Showing 9001 words to 12000 words out of 89000 words
"A'a taje kawae anjima sae taxo ta xuba min," yana fadin hka Aneesah ta juya ta fara sauka daga dinning din Hajiya ta daka mata tsawa "ke! Ke wace irin yar kauye ce,uban wa ya baki ixinin wucewa daga yayi magana sae kiyi gaba kmr wata tababbiya," yace eh xata iya wucewa mum, anjima xan nemeta," Hajiyar ta galla mata harara taci gaba da cin abincinta. Haiydar bae tashi kiran Aneesah taxo tayi serve dinsa ba sae da kowa ya watse daga dinning din suka haye sama, ta karaso dinnin din ba tare da ta kalli inda yake ba fuskarta a hade tace "me xan xuba maka," ya mike tsaye yana kallonta yace "nace ke me kika ci," ta galla masa harara gabanta na faduwa don tsoro yake bata tace "ina ruwanka malam, ni kaji dani na bar nn wajen," ya dan kalli hanyayr stairs ko wani na xuwa ya ga ba kowa, ya fixgota yace "ae sae kin gaya min me kika ci ke idan ba hka ba sae dae mu kwana nn" ta tsorata sosai jikinta ya dauki rawa lkci daya ta fara hawaye muryar ta na rawa tace "nashiga uku na lalace ka rufa min asiri ka rabu dani wllh ni ba 'yar iska bace," hkn ya basa dariya, ya wara mata ido har lkcin hannunsa na kan kafadarta yace "dagske" ta gyada masa kai tana hawaye sosai, ya sake ta yace "to xo ki xuba min fried rice da plantain din," jikinta na rawa ta xuba masa abinci don duk ya tsoratata, tana gama xubawa kuwa ta juya xata bar wajen yyi saurin kamo hannunta ya dauki plantain daya ya sa a baki snn ya dauki wani ya kai bakinta yace "ina xaki kuma, ae dolen ki ma tare xamu ci, idan ba hka ba wllh baxa ki bar nn ba, kin dae ji nace wlh, oya bude bakin" ta dafe kirji tayo waje da ido tace "ni? Ka rufa min asiri wllh wanke wanke xanyi na koshi," ya mike tsaye ya tsaya gabanta yana kallonta ta koma baya ta jingina jikin fridge a tsorace tana hawaye, yyi murmushi yace fridge din xaki shiga, Ta fashe da kuka tace, "kanae ma darajan Allah ka rabu dani nace mka wllh ni ba 'yar iska bace, ka tausaya ma rayuwata ka rufa min asiri ka kyaleni"
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: haleesat Haiydar's post
Khaleesat Haiydar
~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 13...... Haiydar yyi murmushi yana kallon cikin idonta yace "to bude baki na sa maki plantain sai ki wuce," ta fara waige-waige a tsorace tana kkrin barin jikin fridge din don dab da ita yake har tana iya jin breathin dinsa a fuskarta, yyi saurin sa hannu ya tokare hanyar da xata bi, ta marairaice murya kmr xata yi kuka tace "A'a ni na koshi," yace "ashe dae baxa ki bar nn ba yarinya," ganin da gske yake yasa ta bude bakin a hankali yana kallon kwayar idonta ya saka mata plantain din a baki, ta shiga taunawa a hankali yana mata wani irin kallo, ya matsar da ita daga jikin fridge din, ta fixge hannunta da sauri xata bar wajen, ya maxa ya rikota yace "baki isa ba tukun," ya na rike da ita ya bude fridge din ya dauko chill hollandia yoghurt, snn ya maidota jikin fridge din ya jinginar, ya bude drink din ya xuba cikin glass cup, ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri ya hade rai yace "Allah baxa ki bar nn ba idan baki sha ba" kuka ta dinga yi tana rokansa ya kyaleta ta wuce, amma yaki sakinta wae sae ta sha hollandian, ganin ba sarki sae Allah ne yasa ta bude bakin a hankali ya shiga bata drink din tana sha, muryar Hajiya suka ji daga sama tana cewa " wae Aliyu ya fita ne meenah," a tsorace Aneesah ta turasa ta durkushewa wajen tace "nashiga uku na lalace," shi kuma yyi saurin juyawa ya koma dinnin ya xauna, dae-dae nn Hajiyar ta karasa saukowa da meenah, idonta ya sauka kan Aneesah da har lkcn ta kasa mikewa tsaye daga wajen, cikin tsawa tace "ita kuma warcan me take min jikin fridge hka," Haydar yyi saurin cewa "No ni nace ta bude ta kawo min drink, tace "Ayyo" snn ta karaso dinning din ta xauna tana cewa "har yanxu baka gama cin abincin ba son," Aneesah ta dauko hollandian da ya ajiye mata gabanta duk ta rude tama rasa abun yi ta hado da cup din ta dan risina ta ajiye masa gabansa kan dinin table din ya kashe mata ido ya bita da kallo ta bar wajen da sauri har tana tuntube. Ranar cikin rashin kuzari ta isa gida ta xube kan katifa, Ammi ta tambayeta lfya, tace kawae kanta ne ke ciwo, Ammi ta bata magani bayan ta sa ta gaba taci tuwon da tayi masu, snn taje tayi wanka tayi sallah ta koya ma yusuf assignment dinsa, ta danyi karatun qura'ani har karfe takwas, snn tayi sallahn isha tayi ma Ammi sae da safe ta kwanta duk da ba bacci take ji ba, kawae abun duniya ne ya isheta, ita kam duk aikin ma ya gama sare mata xuwan Haiydar, su dinga dabi'a irin ta nasara kmr wa inda basu da ilimin addini, ita a al'adarsu ta hausa fulani bata ga namiji na taba macen da ba muharramarsa bace, gskya ta kara tabbatar da cewar gidan nn basu da tarbiya, in Allah ya yarda aikinta ya kusan xuwa karshe a gidan, xata sa Ammi ta samo mata wani wajen daban da xata dinga aiki, baxata je ya cuceta a bnxa ba don bae mata kama da mai kamun kai ba. Hka Aneesah ta dinga aiki a takure a gidan, don Hydar duk ya bi ya sa ta gaba, indae yana gidan to bata da kwanciyar hankali don kawae sae dai taji mutum tsaye a bayanta, in tana garden to shima yana can, shi dae kawae so yake yaji lbrinta wae bata yi kama da 'yar aiki ba, kuma yasan tana da ilimi both, sau dayawa ya kan mata turanci don ta maida masa, amma ko sau daya bata taba mayar masa ba, sae dae ma tayi kmr bata ji mai yace ba, da ya kawo mata xancen yana son sanin ko ita wacece sae tace masa ba matsalarsa bace wnn, in kuma ta tashi serve dinsa abinci to sae ya tilasta mata ta ci abincin da ta xuba mashi, duk ya bi ya tsorata ta a gidan kuma duk wnn abun da suke ko sau daya Hajiya bata taba lura ba, hka ma yan matan gaba daya, yau ma kmr kullum tana xaune garden tayi xurfi cikin tunaninta bayan ta gama duk aikin da xata yi a gidan, ita kam kila yau ce rana ta karshe da xata kara aiki a gidan, don bata ga dalilin da Haiydar xae takura mata a kan sae yasan ko ita wacece ba, ga abun Hajiya sae gaba yake karawa ta rasa abinda tayi masu ba ita ba ba 'ya yanta ba, in ta tashi tafiya yau kawae ce mata xatayi ta bar aiki, ta gaya mata ranar da xata xo ta karbi kudun aikinta na rabin watan da tayi, idan kuma tace baxata bata ba, shkkn ta bar masu, tayi tagumi tana kallon tsuntsaye tana tunanin ko shawarar da ta yanke yyi taji hannun mutum a wuyanta, ta juya a fusace ta dan matsa cikin fada ta fara magana "wae meye hka malam, bana son iskanci ka rabu dani nasha gaya mka ni ba 'yar iska bace," ta mike ta shige kitchen ya bi ta da kallo, ko da ta shiga gidan ta tarar su Hajiya sunyi shiri xasu fita, tana cikin goge masu takalman da xasu sa ya shigo falon, fuskarsa a daure ya xauna kan kujera Hajiya ta shiga tambayarsa me yafaru bai tanka mata ba, tace "xamu fita son amma ni ba dde wa xanyi ba ynxu xan dawo," ya gyada mata kai kawae yana kallon Aneesah da gabanta ya shiga bugu da sauri, suna fita kuwa ita ma xata bar gidan tana gani, ya hade rai yace "ya ma kike da suna" ta juya tana kallonsa tace "Ni," hajiya ta haureta tace "to da uwarki ce idan ba ke ba" a hankali tana hawaye tace "Aneesah," yace "gud, bedroom dina xaki gyara min idan kin sallamesu
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
15.....
Aneesah tayi shiru tana kallonsa ta kasa cewa komai, ya gyada mata kai yace "am ol ears," ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Abbana ya rasu, Ammi ta ce kawae sae kanina yusuf" sae ga wani sabon hawayen tana yi, ya girgixa mata kai yace "a'a bance kiyi min kuka ba Aneesah," ya sa handkerchief ya goge mata fuskar snn yace "go on momyna" ta sunkuyar da kanta a hankali ta fara basa lbrin rayuwarsu tun daga rasuwar abbanta har ixuwa ynxu da yake xaune kusa da ita, tayi kuka sosai kmr ranta xae fita, ya xuba mata ido yana kallonta ya kasa cewa komai, ta goge fuskarta ta mike xata bar dakin ya kamo hannunta ya maido da ita ya xaunar, a hankali cikin nutsuwa ya fara magana "shi baffan naku a wani anguwan yake, snn relatives dinku mae suka ce dangane da abinda yyi, kuma wish din Abbanku knn ya rike maku gadon ku har ku mallaki hankalinku ko tsarinsa ne, snn me abokanan abbanku suka ce game da hkn, Abbanku na da lauya ko bae da??" Aneesah tayi murmushin da bata shirya ba xata yi magana suka ji muryar Hajiya downstairs, ta mike a tsorace tana kallon agogo, karfe uku har ya wuce, tace "nashiga uku na lalace," ya mike da sauri ya koma kan kujera yace ta cire bedshit din, jikinta na rawa ta cire bedshit din, dae-dae nn Hajiyar ta shigo dakin tana kallonta da mamaki cikin tsawa tace "ynxu shegiyar yarinyar nn baki girka abinda nace maki ba, gyaran dakin ne tun daxu," Aneesah ta fara kame kame a tsorace xata yi magana Aliyu ya riga ta "A'a aikenta nayi mum, bata dde da shigowa ba nace ta wanke min bathroom kafin ta gyara dakin," Hajiyar tace "Ayyo," snn ta galla mata harara ta ja kujera ta xauna tana kallon Haiydar din da damuwa tace "wae son ya maganar companies din Abbanku na lagos ne, kasan fa mutane basu da tsoran Allah tun da mahaifinku ya rasu Haiydar sau biyu ka waiwaye lagos," cikin fada ya fara mgana yana kallonta "to wae mum so kuke na kasa kai na ne, meye hadin barrister da wani bussiness can, ni ynxu cases din dake gabana ma sun fi karfina, su Amina da sumayya uban me suke yi ba abinda suka karanta ba knn, sun gwammace su yi ta gantali a garin Abuja," ya jawo laptop dinsa ya kunna ba tare da ya kara kallonta ba, tace "to kayi hkuri kuma fa gskya ne," Aneesah ta gama gyara gadon ta fita ta bar masu dakin tayi hanyar kitchen daura girkin da aka sa ta. Karfe shidda ta dauki hijab dinta tasa xata tafi gida, ta durkusa gaban Hajiya gabanta na faduwa ta dai yi shahada tace "Hajiya ina son ajiye aiki daga yau, idan yaso sae ki gaya min randa xan xo karban kudi na na rabin watan da nayi aiki," Hajiyar ta shiga mata wani irin kallo snn tace "gidan uban wa xaki da xaki ajiye aiki," ta girgixa kai a hankali tace "ba inda xani," cikin tsawa Hajiyar tace "baki isa ba to muguwa, a gidan uwarki ake hka, kinsan xaki tafi tun da can baki gaya min ba na samo wata sae ynxu da rana tsaka, kuma wllh baki karasa min aikin wnn watan gaba daya ba baxan baki kudin rabin watan ba, snn sae kin tsaya har an samo min wata yar aikin idan ba hka ba in na maki Allah ya isa sae ya biki wllh, tunda ban san ubanda xai dinga min aiki ba idan kika tafi bbu wata," a hankali tace "to xan jira ki samo wata 'yar aikin," Hajiyar tace "oho dae ya rage naki muguwa kawae" jikinta a sanyaye ta fita daga gidan, ta tarda Haiydar bakin gate a waje yana tsaye da alamar ita yake jira, ya karaso kusa da ita yace "lemme drop yhu," ta hade rai tace "A'a ngd" ya harareta yace "baki isa ba," tace "Allah bana so" bata sake jiran me xe ce ba ta kama hanyar gida da sauri da sauri. Tana isa gida tayi wanka tayi sallah ita da Amminta da yusuf, suna cikin cin abinci karfe kusan bakwae da rabi, suka ji ana bubbuga kofa daga can waje kmr xa a balla, duk suka yi tsit suna kallon bakin kofar dakin, aka shigo gidan aka banko kofar dakin, baffa shehu ne, ya tsaya yana hura hanci yace "ikon Allah, na sami lbrin abin kunyan da kuke yi a gari ke da tsinanniyar 'yar ki maryam, ynxu sbda tsabar butulci irin naku da rashin godiyar Allah duk abinda nake maku sae kin tura yarinyar nn karuwanci," Ammi tace "karuwanci kuma yaya, to Allah ya saka mana," cikin tsawa yace "sharri nai maki munafuka, idan ba shi kuke yi ba ubanwa ke ciyar daku tunda ni dae na fi wata uku bnga kun xo gu na maula ba, kuma a gari naji wnn xancen ana ta yayada wa, kuma gashi na xo na gani da idona wae kune da cin shinkafa da miya da nama yau," Aneesah dae abincin ta kawae take ci, Ammi ta goge hawayen dake xubo mata tace "in'sha Allahu sae Allah yyi mana shari'a daku ranar gobe kiyama," haba kamar kar ta fadi hka baffa ya dinga bala'i yana yo wa kanta kmr xae mareta, ita dae kanta sunkuye yake tana hawaye, hka ma Aneesah da ta kasa daure wa ta fashe da kuka, kmr daga sama suka ga an wullo torch light ya kwalesa da karfi a ka, ya dafe wajen yana salati a gigice, yusuf ne ya jefesa yana huci yace "xan fasa maka kai na cire maka hakori idan ka sake sa Ammina da Antyna kuka," ya karasa bakin kofar da gudu ya rufe masa kof[truncated by WhatsApp]
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By khaleesah Haiydar 14..... Aneesah
ta dago a hankali tana kallonsa hawaye na bin
kuncinta, shima ya tsura mata manyan idonsa,
Hajiya tace "idan kinga dama kina gama gyaran
bedroom din ki girka mana fried rice da cream
salad sae farfesun naman rago da coconut drink,
kuma kiyi dayawa don xan yi baki daga lagos
anjima, muryarta a dashe tace "to Hajiya," su
meenah dama tuni suka fita suna jiran Hajiya a
mota, Hajiya ta juya tana kallon pretty dake
kwance gefen yayanta tace "ke baxaki je bne bby,"
ta dan yatsine fuska tace "na fasa xuwa momy xan
taya yayana hira," Haiydar yyi saurin cewa "A'a
nima fita xanyi, tashi kawae ki bisu," ta xumburo
baki tace "to ba sae mu fita tare ba," ya galla mata
harara yace "nace ki tashi ki bisu don bbu inda
xan kai ki," gaban Aneesah dake durkushe bayan
ta gama goge ma Hajiya takalmanta ya shiga bugu
da sauri, lallai suna fita kuwa ita ma xata bisu a
baya don bbu abinda xae kai ta dakinsa, dama yau
ai take son ajiye aikin, Hajiya ta bude baki tana
kallonta bayan ta gama sa takalminta cikin tsawa
tace "wae kina nn xaune ne har ynxu wnn dabbar
yarinyar," ta mike tsaye da sauri jikinta a mace tayi
hanyar kitchen, ta sake mata wani uban tsawan
tace "gidan ubanwa xaki," a tsorace tace "girkin
xan daura," ta fixgota a fusace ta kai mata mari
tace "don uwarki kin gyara masa bedroom din ne,"
cikin kuka tace "A'a ynxu xan gyara," Hajiyar ta
wurgar da ita hanyar stairs tace "kuma ki bari na
dawo naga bbu girkin da na saki wllh sae na
kusan sumar dake yau tunda kince ke bakya jin
magana," duk wnn abun da suke Haiydar na
kallonsu bai ce komai ba, tana kuka ta hau stairs
din tayi hanyar bedroom dinsa da kyar don har
wani jiri take gani don tashin hnkli, tana shiga
bedroom din ta ga ko ina a gyare, TV na aiki hka
ma A.c dakin sae kamshi yake, sae laptop dinsa
da files dake kwance kan gadon, tun bayan ranar
da xae dawo da ta gyara masa daki bata sake
shigowa dakin ba sae yau, kullum da safe pretty ce
ke gyara masa daki don yarinyar na bala'in son
yayanta, Aneesah ta goge hawayen da ya kasa
tsaya mata, tasan ba alkhairi yake nufi da ita ba,
tana jin budewar gate alamar su Hajiya sun shiga
mota xasu fita ta juya da sauri ta yi hanyar kofar
dakin don dama hka take jiran ji kafin ta fita daga
dakin daga nn kuma ta bar gidan ma gaba daya,
tana isa bakin kofa ya riga ta bude kofar ya shigo
dakin, ta fasa ihu a tsorace ta koma baya tana xaro
ido, bae juyo ya kalleta ba har sae da ya kulle
kofar dakin, ta fashe da kuka tana komawa baya
murya a raunane ta fara magana, "don Allah don
Annabi don darajar iyayenka ka tausaya ma
rayuwata ka rufa min asiri wllh ni marainiyace, ka
taimake rayuwata ka ceceni ka kyaleni, nayi maku
alkawarin xan bar maku gidanku plss am beggin"
tana magana ne tana kuka sosai tana komawa
baya shi ko binta kawae yake har ta isa jikin
bangon dakin ta sulale kasa ta sa hannu ta rufe
fuskarta jikinta na rawa tana ci gaba da rusa
kukanta, ya durkusa gabanta yana kallonta snn
yace "idan kin gama kukan, tashi ki xauna nn
magana xa muyi," ta dago kanta a tsorace tana
kallonsa ya nuna mata kan gado, ta girgixa masa
kai ta kasa cewa komai, hkn yasa ya koma kan
gadon ya xauna, ya danyi shiru na wani lkci snn
yace "idan kika bani hadin kai nasan ko ke wacece
ba ddewa xakiyi a dakina ba, don hka kiyi save din
tym dinki duk tambayar da nayi maki ki bni amsa,
kuma ki bar tsorona ni bbu abinda xan maki, ko
da me kike tunanin xan maki??" tayi shiru kanta na
kasa sae hawayen da take yi, ya mike tsaye ya
dago ta ya xaunar kan gadon ya ciro handkerchief
ya goge mata hawayen fuskarta yana kallonta yace
"tell me about yhur sef, am ol ears," tayi shiru taki
cewa komai har sae da yace "kin yi