Showing 18001 words to 21000 words out of 39355 words

Chapter 7 - BOYAYYEN ALAMARI Complete Hausa Novel

unknown   

14 Oct 2024

2573

goge hawayen, Tare da cewa."Anisa ba kuka nakeyi ba ' karki damu."Suna cikin haka ' aka shigo aka d'ibi jinin Umma, Sannan akayi settling scanning machine ' cikin y'an lokuta k'alilan aka kammala komai aka fitar da duk wani abunda ke damun Umma.Hakan yasa Doctor ya kirasu ita da Hafiz ' sukaje Office d'inshi suka sameshi.Bayan sun zauna ne Doctor ya fara yi masu bayani ' yadda zasu fahimta, Sannan ya k'ara da cewa."Ba komai ke damunta illa hunhunta da kitse ya rufe."Nan gaban Safna ya fad'i, Cikin rawar baki tace."Likita ban gane ba!.""OK!, Ina nufin kitse ya shiga cikin hunhunta, Yayi causing problems da dama ' Sannan kuma aka bata maganin da bai dace da wajen ba tasha! Wanda hakan shine yasa ta fara aman jini.""Yanzu Doctor meye abunyi?."Hafiz
yayi tambayar."Well, Aiki za'ayi mata idan kun amince, Wannan shine kawai solution d'in inba haka ba kuma zata iyarasa ranta ' Kuma wannan aikin yanada buk'atar kimanin kud'i har miliyan d'aya! (1 million)."Safna zaro jajayen idonta tayi wanda suka rune saboda kuka, Tace."Likita ka taimakeni ' ka kuma rufamun asiri, Wallahi ita kad'ai ta tarage mana gashi kuma ba muda kud'i don... "Bata k'arasa ba Hafiz ya dakatar da ita da cewa."Karki damu ' wannan aiba wasu kud'i bane masu yawa."Safna baki ta saki ' tana kallonshi cikin mamaki, Sannan Hafiz ya maida kallonshi kan doctor."Doctor, wannan bazai zama matsala ba ' yanzu dai a d'aurata akan magunguna kafin kud'in su samu.""Alright, To shikenan ' yanzu na baku nan da sati d'aya ku kawo kud'in."Cewar Doctor.Safna da Hafiz tashi sukayi suka bar Office d'in zuwa ward d'in da Umma tace, Safna ta tsaida shi da cewa."Amma a ina zaka sami wad'an nan kud'i?."Ta furta haka cikin sanyin jiki"Safna kenan! Ai kinada inda zakije ki nemo kud'in.""Wallahi babu inda zanje abani wad'an nan kud'in masu yawa.""Akwai!."Hafiz ya fad'i haka, Hakan yasa ta juyo ta kalleshi ' taga fuskar shi babu wasa aciki."Ina kenan?.""Wajen wanda kika tsana ' kika k'i yarda da abunda ya nema a wajenki, Tabbas zaki sami kud'in wajen Abokina Fauzan."Ajiyar zuciya ta saki mai k'arfi, Sannan ta fara tuna halin da Umma ke ciki ' da kuma bayanin da Doctor yayi masu.Cikin Muryar kuka ' tace."Amma kana ganin zai bani kud'in?.""Why not?, Karki damu zanyi mashi bayani ' kuma am very sure zai baki, Yanzu ki koma wajen Ummanki ' zanje indawo."Abunda yace kenan! Ya juya bar Hospital d'in, Sannan itama ta wuce wajen Umma.*** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 1:00PM*Bayan Hafiz ya koma gida ' yayi wanka yaci abinci, Tukunna ya kira Mr-Fauzan awaya ' bayan ya sanar dashi komai da duk damuwar da Safna ke ciki a yanzu, Mr-Fauzan yace."Zanyi amfani da wannan damar ' in tursasa mata dole sai ta aure ko tana so ko bata so.""Hmm... Aboki kenan bakada dama ' kamar kana sonyarinyar nan fa!.""Oh Come on! Sam babu sonta a raina ' me zanyi da wannan k'azamar? Kawai zan aureta ne don banason Mummy na ta auramun wanda banaso, You know me very well Hafiz."Murmushi kawai Hafiz yayi ' yana jinjina maganar Mr-Fauzan."Yanzu a wane hospital suke?."Cewar Mr-Fauzan."Suna private hospital girmi, And please ka aika akai musu abinda zasuci ' because basuci komai ba.""Alright, Zan tura P.A Kamal, Hafiz inason Monday ka kawo ta Office d'ina."Ya fad'i haka agadarance."OK I will do that."Nan sukayi sallama da junan su ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Sannan yace."Duk abunda ' na buk'ata saina sameshi!!!, Zaki aureni ko kinaso ko bakyaso ' That's Fauzan."Yana gama fad'in haka ya fito daga d'akin shi zuwa garden._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_@My Bestie~Jameesha..., Wannan page d'in naki ne ' kuma zanyi amfani dashi domin Nuna how muchI care about you! You're just different Besty, You're different indeed... Bari dai inyi shuru saboda sa'idawa!, In short! I love you... _**30-31*Bayan ya zauna ne ' Mr-Fauzan ya d'aga wayar shi ya kira Sir-Kamal, Ringing d'aya tayi ya d'aga."Hello Sir.""Amm... Kamal ' what are you doing now?.""Nothing Sir.""Good!, Inason kaje private Hospital Girmi ' yanzun nan, Wannan yarinyar na nan Mummyn ta batada lafiya, So I want you to go there! Ka siya musu abunda zasuci ' Ok?.""Ok Sir!."Cewar Sir-Kamal."And if you guys need something ' you let me know.""Ok Sir."Abunda Sir-Kamal yace kenan, Mr-Fauzan ya kashe wayar shi.Sir-Kamal mamaki ne ya cika shi ' zuciyar shi na rayamai wani abun daban.Tashi yayi ' ya fito daga gida ya shige motar shi gateman ya bud'e gate, Sannan ya fice a guje.B'angaren Mr-Fauzan zaune yake a garden tunda suka gama waya da Sir-Kamal, Tsuntsaye da furanni kawai yake kallo.Yana cikin hakan yaga Nafee tazo wajen taja kujera ta zauna ' tunda ya kalleta sau d'aya bai sake kallon taba, Nafee gyarar murya tayi zatayi magana ya d'aga mata hannu alaman dakatarwa."Meyasa kika zamo tamkar karya ' wacce batada zuciya?."Kalmar daya fad'i ne ta bugi zuciyar Nafee, Don kuwa abunda tayi hating arayuwarta shine akira ta da karya."Ko ce miki akayi ana so dole? Mum tana deceiving d'inki ne kawai ' amma babu yadda za'ayi na aura wacce bana so."Cewar Mr-Fauzan.Nan Nafee ta sunkuyar da kai ' hawaye na shirin zubo mata, Tace."Fauzan! Inason ka! Kuma nid'in mai k'aunar kace, Ka zageni ka kuma muzantani iya muzantawa ' amma inason ka sani cewa a yau d'in nan zan bar gidan nan naku... Kuma tabbas zan dawo domin saina rama abunda kaimun."Hawayen idonta ne suka zubo ' tayi sauri ta share, Sannan ta tashi tabar wajen.Mr-Fauzan karan kanshi yasan she is hurt, Amma sam baiyi nadamar abunda ya fad'a ba.Haka ya tashi yabi bayanta domin ya tabbar ko dagaske takeyi, Mr-fauzan koda ya shiga parlor a zaune ya iske Mummy da Daddy suna fira, Nan ya sami waje ya zauna shima.*After 5minutes...* Nafee ta fito along with her trolley' Khairat nabiye da ita abaya sai faman bata hakuri takeyi, Ganin haka yasa Mr-fauzan yatsine baki tare da nuna halin ko inkula.Mummy ne da Daddy suka mik'e tsaye cike da mamaki."Nafee lafiya?."Cewar Mummy."Mum! Ina d'aki fa naga tashigo tana kuka, Sannan tace mun ita gida zata wuce yau she will no longer stay with us again."Khairat ta fad'i haka cikin damuwa."Nafee? Lafiya? Ko mun maki wani abun ne?."Inji Mummy."No ni bakuyi mun komai ba, Nidai kawai inason in tafi gida yau am tired."Nan Daddy ya shiga cikin maganar."Nafeesat, Zo zo ki zauna nan muyi magana."Nafee sakin trolley d'in nata tayi ta sami waje ta zauna, Sannan suma suka zauna."Inason ki fad'amun dalilinki nacewa zaki wuce gida yau!.""No reason! Ni dai kawai I just want to go home, And please don't stop me."Daddy ajiyar zuciya yayi ' tare da girgiza kai."Shikenan Nafee bari insa driver ya kaiki."Mummy ta fad'i haka tana k'ok'arin mik'ewa tsaye, Nafee ta tsaida ita da cewa."Na riga na kira driver d'in gidanmu and am sure thathe's on his way now, Nagode da hallaccin da kika nunamin."Nafee na gama fad'in haka ta mik'e tsaye tare da jan trolley d'inta ta fice, Nafee cen wajen gate ta nufa ta bud'e, Sannan ta fice ' nan ta tsaya tana jiran driver d'in gidansu.B'angaren Mummy kuwa tunda Nafee ta fice ' take kallon Mr-fauzan, Tasan cewa duk yadda akayi he isresponsible."Son?."Mr-fauzan kai ya d'ago ya kalleta ' idon shi kawai ta kalla taga rashin gaskiya k'arara."Me kaiwa Nafee?.""Mum! Ta fad'a miki naimata wani abune?.""Son! Nasan abunda zaka iya da abunda bazaka iya ba, Haka nan kawai Nafee bazata ce zata wuce ba.""Mum, Kawai fa na fad'a mata gaskiya ne ' cewa bana sonta, Nothing else."Mr-fauzan ya fad'i haka tare da maida kallon shi akan TV."What!!!?."Daddy ya furta haka cikin mamaki."Haba Yaya Fauzan ' wallahi tana sonka sosai."Cewar Khairat."Ke ni abokin wasan kine ko? Sai na kakkaryaki awajen nan ' muddin kika sake sako bakin ki cikin maganar nan."Zumb'uro baki Khairat tayi ' taje kusa da Mummy ta zauna."Wane irin rashin hankali ne wannan? Yarinya tabaro gidansu duk saboda kai!, Sannan kayi wasa da feelings d'inta haka?."Nan Mr-fauzan ya d'an nutsu, Don ko kad'an bayason yaga ya b'atawa Daddy rai."To bari kaji in fad'a maka, Tunda har ka wulak'anta yarinyar nan haka! Na baka nan da 2weeks ka kawomin wacce zaka aura, Idan kuma ba haka ba! To kasa aranka tamkar Nafeesat taga gama matar kace."Nan hankalin Mr-fauzan ya tashi, Sunkuyar da kai kawai yayi ' sannan yace."Daddy ' karka biyema Mum mana, Kuma... "Bai k'arasa abunda yake shirin fad'a ba Daddy ya dakatar dashi ' ta hanyar yimasa tsawa."Fauzan!!, Zaka b'acemun da gani ko saina sab'a maka?."Mr-fauzan tashi yayi ya wuce d'akin shi sumumu tamkar wanda yai k'arya.Bayan wucewar Mr-fauzan ne Daddy yace."Kinji mun ja'iri? Please ki tabbatar kin kira mahaifiyar yarinyar nan.""Insha Allah."Daddy tashi yayi ya wuce part d'inshi, Mummy da Khairat kuma suka cigaba da kallo.B'angaren Mr-fauzan, Yana shiga d'akin shi ya zauna a kujerar sofa tare da jinginar da kanshi yana sauke ajiyar zuciya, Wayarshi ya d'auka datake gefensa ya kira number d'in Sir-Kamal.Sir-Kamal yana restaurant tare da Safna da k'annan ta, Yaga shigowar kiran Mr-fauzan ' d'agawa yayi cikin sauri."Hello Sir?.""Kamal! Ina fatan kayi abunda nasaka.""Eh nayi ' gamu nan ma tare dasu a restaurant, Yanzu zan maidasu Hospital d'in.""Ok ' ka tabbatar kayi abunda ya dace.""Ok Sir."Abunda Mr-fauzan ya furta haka ya kashe wayar shi,Nan Sir-Kamal dasu Safna suka fito daga restaurantd'in gami da rik'oma Umma nata abincin ' domin ta samu taci bayan ta dawo conscious.Bayan sun shiga cikin mota ne ' Sir-Kamal yace."Kinga wannan Restaurant d'in?."Safna ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan yace."To anan na sama miki aiki ' kuma anriga anyi settling komai, Sunci inhar kin shirya zaki iya zuwa Ranar monday!."Safna wani dad'i taji har cikin ranta, Batama son lokacin data bud'e motar ta fito ta tsaya tana kallon restaurant d'inba don kuwa babban restaurant ne.Safna saida ta kai 5minutes a tsaye a wajen ' tukunna ta koma cikin mota."Na gode!, Na gode sosai ' Insha bazan yi maka butulci ba, To amma ya maganar school d'in da kacezaka sani?.""Wannan duk ba matsala bace ' sunce zaki iya zuwa haka nan."Safna juyawa tayi ta kalli su Rumaisa ' da farinciki ya bayyana a fuskarsu, Tace."Rumaisa kuyi masa godiya."Rumaisa da Anisa godiya sukayi mashi tare da nunafarin cikin su a fili, Sannan Sir-Kamal ya tada motar shi yaja suka d'auki hanyar komawa Hospital.Bayan sun isa cikin hospital d'in ne ' yayi packing a gefe, Sannan yace ."Amm... Safna akwai maganar da nakeso muyi dake,Amma ba yanzu ba tukunna ' sai Umma ta sami lafiya .""To."Tace cikin nutsuwa, Sannan sukayi sallama ' ta fito daga motar, Suma su rumaisa suka fito.Sir-Kamal saida yaga shigewar su ciki tukunna yaja motarshi ya wuce.*_Fan's d'ina kuyi hak'uri
da wannan!, kuma kuyi hkr da rashin yin posting in time ' duk da dai dama banyimuku alk'awarin zaku ruk'a samu kullun ba kasancewar nima inada abunyi!!! And then Aisha Inaso ki gane cewa bazan mayar miki da martani ba har saikin je kin koyi yadda ake magana tukunna..._*_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_@Been in love ' is something special, Ever since I meet you Samra ' my heart keeps telling me that you are the right person to be with,You are my Sweetheart' my lollipopty. This page is yours kawai..._*_And for you my Besty(Jameesha), Am very sorry, you know I heart you, so inasonku both._*32-33*Bayan shigarsu Safna cikin hospital d'inne ' suka zarce ward d'in da Umma take, Suna shiga suka iskeUmma zaune ita da wata nurse ' tana mata settling drip.Safna dasu Rumaisa waje suka samu suka zauna, Sannan Safna tace."Umma ya jikin?.""Da sauki."Rumaisa da Anisa sannu sukabi Umma dashi, Bayan nurse d'in ta gama ne ta juyo ta fuskanci Safna gamida cewa."Yanzu ansa mata ruwa, Ki tabbatar taci abinci domin akwai wasu magungunan da zanzo inbata."To kawai Safna tace, Sannan Nurse d'in ta juya ta fita.Bayan fitar tane ' Safna ta bud'e ledar da suka shigo da ita, Ta d'aukowa Umma take away na abincin ta ' ta bata gamida cewa."Umma ga abinci ki ' tuwon shinkafa ne, Ki daure kici."Ansa Umma tayi ta aje agefenta ' tace."Safna ina aka sami kud'i haka?"Nan Safna ta bawa Umma labarin duk abinda ya faru ' da yadda sukayi da doctor.Umma ajiyar zuciya tayi ' tare da girgiza kai alaman damuwa."Yanzu a ina zamu sami wannan mak'udan kud'in?.""Umma karki damu, Abokin Oga na yace ' babu matsala inhar taje na tambayeshi zai bani."Safna ta fad'i haka cikin walwala, Umma kuwa ajiyarzuciya kawai tayi ' ta fara cin abincin ta.Haka rayuwa ta cigaba da juyi dasu Safna ' Hafiz abokin Mr-Fauzan shi ke zuwa yana maidasu gida, Ita kuma Umma nurses na kula da condition d'inta.*** *** *** *** *** *** *** ****Yau take Monday...*Da sassafe Safna ta tashi daga bacci, Ta had'a musu koko suka sha ' sannan suka yi wanka.Bayan sun gama shiri ne ' sukaji ana sallama."Wannan muryar Abokin Oga ne."Safna ta fad'i haka tare da sanya hijabinta ta fita domin dubawa.A tsaye ta ganshi, Nan taimashi sallama suka gaisa tukunna yace."Amm.. Kundai shirya ko?.""Eh mun shirya.""To ku fito inkaiku hospital d'in, Daga nan sai muje wajen Abokin nawa."Safna juyawa tayi ta koma ciki domin su fito ta kulle gidan, Cikin 'yan k'ank'anin lokaci suka fito gaba d'ayansu Rumaisa na rik'e da kwanon kokon Umma wanda zata karya dashi.Dukkansu mota suka shige ' shima Hafiz ya shiga yatada motar, Sannan yaja suka wuce.Bayan *2hours*, Suka isa hospital d'in, Bayan yayi packing ne yace."Safna, Kije kiyiwa Ummanki bayanin inda zakije ' kuma sannan kice inai mata sannu.""To."Abunda tace kenan ta bud'e k'ofar ta bar motar, Rumaisa da Anisa na biye da ita.Safna sai da tad'an jima, Sannan ta fito daga hospital d'in.Hafiz kuwa wak'a ya saka a motar ya k'ure sauti, Yana facing left side d'inshi.Haka Safna ta iso wajen motar ta dunga sallam ' amma sam baiji ba, Sai da ta bud'e motar ta shiga tarufo k'ofar da k'arfi tukunna ya juyo da sauri ya kalleta tare da rage volume d'in sautin, Sannan ya tada motar suka wuce.Hafiz gudu kawai yakeyi babu abinda ya dameshi, Cikin 'yan lokuta k'alilan suka isa company d'in.Hafiz packing yayi, Sannan suka fito suka shiga ciki, Safna kallon mutanen da ke ciki taitayi kasancewar kallon komai takeyi sabo, Domin ko kad'an bataga idon sani ba.Hafiz tafiya kawai yakeyi zuwa office d'in Mr-FauzanSafna na binshi abaya.Bayan sun kai bakin office d'inne Hafiz yace."Ki jira anan ' tukunna."Yana fad'in haka ya bud'e office d'in ya shige.Safna dai tsaye take tana ta baza ido tako ina, Don batasan abinda suke tattaunawa ba.Hafiz bai wani b'ata lokaci ba ya fito gami da cewa."Ki shiga kuyi magana, In kinfito ina mota."Kai ta d'aga mashi kawai ' zuciyar ta na bugawa, Don kuwa bazata mance wanene Mr-Fauzan ba.Bayan wucewar Hafiz ne Safna ta bud'e office d'in ahankali tamkar wacce tai k'arya.Sallam tayi sannan ta k'arasa ciki, Koda ta shiga ta iske shi a zaune amma ya juya bayan sa."Ki nemi wajen zama."Abunda taji yace kenan, Taje ta zauna tana kallon bayansa."Hafiz ya fad'amun cewa Mum d'inki bata da lafiya."Murmushi tayi tace."Eh ashema yayi maka bayani, Wallahi bata da lafiya' tun a gida ta fara rashin lafiyan to shine...."Bata k'arasa ba Mr-Fauzan ya dakatar da ita da cewa."Idan surutu zakimun ' tun wuri ki tashi ki fita."Ya fad'i haka tare da juyowa.Safna sunkuyar da kanta kawai tayi, Don kokad'an batason suna had'a ido."Amm... Dama taimako nazo nema wajenka, Sir please ka taimakamun da kud'in da zan bada aima Umma ta aiki, Likita yace idan ban nemo kud'in ba zata iya rasa ranta.""Are you afraid to loose her?."Safna saurin d'ago kai tayi ta kalleshi ' da hawaye cike da ido, Ita dama abun kuka baya mata wuya."Ita kad'ai ce ta ragemun sai kuma 'yan k'annai na, Kuma likita yace miliyan d'aya suke buk'ata, Sir don Allah ka taimaka mun."Safna ta fad'a haka tana share hawaye."Zan baki kud'in da sukafi haka muddin kika amince da abinda zan fad'a miki yanzu.""Sir, Indai akan infanshi ran Umma na ne ' to nai maka alk'awari zan amince da duk abinda kace."Safna sam ta manta tayin da Mr-Fauzan yayi mata.Mr-Fauzan murmushi yayi ' sannan yayi calming hands d'inshi yana kallon ta."Zan kaiki gidanmu In gabatar dake amatsayin wacce zan aura."Zaro ido Safna tayi tana mamakin abunda Mr-Fauzan ke fad'a."Yes! And after that zan aure ki! Ba don komai sai don banason Mummyna ta aura mun wata, If not ' kema kinsan babu abinda zanyi dake amatsayin mata."Sunkuyar da kai tayi ' idanunta cike da k'walla, A zuciyarta tace."Nasan dama saina fuskanci wulak'anci awajen mutumin nan, Amma babu komai...""Taimaka miki zanyi kawai ' amma ba don inasonki ba, Kuma cikin wannan satin nakeso ayi auren!, Za'a cigaba da kula da Ummanki a hospital har ranar aure kin cika alk'awarin da kika d'auka sannan zanbaki kud'in."Safna saurin kallon shi tayi tana girgiza kai."Sir, Kada kaimun haka don Allah ' likita yace zata iya rasa rayuwarta a kowane irin lokaci, Ka taimaka mun.""Ke zaki taimaka ma kanki ' kibi duk abinda nace, Muddin kika kwantar da hankalinki to babu abinda zai sami Ummanki."Dogon numfashi Safna taja ' sannan tayi shuru nad'an lokaci tace."Kana ganin baza'a sami matsala ba?.""Bana buk'atar tambayoyi daga gareki, And mind you ' koda na Aure ki kada kiyi kuskuren sakani aranki because zakisha wahala a banza."Safna kuwa k'asa kawai take kallo don kuwa hawayen ma sunk'afe, Zuciyarta a bushe take ' tsantsar tsanace ke d'awainiya da ita."Gobe, *Around 11:00am* zan turo P.A Kamal ya d'auko ki, And make sure kin fad'ama Ummanki."Safna harzata tashi da niyyar wucewa ' ya dakatar da ita."Ki sanarma Ummanki ' cewar mun dad'e tare so mun riga mun fahimci juna, If not zaki iya rasa ta inhar aka sami delay!!!."Safna kai kawai ta d'aga mashi, Sannan ta tashi ta fita cikin sanyin jiki.Tafiya kawai takeyi amma hankalinta baya jikin ta ' Safna condition d'in Umma kawai take tunawa.Inda Hafiz ya tsaya ta nufa ' tana isa ta bud'e motar ta shiga, Hafiz bacci ma ya fara

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login