Showing 21001 words to 24000 words out of 89000 words

Chapter 8 - ANEESAH Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

3119

har ya wangala gate din jikinsa na rawa Aliyu ya fice da gudu ya bar compound din, kmr xasu tashi sama.
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 28.....
Aneesah ta shiga daki ta fito da tabarma ta
shimfida masa ya xauna, Ammi ta fito ta dauko
kujera ta xauna tanai masa sannu da xuwa
murmushi bayyane a fuskarta, ya gaisheta a
ladabe yana tambayar ya gidan, tace masa
lfya lau ya nasu gida, yyi mata gaisuwan
rasuwar yusuf, tayi masa gdya sosai daga
bisanni ya sake bata hakura a kan abinda ya
faru snn yyi mata sallama yace xae wuce, tayi
masa gdya tace Allah ya saka da alkhairi snn
ya fita daga gidan yana kallon Aneesah. Sae
da ya fita snn a hankali tace ma Ammi bari ta
rakasa Ammi tace mata to, ta mike ta bi
bayansa, yana jingine jikin motar yana jiranta,
ta karaso gefensa ta tsaya a sanyaye tace
"nagode yaya Haiydar," yyi murmushinsa mai
kyau yace "nima ngd fateema," ita ma
murmushin tayi ta boye fuskarta, yace
"Aneesah an rufe registration din waec din
ne?" a hankali tace "nima ban sani ba," yace
"ok find out frm yhur sch mates," tayi shiru
bata ce komai ba, yace "Aneesah naxo gidanku
ko ruwa baki bani ba, gashi dama yunwa nke ji,
kin san bnyi break ba," ta xaro ido tace "lah ae
ban san xaka sha ba, bari na debo maka," yyi
dariya yace "wasa nake maki," ya bude motar
ya fito da ledar Hijabs din ya mika mata tace
"na me," yace "naki mana," ta marairaice tace
"A'a ni dae wnn ya isheni wllh," ya harareta
yace "ki karba wucewa xanyi," a hankali tasa
hannu ta dan risina ta karba snn tayi masa
gdya, yyi murmushi yace "welcm Aneesah, i wil
be goin now," ta gyada masa kai ya bude motar
ya shiga ta daga masa hannu snn ta juya ta
shiga gida, shi ko yyi reverse ya bar anguwar,
hanyar gidansa yyi, don yasan Hajiya na can
kila ta tara masa mutane ana jirasa don ma ya
kashe wayoyinsa. Aneesah na shiga ta nuna ma
Amminta hijjaban, Ammi tace "shine xaki karbo
Aneesah ni fa ba ruwana," Aneesah tace "wllh
Ammi nace ya bar shi yaki," a hankali ta shiga
fito da su tana dudduba, tana fito da na ukun
knn bandir din dari biyar biyar ya fado, ta
koma baya da sauri tana kallon Amminta, ammi
tace "wnn kuma daga ina?" Aneesah tayi shiru
tana kallon kudin snn ta dago tana kallon
Amminta a hankali tace "shi ya saka Ammi,"
Ammi ta kasa cewa kmai sae kallon Aneesar da
take yi, can dae ta mike ta shige daki kawae,
Aneesah ta bi ta ta fashe da kuka tace "wllh
Ammi ban san ya saka ba," Ammi ta girgixa kai
tace "to ki ajiye masa kudinsa kar ki taba,"
Aneesah tace "to" snn ta ajiye hijabs din da
kudin cikin jakar kayanta. Washegari da yamma
ta je dibo ruwa a borehole tana dawo wa xata
shiga gida taji an mata horn, ta juya da sauri
tana kallon motar da mamaki, Haiydar ne, ya
bude motar ya fito ya wara mata ido yace "me
hannunki yake da xaki daura ruwa a kai
Aneesah," tayi murmushi tana kallonsa bata ce
komai ba ya karaso gabanta ya sauke mata
bokitin ruwan ya ajiye kasa yana mata wani
irin kallo, ta boye fuskarta da tafin hannunta
tana 'yar dariya tace "xafi hannun xae min shi
yasa na daura a kai," ya harareta yace "to
karki sake," tace "uhum," snn ta dauki bokitin
ruwan a hannu yace "bari na taya ki mana," ta
ce "A'a ina xuwa," ta shiga gidan, bayan kmr
minti biyar ta fito rike da leda tana kallonsa
tace "jiya kayi mantuwa cikin ledar da ka
ban," ya galla mata harara yace "Ammi na ba
bake ba, ni ina ruwana dake," ta marairaice
fuska tana kallonsa tace "dn Allah ka bari ka
amshi kayanka ni dae," ya hade rai yace "ba
fa na son hka Aneesah," tayi shiru tana kallon
kasa, yace "ya maganar da na maki jiya na
waec kin tambaya?" ta wara ido tace "na
manta," yyi mata wani irin kallo yace "you re
nt cerious," ya ciro wayarsa daya ya mika mata
yace "idan kin tambaya kya kirani ki gaya min
nmbrna na ciki xaki ga anyi save da barrister,"
ta xaro ido tace "A'a ni bana so wllh ka tafi da
kayanka watarana idan kaxo xan gaya maka
idan na tambaya," ya ajiye mata kan wani
dutse yace "idan na tafi ki barshi a wajen, ki
gaida min da Ammi," yana kai wa nn ya shige
motarsa ya juya ya bar anguwar, tayi kmr xata
yi kuka har ta daina ganin motar snn ta dauki
wayar ta shiga gida dashi. Da daddare tana
wanke wanke a tsakar gida Ammi na daki taji
kamr motsin mutum a xaure, ta dan tsorata ta
mike da sauri tana jiran taga wa xae shigo
taga bbu kowa, a ranta tace to ko dae ya
Haiydar ne, hkn yasa ta karasa da sauri don
tunaninsa take lkcn, ta shiga xauren tana dan
waige waige cikin duhu bata ga alamar kowa ba
ta dan leka waje ta dae ga motar a parke
amma ba na Haiydar bne, kuma ba a kusa da
gidansu akayi parkin din ba, ta danyi tsaki ta
juya xata koma cikin gidan taji ta ci karo da
mutum ta tsorata sosae xata fasa ihu ya
fixgota ya rufe mata baki a hankali yace
"menayi maki xaki fasa min ihu," a tsorace ta
koma baya tace "ya Abdul," ya wara mata ido
cikin duhun yace "waww kin xama 'yan mata
bbyn nn," ta turasa da karfi a fusace xata bar
xauren ya fixgota yace "yaushe na fara wasa
dake?"
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
27.....
Sun yi nisa sosai, kawae tafiya yake ba tare da
ya san inda xa shi ba, Aneesah ko bbu abin da
take sae aikin kuka, ganin kawae tafiya yake
bai da alamar tsayawa yasa cikin muryar kuka
tace "ni ka sauke ni a nn na wuce gidanmu,"
sae a snn yyi parkin gefen titi, ya juyo yana
kallonta, ta rufe fuskarta tana ci gaba da
kuka, ya kamo hannunta yace "ya isa hkan
Aneesah kiyi hkuri, bana son kina kuka, nn"
bata ce masa komai ba amma ta kasa daina
hawaye, ya ciro handkerchief ya goge mata
fuskarta yana kallon gashinta da duk da
talaucinsu ba a haramta mashi gyara ba, don
sae kyalli yake ga tsantsi snn baki wuluk, ta
cire hannunsa daga kan gashin nata da ya
dafa a hankali tace "hijabina," ya gyada mata
kai kawae, snn ya ja motar suka bar wajen, sun
danyi tafiya mai nisa snn taga yyi park yace
"fito ki xabi wanda ki ke so," ta kasa cewa
komai tana kallonsa, ya gyada mata kai ta fito
a sanyaye daga motar suka fara tafiya a
hankali taga duk ido ya dawo kansu barin ita,
da sauri ta fixge hannunta tace "ni baxan iya
ba, ban da dankwali," ya komar da ita motar
snn shi yaje xabo mata Hijab din, bayan kmr
minti goma ya dawo da katon ledar boutique a
hannunsa ya shiga motar yana kallonta ta
sunkuyar da kai, yyi murmushi ya bude mata
ledar yace "gashi ki xabi wanda xaki sa," a
hankali ta jawo wani milk colour taga yana da
tsayi hkn yasa ta saka shi kawae, tana kallonsa
ya gyada mata kai yyi murmushi snn ya tada
motar suka bar wajen, sae da suka hau kan titi
snn a hankali yace "ina ne gidanku?" ba tare
da ta kallesa ba tace "ka ajiye ni a nn, sae na
wuce," ya girgixa mata kai yace "baxa ki fita
daga motar nn yau ba knn," ganin da gaske
yake yasa ta gaya masa anguwarsu kawae in
yaso sae ta karasa gida da kafa, "aneesah," ta
ji ya kirata ta juya tana kallonsa, idonsa na
gaban titi yace "me ya sami yusuf?" nn da nn
taji hawaye ya ciko mata ta girgixa kai da
kyar tace "mota ce ta bugesa suna dawowa
daga sch," yace "mota kuma, to ina mai
motar," ta goge hawayen idonta tace "bae
tsaya ba, kuma withness sun ce da gangan ya
buge sa bayan ya bugesa kuma ya taka sa ya
gudu," yyi parkin da sauri yana kallonta, ta
sunkuyar da kanta tana ci gaba da xubda
hawaye, yace "baffanku ya samu lbri," tace
"eh amma bae xo ba har ynxu wae matarsa tace
ya tafi lagos, kawae baffa ibrahim ne ya xo
shima shekaranjiya yace gangancinmu ne ya
kashe yusuf," Aliyu ya gyada kai bae ce komai
ba ya ja motar suka bar wajen, har suka isa
anguwar bai sake ce mata komai ba, sae da yyi
da gske da ita snn ta nuna masa gidansu don
ca tayi ya ajiyeta xata karasa da kafa, tace
masa tana xuwa snn ta shiga cikin gidan, Ammi
na share tsakar gidan don ita har lkcn bata
koma aiki ba sun bata hutun wata daya ne, ta
mike tsaye tana kallon Aneesar da mamaki
tace "me ya faru Aneesah," Aneesah ta kirkiro
murmushi don bata son daga ma Amminta
hankali, suka shiga dakin snn tace "Ammi tun
safe baki gama aikin ba ashe," Ammi tace "ki
gaya min Aneesah me ya faru ga idanuwanki
duk sun kumbura kice min bkm," Aneesah ta
sunkuyar da kai gudun kar ta fara hawaye
kuma, a hankali cikin nutsuwa tayi ma Amminta
bayanin abinda ya faru, ammi tayi shiru tana
kallnta da tausayi snn tace "shi kuma me ya
biyo ki yi Aneesah," ta goge hawayen idonta
tace "nima ban sani ba," Yana waje Ammi,
Ammi tace "to shknn kice ya shigo," ta mike a
sanyaye ta fita gidan tayi hanyar motarsa,
tace "Ammina tace ka shigo," yyi murmushi ya
fito daga motar ya rufe snn ya bi bayanta
suka shiga gidan a tare.
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 25..... Aneesah ta fara kkrin mikewa xaune, makwabciyarsu maman salim tayi saurin kamata tanai mata sannu, da kyar take bin dakin da kallo tana kkrin tunano abinda ya faru don kanta yyi mata nauyi sosae, a hankali komai ya dawo mata, murya can ciki ta kama hannun matar dake gabanta tana kkrin mikewa tsaye tace "ina yusuf," matar ta komar da ita ta xaunar tace "Haba Aneesah so kike ki daga ma Amminki hankali ne yusuf addu'a xakiyi masa kawae " Aneesah na jin hka ta fasa mata ihu a gigice tana girgixa ta tace "don Allah ku gaya min me ya sami yusuf dina," duk matan dakin suka yo kanta suna lallashi amma kamar ana sake tunxurata don ihu ta dinga masu tana kuka cikin daren har makwabta da yan unguwa sun fara shigowa, Ammi dae har lkcn tana xaune kan darduma tana nata kukan, ganin abun nata ba na hankali bne yasa daya daga makwabtansu maman yazid ta fara mata magana cikin fada "haba Aneesah so kike ki daga ma Amminki hankali ne ki sa ta cikin wani yanayi ita ma ko me, da wanne xata ji, mutuwar danta ko haukanki, ihu da birgimar taki ce xata dawo da yusuf ko me, don me baxa ki ji tausayin amminki ba ki rarrasheta ku rungumi kaddara, sae kace ba musulma ba, ynxu dae yusuf ya rasu addu'a kadae xakiyi masa ba ihu da birgima ba," a hankali Aneesah ta fara nutsuwa tana kuka a hankali, hka suka taru suka dinga mata nasiha da bata baki, daga karshe suka ce taje tayi alwala tayi sllh tayi ma kanninta addu'a" jiki ba kwari ta mike ta fita daga dakin xuwa yin alwalan, ranar daga ita har Amminta xaune suka kwana bayan kowa ya watse, ta kasa daina kuka yi take kmr ranta xae fita, ganin kukan da take yi ne ke sa Amminta kuka yasa ta daina kukan da kyar ta dawo gefen Amminta ta xauna tana kallonta, Ammin ta rungumota a hankali tace "ya isa hka Aneesah, addu'a xamui wa yusuf kinji, Allah yasa karshen wahalarsa knn," ta gyada ma amminta kai a hankali, a hka bacci ya kwasheta jikin amminta kusan asuba. Yau akayi sadakan bakwan yusuf amma har lkcn Aneesah ta kasa sa ma kanta nutsuwa ba karamin girgixa ta mutuwar kanin nata yyi ba, sae a lkcn ta gane ashe sign din mutuwar kaninnata ta dinga ji kwanakin baya take ta ciwo ita da Ammi, Ammi kam har ta gaji da lallashinta ta sa mata ido ganin abun nata bana karewa bane don komai na yusuf ta kwashe a gidan ko hkn xae sa Aneesar ta nutsu idan ta daina ganinsu amma duk a bnxa , duk da ita ma daurewa kawae take barin idan taga 'yar tata na kuka, ita ko Aneesah irin mutuwar da yusuf yyi ne kadae ke bata takaici. Bayan sati biyu da rasuwar yusuf Aneesah na xaune bakin kofar dakinsu Ammi kuwa na cikin daki tana masu linki ta kirata ganin tun da gari ya waye take xaune bakin kofar, Aneesah ta mike da sauri ta shiga dakin ta xauna tace "gani Ammi," Ammi ta harareta tace "kuka kike yi komai," ta girgixa kanta da sauri duk da kukan ta gama tace "A'a ni ba kuka nake yi ba Ammi," cikin lallami ammi ta fara magana "Haba Aneesah so kike ki janyo ma kanki wani ciwon ko, ya kike son nayi da rayuwata idan ke ma na rasa ki," ta fashe da kuka tace "na daina daga yau Ammina amma idan na xauna kullum nakan yi tunanin me yusuf yyi ma baffa da xae turo a kashe shi," cikin fada Ammi tace "wa yace maki baffa ne ya turo a kashe shi, ni fa bana son surutun bnxa, daga mota ta bugesa ta gudu kuma sae ya xamanto baffa ne yasa a xo a bugesa a gudu," tace "Ammi wlh shine, da gangan fa aka ce mai motar ya bugesa snn kuma ya take sa, Allah ya isan ma," Ammi tace "ni dae ki tausaya min ki daena sa ma kanki damuwa Aneesah in ma shi ya sa a kashesa din don kansa, ynxu abinda nke so dake gobe ki shirya ki tafi wajen aikinki kin ga yau sati biyu rabon ki da xuwa kuma bbu ddi hkn, sae kiyi mata bayanin abinda ya faru," Aneesah tayi shiru gabanta na faduwa jin an kira mata gun aikinta, can dae tace "to Ammi," washegari Aneesah ta shirya ta kama hanyar gidan aikinta gabanta na faduwa, jikinta a sanyaye ta shiga gidan bayan ta gaida mai gadin, ta karasa stairs din balcony ta hau ta tsaya bakin kofar falon xuciyarta na bugawa ta kasa shiga, da kyar tayi shahada tayi sallama ta shiga falon tana addua a xuciyarta da ya kasa daina bugawa, suna xaune gaba dayansu a falon hankalinsu kwance suna kallon tauraron dan adam, Haiydar na kwance kan kujera amma shi ba kallo yake ba idonsa a lumshe, duk suka juya suna kallonta ta karaso cikin falon a sanyaye ta durkusa tana gaida Hajiyar da ke ta girgixa kafa tana mata wani mugun kallo, ta sunkuyar da kanta da sauri ta rasa ta ina xata fara ma, cikin tsawa meenah tace "don uwarki ki fice mana gaban TV ko baki ga abinda muke yi bane wawiya kawae," ta ja gefe a hankali hawaye ya cika idonta ta juya tana kallon Haiydar da ya tsura mata ido.
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
32.....
Aneesah ta fixge hannunta tana masa wani mugun kallo gabanta
na faduwa tace "ka fitar mana a gida kar na maka ihu malam,
wnn ai iskanci ne da rashin tarbiya, xaka fado mata mutane gida
kamar barawo," ya wara idonsa da mamaki yana kallonta, "ni kike
ce ma barawo," ya tambayeta yana kallon cikin idonta, tayi tsaki
ta juya xata bar wajen ya fixgota ya watsa mata mari, tare da
hadeta da bango yana huci, "ke kinsan ko da wa kike magana
don uwarki kuwa," cikin kuka tace "na sani mana, mugu, axalumi,
mara tarbiya, masu cin dukiyar marayu....." wani gigitattcen marin
ya sake wanke ta da a fusace yana huci, ya shake wuyarta yana
kallonta da kyau xae yi magana, aka shigo gidan, Haiydar ne, ya
tsaya daga bakin kofar xauren ya rungume hannayensa yana
kallonsu, Aneesah dake ta faman kuka ta juya tana kallonsa tana
ci gaba da rusa kukan, Almajirae ne suka shigo gidan rike da
kayayyakin abinci tun daga kan, buhun shinkafa, cartons din taliya
man gyada, da doya, Haiydar ya ja gefe ya basu hanya suka
shigo gidan suka dire kayan abincin, ya ciro dubu uku ya mika
masu hade dacewa tnk yhu, suka yi godiya suka fice daga gidan,
Abdul da ke ta bin Aliyu da kallo ya yatsine fuska a walakance
yana kallon Aneesah cikin tsawa yace "waye wnn kuma," bae rufe
bakinsa ba Haiydar yace "Barrister Aliyu Muhammad, kai fa?" ya
tambayesa yana masa wani irin kallo, Abdul yyi wani mugun
murmushi ya sake Aneesar da har lkcn yana rike da ita yace
"uban meye hadinki da wnn," xata yi magana Haiydar ya riga ta,
"abinda ya hadata da kai shi ya hadata ni," Abdul yyi masa kallon
tsab daga sama xuwa kasa snn ya fashe da wani wawan dariya
yace "xamu gani," snn ya juya a fusace ya bar gidan, Aneesah ta
sulale kasa a hankali ta hade kanta da gwiwa tana kuka, Haiydar
ya karaso gabanta ya durkusa ya dago kanta yace "bana son kina
kuka Aneesah, ki kwantar da hankalinki bbu wanda ya isa ya cutar
min ke kinji kanwata" tayi shiru bata ce komai ba tana kallonsa, ya
ciro hankici ya share mata fuskarta snn ya mike tsaye yace "Ammi
fa," a hankali tace "ta tafi kasuwa," ya durkusa gabanta kuma a
hankali yace "kinsan me Aneesah, ki daina tsayawa gida ke daya,
duk inda Ammi xata kuje tare ," ta gyada masa kai ta dan yi
murmushi tace "to yayana," ya dagota shi ma yana murmushin ya
ja ta xuwa kan tabarman da take xaune da litattafenta, suka xauna
ya jawo books din yana dubawa, binshi kawae take da kallo, ya
dago kai suka hada ido ta rufe fuskarta da sauri tana 'yar dariya.
Abdul ne xaune kan kujera yana kallon ubansa dake ta fama latse
latsan laptop, baffa ya dago yana kallon Abdul din yace "ya aka yi
guy?" Abdul ya tabe baki yace "ca nayi ina son cikin satin nn, ka
daura min aure da Aneesah, da ita xan koma london, don aure
nake so, kuma ina sonta," baffa ya mike a fusace yace "Aneesah,
wacece Aneesah, uban me xaka yi da Aneesah, ba gwara ka kawo
min baturiya ba kace na aura maka ita, Aneesar bnxa" Abdul ya
mike ransa a bace yana nuna uban nasa da dan yatsa yace "kaga
dad, Aneesah nace maka xan aura, kuma ita xan aura, wnn ai
mgnr kawae kke min, ni fa xan xauna da ita ba kai xaka xauna
min da ita ba," baffa ya sauke ajiyar xuciya ransa a jagule yana
dan kame kame yace "look guy bae kai ga hka ba, kar ka damu
xan aura maka Aneesah vry soon, amma ba ynxu ba sae nn da
wata daya," Abdul ya buga table din gabansa, a fusace yace "y
one month dad, da ita nke son komawa london nace maka, ko
baka gane bne," baffa yace "cool down son, yau fa satinka biyu,
kafin ka koma xan aura maka ita, kuma sati biyu xakuyi a nn kafin
wata biyun hutunka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login