Showing 12001 words to 15000 words out of 39355 words
makara da yawa."Safna waje ta fito ' ta nufi wajen Umma ta zuk'unna, Umma ta zuba mata kokon ta fara sha ko sugar babu don kuwa idan da sabo aita saba.Tana kammala wa ta mik'e tsaye tare da cewa."Umma ni zan wuce wajen aiki.""To Safna Allah ubangiji ya tsare."Amin Safna tace, Sannan ta zarce d'aki ta d'auki hijab ta sanya ta fice, Tana fita ne taga mai keke-napep a tsaye jingine a jikin napep d'inshi a k'ofar gida."Bawan Allah lafiya?."Cewar Safna."Kece Safna habib ko?."Ta d'aga mashi kai gami da cewa."Eh.""Yawwa cewa akayi inzo inruk'a d'aukan ki kullun idan zaki tafi wajen aiki."Abun ne ya ba Safna mamaki tace."Bawan Allah injiwa?.""Yace in fad'a miki Ogan ki Kamal."Abun d'aure mata kai yayi, Sai dai tayi murmushi tace."To shikenan muje."Safna shiga tayi shima mai keke-napep d'in ya shigayaja suka tafi.*AROUND 8:00AM* Safna ta isa cikin company d'in, tana sauka ta ciro d'ari biyu daga cikin 'yar k'aramar jakarta ta mik'a mashi."A'a ai shine zai rik'a biyana duk k'arshen wata."Safna dafe kai tayi alaman mantuwa, Tace."Ya salaam! Kayi hak'uri na manta ne."Nan ta maida kud'inta ta juya ta nufi cikin company d'in, Koda ta shiga a tsaitsaye ta iske mutanen dake ciki ' Mr-Fauzan sai zabga bala'i yakeyi akan ba'ason zuwa akan lokaci.Jin haka yasa Safna yin ajiyar zuciya ' acikin zuciyarta tace."Uhp ashe ma bani kad'ai bace ta makara d'in."Safna hango Muneeba tayi ' hakan yasa ta k'arasa kusa da ita."Muneeba wai meke faruwa ne?."Cewar Safna."Hmm. Kinsan halinsa ai ' fad'a yake akan wad'anda basa son zuwa in time, Kuma saida ya tambaye ni ina abokiyar aikina."Nan take gaban Safna ya fad'a, Tace."To me kika ce masa?.""Ha'a me kuwa zance masa? Zanyi masa k'arya ne saboda in faranta miki?, Ce masa nayi baki ruga kin iso ba."Nan fa Safna tsoro da fargaba suka bayyana a fuskarta, Mr-Fauzan kuwa ashe ya riga yaga shigowar Safna wajen."Where is Safna Habib?."Mr-Fauzan ya tambaya yana kallon side d'inda take.Safna salati kawai takeyi a cikin ranta."She is here Sir."Cewar Muneeba.Safna k'arasawa tayi gabansa tare da cewa."Gani.""Baki karanta rules d'in aikin ki bane?."Mr-Fauzan yayi maganar cikin tak'ama."Na karanta.""Good! So baki shirya ma aikin bane?.""Ba haka bane, Wallahi nauyin bac...""What?? Nauyin bacci? You are not serious Safna.""Take it easy Sir."Cewar Sir-Kamal..Sai a wannan lokacin ne Safna ta lura da Sir-Kamal a wajen, Ganin sa yasa tayi ajiyar zuciya ' tasan koba komai bazata wulak'anta ba."Zaki bama duk wani ma'aikaci dake cikin wannan company d'in Coffee for good 2weeks ba tare da taimakon abokiyar aikin ki ba, Wannan shine punishment d'inki."Mr-Fauzan ya fad'i haka d'auke da murmushin mugunta, Sannan ya k'ara da cewa."Idan kinso zaki iya cigaba dayin nauyin bacci, Zaku iya komawa kan aikin ku."Ya umarce su, Nan Safna ta juya kowa ya watse ya cigaba da harkar gabansa.Safna direct store ta nufa ' ta fara had'a coffee tana zubawa a cups tanayi tana kaiwa ma'aikatan dake wajen, Saida ta kammala tukunna ta fara kaiwa office.Safna office d'in Sir-Kamal nufa, Knocking tayi ya bata iznin shiga ' sannan ta bud'e k'ofar ta shige d'auke da sallama.Bayan ta aje mashi coffee d'in saman table d'inshi nesuka gaisa, Sannan tace."Sir?."Ya d'ago kai ya kalleta."Naga Abun arzik'i naji dad'i kuma nagode, Allah ya saka da alkairi.""Ki sami waje ki zauna ' first."Safna zama tayi suna facing juna, Sannan Sir-Kamalyace."No need of thanking me Safna, Saboda wannan ai yiwa kaine."Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta."Yanzu kije ki cigaba da aikin ki, Idan kin gama saikizo i have a surprise for you."Ok Safna tace ' ta mik'e d'auke da murmushi a fuskarta, Sannan ta d'auki ragowar Coffee d'in ta nufiOffice d'in Mr-Fauzan dashi.Nan suka had'e da Hafiz abokin Mr-Fauzan yana k'okari shiga cikin Office d'in, Safna tsayawa tayi caktare da cewa."You are welcome."Hafiz kallonta yayi daga sama har k'asa, Sannan yace."Thank you!."Hafiz bud'e office d'in yayi ya shige tukunna Safna tabiyo shi a baya.Haka ta shiga da sallama a bakin ta jikin ta na d'ar d'ar.Bayan Mr-Fauzan da Hafiz sun gaisa ne Safna ta ajemusu Coffee two cups a wajen, Ganin yayi bak'o ne yasa ta juyawa zata wuce ba tare data gaishe shi ba ' saboda kar tayi interrupting d'in shi.Harta kai bakin k'ofa ya daka mata tsawa da cewa."Where did you think you're going to?."Cikin fargaba ta juyo ta kalleshi a sanyaye."Sorry Sir.""Wane irin Sorry Sir, Come on zo nan."Safna dawowa tayi ' tayi tsaye wajen desk d'inshi, Shi kuwa Hafiz kallon su kawai yakeyi yana murmushi."First, Kin kawomin Coffee without sayin anything, Second ' kin juya zaki tafi without greetings, Tarbiyyar da aka koya miki kenan daga gidan ku?."Nan take hawaye suka zubo daga fuskarta."Am sorry Sir!..."Ta furta cikin rawar murya."Calm down mana!, Hak'uri akeyi and she even apologized."Tsaki Mr-Fauzan yaja cikin b'acin rai yace."Leave my office."A tsawace yayi magana, Hakan yasa Safna juyawa cikin hanzari ta bar Office d'in tana hawaye."Haba aboki! Kacika zafin rai da fad'in hash-words."Cewar Hafiz."Yarinyar sam batada alk'ibula ne, P.A nane ya matsa saina d'auke ta aiki ' ita gata k'azama."Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin izza, Hafiz murmushi kawai yayi yad'an tsaya k'are mashi kallo nad'an lokaci."Meye haka, Kana kallo na kana smilling.""Kuma yarinyar nan daga ganinta talakace ko.""Ehen now!."Nan Hafiz ya gyara zama ' gamida duba wristwatch d'in hannun shi."Ina ganin ' yanzu komai zaizo mana da sauki.""What do you mean?."Mr-Fauzan yayi tambayar."Ina nufin ita tafi dacewa da kai Abo....."Hafiz bai kaiga k'arasa maganar sa ba, Mr-Fauzan ya dakatar dashi."No please ' karma ka k'arasa please, Hafiz wace irinmagana kake fad'amin? Yau kuma da wannan k'azamar zaka had'ani?.""Ka daiyi tunani akai Fauzan! Ni abokin kane, Kuma bazan tab'a baka gurguwar shawara ba, Batun rashin tsafta kuma ai kaine zaka gyara ta.""No no no... Mubar maganar nan don bazata sami shiga ba.""Ok! Then, Ni bara in tafi, Idan kayi tunani akai ' saika nemeni."Nan Mr-Fauzan da Hafiz sukayi sallama da junan su, Bayan fitar Hafiz ne Mr-Fauzan ya bud'e laptop d'inshi ya fara aiki.*©SEEMALUV NOVELS GROUP*21*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_*Follow me on wattpad @Seemaluv1*_Dedicated to Momyn-Sultan and Sadnaf,..._**22-23*B'angaren Safna kuwa ' a zaune take a wajen zamansu babu abinda takeyi inba kuka ba, Muneeba ce tsaye a kanta tana tambayar abunda ya faru."Wai don Allah meye ne? Nifa na fara gajiya da wannan koke koken naki, Don karki samun ciwon kai.""Don Allah Muneeba ki kyaleni! Ki barni inji da d'aya mana ' ku baku tab'a damuwa da damuwar wasu saidai taku kuka sani, Na rok'eki ki barni inji da wulak'ancin da mutumin nan kemin."Tab'e baki Muneeba tayi, Ta koma taja kujera ta zauna ta cigaba da danna wayarta.Safna sai da tasha kuka har kanta ya fara ciwo, Tukunna tayi shuru ta fawwalama Allah komai.Saida ta dad'e a zaune, Sannan ta tashi ta nufi toilet d'in mata ta wanke fuskarta, Tukunna ta fito ta wuce office d'in Sir-Kamal kai tsaye.Tana isa wajen ta bud'e k'ofar ba tare data jira anbata izni ba, Sakamakon ciwon kanda take fama dashi.Safna kai tsaye ta shige ciki ta samu waje ta zauna agajiye, Sannan tace."Sir, Na dawo."Sir-Kamal lura yayi da yadda idonta ya kunbura ' yasan cewa babu makawa Safna kuka tayi."Safna Akwai abunda ke damunki ne?."Ta girgiza mai kai, Alaman a'a."No you better tell the truth!, Because daga ganin idonki kinyi kuka.""Sir-, Koma menene ya riga ya wuce ' maimaita maganar batada wani amfani."Girgiza
kai kawai yayi ' sannan ya mik'e tsaye yaje d'auko wata leda dake cike da kaya a jikinta ya mik'awa Safna, Tare da cewa."Ansa ki bud'e ki duba ki gani, Idan sunyi miki saiki sanar dani."Safna karb'ar ledar tayi cike da son ganin abunda ke ciki, Bayan ta bud'e ne ta fara d'aga kayan tana dubawa cikin jin dad'i.Abayas ne masu kyau ' kuma masu tsada, Ko wannen design d'inshi dabam zasu kai kala goma.Safna murmushi kawai ke bayyana daga lips d'inta, Cikin nutsuwa tace."Sunyi kyau! Gaskiya kayan nada kyau sosai."Sir-Kamal komawa yayi ya zauna ' zuciyar shi cike da farin ciki, Yace."Alhamdulillah!Wannan kayan nakine na baki kyauta!, daga yau inason ki ruk'a sanya su, Banason insake ganinki cikin wannan kayan na jikin ki."Cikin fara'a Safna tace."Nagode.""And, Ki duba takalman dake ciki idan sunyi miki ' ki sanar dani."Cikin zumud'i Safna ta fara d'aga takalman tana gwadawa, Cikin sa'a kuwa duk sunyi mata kasancewar su flat-shoes ne."Sunyi."Ta furta, Kanta a sunkuye."Good!, Ki d'auka ki tafi dasu wannan shine gift d'ina na farko.""Na gode ' na gode Sir, Allah ya saka da alkairi."Safna tashi tayi tabar Office d'in nashi cikin jin dad'i, Ta wuce side d'insu sam ta manta da ciwon kanda take fama dashi ' ai tuni taji ta warke.Bayan ta isa bakin store ne taja kujera ta zauna ' gamida ajiye ledar kayan nata ta fara tunane tunane kala kala a zuciyarta."Meyasa yakeson farantamun rai a kullun? Gaskiya Sir-Kamal yana da kirki, Ni duk na k'osa in nunawa Umma wannan kayan."Tana cikin wannan tunanin ne Muneeba tazo wajen.."Lafiya daiko? Kika zauna ke kad'ai kina murmushi.""Uhm! Lafiya k'alau Muneeba."Muneeba kallon ledar dake gaban Safna tayi."Meye a cikin wannan ledar kuma? Don naga dai bada ita kikazo ba."Safna cikin fara'a tace."Kyauta Sir-Kamal yaimun."Nan Muneeba ta had'e rai ta sami waje ta zauna, Tukunna tace."Kyautar menene?."Nan Safna ta fad'a ma Muneeba komai da duk irin halaccin da yake mata."Wow! Ashe dama akwai irin ku a duniya? Marasa wayau?.""Ban gane abunda kike nufi ba!.""Yes da sannu zaki fahimta ai, To bari kiji Safna you have to shine your eyes! So yake kawai yaja ra'ayinkida irin wad'an nan abubuwan domin at the end kingaidan ya buk'aci wani abu daga gareki bazaki k'i basaba.""Yes niko insha Allah ' inhar Sir-Kamal zai buk'aci abu a wajena zan bashi, Muddin inada shi."Muneeba tab'e baki tayi gamida jan tsaki, Tace."Koda kuwa jikin ki ya buk'ata?."Nan Safna ta had'e rai tare da mik'ewa tsaye cike da tunani."A'a, Gaskiya Sir-Kamal bazai taba kasancewa hakaba Muneeba, Kinyi masa mummunar fahimta ' kuma ina rok'onki da kibar fad'amin haka domin kuwa alhakinsa kawai zaki d'auki."Tsaki Muneeba taja, A zuciyarta tace."Ai wallahi baki isa ki fini da komai ba Safna, Talaka dake ma!."Muneeba na gama ayyana hakan ta tashi fuuuu ta bar wajen.Wucewar Muneeba ne Safna ta shige cikin store ' ta duba agogon wajen taga *1:30pm*, Hakan yasa ta fara preparing had'a coffee donta bawa mutanen wajen.B'angaren Mr-Fauzan ' zaune yake da laptop a gaban shi, Amma sam hankalin shi baya kanta ' maganar Hafiz kawai ke dawo masa a rai."Hmm how can i even start this rubbishness? Yarinyar nan according to her Education bawani nisan karatu tayi ba!, So ta ina zan fara? Don ban taba jin sonta ba kokad'an."Yana cikin wannan maganar ne yaji ana knocking k'ofar."Come in!."Abinda Mr-Fauzan yace kenan, Tukunna ya maida kallonshi ga laptop d'in gaban shi.Safna ce ta shigo tare da yin sallama, Hakan yasa shi amsawa ba tare daya d'ago kai ya kalleta ba, K'arasawa ciki tayi ta aje mashi coffee d'in bisa deskgamida cewa."Gashi coffee d'in."Harta juya zata wuce ya tsaida ita da cewa."Banason insake ganin ki da wannan hijab d'in daga yau, Don zaki iya korar customers dake ziyartar company d'in nan, And ni karan kaina ma hijab d'in kyama yake bani! Muddin kinason aikin ki ya zama dole ki cenja dressing!."Safna shuru kawai tayi idonta na kallon k'asa, Sannan Mr-Fauzan ya k'ara da cewa."And look! Idan kud'in siyan kayan sawa ne bakida shi, Why not ki rok'a abaki."Jin wannan maganar ya k'ara b'atawa Safna rai batuk'a, A zuciyarta tace."Hm bana tunani zan juri wulak'ancin mutumin nan, Zan iya jure duk wani abu amma banda wulak'anci.""Ke!!."Ya kirata cikin tsawa, Hakan yasa tayi saurin d'ago kai ta kalleshi."Ok, Na fahimci matsalarki.Abunda Mr-Fauzan yace kenan, Ya mik'e tsaye ya ciro wallet d'inshi ya zaro kud'i 'yan dubu dubu ya watsoma Safna dake tsaye tana kallon shi."Ko ba kud'i kike nema ba?."Nan take idanun Safna suka ciko da hawaye, Kasa cewa komai tayi ta juya a guje ta bar office d'in tana matsanacin kuka.Safna direct ta shige store ' saida tasha kukanta ma'ishi, Sannan ta fito ta d'auki gift d'inda Sir-Kamalya bata, Harta nufi hanyar fita sai kuma ta dawo ta zarce Office d'in Sir-Kamal.Knocking tayi sau d'aya aka bata uznin shigowa, Safna ta shiga ciki ' cikin sanyin jiki ta nemi waje ta zauna."I hope dai lafiya!."Cewar Sir-Kamal."Nazo ne inyi maka sallama ' kuma inyi maka godiyada irin hallacin daka nunamun, Domin daga yau nabar aiki a k'ark'ashin wannan company d'in.""Meyasa? Akwai wanda yai maki laifi ne ko wani abu?.""Sir, Zan iya jure komai amma banda wulak'anci ' ni kuma gaskiya na gaji da wulak'ancin da mai wannanwajen kemin, Shiyasa na yanke wannan shawarar.""To! Da kika yanke wannan hukuncin ' kina da inda zaki cigaba da aiki ne?."Nan ta sunkuyar dakai ' tace."A'a banda shi, Amma zan nema aikatau inyi ' don shine daidai dani dama."Abunda Safna ta fad'a ne yayiwa Sir-Kamal ciwo sosai hakan yasa ya runtse idonshi, Domin har cikin zuciyar shi ' ya tsani mace yarinya tayi aikatau."No Safna ' karkiyi aikatau please..."Yayi maganar cikin sanyin murya.Ita kanta tayi mamaki yadda taji muryar shi ta cenja 'cikin k'ank'anin lokaci."Safna ki bari ' ni zan nema maki aiki mai nagarta, Amma kafin nan akwai school d'inda nakeson insaka ki kinji?.""Sir, Dama kabarshi amm..."Bata k'arasa ba Sir-Kamal ya tsaida ita da cewa."Shhhh… bake kika sani ba! Ninasa kaina so just let me, Yanzu idan kin tafi gida ' *Around 4:00pm* zanzo inyi magana da Mahaifiyar ki."Safna kai kawai ta d'aga mashi alaman to, Sannan ta tashi ta fita daga Office d'in.Bayan fitar ta daga company d'in ne ta sake ganin mai keke-napep d'in nan a tsaye, Hakan yasa ta k'arasa wajen."Bawan Allah! Koda yaushe kana nan ne dama?.""Eh hajiya! Ai dama aikina kenan in d'auke ki daga gida zuwa wajen aiki, Haka zalika daga wajen aiki zuwa gida.""Duk shi Ogan nawa yasaka yin haka?."Ta fad'a tana murmushi."K'warai dagaske hajiya! Yanzu ina zan kaiki?."Cewar mai na-pep."Uhm! Gida zaka kaini."Haka Safna ta shige ciki ' shima ya shiga ya tada na-pep d'in suka wuce.*®SEEMALUV NOVELS GROUP*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**24-25*Bayan tafiyar Safna ne da 'yan lokuta, Sir-Kamal ya baro Office d'inshi zuwa Office d'in Mr-Fauzan.Sir-Kamal bai kaiga k'arasawa ba ' suka had'e dashi yana fitowa daga Office d'in nasa ranshi a b'ace."Sir i want to have a conversation with you."Cewar Sir-Kamal."I don't have time now!."Mr-Fauzan ya fad'a yana k'ok'arin wucewa."Sir, It's about this lady Safna."Jin haka yasa Mr-Fauzan juyowa ya fuskanci Sir-Kamal."Ok! What is it?.""Tazo mun ne da cewa ' wai ta aje aiki, Am confuse and worried about her Sir ' Yarinyar abun a taimaka mata ne.""Confused?."Mr-Fauzan yayi tambayar, Sannan ya cigaba da cewa."Worried about her? Thank God data aje aikin, Don koda bata aje ba nizan koreta! Besides ' wannan k'azamar? Duk inda taje bazata sami aiki ba."Mr-Fauzan yana gama fad'in haka ya gyara bottles d'in suit d'inshi ya wuce.Sir-Kamal girgiza kai kawai yayi, Sannan ya juya cikin company d'in yana zagaye.*After Closing...*Sir-Kamal ya koma gida, Bayan yaci abinci ne yayi wanka ' yadawo parlor ya zauna tare da Ammi suna fira."Ammm... Ammi wallahi akwai wata yarinya da taketa fad'i tashin neman na kanta, Kuma Ammi basu da shine ' amma kuma Ammi kinsan menene?.""A'a saika fad'a.""Ammi wallahi babu wani abu tsakanina da ita ' so nake kawai na taimaka mata with all my efforts, Don ni a matsayin k'anwata na d'auke ta.A tak'aice Sir-Kamal ya fad'ama Ammi duk abunda ya faru da Safna a company."Lallai wannan yarinya abun a tausaya mata ne, To yanzu a ina zaka nema mata aikin?.""Akwai wani restaurant da nake tunanun zata iya samun aiki a wajen because akwai d'an connection da nake dashi a wajen, Amma kafin nan akwai school d'inda nakeson insaka ta mai suna *GYARA KANKI* kinsan suna wayar da 'yanmata musammanirinta, Kuma kinsan restaurant irin wannan saida wayewa ' 2weeks kawai zatayi a wannan school."Inji Sir-Kamal."Kwarai haka ne, To yanzu dai Allah ya bada sa'a kuma duk abunda ya shige maka gaba ka sanar dani.""Insha Allah Ammi, Yanzuma nakeso intashi inje gidansu domin innemi iznin yin komai wajen mahaifiyar ta.""To shikenan Kamal ' saika dawo."Sir-Kamal tashi yayi rik'e da key d'in motar shi a hannu ya fice.*** *** *** *** *** *** ***Tun lokacin da Mr-Fauzan ya dawo gida ya zarce d'akin shi kai tsaye, kasancewar babu kowa a parlor.Bayan ya watsa ruwan d'umi ne ya fito parlor daga shi sai boxer sai singlet a jikin shi.Mr-Fauzan waje ya samu yayi zamanshi gamida d'aukar remote ya kunna TV ya fara kallon news.Yana cikin kallo ne yaga wata bak'uwar fuska tazo ta zauna rik'e da cup d'in youghurt a hannun ta tana sha.Ganin sun had'a ido ne yasa ta tasowa tazo gabanshi ' tare da mik'a mashi hannu tace."Hey! Am Nafeesat but you can call me Nafee.""Who are you?."Mr-Fauzan ya tambaya ' ba tare da ya bata hannu ba.Ganin haka yasa Nafee komawa ta zauna ' gamida aje cup d'inda ke hannun ta a side table, Tace."Well, Am your wife to be! Fauzan.""What!!!?.""Yes, Fauzan."*Wacece Nafee?* Nafee kyakkyawar macece ' fara ce slimly in structure, Ta gama karatunta na jami'a since last year!.Mr-Fauzan harya tashi zaije wajen Mummy ' ya had'e da ita tana saukowa zata k'araso parlon."A'a koma ka zauna, Dama kai nake jira."Cewar Mummy.Mr-Fauzan komawa yayi ya zauna ' tukunna Mummy itama
ta zauna."Nasan zakaita tambayar kanka wacece wannan!."Tayi mashi nuni da Nafee, Sannan Mummy tacigaba da cewa.."Sunanta Nafeesat, 'yar k'awata ce musamman nacea kawomin ita tazo taimin 2weeks, Saboda ku fahimci junan ku.""But Mummy na fad'a miki fa!.""Look! Wannan ita ce shawarar dana yanke , kuma ko kanaso ko baka so auren nan sai anyi shi."Cewar Mummy."Mummy please nifa ba yaro bane! Yakamata a barni inzab'a wacce nakeso.""Da sannu zaka fara sonta!."Mr-Fauzan tashi yayi yabar parlon zuwa garden d'inshi, Nan ya tsaya yana dogon tunani."Ina ganin shawarar Hafiz zanbi ' koma ta yayane dai ni bazan auri wannan yarinyar mai kama da second hand ba."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya juya ya koma cikin gida domin kiran Hafiz a waya.Harya shige parlor suka had'e da khairat ta dawo daga school, Mr-Fauzan wristwatch d'in hannun shi ya kalla yaga *4:00pm*."Ke sai yanzu ne kike dawowa?.""Eh Yaya Fauzan ' lectures!."Ta fad'a a tak'aice sannan ta k'arasa ciki a gajiye ' shima