gaba," ta koma ta durkusa ta shiga xuba masa drink din a kofin, tana gama xubawa taga ya miko hannu ta dago tana mika masa ba tare da ta kallesa ba ga wani mugun bugawa da xuciyarta yake, shi ko so yake kawae ya kalli kwayar idonta hkn ne ma yasa ya mika mata hannu amma Aneesah taki dago kanta, jin dumin hannunsa a nata ne ya sa ta sake masa kofin da sauri ta mike xata bar wajen, ashe bae rike kofin ba ya fadi, juice din gaba daya suka xube jikin farin three quatren jikinsa, ta koma baya a tsorace ta dafe kirji tace "innalillahi nashiga uku wllh ban sani ba"
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 12..... Aneesah ta dan koma baya gabanta na faduwa ga tsoro, cikin tsawa Hajiya tace "uwar me kike yi a nn," muryarta na rawa tace "A'a wae da ruwa nake son na ba flower naga kuma rana yyi," Hajiyar tace "da wani gulman ne ya hanaki yin hkn tun da safe, kin wuce kinyi serve din abinci a dinning ko sae na cire maki wnn mayun idanuwan naki," a raunane Aneesah tace "kiyi hkuri Hajiya," Hajiyar ta galla mata harara tace "idan bana hkuri dake da baki kasheni ba ynxu," taja dogon tsaki ta bar wajen tana cewa "nima dae bana daddara da wa innan matsiyatan 'yan aikin wllh, ya'yan ka basu sa ka magana ba bare ihu su suyi ta saka, da na bi shawara Haiydar ma baxan karbesu gidan nn ba, amma na kusa kawo karshe hka," Aneesah ta bi bayanta jikinta a sanyaye ta shiga falon, duk 'yan matan na kan dinning suna jiranta, ikon Allah ga su ga abincin fa a gabansu amma dole sae an samu me xuba masu sbda tsabar lalaci da gantalewa, Hajiyar ma ta ja kujera ta xauna tana jiran Aneesar ta xuba masu, Aneesah ta karaso dinning din bayan ta wanke hannunta ta shiga tambayarsu abinda xasu ci suna bata amsa a walakance cikin gadara ita kuma tana xuba masu, wani ma sae ta gama xuba masa xae ce bashi yake so ba kuma ta xuba masa wani, tana cikin xuba ma Hajiyar Haiydar ya sauko kasa ya karaso dinning din ya ja kujera ya xauna yana kallon idon Aneesah, tana gama xuba ma Hajiyar ta juyo inda yake ba tare da ta bari idonta ya hadu da nasa ba tace "me xan xuba maka......" a hantare Hajiya tayi saurin katseta tace "'yan aiki basa serve dinsa, shi da kansa xae xuba kayansa, ki bace mana da gani kar mu kware," ta sunkuyar da kanta ta juya xata bar wajen yyi saurin cewa "A'a ta xuba min mum na gaji dayawa," Hajiyar ta juyo tana kallonta tace "sae ki dawo ki xuba masa," a hankali ta tako har inda yake a xaune ta ja plate ba tare da ta kallesa ba tace "me kke son na xuba maka," ya tsura mata manyan idonsa yana kallonta amma taki kallonsa kanta na kasa, a hankali taji yace "to ae bn san me dame aka girka ba nn" shi dae so yake kawae su hada ido, amma ba tare da ta kallesa ba still tace "akwae fried rice da plantain, cous-cous da miyar kwae, jollof din taliya, farfesun kifi, farfesun kayan ciki da na kaxa, sae cream salad," yyi shiru yana kallonta, gabanta ya shiga faduwa, kar dae ya sake ja mata wani dukan ta dan juya ta sacii kallon hajiyar dasu meenah taga dukkansu hankalinsu na kan abincinsu, pretty kadae ce ke kallonsu, ta sunkuyar da kai tace "ina fatan ka fahimceni, me xanyi serve dinka," taji yyi mata shiru, hkn yasa ta dago kanta a hankali tana kallonsa, suna hada ido taga ya wara idanunsa yyi murmushi alamar jin ddin sun hada ido, dama idonta kawae yake son ta daura kan nasa, ta hade rae ta kauda kanta, murya can kasa yace "ke me kika ci?" ta hararesa a hankali tace "wnn ba matsalarka bace malam," yyi murmushi bai ce komai ba, Hajiya ta dago tana kallonsu tace "A'a har ynxu bata xuba maka bne son, ko duk abincin basu maka ba ta girka maka sabo," ya girgixa mata kai yace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login