Showing 21001 words to 24000 words out of 35734 words
bude idon. Hafsi ce zaune a kasa kusa dashi. Tayi yar ajiyar zuciya. Junaid, bata taba kiran sunansa ba sai yau shiyasa yaji wani dadi. Sai ya wayance. Ke mijin naki kike kira haka ba ko yar alkunya irin na matan hausawa. Komai bacin rai baya rabo da wasa. Kafin tayi magana yace kina hararata fa zan...sai ya kashe mata ido daya tsire miki ido zanyi. Ai kayi kama da mugaye dama. Ya mike tsaye ni din? Ashe baki da ta ido yar nan. Yadda ya rike haba yasa tayi dariya. Duk da yana tare da damuwa ya koyawa kansa hakuri. Har yana tsokanarta. Wani serious look ta gani a tare dashi. Yace Hafsi Hafsi why are u being nice to me? Ta dan kalle shi, saboda i believe you. Bangane ba ya fada cikin rashin fahimta. Bazan miki karya ba nasan Tilly kuma cikin jikinta maybe nawa ne. Na sani ta bashi amsa. Na dai yarda ba...ba raping dinta kayi ba. Tana gama magana ta mike zata gudu.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐29
Hannun kofar ta kama amma saboda yadda take hanzarin fita sai ta kasa budewa. Hijab din ma saboda karar jan kofar da Nafisa tayi a baibai ta saka shi. Duk abinda take idanunta na kansa don tsoro take kada ya karaso inda take. Wani irin kallo ya rinka yi mata ko kifta ido baya son yi. A hankali taga yana matsowa inda take. Cikinta har wani sauti yake bayarwa saboda yadda ta kideme. Da kyar ta iya cewa nifa bana son kallo. Bai dakata ba da tafiyar sai da yazo gabanta. Da zaa taba kirjinta sai anji bugun zuciyarta da sauri da sauri. hannunta ya kama ya jawota ciki ya zaunar da ita kan kujerar gaban dressing mirror. Ji yadda jikinki ke bari kamar kinga wani dodo ko irin kinzo yi min sata na kama ki. Yadda yake maganar ne ya sata dan guntun murmushin yake. Shiru tayi tana tsoron kada Hajiya ko Mommy wani cikinsu ya shigo dakin tunda suna shigowar kullum. Ganin yana neman cire mata hijab ta fara kokawar rikewa. Ya kalleta ya sha kunu wai ni da jikina ki rinka rufe min. sai anyi magana ki rinka wani abu kamar wata malama. Ta zumburo masa baki, to yanzu me kake so ayi. Da faraarsa yace ki cire na gyara miki gashinki ko baki ji me Sis ta fada ba. Tayi masa fari da ido ai da ka sani salon ka bude sai ka rinka gyaran gashi. Gaba daya ta ruda shi da yadda tayi masa fari da ido har ya kasa magana. Tana ta surutu ita daya sai gani tayi yana kici kicin cire mata hijab. Ihu ta fara masa wallahi idan ka matso zan bude murya. Ganin duk a tsorace take yayi dariya duk wanda ya shigo taimakonki sai ya tayani cire miki hijab din, bari ma na kulle kofar kinsan leke dakin newly weds hatsari ne. Yana zuwa bakin kofar duk cikinta ya gama durar ruwa sai kawai taga zai fita daga dakin...take care Hafsi Hafsi. Murmushi ta sami kanta da yi bayan ya kulle kofar ta fada gado ta kwanta.
Hajiyan dangi suka gani a dakin Mommy suna ta hira. Suna zama Mommy tace dama jira nake ki fito Nafisa. Lafiya dai ko Mommy? Ta tambayeta. Eh to wannan makociyar taki nurse nake son ki kira tazo gida tayiwa yarinyar can test a tabbatar da cikin. Hamida tace Mommy ana yin scanning fa dashi ake fadar EDD. Nafisa ta buge mata baki to banza wa ya fada miki we are intrested muji lokacin haihuwar. Hajiya tace kunga ni ku nutsu idan kinje gida ki fada mata ko zuwa gobe ne sai kuzo tare. Amma abinda Hamida ta fada gaskiya ne. Idan anyi mata gwajin sai ayi scaning din. Nafisa ta mike bari naje na fada musu don su zauna cikin shiri.
Hafsi tana fitowa zata dakin Mommy ta ga Nafisa tana dawowa daga dakinsu Tilly. Hannunta Nafisa taja suka shiga wani karamin falo. Suna zama Nafisa ta ce Hafsi what do you think of Junaid? Kasa ta sunkuyar da kanta. Tana jin nauyin Nafisa sosai don ma ita din tana da wayewa ta iya jan mutane a jiki. Ta dan taba ma Hafsi kafada ina jinki kanwata. Jin ta sake yin shiru tace nasan Junaid ya taba rayuwa mara kyau irin ta 'ya'yan masu kudi marasa kwaba amma duk irin halayensa he is not a rapist. Kuma a irin ji da kansa na da fa banda yanzu, bazai kula mai kati ba. Ko da wasa bamuyi tunanin zaiyi aure ba nan kusa amma sai gashi yana ganinki ya canja sosai. Banda degree yana da masters har biyu amma yaki aiki sai kashe kudi. Sai gashi jiya Alhajinmu yace yayi masa maganar yana son fara aiki. Hannayen Hafsi ta kama ki daure ki zauna dashi don Allah na tabbatar he will be a better person. Ganin Nafisa na hawaye Hafsi ta suma kuka itama. Cikin kukan ta fadawa Nafisa abinda taji daga dakinsu Tilly. Murnar Nafisa har zuci tace kada ki fadawa kowa da sannu asirinsu zai tonu. Scanning zan kaita shegiya gayyar tsiya. Har suna da guts din shigowa gidan nan. daga nan suka zauna suna tattauna yadda zasuyi karshe Nafisa tace idan kin amince zanyi magana a kaiki wurin mijinki. Dammmm zuciyarta tayi don tsoro.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐30
Washegari gari da safe Nafisa tazo da Mariya nurse. Ita tayi musu jagora zuwa dakin su Tilly. Senator Rufai tun da suka zo gidan zama ya gagare shi ko kadan baya kaunar haduwa dasu gashi bazai iya korarsu ba har sai sunga yadda al'amarin zai kasance.
Tun daren dama Tilly ta gama tsorata Rosie tace ki kwantar da hankalinki nifa abu irin wannan baya tsorata ni. Zamu sami mafita cikin ruwan sanyi. Ko da su Nafisa suka shiga dakin a kwance suka tarar da Tilly , Rosie tana rirriketa tana ta amai. Laulayi dai kamar gaske. Nafisa ta kawar da kai gefe dama bata sanar da Mariya ainihin alaqarsu ba. Ita ko sunansu ma bata sani ba. Ta yi mata kallon banza ki tashi za'ayi miki test. Rosie ta yi kalar tausayi to bari na taimaka mata ta gyara jikinta. Mariya tace ai fitsari kawai nake bukata ma idan kun shiga ga wannan robar ta mika mata irin sample bottle din asibiti sai ku kawo min a ciki. Kadan ma ya isa. Nafisa tace kiyi mata na jini kawai ance yafi nunawa. Nan da nan suka hada ido a tsorace. Tilly ta fara hawaye don Allah kuyi hakuri bana son allura. Nafisa tace ke da zaki haihu meye abin tsoro a allura. Mariya tace ki bari kawai muyi na fitsarin idan bai zama clear ba sai na debi jinin. Rosie ce ta kamata tana tafiya a hankali har suka shiga toilet suka rufo kofar. Tilly ta gyara jikinta tana tsaki ta sassauta murya kinji waccan yarinyar wai blood test? Idan ta shiga hurumi na bazan mata ta dadi ba. Rosie ta rufe mata baki sai an ji mu. Ungo ni ta mika mata robar data cika taf da fitsari. Kamar ta rike kashi haka Tilly ta karba ta fito ta ajiye a gaban Mariya.
Duk suna kallo ta saka PT strip din a cikin robar ta fito dashi ya nuna layi biyu alamun ciki. Mariya tace ai kinga ma Nafisa ya nuna basai munyi na jinin ba. Nafisa a ranta tayi kwafa dama tunda suka shiga toilet tare tasan akwai abinda zasuyi. Ta kalleta harda dan guntun murmushi sannu Allah Ya raba lafiya. Yanzu gobe zan kaiki asibitin da nake zuwa sai ayi miki ultrasound gara mu gani kila ma biyu ne babies din. Nafisa dai dariyar da take harda ta mugunta suka fice ita da nurse.
Suna rufo kofar Tilly tace na shiga uku ya zanyi ne Rosie gobe asirina zai tuno. Kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Wannan yar kwailar matar tasa zamu kullawa. Idan zai aureki ai gara ki zauna ba kishiya muci karenmu ba babbaka Talatu. Suka tafa sannan tace akwai dan taimako daga wurin malam fa sunansa makalemata. Idan lokaci yayi zan baki ki yi amfani dashi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐32
Wani irin radadi ne ya ziyarci kafafunta duka biyun ta runtse ido ko motsi ta kasa yi saboda duk wurin pieces din glass ne. Tilly kuwa kwanciya tayi wanwar a kasa tana kwarma wayyo cikina, wayyo ta kashe min da na shiga uku. Rosie tace kiyi hakuri Talatu ki mike tsaye. Hafsi ta kallesu tana cewa sannu amma duk kafafunta sun kone saboda zafin abincin harda cikinta don karamin mayafi ta yafa sanin cewa babu ma aikata maza da ake bari su shigo cikin gidan. Ga plate din da ya tarwatse wasu duk sun soke mata saman kafafunta. Duk da haka bata damu ba ta duka tana son taya Rosie ta daga Tilly tsaye. Hannunta taji Tilly ta make tana kara sautin murya. Muguwa azzaluma don kawai ina da cikin mijinki shine kike son zubar min dashi. Wallahi duk abinda ya sami dana kotu ce zata raba mu. talakar banza.
Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi. Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy kuwa ta make hannun karki sake nuna min yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su koma falo ayi maganar.
Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira mata Junaid yazo ya kaita asibiti.
Da fara'arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti. Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai ka tambayi matarka da take son zubar wa Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana wani zancen daban. Ka dauko key mukai yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta. Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo? Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata tambayoyi.
Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da security don kada su zama su kadai. A motar Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta zuba masa 'ya'ya tunda su yake so. Hajiyan dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta yafa wani karin zafin a cikin.
Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan.
Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT??? Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba ya nuna masa yadda zai shafa ya fita.
Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan. Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina. Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi yace ba komai. Allah Yayi mana jagora.
Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki. Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana shike maganin zomon bana.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐31
Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare. Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su Hamida su tambayeta irin kalar motar da take so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci na naje har gida muyi magana da babanta.
Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba, Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin damuwar maganar cikin nan. Tana dan tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda take tambayar zuciyarta kenan.
Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu. Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai dami iyayen nasa akan a bashi matarsa ba. Itama yana jin nauyinta sosai a ransa. Ina amfanin badi ba rai? Karamar yarinya tana masa kwarjini saboda ya zubar da girmansa a waje. Ga su Rosie sunyi kane kane a gidansu. Fasa shiga gidan nasa yayi ya koma main house. Mai aikatan gidan suna ta gaishe shi ya haye sama da sauri. Addua yake kada kowa ya ganshi a hanyarsa ta zuwa dakin Hafsi.
Rub da ciki tayi tana karanta wani littafin tarihin Annabawa da Hajiya ta bata taji an bude kofar. Duk a zatonta Nafisa ce tayi saurin juyuwa babbar yaya ina ta jiranki tun dazu yau bani da....kallon da yake mata bayan ta juyu yasa tayi shiru. Ya zaka shigo min ba sallama? Ni da dakin matata har sai nayi sallama? Ya kara kallonta ita duk kayan jikinta suna mata kyau. Dinkin yau ma riga da skirt ne fitted sunyi mata kyau sosai abinka da yar Mama tela. Ya jawo kujerar dressing mirror banda gulma duk wannan kwalliyar kice babbar yaya kike jira? Fada min gaskiya dai ni kika yiwa wannan kwalliyar ko. Bargo ta jawo ta rufe jikinta da sauri ni ba kai nayiwa ba. Kan gadon ya dawo ya zauna a gefenta ya rage murya are you sure? Har fa zuwa kika yi bakin window don na ganki kuma na gani. Daga cikin bargon tace ni Allah ba kai nayiwa ba. Ji tayi kamar ya tashi daga kan gadon sai dai kuma har fuskarta ta rufe yace malaiku na jinki kina cewa yar miji kika yiwa kwalliya ba shi ba. Yau littafinki sai cika da rubutu amma fa daga na hagun. Muryar nan ta shagwaba ta fara yi ni ba haka nake nufi ba...kafin ta karasa magana taji ya daga bargon daga wurin kafafunta ya shigo ciki. Hannuwansa yasa ya danne duka sides din don kada ta bude. Tuni idanunta suka raina fata, they were so close suna shakar numfashin juna. Ya kashe mata ido daya ina jinki wa ma kika yiwa wannan kwalliyar? Ki fadi abinda nake son ji sai na fita salin alin. Kanta a kasa tace kai. Malama ni banji ba fa. Ta sake cewa kai a hankali. Bari na sake matsowa kusa kila zanfi ji. Da karfi tace kai nayiwa. Good girl to ki dan bani chance mana na yaba kwalliyar. Bata ankara ba taji ya janyota ya rungume. Yana shafa mata gashi a hankali. Wata ajiyar zuciya yayi Hafsi Hafsi ki tayani addua yau nayi interview har biyu ta neman aiki. Nasan nayi laifi da yawa shiyasa su Mommy basu da time dina amma don Allah zaki zama friend dina kuma special adviser dina. Dago kanta tayi tayi masa murmushi eh. Thank you so much. Ya mike yau