Showing 30001 words to 33000 words out of 39355 words
tayi bai d'aga ba har sai da Sir-Kamal yayi four missed calls sannan Mr-Fauzan yayi receiving call d'in.“Good evening Sir.”“Evening, Any problem?.”“Well, Yes Sir, Mahaifiyar Safna ce Allah yayi mata rasuwa d'azu.”Mr-Fauzan a kwance yake amma jin haka yasa shi yin saurin tashi zaune.“What!! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Why didn't you tell me earlier??.. Meyasa sai yanzu kake fad'amin?.”“Am sorry Sir, Nima bansani ba sai da naje kai musuabinda zasuci ne ake fad'amun an sallame su shine nabi ta gidan nasu.”“Ya salaam!...”Mr-Fauzan ya furta tare da dafe goshin shi.Mr-Fauzan ending call d'in yayi ya jefar da phone d'in saman gado, Ya fito yana kwala wa Mummy kira.“Mom! Dad!.”Mummy da Daddy kwance suke suna bacci, Jin yadda kiran yayi yawa ne yasa Mummy tayi firgigit ta farka.Parlor ta sauko cikin sauri tana cewa.“Son what's wrong? Meyafaru?.”Mr-Fauzan dafe kanshi yayi, Gami da cewa.“Mom, Yanzu ake fad'amin Mahaifiyar Safna ta rasu.”“Wacece Safna?.”“Ita ce wacce zan kawo miki ita gobe, Surukan ki Mom.”Mummy rufe baki tayi tare da girgiza kai alaman tausayawa.“Ya salaam!... Allah ya jik'anta.”Amin Mr-Fauzan yace gamida dafa saman kujera.“Shit!!.”Ya furta tare da bugun kujerar.“Calm down Son, Yanzu kaje ka kwanta gobe sai ayi mata ta'aziyya.”“I can't sleep at this time Mom... I can't, I know that Safna will never forgive me...”Mummy tsayawa tayi tana kallon shi cikin mamaki.“Meyasa? Me kai mata?.”Mr-Fauzan shuru yayi na d'an lokaci Sannan Mummy tace.“Kaje dai ka kwanta, Saboda abinda safiya batayi badare bazai yi shiba.”Mr-Fauzan juyawa yayi ya wuce part d'in shi, Mummy girgiza kai kawai tayi itama ta koma b'angaren su ta kwanta.Mr-Fauzan koda ya kwanta, D'aga kanshi yayi ya duba clock yaga *10:00pm*.“Huh! Lemme call Hafiz.”Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan, Yayi dialing number en Hafiz.B'angaren Hafiz kuwa kwance yake a d'akin shi ya kwanta harya fara bacci wayar shi ta fara ringing.Jikin shi a mace ya tashi gami da d'aukar wayar ya duba yaga Mr-Fauzan me ke kiran shi.“At this time!!??.”Ya fad'i haka tare da picking call d'in.“Babban Mutum! Ya akayi ne?.”Cewar Hafiz.“Hafiz, Ba lafia ba fa!.”“What is the problem?.”“Wallahi Hafiz an yanka ta tashi.”Hafiz wata doguwar hamma ya saki gami da cewa.“What does that means?.”“Please idan ma zaka aje bacci agefe ka aje, Mahaifiyar Safna ce ta rasu yau.”Jin hakan yasa Hafiz ya saki salati, Sannan Mr-Fauzan yace.“Hafiz I don't think zan iya bacci seriously, Yarinyar nan tana iya cewa bazata yarda na aure ta ba ' nasan ta taurin kaine da ita, And she can even blameme for her mother's death!.”“Ai kaga abinda nake guje maka, Shiyasa tuntuni nakeso abi komai a hankali.”“Oh come on! Yanzu meye nayi wanda ba daidai ba a ciki? Kawai son nake na taimaka mata na aure ta that is it.”Mr-Fauzan ya fad'i haka a gadarance.“You fall for her didn't you?.”Hafiz yayi tambayar cike da zolaya.“Haba dai!...”“Oh har yanzu bazaka bada kaiba ko? Aboki kabi a hankali fa.”“Yanzu dai what's the solution?.”Cewar Mr-Fauzan.“Kawai ka bari sai gobe, We will find a way out.”OK Mr-Fauzan yace sannan suka yi sallama ya kashe wayar shi, Ya kwanta.Mr-Fauzan koda ya kwanta tunani iri iri kawai suke zuwa mashi a rai har bacci yayi awon gaba dashi.*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.44*46-47*Washe gari misalin k'arfe *7:00am* Mr-Fauzan ya tashi, Bathroom ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala sannan yayi sallah.Mr-Fauzan shiryawa yayi kamar yadda ya saba cikin suit sky blue colour, Komai nashi matching color ne.Mr-Fauzan perfume ya fesa Sannan ya fito zuwa parlor, Ko da ya isa parlor iskewa yayi har house girl ta gama shirya breakfast su Mummy sun zauna suna karyawa.Mr-Fauzan k'arasawa wajen dinning table d'in yayi ' yayi joining d'insu ya zauna.Mr-Fauzan Daddy da Mummy ya gaisar sannan Khairat da ke gefe tace."Yaya Good morning.""Ehem, Morning Khairat.Cewar Mr-Fauzan.Mr-Fauzan tsiyaya tea yayi cikin cup at fara sha."Fauzan, Yau da safe Hajia ke fad'amin cewar Safna tayi rashin mahaifiyar ta, Allah ubangiji ya gafar ta mata."Mr-Fauzan cikin nutsuwa ya aje cup d'in hannun sa tare da cewa."Amin Dad.""Idan ka tashi zuwa wajen ta'aziyyar, Zaka tafi da Khairat ' ita ce zata wakilce mu nida Alhaji."Mummy ta fad'i haka."OK, Aima yanzu zan tafi ' because inaso in lek'a office yau."Abinda Mr-Fauzan yace kenan ya cigaba da sipping tea d'in shi.*Some minutes later...*Bayan sun gama breakfast ne Daddy ya tashi ya wuce wajen aiki, Mr-Fauzan shima mik'ewa yayi gami da gyara necktie d'in shi yace."Ki same ni cikin motor."Ya fad'awa Khairat haka, Jin haka yasa Khairat ta ajiye cup d'in tea d'inta ta wuce d'akin ta cikin hanzari.Gele ta yafa a k'irjin ta ' ta d'auki side back d'in ta ta fito, Khairat parlor ta dawo ta sallami Mummy tukunna ta fita.Koda ta fito cikin motor ta sami Mr-Fauzan zaune, Hakan yasa ta bud'e front seat ta shiga ta zauna tareda cewa."Yaya, Na shirya."Nan take Mr-Fauzan yayi dialing number d'in Hafiz.Ringing d'aya tayi Hafiz yayi receiving."Babban Mutum!."Cewar Hafiz."Hafiz, Am on my way coming to your house now ' kashirya tare zamu je ta'aziyyar.""Shit!... OK to sai ka iso."Nan Mr-Fauzan yayi ending call d'in ya tada motor suka nufi gidan su Hafiz.B'angaren Hafiz, Bayan ya gama waya day Mr-Fauzan ne ya tashi ya fad'a bathroom yayi wanka, Sannan ya shirya cikin milk d'in yadi mai tsada.Hafiz shiryawa yayi tsaf ' ya fito parlor yayi breakfasta tsaitsaye, Hajia na lura da hakan.Hafiz harya kama hanyar fita ne Hajia ta dakatar dashi da cewa."Hafiz lafiya kuwa? Ina zuwa haka?."Hafiz juyowa yayi ya fuskanci Hajia tare da cewa."Akwai inda zamuje ne nida Fauzan, Banaso yazo ban gama shiryawa bane."Aleeza dake gefen Hajia a zauna gaban ta ya fad'i dasauri ta juyo ta kalli Hafiz."Oh shine yasa kake ta abu baga baga kamar zaka tashi sama?."Hafiz juyawa yayi ya fice cikin walwala tare da cewa."Eh mana."Aleeza tashi tayi zata wuce kitchen Hajia ta tsai da ita da cewa."Ina kuma zakije Auta?.""Hajia, Kitchen zanje zan yiwa mai aiki magana ne."To kawai Hajia tace, Sannan Aleeza ta wuce kitchen, Iske 'yar aiki tayi tana goge goge."Yawwa, Don Allah inason kimin wani abu ne."Cewar Aleeza."To.""Kije harabar garage ki tsaya, Akwai wani abokin yaya Hafiz da zaizo ' da zarar yazo please kizo ki fad'amin."To kawai 'yar aikin tace ta cigaba da gogen ta, Hakan yasa Aleeza tayi saurin ansar tsumman tare da cewa."No! Kije kawai, Bara na cigaba kafin ki dawo."Haka 'yar aikin ta wuce harabar garage ta tsaya wajen flowers, Shi kuwa Hafiz na zaune k'ark'ashin rumfa rik'e da wayar shi yana jiran zuwa Mr-Fauzan.Aleeza jefar da tsumman tayi nan wajen ta dawo parlor ta fara safa da marwa.Hajia na zaune gefe tana kallon ta, Aleeza tana cikin haka wayar ta dake saman three seater ta fara ringing ' hakan yasa tayi sauri ta je ta d'auka.Ganin Dr Khalil ne yasa tayi receiving cikin fara'a, Bayan sun gaisa ne kamar kullun ' Dr Khalil yace."I hope kin shirya ma zuwa ko?.""Insha Allah."Nan suka cigaba da hirar su, Hafiz na zaune yaji hone hakan yasa shi yin saurin mik'ewa tsaye tare da cewa."Yawwa, Bud'e gate d'in da sauri."Hafiz ya fad'awa gate man haka.Bayan gate man ya bud'e gate ne kamar yadda aka umurce shi, Mr-Fauzan ya shigo da motar shi ciki.Bayan yayi parking motar shine ya fito, Cikin fara'a Mr-Fauzan da Hafiz sukai hands shake.Ganin haka yasa 'yar aikin ta juya ta koma da sauri.Aleeza na cikin wayan ne 'yar aikin ta shigo cikin parlor gami da cewa."Gaya cen ya zo."Jin Hakan yasa Aleeza tayi saurin cewa Dr Khalil."We will talk later, Babye."Abinda tace kenan tayi ending call.Aleeza wajen window ta koma tana lek'en su Mr-Fauzan."Wa kike lek'e ne wajen?."Cewar Hajia."Ohhhhhh! Hajia bafa kowa! Naji kamar tsayawar mota ne shine fa nake dubawa."Aleeza ta fad'i haka cikin shagwab'a."To ai shikenan, Ba sai naji duka ba kuma."Aleeza murmushi tayi tare da karkad'a kai ta koma ta zauna kusa da Hajia.B'angaren Mr-Fauzan bayan sun gama gaisawa da Hafiz ne yace."Hajia na nan ko?.""Eh tana nan, Kuma na fad'a mata zuwan ka.""To bari Khairat taje su gaisa.""Oh! Dama tare da Khairat kuke? Shine ta lafe cikin motor?."Hafiz ya fad'i haka, Sannan yace."Bari naje nayi mata magana da kaina toh."Haka Hafiz ya zarce wajen motar ya bud'e, Da sauri Khairat ta d'ago kai ta kalle shi tare da sakar mashi smiling."Ina kwana?.""Kina nufin da bazaki je ku gaisa da Hajia ba kenan?."Khairat kunya ce ta rufe ta yasa sunkuyar da kai gamida
cewa."A'a dama ina da niyyar yin haka."Abinda ta fad'a kenan ta fito daga cikin motar, Hafiz ya nuna mata hanyar shiga ta wuce ' Hafiz binta yayida kallo harta shige ciki Sannan ya koma wajen Mr-Fauzan.Bayan sun zauna ne Hafiz ya fara tsarawa Mr-Fauzan yadda suyi."Aini matsala ta da kai shegen girman kai."Cewar Hafiz."Hafiz, You know me very well ' bani son raini at all...and you know that.""Just admit it ' kana son yarinyar nan... Meye a ciki? Ni banga abin raini a ciki ba ai...""Shikenan... Naji I love her and I admit that... Yanzu meye abin yi? What if tak'i yarda dani?."Hafiz dogon numfashi yaja, Sannan yace."Idan tak'i yarda da kai sai ka barta kawai don ba'a so dole, Although nasan Safna na sonka ' sai dai idan kak'i bata hak'uri.""Oh come on... Meya kawo maganar bada hak'uri? Hafiz babu abinda yake bani wahala irin in bud'e baki in bada haku'ri, Musamman ga mace!.""You see your life? Aiko hak'uri ya zama dole ka bata, Because ita mace 'yar tarairaya ce."Mr-Fauzan nuna gamsuwar shi yayi game da maganganun Hafiz, Nan suka tashi suka nufi mota."Af! Wannan taje ta shantake, Let me go and call her."Hafiz ya fad'i haka, Sannan ya nufi cikin gida domin kiran Khairat.Mr-Fauzan kuwa cikin motor ya shiga yayi zaman shi.Hafiz koda ya shiga ciki a parlor ya iske Khairat tare da su Hajia suna fira."Toh, Ke muke jira fa."Hafiz ya fad'i haka.Jin haka yasa Khairat ta mik'e tayi sallama da su Aleeza, Hafiz fita yayi yaje ya shige motor.Aleeza rakiya taiwa Khairat har wajen motor, Sannan sukayi exchanging number tukunna Khairat ta bud'e back seat ta shige.Aleeza harta juya zata wuce taji ance."Madam babu gaisuwa ne?."Aleeza wani farrrrrr taji cikin ranta, Cikin sanyin jiki ta juya ' Ganin Mr-Fauzan tayi yana kallon ta a cikin mirror d'in jikin motor.Hakan yasa Aleeza k'arasawa side d'in da yake tace."Ina kwana?."Mr-Fauzan kasa ansawa yayi, Sakamakon ganin bandage d'in da ke forehead nata."Meya faru dake haka?."Yayi tambayar with cares."Oh! Wai goshi na? I had an accident.""How comes?.""Well... Bayan na bar Company d'in ka abin ya faru dani.""Hafiz kaga irin ta ko? Shiyasa banaso ana barin k'ananan yara suna driving by their selves, I don't like that at all..."Aleeza tsuki taja Mara sauti cikin ranta tace."Ji rainin hankali don Allah! K'aramar yarinya ma yake d'auka ta kenan mtsw."Nan Aleeza ta juya ta wuce rai a b'ace.Mr-Fauzan kallon wucewar ta yayi ta glass sannan ya tab'e baki ya tada mota suka wuce.```MY FACEBOOK FANS, NA GODE SOSAI DA ADDUAR KU GARE NI THANK YOU SO MUCH, YOU GUYS MEAN A LOT TO ME.```*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.*46roups/1649808818646464/*_FAN'S KUYI HAK'URI DA JINA SHURU DA KUKAYI, BANJIN DAD'I NE..._**48-49*K'auyen su Safna suka nufa ' kasancewar tsakanin k'auyen da cikin gari akwai d'an nisa hakan yasa suka b'ata *2hours* kamar kusan kullun.Bayan sun isa cikin unguwar ne, Mr-Fauzan yayi parking daidai k'ofar gidan su Safna."Khairat you get in first, Sai ku gaisa tukunna ki fad'amata zuwan mu.""Okay."Khairat tace, Sannan ta bud'e motor ta fito, Ganin yanayin gidan nasu yasa jikin ta yayi sanyi ta shige cikin gidan."Huh! Ni tausayin yarinyar nan nakeji....Just take a look at the house she is living in!..."Mr-Fauzan ya fad'i haka with sound of sympathy.Bayan shigan Khairat cikin gidan ne ta iske su zaunea tsakar gida saman tabarma.Khairat sallama tayi Safna ta juyo ta kalle ta gamida ansa sallamar.Khairat k'arasa tayi ciki Safna ta bata kujera ta zauna, Sannan suka gaisa Khairat tayi mata ta'aziyya."Sai dai ban gane wacece ke ba."Khairat murmushi tayi ta numfasa, Sannan ta fad'awa Safna wacece ita.Safna ajiyar zuciya tayi ' ta tashi ta d'ebowa Khairat ruwan rijiya ta bata.Khairat kurb'a d'aya tayi ta ajiye ruwan."Ku kad'ai kuke zama ne?."Khairat tayi tambayan cikin tausayawa."Eh mu kad'ai muke zama yanzu, To wama muke dashi da zaizo ya zauna damu? Kinga kuwa dole na tsaya na kula da k'annai na.""To, Kina da wata sana'a ne da kike yi Aunty?."Uhum! A'a bana yin komai, 'Yan kud'in da muka d'an samu ne wajen jinyar Umma kafin rasuwar ta shine nake amfani dashi kafin in nemi aikin yi."Khairat hawaye ne suka zubo mata, Safna tayi saurin share mata hawayen."Haba... Ke kuwa! Idan kina mana kuka ai zakisa na karaya, Kuma a hakan ma aimu munajin dad'i, Idan kikayi la'akari da yanayin da ake ciki."Safna ta fad'i haka cike da bama zuciyar ta k'warin gwiwa.Khairat hannu tasa ta share hawayen ta, Ta maida kallon ta akan Rumaisa dake zaune tare Anisah suna kallon ta."Haka ne..., Bai kamata na zubar maku da hawaye ba, Sai dai tare da Yaya Fauzan nake suna k'ofar gida suna jiran ki."Safna bata rai tayi tare da mik'ewa tsaye, Ganin haka yasa Khairat itama ta tashi tsaye tana kallon Safna."Auntyn mu, Lafiya?.""Kiyi hak'uri Khairat, Bazan iya ganin Yayan ki ba.""Haba Auntyn mu, Ko yayi laifi ne?."Nan take idanun Safna suka ciko da hawaye, Tayi saurin juyawa don kada Khairat ta lura da hakan.Safna d'aki ta shige ta d'auki hijab d'inta ba tare da ta cewa Khairat komai ba, Ta fito ta sanya zata fita Rumaisa tayi saurin cewa."Yawwa, Aunty Safna kafin Umma ta rasu tace kiyi k'ok'ari ki cika mata burin ta."Da sauri Safna ta juyo ta kalli Rumaisa sannan ta kalli Khairat, Safna dawowa tayi ta zauna kusa da Rumaisa."Wane irin buri ne wannan Rumaisa?."Cewar Safna"Tace don Allah ki tabbatar auren nan ya yuwu."Safna saurin kallon Khairat tayi ganin sun had'a ido ne yasa ta d'an sakar mata murmushin k'arfin hali, Sannan ta tashi ta wuce.Safna a zaure ta tsaya ' jikin bango ta jinginar da kanta tana tunanin yadda komai ya juya mata."Insha Allah zan kasance mai biyayya a gare ki ko a bayan ranki ne."Safna ta fad'i haka.Nan ta fita ta k'arasa inda motar su take ta tsaya."Here she comes... Bari na baku guri, And please Aboki kayi abinda ya dace.""Oh come on... You can't tell me what to do!."Cewar Mr-Fauzan."Daga baya kenan dai!."Hafiz ya fad'i haka tare da bud'e motar ya fita, Nan yayiwa Safna ta'aziyya sannan ta zagaya ta bud'e front seat ta zaune gamida ta rufe motar."Ina kwana?."Cewar Safna."Lafiya! Ya k'arin hak'uri?.""Alhamdulillah.""Allah yai mata gafara."Ameen Safna tace, Sannan sukayi shuru na d'an lokaci."Am... Safna...Am..."Safna ita dai ido kawai ta zuba mashi, Tana jiran abinsa zai fito daga bakin shi."Am here to apologize... Safna..."Safna sunkuyar da kai tayi tana sauraron shi."Inason ki manta da duk wani abu da ya faru mara dad'i tsakanin mu."D'ago manyan idanun ta tayi wad'an da sukayi ja ta kalleshi, Hawaye cike a idanun, Phalanges d'inta d'aya kan d'aya."I know that I hurts you several times with my words..."Mr-Fauzan ya fad'i haka in a husky voice."I really regret what I did to you..."Ya fad'i haka With sounds of sympathy tare da dunk'ule hannun shi.Safna d'agowa tayi ta jinginar da kanta jikin seat d'ingami da share hawayen fuskar ba tare da tace mashik'ala ba.Mr-Fauzan harya kai hannun shi zai janyo nata hannun ' sai kuma ya fasa."You totally changed everything in me Safna... Nasanmeye tausayi duk ta dalilinki."Safna juyowa tayi cikin mamaki take kallon cikin idanun shi, A zuciyar ta tace."Anya wannan shine Fauzan d'in da na sani kuwa?.""Surprise right? Yes Safna... Ni d'inne dai Fauzan."Ya fad'i haka tare da janyo hannun ta ya dunk'ule cikin nashi."Please Safna... Will you marry me? Zaki aure ni?."Mr-Fauzan ya fad'i haka.Safna sunkuyar da kai tayi bakin ta yayi mata nauyi, Kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon hannun shi dake saman nata."Bazan ta kura ki ba, Kuma bazan matsa miki ba, Amma inaso ki amince muyi auren nan Safna... Da yardar ki za'ayi komai.""Babu abinda zai cenja akan maganar auren, Na amince."Cewar Safna."Alhamdulillah,And I promise you that ' zan baka duk wani abinda kike buk'ata na rayuwa."Mr-Fauzan ya furta haka da murmushi akan lips d'inshi.Safna zame hannun ta tayi gamida cewa."Ni zan koma cikin gida.""No wait... Ai ban gama magana ba, Inason ki fad'awa Khairat k'anwata duk abinda kike buk'ata a yanzu."Cewar Mr-Fauzan."A'a, Babu abinda nake buk'ata.""Okay then..."Ya fad'a tare da d'aga wani abu ya ciro kud'i masu yawa ya mik'a mata."Take this, Ki d'an fara rage abinda kike buk'ata na biki.""A'a don Allah ka barshi, Ni a yanzu bana buk'atar komai illa kwanciyan hankali.""Yes, I know that... But ki daure ki ansa wannan, Don't you think zaku buk'aci kud'i na hidiman biki?."Cewar Mr-Fauzan.Safna hannu tasa ta ansa kud'in tare da yimashi godiya, Sannan ta bud'e motar ta fita.Bayan wucewar tane Hafiz ya nufi wajen Fauzan.Hafiz motar ya bud'e ya shiga, Ganin fuskar Mr-Fauzan cikin fara'a ne yasa Hafiz cewa."Tofa! Allah yasa dai bakayi abinda zai dagula komai ba, Don nasan halinka.""I totally changed, Hafiz ' duk ta cenja ni wallahi... I truly love Safna with all my heart, Bansani ba ko asiritaimun cikin k'ank'anin lokaci.""Alhamdulillah,And did you tell her that you love her?.""I haven't... But na nuna mata hakan da baki na... Hafiz bansan nayi iya tausasa murya ba sai yau."Hafiz tsayawa yayi yana kallon shi at the same time yana dariya."Fauzan please be a man mana! Duk kabi ka wani rud'e... Mu dai ka saisaita kanka don driving zakayi yanzu."Nan dukkansu suka hau dariya cike da farinciki.B'angaren Safna, Shigar ta cikin gida ta iske Khairat zaune a inda ta barta tana hira dasu Rumaisa.Safna waje ta samu ta zauna, Ta sauke ajiyar zuciya."Auntyn mu har kin gama?."Cewar Khairat."Eh, Na gama ke kawai suke jira.""To amma Auntyn mu, Zaman nan naku ku d'ai is very risk fa akwai had'ari, Don Allah ku koma wajen 'yan uwa mana."Khairat ta fad'i haka cike da nuna damuwa."To ai Khairat jibi ne fa auren dududu bai wuce mu k'ara kwana d'aya anan ba, Su kuma k'an naina wajen dangin Baba zasu koma."Khairat numfasawa tayi ta mik'e tare da cewa."Indai akwai matsala kawai ki fad'a mana, Babu abinda zai gagara kinji Auntyn mu."Safna kai kawai ta d'aga ma Khairat, Sannan ta tashita raka ta har k'ofar gida tukunna ta koma cikin gida.*FACEBOOK@SEEMALUV