Showing 6001 words to 9000 words out of 39355 words
ta dawo da ita a hannu.Dai dai bakin k'ofar shiga security ya tsare ta."Kina da buk'atar taimako ne?."Ya fad'a cikin harshen turanci."Yes."Nan Safna ta mik'a masa Application letter d'in ya karance ta tsaf."Sir Kamal ya baki ko?.""Eh.""Ok barima inkaiki har Office d'in nasa."Haka Safna tabi bayan security man d'in, Har saida ya shigar da ita office d'in tukunna ya juya yayi tafiyarsa.A zaune Safna ta iske Kamal ' tare da laptop a gabanshi.Jayo attention d'inshi tayi da cewa."Good morning, Sir!."A hankali Kamal ya d'ago kai ya kalleta da manyan idanun shi, Ganin itace yasa shi rufe laptop d'in gamida calming hands d'in shi."Have a seat!."Abunda yacewa Safna kenan ' ta sami waje ta zauna, Tukunna ya kafeta da ido."I have been expecting you!."Nan tad'an sunkuyar da kai alaman ladabi.Nan ya d'aga waya ya kira messenger d'inshi.Cikin hanzari messenger ya shigo cikin office ' cike da ladabi."Sir! Gani.""Yes, Inaso ka kaita inda ake screening coffee makers.""Ok."Haka Safna ta tashi jiki a sanyaye tabi bayan messenger d'in, Har sunkai bakin k'ofa ya tsaidai ita da cewa."Be praying."Uhum, Kawai Safna tace suka fice daga wajen ' waniwaje suka shiga an k'ayatashi da kujeru yadda kasan parlor komai pink colour yayi kyau sosai, Ita dai kalle kallenta kawai takeyi bata ankara ba taji ance."Madam, Ki sami waje ki zauna."Inji Messenger.Saida ya tabbatar ta zauna ' sannan ya juya yabar wajen.Bayan ta zauna ne ta ankara da mutanen da ke zazzaune a wajen, Mata ne dukkansu ' sunci kwalliya sunci gyale wasuma babu ko gyalen a jikinsu, Daka gansu kaga 'ya'yan manya.Cikin 'yan lokuta k'alilan aka kawowa kowanen su cup&spoon da ingredients d'in da zasuyi amfani dashi wajen making coffe d'in.Nan Safna taji wata murya tace "start!".Kasancewar bata tab'a had'awa ba hakan yasa ta fara kallon yadda ta kusa da ita keyi, Cikin hikima Safna ta fara making coffee har ta gama ' sannan tajiansake cewa."Your time is off! Young ladies."Mr-Fauzan yayi maganar in slangs.Nan ne Safna ta d'ago kanta domin taga inda maganar ke fitowa, Hakan yayi daidai da juyowar Mr-Fauzan wanda yake zaune a saman kujerar shi ' nan sukayi ido hudu da Safna."Subhanallahi! Wannan bashine wanda nabige shi ' abisa rashin sani ba?."Tayi tamabayar a cikin zuciyar ta.Nan take zufa ta fara karyo mata.Shi kuwa Mr-Fauzan tunda ya fahimci Safna cike take da tsoro yasaki wani irin murmushin da baikai zuci ba.Nan ya umarce su ' da kowaccen su ta kawo mashi coffee d'inda ta had'a yayi tasting, Haka sukaita tashi suna kaiwa yana tasting kuma yana rubuta masu score.Safna ganin an kusa kaiwa kanta ne yasa ' ta fara addu'o'i, Tana gama rufe baki line d'in ya kawo kanta' nan ta tashi cikin sauri rik'e da cup d'inta ta nufi wajen shi.Mr-Fauzan ko kallon ta beyiba ya karb'a yayi tasting ya rubuta mata score d'inta, Sannan ta juya ta koma ta zauna.*After some minutes* ya tashi ya koma office d'inshi,messenger na biye dashi, Bayan Mr-Fauzan ya zauna ne messenger yace."Sir, akwai wani aike ne?.""A'a babu, Zaka iya fita."Bayan fitar shine ' Mr-Fauzan ya d'aga waya ya kira P.A Kamal, Ringing d'aya zuwa biyu tayi ya d'auka."Sir?.""Kamal, Kazo yanzu.""Ok."Abunda Kamal ya fad'a kenan Mr-Fauzan ya kashe wayar.Cikin 'yan lokuta k'alilan Kamal ya shigo cikin Office d'in Mr-Fauzan, Bayan ya zauna ne Mr-Fauzan ya mik'o mashi paper tare da cewa."Kamal, inaso kaje kasa a nuna ma Safna Habib and Muneeba Imran yanayin aikinsu ' sauran kuma a sallamesu because they are not qualified.""Ok."Abunda Kamal yace kenan ' sannan ya juya yabar wajen, Jin sunan Safna a ciki abun yasa shi farinciki matuk'a.Kamal hole d'in ya shiga da kansa, Nan yayi calling attention d'in ko wacce a wajen.Kamal ' hak'uri ya fara bama wad'anda basu sami aikin ba, Ita kuwa Safna babu abinda gabanta keyi inba fad'uwa ba.Bayan ya gama dogon bayanin shine ' ya kira sunan Safna da Muneeba tare da cewa."Safna Habib da Muneeba Imran, Su kad'ai ne aka d'auka amatsayin Coffee makers."Safna mik'ewa tayi cikin jin dad'i tana murmushi, Don kuwa samun aikinta shine burinta na farko dayafara cika.Kamal ganin yadda hole d'in ya hargitse ne ' yasa shikomawa Office tare da kiran messenger d'inshi a waya cewa."Kaje cikin hole d'in nan, Ka zomun da Safna Habib da kuma Muneeba Imran."To kawai d'an aiken(messenger) yace, Sannan Kamal ya kashe wayar shi.B'angaren Safna kuwa! Ai baki har kunne, Nan take ta fara neman Muneeba gami da kwala mata kira."Muneeba Habib!."Muneeba kuwa jin yadda aketa kiran sunan tane yasata juyowa a tsorace' cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu."Lafiya kiketa kiran sunana?.""Lafiya kalau ' Muneeba nice Safna Habib, Ina fata zamu had'a kanmu domin muyi aiki tare."Muneeba tab'e baki tayi cike da downgrading ta juya tacigaba da harkar gabanta, Ba tare da tacewa Safna komai ba.Safna ganin haka ne yasa ta koma ta zauna ' jiki a sanyaye taci gaba da k'arewa mutanen da ke wajen kallo.©Seemaluv_Novels*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_Ina dai sake bama Fan's d'ina hak'uri , Masu bin Novel d'ina ' Ayyuka ne sukai yawa..._**12-13*Suna cikin haka ne Messenger yazo cikin hole d'in yakira sunayen su kamar yadda Sir-Kamal ya umurce shi, Safna jin ankira sunan ta yasa tayi saurin mik'ewa tsaye tare da k'arasawa wajen shi.Ita kuwa Muneeba saida aka kira sunan ta ' kusan sau uku tukunna taje inda ake kiranta, Nan Messenger ya juya zuwa office d'in Sir-Kamal su kuma suna biye dashi a baya.Bayan sun isa bakin office d'inne yayi musu nuni da yatsa alaman su shiga, Bayan shigar sune ya juya yayi tafiyarsa.Safna shiga tayi tare da yin sallama ' Muneeba na binta abaya.Sir-Kamal ansa sallamar yayi ' ba tare daya d'ago kai ya kallesu ba har saida ya kammala danna laptop d'inshi."Ku zauna."Ya fad'a haka yana musu nuni da kujerar dake gefensu.Bayan sun zauna ne yace."Hope kun shirya ma aikin nan?.""Insha Allah."Suka fad'a a tare."Good! So yanzu zan fad'a muku yadda aikin yake."Sai da yad'an d'auki lokaci yana kallonsu, Sannan yace."Ko waccen ku za'a rik'a biyanta salary akan naira 100,000(dubu d'ari) ' kuma idan har kika tsaya kan aikin ki, To salary d'inki zai ruk'a increasing."Muneeba smiling tayi tare da gyara zama, Sannan Sir-Kamal ya cigaba da cewa."Early morning *7:00am* idan kukazo aiki ' zaku had'a coffee ku kaima workers, Sannan After that zaku bi kowane Office ku kai."Sir-Kamal, Bayan ya gama musu bayani ne ' ya mik'e tsaye tare da cewa."Ku tashi muje in kaiku Store."Safna da Muneeba tashi sukayi suka bi bayan shi zuwa store, Suna isa wajen yasa hannu ya murd'a handle d'in k'ofar ya bud'e suka shige ciki.Nan ya nuna musu komai da komai, Wanda zasuyi amfani dashi fannin aikinsu.Sir-Kamal, Bayan ya gama introducing masu komai ne ' harya juya zai koma office sai kuma ya tsaya gami da juyowa ya kalli Safna wacce hankalin ta kekan cups d'inda ke wajen."Safna Habib!."Jin kiran sunanta da yayi ne ' yasa tayi saurin juyowa ya kalleshi, Tare da cewa."Yes Sir?.""Ki biyoni zuwa Office."Ok tace ' sannan ta bishi suka wuce, Muneeba ganin haka yasa ta tab'e baki tare da calming hands d'inta zuciyarta cike da sak'e sak'e.Safna bayan isarsu cikin office d'in ne, Yayi mata iznin zama ' tukunna shima ya zauna."Am.. Safna i need to discus something with you!.""Ok Sir.""You see!, Nan Company ne mai son tsafta da gayu ' da k'yale k'yale you know! Da dai sauransu."Nan ta fara duban jikin ta ' tana mamaki."No, Bawai bakida tsafta bane ' what i mean is that, Ki k'ara because matsalan ba daga ni bane ' understand?."Kai Safna ta d'aga mashi alaman Eh."Anyway! Koma yayane dai ' a hankali zaki fahimta.""Insha Allah! Zan gyara."Cewar Safna."Good! Zaki iya tafiya."Safna tashi tayi tabar office d'in, Harta nufi side d'insu sai kuma ta tsaya ' a zuciyarta tace."Ina d'aya daga cikin ma'aikatan company d'in nan, Ya kamata in kewaya inga ko ina."Bayan ta ayyana haka a ranta ne ' ta saki murmushi, Tare da juyawa ta nufi wani b'angaren da yake tsit! Tamkar babu mutane.A hankalin Safna ke tafiya ' kasancewar yadda wajen yake ba hayaniya, Wata k'ofa ta hango and'an bud'eta kad'an.Safna k'arasawa wajen tayi ta bud'e k'ofar. Guess-room ne k'ayatacce, Komai na cikinsa designer ne ' ganin haka yasa ta shigewa ciki domin ta bama idonta abinci.Tana shiga ta sami waje ta zauna a bakin gado ' tana tab'a drowers d'in dake gefen gadon."Rayuwa kenan! Idan da ranka zakasha kallo."Ta fad'i haka tana murmushi.B'angaren Mr-Fauzan, Zaune yake tare da ma'aikatan shi a chamber inda suke had'uwa suna meeting ciki kuwa harda Sir-Kamal.Meeting d'in bai wani d'auki lokaci ba suka kammala, Kowa tashi yayi ya koma kan aikin shi ' Sir-Kamal office ya koma yayi zaman shi.Mr-Fauzan kuwa yana fitowa daga chamber ' kai tsaye ya nufi guess-room d'inshi domin ya kwanta ya huta.Koda ya doshi wajen gani yayi k'ofar a bud'e, Hakan yasa shi k'arasawa wajen da izza tare da cewa."Is like ' wani ya shiga ya barta a bud'e, To waye kuma meyasa?."Safna jin ana magana sama sama ne ' yasa tayi hanzarin b'oyewa bayan labule cike
da tsoro.Mr-Fauzan koda ya shigo ciki ' baiga kowa ba illa takalmi daya gani a bakin k'ofa, Hakan ya k'ara tabbatar mashi da cewa akwai mutum a ciki.Nan ya fara dube dube ' shine har under bed da k'ark'ashin kujera, Amma baiga komai ba.Safna kuwa jikinta rawa kawai yakeyi."Ya Rabb! Ya kafitar dani lafiya."Ta fad'i haka a cikin zuciyarta.Mr-Fauzan bakin gado ya samu ya zauna, Safna gumi kawai take had'awa bata ankara ba taga kenkyaso a saman hijabin ta.A 360 Safna ta fito daga bayan labule ' sam ta mantada mutum cikin d'akin, Cikin rawar jiki da tsoro ta yaye hijabin dake jikinta ta yarfar dashi gefe, Sannanta koma jikin bango ta jingina tare da rufe idonta tana maida numfashi.Mr-Fauzan kuwa abun dariya ya bashi ' amma sam bai bari ta fito fili ba, A zuciyar shi yace."Oh God! Ji yadda take sakin ajiyar zuciya, Tamkar taga wani mugun abu."Mr-Fauzan tsayawa yayi yana k'arewa halittar jikinta kallo.Kasancewar Safna rigar dake jikinta tad'an matseta kad'an duk da dai kayan duk sun kod'e, Don akwai inda yad'an fara yagewa, Sannan ga gashin kanta yazubo har izuwa k'asan k'irjin ta.kasancewar kitson dake kanta all-back ne, Uhm abunka da bafullatana ' abun dai ba'a cewa komai.Har izuwa yanzu Safna runtse take da idonta ' tana ajiyar zuciya, Mr-Fauzan kuwa murmushin mugunta ya sakar mata."Lallai yanzu zaki dawo hayyacinki kuwa!."Ya fad'i haka a zuciyar shi, Tare da mik'ewa tsaye."What!!! You?."Ya furta hakan cikin tsawa, A razane Safna ta bud'e idonta ' sai a wannan lokacin ne ta tuna cewa akwai mutum a d'akin.Safna koda suka had'a ido da Mr-Fauzan saida cikinta ya murd'a, Ganin babu hijab a jikin tane ' yasa tayi saurin kare jikinta da hannayen ta.Yunk'urawa tayi zata d'auki hijabin ta yayi saurin take hijabin da k'afarshi tare dayin calming hands."First! What are you doing in my guess-room."Safna sunkuyar da kanta tayi ' ba tare da tace komai ba."Bakiji ba?.""Sir, please am sorry ' kayi hak'uri wallah..."Bata k'arasa maganar ba ya daka mata tsawa, Da cewa."Answer me!!!, What are you doing in my guess-room!.""No answer right? Dama matsalan ku talakawa kenan!, Sata kikazo yi dama?."Zaro ido Safna tayi ' tare da girgiza mashi kai alaman a'a."Then what? Ki fad'amun idan ba sata ya shigo dake ba to meye?."Safna k'walla ce cike a idonta k'iris ya rage hawaye su zubo."I wil expose you infront of everyone, Gobe bazaki k'ara shiga wani waje da sunan sata ba."Jin haka yasa Safna tayi saurin zubewa k'asa tana kuka."Sir!, Don Allah kayi hak'uri ka yafeni ' wallahi ba sata ya shigo dani ba, Wajen ne ya burg..."Bata kaiga k'arasawa ba ya fizgo hannunta, Tare da janta suka fito daga guess-room d'in.Safna hawaye kawai ke zuba a fuskarta ' ganin suna gab da shiga inda mutane suke ne, Yasa tayi saurin kare jikinta da hannu d'aya.Mr-Fauzan kuwa, Fizgarta kawai yakeyi.*_©Seemaluv Novels…_*[10:29PM, 8/19/2017] Hannatu: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*
*_Pure Moment Of Life writers_*
® ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄
*_Assalamu Alaikum, Nasan k'ila hak'urin ku ya k'are, Ko dayake nima balaifina bane ' kunsan al'amarin yadda ciwo yake!, To a yanzu dai na sami sauki.... ( Always in my heart ' baby!..S2😘.)_*
*14-15*
Mr-Fauzan tunda yaja Safna bai tsaya ba saida ya tabbatar sun shiga cikin mutane, Sannan ya tunkud'ata tsakiyar su, Hakan yasa gaba d'ayansu suka juyo suna kallon shi.
Sir-Kamal ya fito kenan rik'e da files a hannunshi zai shiga Office d'in Mr-Fauzan, Yaji surutai ' hakan yasa shi juyawa ya nufi wajen.
Bayan isarshi wajen ne ' ya lura da yanayin da Safna ke ciki, Sir-Kamal harya bud'e baki zaiyi magana yaji Mr-Fauzan yace.
"Attention please!!, Musamman securities ' muddin bazaku rik'a kula da properties na company d'in nan ba to tabbas zan cenja ku in nemi wasu, Look at her."
Ya nuna Safna da yatsa, Hakan yasa dukkansu suka maida kallonsu akan Safna ' wacce hawaye kawai ke zubowa a fuskarta a sunkuye.
"Ta shiga guess-room d'ina da niyyar sata ' domin kuwa aciki na kamata, Shi dama tsiyar talaka kenan! Bai iya samun waje ba, let me warn everyone of you here! Especially securities ' dole ne ku zama masu lura, Idan kuma ba haka ba ' to lallai zan d'auki mummunar mataki.
Muneeba dake tsaye a wajen ne zuciyar ta cike da farin ciki.
"So disgusting!, Nan gaba korar ki za'ayi ma."
Ta furta hakan in murmured.
Mutanen da ke wajen ' daga mai cewa aida ganinta zata iya sai masu suratai kala kala, Safna kuka takeyi sosai ' tana girgiza kai.
Mr-Fauzan nuna Safna da yatsa yayi yace.
"And let me tell you something Ki tsaya ' a matsayin ki kawai zaifi, If not! To kina tattare da wahala arayuwarki ' k'azama kawai."
Yana gama fad'in haka ya juya ya koma office, Safna kam kasa motsawa tayi ko nan da cen saboda kunyar data sha.
Sir-Kamal, Wanda ya dad'e tsaye a wajen ranshi a b'ace cike da tausayawa ne, Ya k'arasa wajenta tare da maida kallon shi akan mutanen da sukayi carko carko awajen.
"Ina son kowa ya koma kan aikin shi ' yanzun nan!!!."
Ya fad'a a tsawace, Hakan yasa kowa ya juya ya koma kan aikin shi.
Sir-Kamal, Files d'in dake hannun shi ya aje gefe ' sannan ya cire Suit d'inshi ta saman ' ya rufema Safna jikinta dashi tare da cewa.
"Kije office d'ina ki jira ni."
Haka Safna ta juya ta nufi office d'inshi a gaban idon shi, Tukunna shi kuma ya wuce office d'in Mr-Fauzan.
Bayan ya kammala duk wani aiki ne ' ya dawo cikin office d'in shi, Ya iske Safna a zaune tana kuka.
Kai kawai ya girgiza ' sannan ya k'arasa ciki ya zauna, Gami da yin gyaran murya.
Safna kai ta d'ago ta kalleshi da rinannun idanun ta.
"Inason ki daina kukan nan haka, Ki fad'amun gaskiyar abunda ya faru."
"Sir, Wallahi babu abunda nayi ' babu abunda na d'auka, Kawai wajen ne..."
Safna k'arashe maganar tayi cikin kuka, Kuka mai tsuma zuciya.
Sir-Kamal runtse ido yayi domin kuwa kukan har cikin ranshi yake jinsa.
"Calm down Safna! Is ok, Na fahimci cewa ya yanke hukunci ne abisa rashin sanin gaskiyar lamarin, But it's ok."
"Sir, Nidai kawai ina ganin ban shigo company d'in nan da sa'a ba, Ina ganin zan aje aikin kawai..."
"What!!! Don't you ever say that again!."
Sir-Kamal ya fad'a cikin fad'a.
"Yau yau da baki aiki ' sannan kice zaki aje? For what reason? Kinsan yadda aiki yake da wuyar samu kuwa? Ko don kinga kin samu cikin sauk'i?."
Safna lura tayi ranshi ya b'aci, Hakan yasa ta sunkuyar dakai ' tare da cewa.
" Sir!, idan abunda na fad'a ya b'ata maka rai kayi hak'uri..."
Ajiyar zuciya kawai yayi ' sannan yace.
"Idan lokacin tashi yayi ' karki tafi ki tsaya ki jirani, Ina hijab d'inki?."
"Yana a d'akin nashi."
"D'aki kuma? Uhm! Guess-room ake cewa."
Sir-Kamal wayar shi ya d'aga wacce ake amfani da ita cikin company d'in, Ya umarci security da su binciko hijab d'in Safna cikin guess-room d'in Mr-Fauzan.
Haka ko akayi ' cikin lokuta k'alilan security man d'in nan ya shigo da hijab d'in Safna cikwikwiye a hannun shi, Tare da cewa.
"Sir, here it is."
"What!!! Haka kaga ya dace ka kawomin shi? Because bakasan darajar hijabi ba ko?."
"Am sorry Sir."
Security man d'in ya fad'i haka, Sannan ya ninke hijabin ya mik'a mashi.
"Ita zaka bawa, Ba niba."
Sir-Kamal ya furta hakan cikin isa.
Safna hannu ta mik'a ta karb'a hijab d'in nata ta sanya a jikin ta, Sannan security man d'in ya juya ya fice.
"Yanzu ki tashi ' ki kawomin coffee."
Safna tashi tayi cikin hanzari ta nufi store ta had'a mashi coffee d'in cikin d'an k'an k'anin lokaci, Sannan ta dawo office d'in ba tare da tayi knocking k'ofar ba ta fad'a.
Safna sallama tayi Sir-Kamal ya amsa, Tukunna ta k'arasa ciki ta aje mashi coffe d'in gami da cewa.
"Sir, Gashi."
Sir-Kamal d'ago kai yayi ya kalleta, yace.
"Sami waje ki zauna!."
Babu musu ta sami waje ta zauna.
Nan yayi gyarar murya yace.
"Safna Habib!."
Ta d'ago kai ta kalleshi.
"Ki kasance mace mai nutsuwa, And in tambayeki?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh.
"Kinaso ki shirya da Ogana?."
"Eh Sir, Inhar hakan mai yuwuwa ce."
"Good!."
Ya furta