Showing 27001 words to 30000 words out of 39355 words
zuciya ta ba."Safna girgiza kai tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa idanuwan tane suka cicciko da kwalla."Kamal, Ka cewa Ogan ka nagode ' kuma don Allah inaso ka cire zancen sona a ranka, Mu zama abokai."Safna na gama fad'in haka ta juya ta koma ciki, Sir-kamal right hand d'in shi ya dunk'ule zuciyar shi na mashi k'una.Sir-Kamal wajen motar ya nufa cikin hanzari ya tadamotar ya bar hospital d'in.Sir-Kamal gida ya wuce direct, Bayan yayi parking motar shi a compound ne ya fito ya shige cikin gida.Kasancewar bai sami kowa a parlor bane yasa shi shigewa bedroom d'in shi kai tsaye.Sir-Kamal kayan jikin shi ya cire ya ya shige bathroom, Koda ya shiga shower ya kunna ya tsaya tsakiya ruwa na ratsa jikin shi.Takaicin maganganun Safna kawai ke fad'o mashi a rai."Meyasa baza kice kina sona ba? Why? Didn't I deserve to be loved?."Abinda Sir-Kamal ya rik'a fad'a a cikin zuciyar shi kenan, Nan ya rufe shower d'in gami da d'aura towel a k'ugunshi tukunna ya fito.Sir-Kamal koda ya fito k'ana nan kaya ya ciro ya sanya sannan ya fito daga d'akin.Ta parlor ya biyo zai fita suka had'e da Ammi tana shigowa cikin parlon."Kamal?.""Na'am Ammi.""Ina zuwa kuma ' ka dawo ko hutawa baka yi ba?."Ammi ta fad'i haka tare da zaunawa saman kujera."So nake inje ziyarar wani friend d'ina.""Kamal dawo ka zauna na tambaye ka."Jin hakan yasa Sir-Kamal dawowa harabar parlor ya zauna a k'asan kujerar da Ammi ke zaune."Ammi gani.""Kamal, Kana cikin damuwa ko?."Cewar Ammi.Sir-Kamal 'yar dariyar k'arfin hali yayi yace."Ammi kenan, Ni banda wata damuwa please karki d'aga hankalin ki.""Ka tabbata?.""Eh Ammi."Sir-Kamal ya fad'i haka tare da duba wristwatch d'in hannun shi yace."Ammi, Bara inje."To Ammi tace sannan Sir-Kamal ya tashi ya fice.*** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 4:00PM*Mr-Fauzan ya tashi yayi daga baccin da yakeyi gamida sakin doguwar mik'a tare da yin salati.Mr-Fauzan d'aga kanshi yayi ya kalli a gogon d'akin,Yaga *4:00pm*."Oh God!."Ya furta, Sannan ya sauko daga saman gadon gami da cire wandon suit d'in da ke jikin shi ya dawo dagashi sai singlet.Mr-Fauzan d'aura towel yayi a jikin shi sannan ya shige bathroom don yin wanka.Bayan ya fito ne ya shirya cikin jeans and white shirt mai tambarin polo.Mr-Fauzan wristwatch ya d'auko ya sanya a right hand d'in shi mai k'irar gold sannan ya sanya sun glass.Mr-Fauzan takalmin sa ya sanya ' gami da d'aukan car key.Fitowa yayi daga d'akin shi ya shigo cikin parlor zai fita ya had'e da Khairat tana shigowa da alaman daga school ta dawo.Mr-Fauzan harya kama hanyar fita Khairat ta tsaida shi da cewa."Yaya Fauzan?."Nan Mr-Fauzan ya juyo ya kalle ta tare da cewa."Any problem?."Cikin shagwab'a Khairat tace."Bro, Kud'ina ne suka kusa k'arewa.""So?.""Yaya Fauzan, Kad'an bani one hundred thousand nad'an si..."Bata kaiga k'arasa maganar ba Mr-Fauzan ya tsaidaita da cewa."Naji, Basai kinmin dogon surutu ba ' kiyimin sending account number d'inki, I will send more than that."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya juya ya fice, Nan Khairat ta k'arasa d'akin ta cike da murna.Mr-Fauzan wajen motar shi yaje ya bud'e ya shiga ya zauna, Sauke ajiyar zuciya yayi yace."What am I going to do now? Nasan halin Mom, Ana iya samun matsala idan na kawo mata wannan yarinyar a yanayin da take."Mr-Fauzan jinginar da kanshi yayi a jikin seat d'in mota, A zuciyar shi yace."Or should I take her out for shopping? To idan tak'i yarda fa? Oh no!...."Mr-Fauzan d'an k'aramin tsuki yaja, Sannan ya tada motar shi tare da cewa."Dolenta ma ta yarda ' Whether she like it or not."Abinda ya fad'a cikin ranshi kenan, Gate man ya bud'e mashi gate ya fice.Mr-Fauzan GIRMI hospital ya nufa, Bayan ya isa cikin hospital d'inne yayi parking motar shi sannan ya fito.Mr-Fauzan ciki ya k'arasa, Nan yaga wata attender tana goge goge.Mr-Fauzan aika attender d'in yayi taje ta kira mashi Safna gami da fad'a mata ward d'in da suke.Ba'a wani wasting time ba attender d'in ta dawo wajen tare da Safna.Safna ganin shine yasa mode d'in ta ya cenja, K'arasawa wajen shi tayi ta tsaya tare da sunkuyar da kanta.Jin shurun yayi yawa ne yasa ta d'ago kai ta kalle shi taga wayar shi kawai yake dannawa."Kazo lafiya?."Cewar Safna.Mr-Fauzan maida kallon shi yayi akan ta yace."Lafiya.. Akwai maganar da nakeso muyi but bazan iya yinta anan ba."Safna kwalalo mashi Ido tayi tace."To sai a ina kenan?.""Ki biyoni cikin mota na."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya juya ya wuce wajen motar shi, Mr-Fauzan bud'e motar yayi ya shige Safna na tsaye tana kallon shi."In biyo ka cikin mota kuma?."Safna girgiza kai kawai tayi cike da takaice ta nufi wajen motar tashi.Safna tsaye tayi a wajen tana tunanin ta shiga ne ko karta shiga?.Tana cikin haka ne Mr-Fauzan ya danna mata hone, Hakan yasa ta razana tayi saurin bud'e motar ta shiga."Wace magana za muyi?, Don Allah kar kace ka cenja shawara ' Umma na tana buk'atar taimako."Cewar Safna.Mr-Fauzan tab'e pink lips d'in shi yayi gami da sakinshu'umin smiling."Inaso in kaiki wajen Mom d'ina ta ganki."Nan Safna ta zaro ido tare da rufe bakin ta cike da kunya, Hakan yasa Mr-Fauzan ya tsaya yana kallon ta nad'an lokaci tukunna yace."And I can't take you to her ' cikin k'azanta, The way you are now."Nan take Safna ta dubi jikin ta, Girgiza kai kawai tayicike da tausayawa kanta tace."To ko zaka bari naje gida na cenja kaya?.""No need of that, Zan siya miki kayan sawa ina kud'i kuma na tarasu I got a lot of money, Babu abinda zaimin wahalar samu a duniya."Safna, Jin abin ya fad'a yasa ta fahimci inda ya dosa."Ka barshi ba saika siyamun ba, Inada kayan sawa."Ta fad'a a tak'aice tare da calming hands d'in ta tanakallon waje.Mr-Fauzan juyowa yayi ranshi a b'ace ya kalle ta, Tare da cewa"Ke..? Harni zance zan siya miki abu kice bakyaso?.""Kayi hak'uri, Kamar yadda kake k'yamatar talaka haka nima nake k'yamatar duk wani abinda zai fito daga wajen ka, Taimakon da zakaiwa Umma na kad'ai ya isa."Safna ta fad'i haka ba tare da ta kalle shi ba.Mr-Fauzan cije pink lips d'inshi yayi ' yayiwa motar key, Da sauri Safna ta juyo ta kalle shi.Mr-Fauzan figar motar yayi a 360 suka bar cikin hospital d'in."Ina zaka kaini?."Ta fad'i haka idanun ta cike da k'walla.Mr-Fauzan shiru yayi ya kyaleta gudu kawai ya tafkawa."Meyasa ka kasance mugu a gareni?."Ta fad'i haka cikin shauk'i na kuka, Mr-Fauzan kuwako a jikin shi driving d'in shi kawai ya keyi."Na tsane ka Fauzan Na tsane ka! Ka maida ni inda ka d'auko ni."Mr-Fauzan dogon burki yaja ya tsaya.*_FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS_*
*42-43*Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalli Safna tare da cewa."Muje.""Ni babu inda zanje, Don Allah ka maida ni inda ka d'auko ni.""I don't want to argue with you Safna, Don't forget akwai yarjejeniya tsakanin mu, Kar kuma ki manta da Mahaifiyar ki dake hospital ba lafiya."Safna sunkuyar da kanta tayi tana nazari, Sannan Mr-Fauzan ya cigaba da cewa."Sabida haka ya zama dole kibi abinda nace, Because I can change my mind at any time.""Saboda kana azzalumi? Meyasa ku masu kud'i bakwayin abu tsakani da Allah?."Safna maganar cikin rawar murya."Daki aure ni Mahaifiyar ki ta warke, Da kik'i amincewa kuma ta mutu wane kika zab'a?."Mr-Fauzan ya fad'i haka ba tare da ya kalle ta ba."Wai kai wane irin azzalumi ne? Wane irin mugu ne kai? Meyasa bakwa taimako tsakani da Allah?.""Why? I thought ke kina da tarbiyyar da zaki iya sadaukawar Mahaifiyar ki farin cikin ki."Mr-Fauzan ya fad'i haka tare da jan tsuki, Sannan yak'ara da cewa."Let me just call the doctor ' na fad'a mashi cewa nina cire hannuna game da mahaifiyar ki."Ya fad'a tare da d'aga wayar shi zaiyi dialing numberd'in Doctor, Safna saurin dakatar dashi tayi da cewa."A'a Don Allah... Kar kayi haka...Kayi hak'uri naji na amince zanbi duk abinda tace."Ta fad'i haka hawaye na gangaro mata saman fuskar.Mr-Fauzan handkerchief ya mik'a ma Safna domin ta share hawayen dake fuskar ta, Haka ta karb'a ta share cike da takaici."Kuma as from today ' inaso ki adana hawayen ki, Because am not bullying you."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya bud'e mota ya fita.Safna itama budewa tayi ta fito, Wani babban shop suka shiga wanda ya k'unshi komai da komai.Bayan shigar sune Mr-Fauzan ya nufi b'angaren Abayas Safna na biye dashi a baya.Safna tsayawa tayi wajen wata Abaya mai kyau, Ganin haka yasa Mr-Fauzan tsayawa ya duba kud'inAbayan da Safna ke kallo."So cheap."Ya fad'a gami da kamo hannun ta yaja ta suka k'arasa ciki.Mr-Fauzan bai tsaya ko ina ba sai a wajen wasu Abayas masu kyau wanda daka gansu kaga kud'i.Safna k'ok'arin raba hannun ta take da nashi amma ta kasa.Mr-Fauzan kuwa Abayas kawai yake jida, Yana sakawa cikin basket.Suna cikin hakanne Suhailah ta shigo cikin shop d'in,Itama wajen Abayas d'in taje tana zab'ar wanda yai mata.Suhaila hango Mr-Fauzan tayi rik'e da hannun Safnayasa ta aje basket d'in nan wajen ta nufi inda yake.Mr-Fauzan kuwa tunda suka had'a ido da Suhailah yasa ke rik'e hannun Safna sosai."Fauzan?."Suhailah ta ambaci sunan shi cikin mamaki.Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalle ta, Safna kuwa k'ok'arin ta shine taga ta raba hannun ta da nashi."Who is she?."Tayi tambayar tana yi mashi nuni da Safna."She's my wife to be."Ya furta with proud.Suhailah zaro ido tayi gami da k'arewa Safna kallo, Ganin haka yasa Safna sunkuyar da kai.Nan Suhailah ta matsa kusa da Safna tare da fincikar hijab d'in gami da cewa."Wannan abun ce kakeso ka aura Fauzan? Dame ta fini?."Mr-Fauzan kab'ewa Suhailah hannu yayi tare da yi mata kasheda yace."Don't try something stupid here Suhailah, And i advise you to leave us alone...!!' kafin ki raina kanki awajen nan!.""Fauzan abinda zakace kenan? Ni kake fad'awa haka akan wannan k'azamar?."Suhailah ta fad'i haka cike da tsirawa Safna hannu.Mr-Fauzan tsuki yaja suka bar wajen."What! Ni Fauzan zaima haka? Ni zai yaudara? Ni zai ciwa fuska sabida wannan abin? Lallai zan nuna mishi kad'an daga cikin aikin Suhailah."Abinda Suhailah ta fad'a kenan tare da karkad'a kanta ta koma wajen inda take zab'an Abayas.A wajen mai karb'ar kud'i Mr-Fauzan ya tsaya, Ciro wallet d'in shi yayi ya zari ATM card d'in shi ya mika musu domin su cire kud'in su.Tunda suka tsaya wajen Safna ke kallon Mr-Fauzan jikin ta a sanyaye."Sona kake da gaske ko kuwa?."Ta fad'i haka cikin ranta.Tana cikin wannan tunanin ne taji ya jata sun nufi wajen k'ofar fita.Fita sukayi daga cikin shop d'in, Mr-Fauzan saida suka isa wajen mota tukunna ya sakar mata hannu.Key ya sanya ya bud'e motar, Sannan ya saka kayancikin bode ya koma cikin mota ya zauna, Tukunna itama ta bud'e front seat ta shiga ta zauna.Mr-Fauzan tada motar yayi suka nufi hospital dominmaida ta.Mr-Fauzan driving d'in shi kawai yakeyi Safna na satar kallon shi.Tabbas Mr-Fauzan kyakkyawa ne kuma ya cancanciduk wata mace ta kalle shi ta yaba.Cikin 'yan mintoci suka isa cikin hospital d'in, Bayan yayi parking ne ya danna wani waje cikin motar hakan yasa bode ya bud'e."Kije ki cire kayan ki."Ya fad'a cike da tak'ama ba tare da ya kalle ta ba."Na gode."Safna ta fad'a, Sannan ta bud'e motar ta fito.Safna wajen bode ta zagaya ta d'aga ' ta d'auki ledarkayan, Sannan ta rufe bode d'in.Nan Mr-Fauzan yaja motarshi ya wuce.Safna koda ta shiga cikin hospital d'in cikin ward ta wuce kai tsaye.'Yan uwan su Umma ta iske a ciki hakan yasa gabanta ya fad'i.Da sauri Safna ta k'arasa ciki, Ganin yadda su Rumaisa ke kuka ne yasa nan take k'afafun Safna suka fara rawa.Anisah ce ta taso ta rungume Safna cikin kuka tace."Aunty Safna, Likita yace wai Umma ta rasu..."Raras gaban Safna ya sake fad'uwa, Nan take idanuwanta suka ciko da hawaye.Safna maida kallon ta tayi ga mutanen da ke tsaye a wajen, Ganin yadda suke girgiza kai alaman tausayawa ne yasa Safna ta matsa wajen gadon Umma.Safna ganin an rufe Umma da farin k'yalle ne yasa tazubewa k'asa, Cikin kuka take cewa."Umma don Allah ki tashi...karki mana haka... Ummaki tashi don Allah."Safna ta k'arashe maganar cikin kuka.Rumaisa tasowa tayi tazo kusa da Safna ta tsaya gami da dafa kafad'an ta.Hakan yasa Safna d'ago kai ta kalle ta."Rumaisa meyafaru da Umma haka?.".Tayi maganar cikin disashewar murya.Rumaisa share hawayen da ke mata zarya tayi tace."Lokacin da kika fitane ciwon ta ya tashi harta kaiga yin kashin jini, Shine na fita na kira likita, Koda yazo ya duba ta sai kawai naga ya rufe mata fuska yace in kira 'yan uwanmu, Shine na d'auki kud'i naje na kira su Goggo mariya."Da sauri Safna ta rungume Rumaisa cikin matsanancin kuka.Goggo Mariya ce ta taso tazo inda Safna take."Kiyi hak'uri Safna ki kuma d'auki k'addara."Cewar Goggo Mariya.Goggo Mariya k'anwa ce ga Umma.Wani ne ya shigo ya cikin ward d'in tare a cewa."Ga motar cen an kawo."Abinda ya fad'a kenan ya shigo ciki tare da Nurses guda biyu suka d'auki gawar Umma suka d'aura ta atrolley chair, Suka nufi wajen mota da ita.Safna dasu Rumaisa kuka kawai sukeyi har suka shiga cikin mota, Aka sanya gawar Umma a baya.'Yan uwan Umma suma shiga suka yi cikin motar, Kasancewar boss ce motar shiyasa ta d'auke su gaba d'aya..*_@Dedicated to SEEMALUV NOVELS GROUP & B'OYAYYEN AL'AMARI FANS GROUP,,,,,,,,,Masoya na ina ganin sak'on nin ku ' Seemaluv really appreciate it._**44-45*Koda su Safna suka isa gida kafin kace kwabo gidanya cika da mutane, K'ofar gidan kuwa cike yake da maza.Bayan anyiwa gawar wanka ne, Safna tana ji tana gani aka d'auki gawar aka fita a ita domin yi mata sallah, Daga nan akaita masaukin ta.“Wayyo Allah na shiga uku... Ni yanzu yazan kasance da k'annai na?.”Safna dake zaune cikin hijab ta fad'i haka cikin matsanancin kuka.Goggo Mariya ce, Ta taso tazo inda Safna take tace.“Haba Safna meyasa bazakiyi tawakkali ba? Meyasa? Karfa ki manta duk mai rai mamaci ne, Kuma ai Allah yana tare daku.”Haka duk mutanen dake wajen suka dunga lallashin Safna.*** *** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 5:00PM*Bayan ankaita andawo ne, Mutane suka fara watsewa ya rage daga su Safna sai Goggo Mariya.“To Safna ki daiyi hak'uri kuma ki cigaba dayi mata addu'a kawai, Kuma kinga irin rayuwar da muke ciki ' yanzu tashi zakiyi da sana'a saboda ki samu ku kare mutuncin kanku.”Cewar Goggo Mariya.“Yanzu Goggo Mariya, Bazamu sami tallafi daga wajen ku ba kenan?.”Safna ta fad'i haka.Goggo Mariya ajiyar zuciya tayi tare da girgiza kai cike da nuna tausayawa tace.“Safna kenan! Yanzu wa kike ganin zai baku wani tallafi? Toh ni d'innan kinga nima ba wani hali gareniba ' sai mijina ya nemo ya kawo, Gani kuma da 'ya'ya ' kuma yanzu masu kud'in nan ba taimako sukeyi ba.”Safna wasu zafafan hawaye suke kwaranyo mata, Kallon Rumaisa tayi taga babu abinda takeyi sai kuka.Nan ta maida kallon ta kan Anisah ta ganta rakub'e jikin bango tayi shuru.“Bakomai Goggo Mariya, Nagode sosai da shawararki kuma insha Allah zan nemi aikin yi.”Nan Goggo Mariya ta tashi sukayi sallama sannan ta wuce.Bayan anya sallar isha'i ne, Safna da su Rumaisa suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shigo tare da yin sallama.Bayan an amsa masa ne yace.“Wai ance ana sallama da Safna.”“Kace gata nan zuwa.”Cewar Safna.Yaron juya wa yayi ya fita, Sannan Safna ta tashi ta fita domin duba wanda ke kiran ta.Safna koda ta fita Ganin Sir-Kamal tayi tsaye, Hakanyasa ta k'arasa inda yake jingine jikin motarshi.Bayan sun gaisa ne Sir-Kamal yace.“Safna naje hospital d'in akace min an sallame ku, To yaya jikin Mahaifiyar taki? Anyi mata aikin ne?.”Safna d'ago kai tayi ta kalli Sir-Kamal tare da cewa.“Umma Allah yai mata rasuwa d'azu.”“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...”Cewar Sir-Kamal.Shuru sukayi na d'an lokacin, Sannan Sir-Kamal ya lura da kukan da Safna keyi.“Kiyi hak'uri Safna, Allah ya gafarta mata Allah kumayasa hutun kenan.”“Amin na gode.”Ta fad'a da disash-shiyar murya.“To yanzu waye ke zaune daku?.”“Ba kowa.”“Toh... Insha Allah idan akayi sadakan uku, Zan dawo domin akwai maganar da nakeso muyi.”To Safna tace, Sannan Sir-Kamal ya bud'e mota ya ciro abincin da Mr-Fauzan ya umurce shi daya siya masu as usual.Sir-Kamal mik'awa Safna yayi ta amsa, Sannan yace.“Inji Mr-Fauzan, Oga na kenan ' yace inkawo muku wannan, Baima san da rasuwar ba shiyasa but zan fad'a mashi idan na koma.”Nan Safna ta mayar mashi ledar gami da cewa.“Ka mayar mashi da abincin shi, Domin bama buk'ata.”“Ha'a Safna meye dalilin yin hakan?.”“Kamal... Abubuwa da dama sun faru ba tare da saninka ba, Saboda haka kawai abarni inji da mutuwar rasuwar Umma na kad'ai ta ishe ni.”Ta fad'i haka gami da share hawayen ta.“Insha Allah Safna komai zaizo maki da sauk'i, Kuma as far as am alive ni zanyi maki komai, Yanzu kuna da abinda zaku ci ne?.”Kai Safna ta
girgiza mashi alaman a'a, Tukunna yace.“To, Kiyi hak'uri ki ansa wannan kuci, Saboda kada ku kwanta da yunwa.”“Kada ka damu Kamal, Zan nema mana abinda zamu ci don akwai sauran kud'i a waje na.”OK kawai Sir-Kamal yace sannan ya maida ledar takeaways d'in cikin mota.Sir-Kamal dawo wa yayi ya tsaya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya ciro 10k ya mik'awa Safna gami da cewa.“Kiyi amfani da wannan, Kafin na sake dawo wa.”Nan Safna ta fashe da kuka, Cike da cewa.“ hak'uri, Amma ni kunyar ansan kud'in ka nakeyi yanzu, Sabida na kasa karb'ar soyayyar ka.”Murmushin takaici Sir-Kamal yayi tare da cewa.“Karki damu Safna, A yau koda ace ban furta miki kalmar so ba ' to zan cigaba da kasancewa inuwa a gareki.”Safna d'ago kai tayi ta kalle shi cikin shauk'in kuka da sautin shagwab'a tace.“Da gaske kakeyi?.”“Uhm.. Da gaske nake mana! Idan har kika bani dama.”“Na gode.”Ta fad'a tare da sunkuyar da kanta, Nan sukayi sallama Sir-Kamal ya shige motar shi yaja ya wuce sannan Safna ta shige gida.Bayan shigar ta gida ne ta iske har Anisah tayi bacci.“A'a Rumaisa tada Anisah, Babu wanda zaiyi bacci baici abinci ba.”Safna ta fad'i haka gami da cire hijab d'in jikin ta.Bayan Rumaisa ta tada Anisah ne Safna tace.“Indomie zaki je ki siyo mana dafaffa wajen mai shayin cen.”To Rumaisa tace sannan Safna ta cire d'ari biyar ta mik'a mata tace.“Kice uku zai dafa maki.”Kai Rumaisa ta d'aga alaman to, Sannan ta sanya hijab d'inta ta fita.B'angaren Sir-Kamal, Bayan ya koma gida ne yayi shirin bacci ya kwanta ya d'auki wayar shi yayi dialing number d'in Mr-Fauzan.Ringing tai