Showing 1 words to 3000 words out of 89000 words

Chapter 1 - ANEESAH Complete Hausa Novel

14 Oct 2024

3116


~ANEESAH~.... By Khaleesah~Haiydar
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.


We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.



***
1.....
A guje ta fado dakin ta xube kan Amminta dake linkin kaya tana sakawa cikin jaka, Ammi ta dago fuskarta a rude tana tambayarta "lfya? me yafaru?" tana mayar da numfashi a dan tsorace ta kasa ce ma Amminta komai, sae da Ammi ta maimaita mata tambayar a fusace snn ta fashe da dariya tace "wae Ammi yusuf ne xae dokeni, don mota ta take masa kwallonsa nayi dariya," Ammi ta haureta cikin fada ta fara magana "wae ke yaushe xakiyi hankali ne Aneesah, ba wanke-wanke na sa ki ba kika fita waje kina biye ma yusuf, shi yusuf din kike ma gudu idan ba wauta ba," ganin yanda Amminta ta fusata yasa ta mike tsaye da sauri ta marairaice murya tace "kiyi hkuri Ammi, amma idan na fita wllh dukana xae yi, kuka fa yake yi," Ammi xata yi magana sae gashi ya shigo dakin, da gudu tayi bayan Ammin tana cewa "wayyo ammi kin ganshi ko," Ammi ta dada mata duka snn tace "kai yusuf yayar taka xaka duka don ba ka da kunya," yyi ma Aneesar wani irin kallo yace "Allah ya taimake ki mutumin ya bani Naira ashirin na siya wani kwallon," Aneesah ta dinga dariya tana cewa "Naira ashirin" yace "eh mana" snn ya fito da sabbin dubu daya guda biyu, Aneesah ta xaro ido tana kallonsa, Ammi tace "kai yusuf wa ya baka wnn kudi hka," yace "mutum da ya fasa min ball da motarsa yace naje na siya sabo," Ammi ta juya tana kallon Aneesah, can tace "to kawo nn yusuf, anjima da kaina xanje kasuwa na siyo maka wani, amma kace masa ka gode ko?" yusuf yace "aa na manta, snn ya mika mata dubu biyun ya fice ya fice daga dakin," Ammi tace "oh Allah dae ya biya wnn mutumin, kmr yasan ynxu tunanin me xamu ci anjima nake Aneesah," Aneesah tayi murmushi tace "ki siyo kayan abinci kawae Ammi," ammi tace "hkn xanyi, bari na gama hada kayan nn sae na tafi kasuwa," Aneesah ta mike jikinta a sanyaye ta fita daga dakin taje yin wanke wanken dake tsakar gidan.
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 3...... Yan uwansa na ganin hka suka fara shisshige masa suna nuna masa so, da yake shi Allah yyi sa mutum ne mai son xumunci kuma mara riko, ko kadan bai kullace su kan abinda suka yi masa ba ya ja su a jiki ya sama masu aiki don dama duk buga buga suke, ya kuma taimaka ma yan uwa da dama tun daga kan relatives har xuwa wa inda ma bai hada komai dasu ba. Ana hka suka hadu da Mahaifiyarsu Aneesah Maryam a bikin wani abokinsa, sunyi soyayyar gskya wanda ya kaisu ga aure duk da dangin ubanta basu so hkn ba don auren xumunci suka yi niyyar mata, amma da yake Allah yyi shine mijinta a hka su ka yi aurensu wanda bayan shekra daya Allah ya axurta su da samun Aneesah, daga ita ko basu sake haihuwa ba har sae bayan shekara takwas, don kaninta yusuf na da wata biyu mahaifin nasu ya rasu, ba karamin girgixa Ammi mutuwar mijin nata yyi ba, kuma duk da tsanar da danginsa ke mata don ko kadan basa sonta a hka ta gwammace ta xauna ta tarbiyantar da 'ya yanta a gidan ubansu don iyayenta talakawa ne sosae snn tun tana da shekara goma mahaifiyarta ta rasu matar uba ta sa ta gaba, hkn yasa kakarta na wajen uwarta ta maidota wajenta har Allah ya hadata da Alhaji Mukhtar suka yi aurensu, kuma tasan ko ta tunkari gidan mahaifinta ynxu baxae karbeta ba don duk abinda matarsa ta gaya masa shi yake bi, kuma matar bata so ta auri mai kudi ba tunda yayanta duk ba masu kudi suka aura ba, hkn yasa ta hkura ta xauna gidan mijinta da yaranta. Ko wata uku ba'ayi da rasuwan Alhaji Mukhtar ba yayansa da suke kira da Baffa shehu ya fitar dasu daga lafiyayyan mansion din da suke ciki wae xae sa yan haya ya dinga tara ma marayu kudinsu, duk da gidajen da mahaifin nasu ke da, Ammi bata yi masa musu ba ta harhada kayansu don a tunaninta dan madaidaicin gida xae basu su xauna, amma sae suka ga ya maidosu suleja ya basu daya daga cikin gidajen da Alhaji Mukhtar ya kyautar dasu ya bar ma mara su halin kama gida talakawa su xauna, ya kori occupant din ciki gaba daya wae ba kyauta kaninsa ya basu ba dama, a hka Ammi da yaranta suka xauna gidan cike da bakin ciki tunda basu da mai tsaya masu sae Allah, don cikin yan kwanakin nn da rasuwar mahaifinsu bbu abokinsa daya da ya sake lekosu, sun dae ci sa'a ya sa su private sch mai karamin kudi, ixuwa ynxu da Aneesah ke ss3 tana shirin xana waec da neco duk da sai term ya kusan karewa ma yake biyan kudin makarantar don sae suyi xaman sati shidda a gida basu je makaranta ba, kayan abinci kuwa idan ya ajiye masu buhun shinkafa da man gyada galon daya sae yyi kusan wata shidda bae waewayesu ba, ba karamin kkri Ammi ke yi ba don sbda future din 'ya yanta har wankau ta shiga yi, ta nn ne suka samu suke rufa ma kansu asiri. Bayan sati daya duk dan kayan abincin da Ammi ta siyo masu da kudin yusuf ya kare ta rasa yanda xata yi, don gidan da take wankau sun yi tafiya xuwa england tun wata daya da suka wuce, tayi jigum abun duniya ya isheta, gashi har kusan karfe goma basu karya ba jiya da daddare ma ba wani abincin kirki suka ci ba, don ita bata ma ci ba ta bar masu ganin bae da yawa ta sha ruwa kawae suka kwanta, Aneesah na xaune bakin kofa tana duba takardun makarantarta duk da yunwan take ji amma ko kadan bata nuna hkn ba tana ta karatu, yusuf ya shigo gidan don dama yana waje yana wasa da yara, ya fada jikin Ammi yace "ni Ammi yunwa nke ji," tayi shiru tana kallonsa, can ta kwalo ma Aneesah kira ta shigo ta nemi guri ta xauna tace "na'am Ammi," ammi tayi ajiyar xuciya tace "je wajen ladi mai kosae kice ta baki na dari xan kawo mata ko xuwa gobe ne," ta mike ta dauki hijab dinta ta fita daga gidan jikinta a sanyaye, tana isa ta tarda ladi na ta tuyan kosanta hankali kwance ga mutane cike wajen suna siyan kosae, ta dan ja gefe ta bari mutanen suka ragu snn ta bata sakon Amminta bayan ta gaisheta, ladi ta hade rai tace "ku ni fa ban ciki da cin bashin nn naku, kosan da idan an baku bashin ma ba biya kuke ba ynxu da xan xauna na lissafo bashin da kuka cin min wllh xae kai dubu daya, kullum gobe xa a kawo alhalin ba kawowan ake ba, to ni yau kullina bai da yawa bna bada bashi," ta ja tsaki ta ci gaba da tuyanta tana xage xage, a sanyaye Aneesah ta bar wajen ta koma gida ta xauna bakin kofa xata yi magana Ammi tace "shknn tunda bata ba ki ba," Aneesah ta dauke kanta kawae bata ce kmai ba, hka yusuf ya cika masu gida da kuka shi a bashi abinci yaci, Aneesah ta hade kanta da gwiwa ta shiga rera kuka a hankali a bakin kofar, ko Ammi ma bata san abinda take ba.
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 2..... Aneesah na shirin islamiyya karfe
hudu saura Ammi ta shigo gidan, ta karbi ledojin dake
hannunta da sauri tanai mata sannu da xuwa ta fito
mata da kujera waje snn ta debo mata ruwa a randa
ta kawo mata, ta xauna gabanta tana tambayarta ya
hanya, Ammi ta ajiye kofin ruwan dake hannunta bayan ta shanye ruwan tace "maxa ki tashi ki kama
hanyar makaranta lkci na wucewa, ina yusuf?" tace
"nace ya jirani yace shi su khabir xae bi," ta mike ta
dauko goggen Hijab dinta da Nikaf ta saka snn tace
"to Ammi sae na dawo," Ammi tayi mata Allah ya
kiyaye ta fice daga gidan. Karfe bakwae saura su ka shigo gidan ita da kaninta, Ammi na share tsakar gida
su ka yi mata sannu da gida suka shiga daki, tana
gama cire uniform ta fito karbar sharan ammi tace "su
yi sallah, ga abincinsu a kitchen," yusuf na ganin
shinkafa da miyace ya dinga tsalle yana murna yau
xa su ci shinkafa, Aneesah ta galla masa harara tace "yau ka saba cin shinkafa ne? wawa kawae," ya daga
hannu xae kai mata kulli ta goce da sauri tare da
kwala ma Ammi kira ganin wani kullin xae kai mata,
Ammi ta shigo dakin da sauri ta raba ma kowa nasa
tana masu fada snn ta nemi guri ta xauna tana kallon
'ya yan nata. Aneesah yarinya ce da bata wuce shekara 17 ba, sun taso cikin wahala da talauci tun
bayan rasuwan mahaifinsu Alhaji Mukhtar, Alhaji
Mukhtar shararren mai kudi ne a garin Abuja, Allah
yyi masa rasuwa shekara takawas da suka wuce a
hatsarin mota da yyi a hanyar sa ta dawowa Abuja
daga kano bayan ya kai ma 'yan uwa da relatives ziyarar sallah, tun bayan rasuwarsa suka fara
fuskantar kalubalen rayuwa duk da dukiyar da ya bari
mai dumbin yawa don a lkcn ma gidajen da ya bari
sun kai 6 bayan motoci da filaye, kiri kiri yayansa
Alhaji shehu ya karbe komai nasa da sunan xae ajiye
har sae yaransa sun mallaki hankalin kansu, Alhaji Mukhtar shine auta a gun mahaifinsu malam sule, da
mahaifiyarsu saudat, su uku kadae Allah ya basu duk
maxa, shehu, ibrahim da shi Mukhtar, tun yana
primary Allah yyi ma mahaifiyarsu rasuwa, yana gab
da gama secondary mahaifinsa ma ya rasu, tun daga
lkcin komai ya tsaya masa don duk yayyinsa sun dauki karan tsana sun daura masa tun iyayensu na
da rae bare ynxu da suka koma ga Allah, duk suka
juya masa baya ga 'yan uwa ba xumunci, ya sha
wahala sosae a rayuwa don da kyar da taimakon
sana'ar da yake yi na wankin mota cikin ikon Allah ya
kammala karatunsa ya sami aiki a House of Assembly Abuja.
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 4..... Sallamar wata makwabciyarsu ne ya sanya Aneesah ta dago tana goge fuskarta, ta karaso cikin gidan Aneesah ta gaida ta ta amsa tana tambayrta ya karatu, ta shiga dakin ta gaida Ammi snn ta ajiye kwano tace "gashi a ba yusuf ya kara Ammi, bbu yawa," Ammi tayi mata godiya tana tambayrta danta umar, tace "yana can waje suna wasa" snn ta fice. Ammi ta jawo kwanon ta bude taga dumamen tuwo ne, tasan kila yusuf yace mata yana jin yunwa ne shine ta kawo abincin don matar tana da kirki sosae duk da su ma manage suke don sae mijinta ya fita yyi shoe maker snn suke samun abinda xasu ci suma , ta kira Aneesan su xo su ci, bakin ciki da takaici yasa taji ta daina jin yunwan ma kwata kwata tace bata ci, da kyar Ammi ta lallabata ta ci dn tasan halinta. Karfe sha biyu saura Ammi ta fito da dinkekken atamfarta da kakarta ta aiko mata da wani sllh, Aneesah ta tambayeta inda xata da shi ganin tayi shirin fita ne, Ammi tace "xan je kasuwa ne na sayar Aneesah kafin su Hajiya salamatu su dawo," Aneesah tace "haba Ammi ke knn kullum sayar da xani don Allah don annabi," Ammi tace "to meye amfaninsu Aneesah," ki kula da yusuf kafin na dawo don daga can xan siyo abinda ya sauwaka na abinci," bata jira cewar Aneesahn ba ta fita daga gidan. Tana tsaye bakin kofar dakinsu bayan ta gama shirin boko, yusuf yace "Anty mu wuce kar su Jamila da khabir su ruga mu yau ma," Aneesah ta jawo sa tace "kasan me yusuf, maxa ka bisu ni ina nn xuwa kaji," bae yi mata musu ba ya fice daga gidan, Ammi tace "to ke me kike jira Aneesah," Aneesah ta shigo cikin dakin ta xauna tana kallon Amminta tace "kudin waec nd Neco Ammi, kuma ance kar mu xo yau idan har mun san xa muyi kuma bamu kawo kudi ba," Ammi ta tsura mata ido tana kallonta tace "to yaushe ma ya bada kudin makarantar da har xa'a tunkaresa da wani kudin waec, amma dae ki shirya kije ki samesa ki gaya masa ynxu kila Allah ya daura ki a kansa Aneesah" Aneesah ta hade rai, can ta tabe baki tace "bbu inda xanje Ammi, gwara kar na sake xuwa makarantar ma kwata kwata," Ammi ta galla mata harara tace "to ki xauna," Aneesahn tace "to wnn mutum ne Ammi, ko fa naje ba bani xae yi ba sae dae ya walakanta ni ma, ba gwara kawae kar naje ba," Ammi tace "ko ma de mae xaki ce, yayan babanki ne, baffanki ne dn hka ki iya bakin ki, kuma ki tashi ki shirya ki tafi kafin ya fita," ta mike jikinta a mace ta tube uniform dinta, ta dauki wani material dinta ashe da maroon ta saka, duk da talaucinsu in ta fita baka taba cewa tana cikin wahala don kullum fes xaka ganta. Ammi ta bata kudin motar tace ta barshi kawae xata taka, dole ta tilasta ta ta amshi kudin dn can cikin gari xata da nisa sosai. Aneesah na isa gidan baffan nata ta danna kararrawa daga waje mai gadi ya leko ta gaishe shi ya bude mata gate din ta shigo, ta tambayesa ko kawunta na ciki yace eh, da kyar gabanta na faduwa ta shiga gidan da sallamarta ta gaida 'yan aikin dake ta harkar gabansu a gidan, snn ta karasa cikin falon ta xauna kasan tiles tana jiran fitowar baffan nata.
Like · Report · 4 minutes ago
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 5...... Aneesah ta kusan minti ashirin xaune a falon kafin baffan nata ya fito cikin shiga ta shadda green colour sae walkiya yake, ga kamshin turare ya baxa ko ina, yana ganinta ko ya hade rai cikin daga murya yace "dama kece ki ke nemana wae?" ta sunkuyar da kai tace "eh nice ina kwana baffa," ya amsa a dakile snn yace "lfya da sassafen nn hka," tace "A'a dama kudin waec da Neco ne aka fara karba a schl, shine naxo na gya mka don sun ce kar mu xo yau ma," sae da ya saurareta ta kai aya snn ya daka mata wani mugun tsawa yace "don uwarki ca nayi maki ina da kudi ynxu da har xaki xo da sassafe karban kudin waec da Neco, kin bani ajiya ne ko uwar taki da ta aiko ki ta bani," ta girgixa kai tace "naga dae Baffa ba mu da wanda xamu tambaya bayan kai, kuma in ma hka ne ni fa ba kudinka nace ka bani ba, daga cikin kudin mahaifina xaka bani naje na biya abinda xan biya, kace sae mun mallake hankalin kanmu Baffa to ni dae na mallaki hankalina, a raba mana gadon mu kawae ka huta da tambayarka kudi ko makamancinsa da muke yi" tun da ta fara magana ya bude baki kmr soko cike da mamaki yana kallonta, tana gama fadin abinda xata fadi ya daka mata tsawa yace "ohho dama rashin kunya uwar taki ta turo ki kiyi min fateema, ni kike gaya ma wa innan maganganun don baki da kunya" ya saka salati yana jijjiga kansa yana kallon ceilin, ta dan tabe bki tace "ni fa ba rashin kunya nayi mka ba baffa" "to wllh wllh kinji rantsuwar musulmi ko, daga yau xuwa makarantarki ta kare, don aurar dake xayi don ubanki, kuma daga yau ko tsinke na ya daina shiga hannunku, shi uban naki da yake da rai uban me ya tsinana ma mutane sae uban rowa duk dukiyar da Allah ya basa, don uwarki duk hidimar da na ke maku har ixuwa yau da kudina nace maku ina maku, ai ki bar ma maganar gado don ko dubu dari bae rage cikin accnt din ubanki ba, duk kun cinyesu," ta mike tana yi masa wani irin kallo snn tace " lbri ma knn, shi kuma wnn gidan da kke ciki da sauran gidajensa da motocinsa fa ba a mayi maganar filaye ba, idan ma kace mun cinye kudin acc, ae wa innan suna nn baffa," ya kwasheta da wani gigitattcen mari yana huci "ni kke gaya ma wnn maganar," dae dae nn matarsa hajiya zuwaira ta fito da sauri, tace "me ya faru Alhaji, me ya kawo wnn kuma da sassafen nn," cikin in ina don ransa yyi mugun baci ya shiga yi mata bayani, Aneesah dae na tsaye dafe da kuncinta tana kallonsu, matar tasa bata bari ya kai aya ba tayi cikin kitchen da sauri tana cewa "ka kyaleni da shegiyar Alhaji," Aneesah na jin hka ta fice daga gidan da gudu don tasan matar bata da mutunci, bata manta randa ta biyo ta da yaji ba, yau kuma bata jira ganin me xata je daukowa ba ta yi ta kanta, tana barin anguwan ta dinga kuka a hanya tana bakin cikin wnn rayuwa irin tasu, da kyar ta isa gida don har wani jiri take ji dn yunwa dama koko kadae tasha da safe. Ammi ta mike da sauri tana kallonta tace "ya akayi kika dde Aneesah, me ya sa ki kuka," ta girgixa mata kai tace "ban samu ganinsa da wuri ba ne Ammi," sae da ta nutsu snn tayi ma Amminta bayanin duk yanda suka yi da baffan nata, Ammi ta dinga mata fada kmr xata mareta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login