Showing 15001 words to 18000 words out of 39355 words

Chapter 6 - BOYAYYEN ALAMARI Complete Hausa Novel

unknown   

14 Oct 2024

2591

yabi bayanta, Mr-Fauzan part d'inshi ya wuce ita kuma Khairat ta zauna nan a parlor domin su gaisa da Nafee.Bayan shigar Mr-Fauzan d'akin shine ya d'aga wayar shi ya kira Hafiz, Saida yayi mashi two missed calls tukunna ya d'auka."Hello dude! Ina ka shiga ne ina kiran wayarka naji shuru?.""Babban mutum! Bana kusa da wayar ne ai."Cewar Hafiz.""Ok! Akan maganar nan ne dai na kira ka.""Wace magana?.""Oh come on! Maganar yarinyar daka ce in nema mana!, Yanzu dai na yarda da shawarar ka Hafiz ' amma saidai tabar company d'ina yanzu haka.""Shit! What happen?.""Well. Ba wannan ya kamata ka tambayeni ba yanzu ' Inda zamu sameta ya dace ka tambaya!."Cewar Mr-Fauzan."Yeah!.""But wannan ma bazai bada wahala ba! Zan umurci P.A d'ina Kamal, Domin naga yafi kusanci da ita.""Amma Fauzan kana tunanin zata yarda dakai kuwa?."Mr-Fauzan hannun shi ya damtse tare da cijewa, Yace."Duk abunda na nema ' to saina same shi, Ballema irin wannan mutanen kud'i kad'ai ya isa nasayi soyayyarta duk da ba sonta nakeyi ba!!."Kalaman da Mr-Fauzan yayi ne yasa Hafiz sakin ajiyar zuciya, Yace."Alright then, Idan ansami address d'in nata sai ka sanar dani."Abunda Hafiz yace kenan ' Mr-Fauzan ya kashe wayar shi.Bayan Hafiz ya aje wayar ne ' Aleeza tazo ta zauna kusa dashi tare da cewa."Yaya Hafiz! Please aramun phone d'inka in kira wata friend d'ina.""Ke me naki phone d'in keyi?.""Well. Ina cikin wayane credit d'in suka k'are."Hafiz tsaki yaja ' sannan ya d'auki wayar ya mik'a mata, Tare da cewa."25 minutes na baki.""Ok."Abunda Aleeza ta fad'a kenan ta tashi ta wuce d'akinta, Nan ta duba number d'in Mr-Fauzan kasancewar tasan dashi suka gama waya, Aleeza saida ta tabbatar tayi copying number d'in to her phone sannan ta mayar wa Hafiz wayar shi gami da cewa."Thanks bro."Sannan ta koma part d'in hajiya.B'angaren Safna kuwa a zaune take a tsakar gida saman tabarma tana kuka, Umma tayi juyun duniyarnan ta fad'a mata abunda ke faruwa amma Safna tak'i, Saboda tsabar k'uncin dake zuciyarta ne ko abinci bata nema ba.Tana cikin wannan yanayin ne aka aiko yaro ' cikin gidan cewar ana sallama da Safna.Jin haka yasa Safna tashi tsaye ' ta janyo hijab d'intadake saman igiyar shanya ta sanya, Sannan ta fita.Safna koda ta fita Sir-Kamal ta iske jingine jikin motar shi yana shafa waya, Hakan yasa taimashi sallama ' Sir-Kamal ya d'ago kai ya kalleta tare da amsa sallamar.Bayan sun gaisa ne ' Yace."Safna nazo akan maganar da mukayi ne ' ina fatan babu matsala.""Eh babu matsala ' bari inshiga in fad'ama Umma zuwanka tukunna."Ok Sir-Kamal yace, Sannan Safna ta juya ta shige gida ' tana shiga ta cewa su Rumaisa su tashi su koma ciki ' bata wani b'ata lokaci ba ta fito gamida cewa."Ka shigo."Sir-Kamal bin bayanta yayi har suka isa cikin gidan, Nan Safna ta bashi kujera ya zauna ' tukunna Sir-Kamal ya gaishe da Umma.Bayan sun gaisa ne ' Sir-Kamal ya sanar ma Umma duk abinda ke faruwa da Safna, Da duk irin k'alubalen data samu a rayuwa.Umma ajiyar zuciya tayi ' ta maida kallon ta kan Safna."Amma Safna shine kika kasa fad'amun?."Nan idanun Umma suka ciko da k'walla ' ganin haka yasa Sir-Kamal cewa."Ayi hak'uri Umma, Ai Insha Allah komai yazo k'arshe, Domin kuwa iznin ki nazo nema don insamama Safna aiki ' aikin da babu mai takura mata."Ajiyar zuciya Umma tayi ' ta maida hawayenta dake shirin zubowa, Tace."Yaro, Ni babu abinda zance maka sai godiya! Kumana amince kuma na yarje maka ' inhar kanada halin yin hakan to kayi.""Alhamdulillah!Na gode da naji haka."Nan Sir-Kamal ya cire kud'i daga aljihun shi 'yan d'ari biyar rabin bandir ya aje a saman tabarman da Umma ke zaune."Umma ga wannan! Kud'anyi amfani dashi nad'an wani lokaci."Godiya Umma taimashi, Sannan ya fita Safna ta bishi a baya.Bayan fitarsu ne ' sukayi sallama, Sir-Kamal ya shige motar shi ' tukunna Safna ta shige gida._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv*....*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_Seemaluv is back again!!!..._**26-27*Bayan komawar Sir-Kamal gida ne yaga shigowar kiran Mr-Fauzan, Cikin sauri yayi receiving."Hello Sir!.""Kamal, Inason ka turomin da address d'in wannan yarinyar."Mr-Fauzan ya fad'a a tak'aice."Wace Yarinya kenan?.""Ha'a karka cemun baka gane abunda nake magana ba! That k'azama wacce tabar company na.""Oh! Safna?.""Whatever her name is! Nidai ka turomun address d'in gidan right away.""OK."Abunda Sir-Kamal yace kenan, Mr-Fauzan ya kashe wayar.Sir-Kamal, Mamaki ne yacika shi ' ganin yadda Mr-Fauzan ke neman address d'in gidan su Safna."Ha'a to meyafaru haka? Me kuma ya k'ara had'ata dashi?."Sir-Kamal bai wani b'ata lokaci ba, Yayima Mr-Fauzan sending address d'in gidan ' sannan ya fice zuwa masallaci, Kasancewar lokacin sallar magrib yayi.*AROUND 8...PM*Bayan Mr-Fauzan ya dawo daga mosque ne ' ya sami waje ya zauna a parlor ya fara duba wayar shi 'ya ga text d'in Sir-Kamal, Hakan yasa shi dubawa ' ganin abunda ya buk'atane yasa shi dialing number d'in Hafiz, Ringing d'aya zuwa biyu ya d'aga."Babban mutum, Ya akayi ne?."Cewar Hafiz."Lafiya k'alau, Nasami address d'in gidan su fa... Soboda haka Hafiz ' kai zakaje ka fara yi mata magana.""Oh come on! Kai d'in fa? Tare ya dace muje ai.""Hafiz, kaje kawai! Please inda hali ma ni kawai akawomin ita gidana as my wife ' ba tareda nayi wasting time d'ina ba."Cewar Mr-Fauzan."Ha'a haba Aboki? Wace irin magana ce haka?.""To shikenan, Yanzu dai ka fara zuwa tukunna ' and you know what?."Sai ka fad'a."Cewar Hafiz."We have to meet ' kafin kaje wajen ta, Zan baka kud'inda zakayi spending mata ' because kasan irin su saida haka.""Alright, Shikenan ' Gobe Around *12:00pm* zanzo inansa sai inwuce gidan nasu.""To shikenan."Sallama sukayi ' sannan Mr-Fauzan ya kashe wayar shi, Ya Cigaba da kallo.Mr-Fauzan na cikin kallo ne ' Daddy ya dawo daga wajen aiki d'auke da sallama ya shigo cikin parlor, Mr-Fauzan amsa sallamar yayi gamida yi mashi sannu da dawowa.Bayan Daddy ya wuce ne ' Mr-Fauzan yace."I don't think ' Daddy yasan abunda Mummy ke shirin yi."A zuciyar shi ya furta hakan.Tashi yayi ' ya koma d'akin shi ya zauna a kujerar sofa tare da janyo laptop d'inshi zai hau aiki.Mr-Fauzan yana cikin hakan yaji wayarshi ta fara k'ara alaman kira, D'auka yayi ya duba ' ganin Number ce yasa shi tab'e baki gami da cewa."What a trashy!"Ya fad'a gami da maida kallon shi zuwa kan laptop ba tare da yayi receiving call d'in ba.B'angaren Aleeza kuwa zaune take a d'akinta rik'e dawayarta a hannu tana kiran number d'in Mr-Fauzan, amma baya d'agawa."Meyasa bazakayi picking ba? Please pick up my call Fauzan..."Abunda Aleeza taita nanatawa kenan a zuciyar ta, Gami da sake dialing number d'in ' ganin baiyi receiving bane yasa tayin wurgi da wayan saman gado cikin zafin rai.Aleeza kwalla ne suka ciko Idonta ' tayi saurin mayarda hawayen."Wallahi inason shi..."Abunda ta furta kenan, ta bud'e wadrope ta ciro nightgown ta sanya ' sannan ta haye gado taja blanket.*** *** *** *** *** *** *** ****Washe gari...*Da assussuba Safna ta tashi ' ta tada su Rumaisa daUmma, Sukayi Sallah ' sannan Umma ta koma bacci kasancewar ta tashi da zazzab'i.Safna Umarni ta bawa Rumaisa dataje ta fara wankewanke, Ita kuma sai tayi shara daga nan ta d'aura ruwan zafi a murhu domin dama koko.Misalin k'arfe *6:00am*, Su Safna suka kammala aikin gidan ' Safna d'aki ta nufa ta tada Anisa daga bacci."Jeki wajen Rumaisa ta zuba maki koko kisha, Ki kuma wanke baki tukunna."To kawai Anisa tace ' ta wuce, Sannan Safna ta fara yiwa Umma magana cikin siga ta tausayawa."Umma?."Umma d'an motsawa tayi tare da sakin ajiyar zuciya."Umma, Ki tashi kisha koko ' daga nan sai inje chemist in anso maki magani."Umma tashi zaune tayi ' tana shivering, Safna ta fita cikin hanzari ta d'iboma Umma kokon a cup ta kawo mata."Gashi Umma! Ki daure ki shanye ' kinga ko suga bansa ba, Ni bari inje chemist d'in insiyo maka magani.""Toh."Abunda Umma ta iya furtawa kenan ' Safna ta d'aukihijabin ta ta sanya ta bar d'akin, Harta kama hanyar fita sai kuma ta dawo."Rumaisa! Ku tashi ku koma d'aki wajen Umma, Donbatajin dad'i."Rumaisa da Anisa, Tashi sukayi suka koma d'aki wajen Umma ' Sannan Safna ta fice.Kai tsaye Safna ta nufi chemist aka harhad'o mata magun guna kala kala sannan ta juyo ta kama hanyar dawowa gida.Cikin sauri take tafiya ' daka ganta kasan a uzurce take.Bayan ta dawo gida ne ' ta kaima Umma magun gunan had'e da ruwa tasha.Haka Umma ta ansa tasha maganin ' tukunna ta koma ta kwanta, Safna dasu Rumaisa sannu kawai suke mata tana ansawa agajiye.Safna kwantawa tayi k'asa saman tabarma ' tare da cewa."Rumaisa bari ind'an runtsa, Nad'an lokaci."To kawai Rumaisa tace, Sannan Safna ta fara bccinta cikin kwanciyar hankali.*AROUND 11:30AM*Hafiz yazo gidansu Mr-Fauzan tare dayin packing motar shi a packing space, Sannan ya ciro waya yayidialing number d'inshi.Mr-Fauzan na zaune a garden d'inshi yaga shigowarkiran Hafiz cikin wayar shi, Nan yayi receiving
call gamida karawa a kunne."Ya! Kaifa gani na k'araso cikin gidanku yanzu.""OK, just give me 5minutes ' gani nan fitowa."Mr-Fauzan cikin gida ya shiga ' direct ya wuce d'akinshi ya bud'e side drower ya d'auko bandir d'in y'an dubu sababbi fil, Ya fito wajen dashi a hannu.Bayan ya isa wajen Hafiz ne suka gaisa ' tukunna ya mik'a mashi kud'in tare da cewa."Behave well!.""OK."Abunda Hafiz yace kenan, Ya shige motar shi yaja ' ya wuce, Sannan Mr-Fauzan ya juya ya koma gida.Koda ya shiga gida kai tsaye ya wuce part d'insu Mummy, Bayan sun gaisa ne Mummy tace."Son? Kunfara magana da Nafee kuwa?.""Oh Mummy come on! Nifa bazan auri wannan ' mara tarbiyar ba."Cewar Mr-Fauzan.Mummy zaro ido tayi cike da mamaki and at the same time tare da nuna b'acin ranta."What!!! Son? Yarinyar k'awar tawa ce mara tarbiyya?."Mr-Fauzan sunkuyar dakai yayi ' gami da nuna ko a jikinsa."OK! Lallai zan sanar ma Daddynku bari ya tashi bacci, Tunda ni bakajin magana ta yanzu."Mr-Fauzan tashi yayi yawuce ' Mummy ta bishi da kallo, Kai tsaye ya nufi kitchen ya bud'e fridge ya d'auki yoghurt domin kuwa yunwa yakeji ' kasancewar baiyi breakfast ba.Mr-Fauzan harya d'auko ya juyo zai bari kitchen d'in suka had'e da Nafee itama zata shigo kitchen d'in.Wata fitinanniyar rigar bacci ne a jikinta ' wacce takeiyakarta gwiwa gata armless, Mr-Fauzan tunda ya kalleta sau d'aya ya d'auke kanshi daga kallonta zai wuce ' ta tsaida da cewa."Good morning ' Sweetheart.""Morning."Ya fad'a yana tafiya bata tare daya juyo ya kalleta.Ganin haka yasa Nafee yin smiling gamida girgiza ' tace."Zakazo hannu."Abunda tace kenan ' ta k'arasa cikin kitchen d'in itama ta d'auki yoghurt ta nufi bedroom d'in Mr-Fauzan dashi.Nafee shiga tayi ba tare da tayi knocking ko sallama ba, A zaune ta iske Mr-Fauzan rik'e da yoghurt hannu d'ayan hannun kuma yana danna laptop dashi.Mr-Fauzan tsayawa yayi yana kallon ta ' daga bisanikuma ya kauda kanshi, Tare da cewa."Get out of my room! Now."Ya fad'a a uzulce."Why?."Tayi tambayar tana k'arasowa tsakiyar d'akin.Ganin haka yasa Mr-fauzan mik'ewa tsaye cikin b'acin rai."Don't you dare come near me!.""Meyasa bazaka bi umurnin Mummy ba? Meye aibuna?."Mr-fauzan ganin zata b'ata mashi lokaci ne yasa shi fizgota suka nufi bakin k'ofar."Get out! And be out of my life forever."Yana gama fad'in haka ya bud'e kofar ya tunkud'a ta waje, Sannan ya rufe k'ofar shi ya koma ya zauna.Nafee juyawa tayi ta koma d'aki tana dannan hannun ta inda ya rik'eta, Ba k'aramin zafi wajen ke mata ba."Dole sai na gasa wajen."Abunda nafi tace kenan ' ta tashi ta cire rigar baccin jikin ta ta d'aura towel, Sannan ta shige bathroom._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad *....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**28-29*B'angaren Safna kuwa ' baccinta kawai takesha, Rumaisa da Anisa suna cikin yima Umma tausane sukaji ana sallama ' hakan yasa suka amsa.Rumaisa ce ta tashi tare da sanya hijabin ta ' ta fita.Hafiz ne tsaye a k'ofar gidan, Yayi calming hands d'in shi."Ina wuni."Hafiz jin maganar yayi kamar daga sama kasancewar baiga zuwan ta ba, Hafiz kallon Rumaisa yayi cike da tausayawa yace."Y'an mata ya kike? Ya mama?.""Lafiya lau.""Nan ne gidan su Safna ko?."Yayi tambayar yana kallon cikin idon Rumaisa."Eh nan ne! Yaya tace ma, Bari in kirata."Rumaisa juyawa tayi ta shige ciki ' Hafiz ya girgiza kai alaman tausayawa.Bayan Rumaisa ta shige gida ne ' ta fad'a cikin d'aki jikinta na rawa."Yaya Safna! Ki tashi wani mutum yazo wajen ki ' mai mota."Safna cikin magagin bacci ta tsinci maganar, Hakan yasa tayi firgigit ta farka cike da mik'a."Wai meye? Waye shi?."Cewar Safna."Wallahi wanine dai ' kuma ba wanda yazo jiya bane."Rumaisa ta fad'i haka with full of excitement.Safna mik'ewa tayi ta fito tsakar gida ' ta wanke fuskarta, Tukunna ta dawo d'aki ta sanya hijabi ta fita domin duba wanda ke kiranta.Safna koda ta fita a tsaye ta iske Hafiz jingine jikin bangon gidansu ' yana kallon mutanen da ke wucewa, Hakan yasa tayi mashi sallama ' shima ya amsa tare da juyowa ya fuskance ta.Bayan sun gaisa ne ' Hafiz yace."Nasan dai baki sanni ba ko?."Ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan Hafiz ya cigaba da cewa."Sunana Hafiz Khalif, In short dai ni Abokin Mr-fauzan ne wanda kika tab'ayin aiki a k'ark'ashin Company d'insa."Sunkuyar da kai tayi ' domin sam batason ta tuna darayuwar da tayi awajen."Safna! Maganan da nakeso muyi dake ' inason ki natsu kuma ki fahimceni.""Insha Allah."Ta fad'a a natse."Abokina ne ' yace inzo wajenki domin neman wata alfarma.""Alfarma?.""K'warai kuwa!."Ajiyar zuciya tayi ' sannan tace."Wace irin Alfarma?.""Good! Alfarma ce ta yagani yana so kuma yana so ku daidai ' domin ayi maganar aure."Safna still tayi a wajen ta tana kallon shi ' domin kuwa makamanciyar wannan ranar take jira."Ko kad'an banga laifin ka ba, Domin kuwa kai abokinsa ne ' kuma shi yasan cewa bazan saurare shiba shiyasa ya turo ka kai."Dogon numfashi Hafiz yaja ' yace."Ki kasance mai yafiya Safna... Kasancewar bazai iya had'a ido dake bane yasa shi ya turo ni.""Mutumin da baisan darajar mutane ba? Mutumin dayake kyamatan talaka?."Cewar Safna."Kiyi hakuri ki amince masa Safna, Kuma ki gwada ki gani..."Tunda kafin ya k'arasa rufe baki, Tace."Bazan tab'a iya saka sonshi a zuciyata ba, Balle harna auresa ' domin kuwa tsanarsa ce cike a cikin raina.""Is OK! Na fahimce ki."Ya fad'a tare da saka hannun shi cikin aljihu, Ya ciro bandir d'in kud'in da Mr-Fauzan ya bashi ' ya mik'a mashi tare da cewa."Ga wannan, Ko zaki sai wani abun."Safna kud'in ta kalla ta had'iye miyau don kuwa sunacikin buk'atar su, Lokaci d'aya kuma ta kauda kanta tare da cewa."Ka barshi na gode.""A'a ki karb'a ni da zuciya d'aya na baki."Safna k'in ansa tayi ' shi kuwa ya nace, Suna cikin haka ne Rumaisa ta fito a guje tana haki ' cikin tashin hankali Safna ta rik'ota."Ke lafiya?."Cikin rawar baki Rumaisa tace."Yaya Safna, Umma ne ke aman jini.""Innalillahi!."Hafiz ya fad'i haka, Ganin yadda Safna ta shige gida a rud'e ne yasa shi bin bayanta.D'aki Safna ta fad'a cikin rawar jiki taga Umma rigingine a k'asa tana aman jini, Hafiz d'akin ya shiga shima."Subhanallah this is a critical condition."Safna kuwa hawaye kawai ke zuba daga idonta ' Rumaisa da Anisa ma kuka kawai sukeyi."We have to rush to the hospital, Safna ku kamata asata a mota ' akaita hospital.""To."Ta fad'a, Sannan ita da Rumaisa suka d'aga suka fito waje Hafiz ya bud'e mata motar suka saka ta a back seat."Rumaisa keda Anisa ku tsaya gida ' kafin indawo."Safna ta fad'i haka tana share hawayen fuskarta."Haba, Ya zakice su tsaya gida su kad'ai? Su shiga mu tafi kawai.Cewar Hafiz.Haka kuwa akayi ' Rumaisa ita da Anisa suka zauna a back seat kusa da Umma, Sannan Safna ta shiga front ta zauna.Hafiz zama yayi cikin motar ' yayi saurin tadawa suka tafi, Kai tsaye ya wuce dasu wani babban private hospital ' yayi packing motar shi a ciki tukunna ya bud'e suka fito.Safna ce ta bud'e inda Rumaisa ke ciki suka fito da Umma tukunna Hafiz yayi musu jagora zuwa cikin hospital d'in.Bayan shigar sune ' Nurses suka zo cikin hanzari suka anshi Umma daga hannun su Safna."Please kuyi admitting d'inta kuma kuyi duk abinda ya dace, Kafin inga Doctor d'in."Hafiz ya fad'i haka yana k'ok'arin ciro waya daga aljihun shi, Safna ta tsaida shi tayi da cewa."Bawan Allah na gode da k'ok'ari."Ta fad'a cikin rawar murya ' idanu ciccike da hawaye."Karki damu babu komai, Yanzu dai kije ki sami wajeki zauna ' kafin inga doctor d'in."Safna hannun Anisa ta kama Rumaisa na biye da ita suka sami waje suka zauna a wajen.Hafiz kuwa dialing number d'in Mr-Fauzan yayi ' ringing biyu tayi yayi receiving."Hello! Aboki?."Cewar Hafiz."Na'am Hafiz how far? Ya ake ciki?.""Aiba k'aramar matsala aka samu ba ' in fact madai bata amince da maganar ka ba, And you know what?.""Kai nake saurare ai.""Muna hospital yanzu ' Mum d'inta is in critical condition, Yakamata inbaka Safna kuyi magana.""No! No need of that."Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin gadara."Wai meyasa kake haka ne?.""Hm Hafiz raini ne bana so!!! You know me very well,Kunyi magana da Doctor d'inne?."Mr-Fauzan yayi tambayar."A'a, akwai patients d'inda yake dubawa ne, Idan ya gama zamu sameshi.""OK then, Duk yadda kukayi dashi ' you let me know.""OK."Abunda Hafiz yace kenan ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Cikin sa'a saiga doctor d'in ya fito daga wani Ward.Nan ya tsaya suka gaisa da Hafiz ' tukunna Safna ta taso tazo inda doctor d'in ke tsaye, Nan ta fara mashi bayanin condition d'in Umma.Doctor juyawa yayi ' ya nufi ward d'inda aka kwantarda Umma, Hafiz dasu Safna suna biye dashi a baya.Bayan ya shiga ne ya fara yima Umma y'an dube dube ajikin ta, Sannan yace."Za'a dib'i jinin ta yanzu, Akwai blood test da za'ayi mata da Scanning kafin a tantance abunda ke damun ta."To kawai Hafiz yace ' sannan Doctor d'in ya fita, Hafiz ya sami waje ya zauna kasancewar ba k'aramar gajiya yayi ba.Safna kuwa idon ta na kan Umma wacce take unconscious ' batama san inda take ba, Bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye suna sauko mata."Yaya Safna, Ki daina kuka ' ai Umma zata warke ko?."Cewar Anisa.Safna jin abunda Anisa ta fad'ane yasa tayi saurin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login