Showing 27001 words to 30000 words out of 35734 words

Chapter 10 - TUN KAFIN AURE

09 Nov 2024

3654

Tun tana sharewa har ta kasa hakuri. Lekowa tayi wajen gidan babu daya daga cikin motocin da yake shiga. Komawa tayi ta zauna tana ta sake sake. Gajiya tayi ta tashi tayi sallar isha da nafila ta zauna kan darduma tana karatu.
Hotel ya kama musu don yasan babu mai bashi mukullan gidan da Alhaji ya kama masa kafin ayi masa wani ginin inda zai iya hada matan biyu. Tilly ansha gyara ciki da waje. Ta nuna masa salo salo na kwarewarta a fanin shegantaka. Wayarsa ce tayi kara wurin shadayan dare. Har ya fara bacci Tilly ta dauka taga ansa H dear. Kashe wayar tayi gaba daya tayi tsaki sannan da dariyar mugunta. Yarinya yau zaki bushe ta fada a fili..
Saroro ta tsaya kallon wayar. Yanzu ita Junaid ya kashewa waya? Ko tayi masa laifi ne? A falo ta kwana ranar tana kuka ita wannan wace irin rayuwa ce daga wannan sai wannan kullum. Ta yanke shawarar idan bai dawo ba da safe zata sanar da iyayensa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐37
Hafsi da Ummati sun kusa rabin awa a waya suna ta shawarwari don yanzu kam Hafsi tasan bazata iya zama haka babu abokin shawara ba duk da cewa su Hamida suna iya kokarinsu. Yayarta Hadiza ma ta bugu sun dade suna magana. Tana wayar Nafisa ta shigo da wata karamar jaka a hannunta ta zauna kan kujera. Hafsi ta gama waya suka gaisa. Nafisa tace kanwata kinga yadda Allah Yake ta jarrabar mu da abubuwa kullum ko? Yauma hakuri dai zan kara baki. Da yar shawara kadan. Kinga wadanan kayan masu tsada ne amma fa idan kika sha baza ayi asarar kudin tara ba. Suna gyara mace sosai sannan ki rika shan fruits musamman kankana. Akwai kunun aya ma da ake hadawa da ita da cucumber, dabino, kaninfari, citta da kwakwa. Zan hada miki da kaina kafin anjima. Munyi magana da Mommy ke zaki fara tarewa sannan bayan sati daya talatu ta tare amma gidanta daban ne. Kiyi iya kokarinki ki zama tamkar karuwa kema a wurin mijinki kinga ya san wasu matan so raba shi da irinsu sai kin dage sosai. Kan Hafsi a kasa duk kunya ta kamata ta kasa magana. Nafisa ta nuna mata yadda zata yi amfani da kayan data kawo mata. Ke ni ki dena jin kunyata bazan taba bari matan banza su rabaki da mijinki ba. Tunda kika auri Junaid kin gama mana komai.
Talatu yar gidan Mal Jibo mai faskare amaryar Junaidu dan sanata. Kirari ne Rosie da ke zaune kan kujera take wa aminiyarta. Tilly tace yanzu fa dole inyi ta amsa sunan Talatu sunan dana manta dashi tun a kauye. Suka tafa sanan rosie ta miko mata kullin magani. Ga wanan kawata ki shafa hannu ne ki taba shegen. Wallahi zaki sha mamaki don watarana ma sai ya gundireki idan ya fara like miki. Wata shewa suka yi tace Rosie ba kyau. Gara tun wuri na fara kiranki Samiranki kada ayi subutar baki a gaban surukai. Hakane, yanzu dai zan kira shi yazo a sunan kina zubar da jini sai ki fara gwada saarki. Bikin ma da akace muyi a garinmu zasu sha mamaki don sai munyi kara'i. Sake tafawa sukayi sannan Tilly wadanda sun koma dakin da Rosie ta kama musu ta dauki waya ta kira shi.
Tun safe ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tsananin farinciki yau Hafsin sa zata tare. Ya fito daga wanka yaji karar waya a zatonsa ma Hafsi ce don tun dare take tsokanarshi da flashing. Tsaki yayi kamar tana gabansa daya ga number din Tilly. Yana dauka Rosie ra kwarma ihu tace yazo Tilly tana ta zubar da jini. Wani tsakin yayi ya ajiye wayar ya cigaba da shiryawa. Sake buguwa suka yi har sau biyar sannan ya dauko a wulakance yace gani nan zuwa. Cikin gidansu ya shigo ya fadawa Mommy inda zashi. Ta tabe baki sai ka dawo. Kada dai ka dade yace to. Shi har a ce masa kada ya dade yadda yake zumudin nan.
Suna jin tsayuwar motarsa Tilly ta kwanta a kasa tana wai wai. Kudi ya jefa mata yana mata kallon banza gashi nan nasan abinda kike nema kenan. Ganin bashi da niyar taimaka mata ta tashi ta mike ta riko shi. Juni boy ka saki jikinka mana ai an riga an daura. Ina jiranka anjima kazo mu tafi namu gidan don a sannu zansa ka manta wannan kwailar. Hankadeta yayi har ta fadi kamar zaiyi magana ya fasa ya fice. Rosie dake kitchen ta fito da sauri tana mata sannu. Tilly tace aikin banza maganin naki baya komai ji yadda ya ture ni.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐39
Wani azababben ciwon kai ta farka dashi lokacin da taji bugun kofa. Sai bayan asuba bacci ya sace ta, dan goge fuska tayi ta bude kofar. Amaka ce dauke da tray ga wani a kasa shima duk kwanukan abinci ne a ciki. Tace Amariya goodmorning...Hafsi ta dan saki fuska ta amsa tare da daukar tray din kasan suka shigo dashi. Amaka tace Madam say make you tell me wetin you wan chop for lunch. Hafsi tace what? Ita fa bajin pidgin english take ba. Ta dai gane lunch ta ce mata ta tafi kawai zata shigo. Har shabiyu tana jira ganin dai bashi da niyar dawowa gashi wayoyinsa duk ta kasa samu ta fito ta tafi main house. Babu kowa a falon sai akwatuna guda uku daga bakin kujera. Dakin Hajiya ta fara leqawa ta ganta tana daura laffaya. A'a mamana keda kike amarya me ya fito dake kuma. Nima shirin komawa Kano nake yi yanzu Rufai nake jira yazo muyi sallama sai a kaini iyaport. Hafsi tayi dan murmushi tace Hajiya bana son ki tafi. Allah sarki Mamana bakya so naje na gyara nawa auren ne? Tare fa aka kawo mu dake gashi muna neman wata daya. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata Hajiya a rude tace haba Hafsatu kada ki karyar min da zuciya mana. Ki kara hakuri in Allah Ya yarda zaku sami zaman lafiya da Junaidu. Kirawo min shi mu yi sallama sannan ki goge idonki kada yace na taba masa mata. Kanta a kasa tace baya nan Hajiya. Dan bata rai tayi ina yaje kuma daga kai masa amarya. Mummy dake tsaye a bakin kofa tace garin yaya kika bari ya fita amarsu. Har kasa ta kai ta gaishe da mummy sannan soma kuka. Duk hankalinsu ya tashi aka suna tambayarta ko lafiya. Da kyar tace musu bai kwana a gida ba. Sai suka fara salati. Mummy ta dauki waya ta kira shi aka yi sa'a a kunne wayar take.
Tilly ta kalli wayar bari na daukar maka Juni boy. Kasan yau rana ta ce so duk mai kira yayi hakuri. Ba musu ya mika mata batare da yasan mai kiran ba. Hello ta fada bayan ta amsa wayar. Mummy a dan razane tace wacece? Ahhh tuni ta gane muryar jarababbiyar babar tashi. Tace matarsa ce Talatu don Allah a dena kira yana bacci ne idan da sako ki fada na gaya masa. Yadda take maganar a ladabce shi yasa Junaid ta kara lafewa jikinta yana mata cakulkuli please ki ajiye wayar anjima na kira. Karaf maganar sai a kunnen mummy tace Junaid da karfi. Tilly bata bare yaji ba ta ajiye wayar ba tare da ta kashe ba tana ta dariya please baby ka bari kaga jiya baka barni na runtsa ba.
Jefa mummy tayi da wayarta tana kuka mai tsuma zuciya. Maganar Junaid ta tabbata karuwa ce yarinyar nan. Suna tare bansan ko a ina ba amma suna tare. Hajiya tace inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Anya zan iya komawa kano kuwa salma? Yarona yana cikin matsala. Mummy tace ki tafi hajiya ai tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai daka. Rashin jin maganar iyaye yasa ya kwaso mana balai. Bari na tado Yallabai wallahi a nemarwa yarinyar nan saki tun wuri. Ni bazan iya kallon Safiya ba ina kallo dana yana wulakanta musu 'ya.
Tunda suka fara magana Hafsi ke kuka Mummy ta jawota ta rungume. A haka senator Rufai ya samesu. Bayan anyi masa bayanin abinda ke faruwa yace su kwantar da hankalinsu zaisa a nemo shi duk inda yake a kasar.
Wasa wasa sai da suka yi sati biyu a hotel suna shan soyayya. Hutu ya ratsa su da kyau don daga ci sai kwanciya. Ko kadan baya son Tilly amma ji yake idan ya rabu da ita komai na iya faruwa. Kashe mata kudi yake kamar hauka tana karbewa. Rosie master planner ma an manta da ita .A rana ta shabiyar Senator yasa aka yi freezing dukkanin accounts din Junaid. Matsayinsa yasa har aka nuna masa statement of account din dan nasa. Ba karamin barnar kudi yayi ba a iya kwanakin da baya gida. Senator Rufai ya shiga rudani sosai yadda junaid yake neman kara lalacewa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐41
Dakinsa ya shiga ya lalube duk wuraren ajiyarsa ya dauko kudi masu yawa. Yana zuwa wurin parking yaga convoy din Alhajinsu dole ya tsaya suka gaisa zai fita. Senator Rufai bai nuna damuwa ba yace Junaid kafin ka tafi ina son ganinka. Tsaki yayi wanda har uban yaji sautinsa. Tilly ta kira shi ya kai sau ashirin kada yaje taki binsa ko yau ta hana shi kusantar ta.
Yana zaune gaban iyayensa Alhaji ya fara masa nasiha mai tsuma jikin mai imani. Mummy ce ta fara lura da yadda hankalinsa ko kadan baya tare dasu. Duk zancen senator ta bayan kunnensa yake bi. Tana kara kiran wayar yace Alhaji bari nake yanzu dai matata ce so don Allah ku dena daga hankali idan baku ganni ba. Mummy tace Kana da hankali kuwa Junaid ? Bai amsa ba ya mike mummy ba nisa zanyi ba ga keys din gidan ashe suna dakina can zamu zauna. Fita yayi ko waige babu. Ba mummy ba hatta senator yau idanunsa sun kawo ruwa. Ashe da gaske ne idan mutum baya tsarkake dukiyarsa yaran da aka ciyar da ita albarkarsu tana tawaya? Allah Ya dora masa son Junaid har baya son laifinsa. Gashi yau dukiya da dansa sun zame masa silar rashin kwanciyar hankali. Kullum tunaninsa baya wuce kada dansa ya jawo masa abin kunya saboda shi dan siyasa ne. Daga yau zai guji abin kunya saboda shi musulmi ne. Haka suka yi ta saka da warwara kafin daga karshe Senator ya yanke shawarar su dage da addua har Allah Ya kawo musu mafita.
Duk yadda take kokarin boyewa kana ganin Hafsi kasan bata da nutsuwa da kwanciyar hankali. Son Junaid take sosai gashi tana missing din irin wasannin da suke na tsokana. Wataninta biyu a gidan Nafisa hakan ya zama wata uku rabonta da Junaid. Iyakar alkhairi tana samu wurin iyayen wanda bai damu da ita ba. Senator ya siyawa babanta mota ya canja musu gida. Duk sai da aka hada da ban baki Mal Aminu ya karba. Itama Hafsi dubu hamsin ta bawa Ummati saboda bikinta saura wata biyu.
Hafsi da Hamida suna zaune tana ta yiwa hamida tsiyar ciki Nafisa ta shigo falon da faraa. Big sis ta samu ne hamida ta tambaya. Kwarai kuwa yanzu Alhaji ya ce muje ayiwa Hafsi passport dukkanmu zamu umra. Farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskarta. tana ta godiya ga Allah. Ta samu damar zuwa yin addua sosai game da Junaid.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐40
Maaikan daya daga cikin bankunan da Junaid ke ajiya bisa umarnin senator Rufai suka gano masa atm machine din da yake amfani dasu wurin cire kudi. Duk a area daya ne hakan ya bashi tabbacin Junaid yana garin Abuja a sheraton hotel don shi yafi kusa da wurin atm din. Ba tare da ya sanar da iyalinsa ba ya tura ayi masa bincike a hotel din da ma wasu wuraren shakatawar dake kusa da wurin. Cikin ikon Allah bayan kamar awa biyu da tafiyar yan aikin aka kira Senator aka sanar dashi Junaid yana sheraton din harda room number aka bashi.
Damuwa da bakin ciki sunsa hafsi wata irin rama. Bata cin abinci sai abu mai ruwa ruwa. Kullum hakuri kawai suke bata. Karshe Nafisa tace gara ta tafi d ita gidanta saboda ta rage kadaici. Haka ta hada kaya suka tafi. A cän kano yaya hadiza ce kawai tasan abinda ke faruwa ita ma nafisa ce ta sanar da ita. Hadizan ce ta hana a fadawa iyayensu tace zata zo garin karshen wata idan maigidanta zaizo conference don haka kawai idan ta tafi baffa fada zaiyi yace Hafsi bata dade ba baya son yawo. A gidan nafisa ita da yaranta koda yaushe suna tare da Hafsi. Hatta abinci tare suke ci shiyasa bata da lokacin tunani da kuka sai ta shiga daki kwanciya.
Kwanaki biyu bayan an yi freezing account dinsa yaje atm ya dawo ya dubi Tilly dake rawa a tsakar daki. Naje atm fa duk machine din yayi rejecting dinsu. Ta rage sautin kidan tare da hade rai me kake nufi to? Ka duba a na wasu areas din mana. Ya zauna bakin gado naje wuri biyar fa. To ai sai kaje banki don yau dole sai ka biya ni. Hannunta ya kama ya zaunar da ita. Haba Tilly bafa call girl kike ba. Yanzu aurenki nake so banga dalilin biyanki ba duk kwana. Ki bari gobe naje na karbo keys din gidan sai mu koma can. Na gama gajiya da abincin hotel ga rashin abinyi. Hararsa tayi sai yaji gabansa ya fadi....Hafsi ce mai yawan yi masa irin wannan kallon. Ko sau daya baiyi mata waya ba gashi har yayi sati uku rabon da ya ganta. Tace kai malam dakata min, kudi fa sai ka bani ka tashi kaje banki kawai. Ya sauke murya kinga tym fa tilly gashi yau friday dole sai monday zan iya zuwa. Amma ina da cash a gida if you cant wait. Da yake akwai ta da hadama tace jeka ka dawo ina jira. Zan fita nima kafin ka dawo.
A kwance ta tarar da Rosie tayi amai har ta gaji. wani matsatsten wando tasa da karamar riga sai dan karamin mayafi shaidar ita musulma ce. Gidan duk yayi kura saboda sanyi ita kanta Rosie duk ta rame tayi baki. Abinka da hasken bleaching. Lafiya Rosie me zan gani haka tana magana tana toshe hanci. Cikin kuka tace Tilly da kina duniyar nan? Kwana nawa babu ke babu labarinki ko wayata ba kya dauka. Irin sakayyar da zaki min kenan? Na gama kashe kudi na tas a kanki duniya ta samu kin sani a shara. Tilly ta zauna can gefe. Yi hakuri bana son juni ya zargeni ne. Me ya sameki? Yunwa Tilly yunwa. Gashi na kasa girki saboda rashin kuzari. Tilly ta kalli cikin da ya fito sosai ko don rosie ta rame ne oho. Su shege manya ashe ana nan baa rabu ba. Ai na dauka tuni kin koma harka. Maganar ta sosa ran rosie sai ta dake dai. Me nema dole yayi hakuri. Wata yarinya mai sayar da plantain Tilly ta samu kusa dasu ta gyara gidan ita kuma tayi abinci. Bayan Rosie ta dan dawo hayyacinta Tilly tace na fa shiga problem kawata. Maganin nan kamar ya fara loosing effect dinsa. Kinga yau motsi kadan sai yace zashi gida to gudun kada naji a jikina na bari ya tafi. Idan akwai sauran sa ki bani. Cikin takaici ta kalli Tilly, lallai samun duniyar dan tsako. Dama nasan dole ce ta kawo ki wurina. To bani dashi ki koma halinki ya zaunar dake. Tilly ta mike aikin banza biyanki fa zanyi. Nan ta jefi rosie da kudi gashi nan dubu hamsin ne. Karyarki tilly har kin isa ki wulakanta ni. Har kin manta duk abinda nayi miki a rayuwa? Idan kika ci amanata Tilly nima zanci taki. Tilly ta ja tsaki da wannan kayan a gabanki...to naji duka sai nasan kina yi. Haka suka yi ta fada kafin da kansu su sauko don tilly bata da niyar barin gidan ba biyan bukata.
a firgice ya shigo gidan Mummy har tsoro taji. Junaid dama kana nan? Baka neman iyayenka da matarka. Ya gaisheta ta kau da kai lallai yaron nan bama ka da kunya. Yace mummy kiyi hakuri. Ina oldman? Baki ta bude oldman kuma Junaid? Hala abin ya naka ya dawo. To bari kaji in fada maka wannan iskancin bazan sake dauka ba. Yace kiyi hakuri mummy Alhaji nake nufi. Ina dayar to? Dama ita yake son tambaya amma ya kasa. Ban sani ba ta bashi amsa tare da mikewa ta haye sama. Tana hawa ta kira Bulus maigadi tace kada ya bari kowa ya fita sai Alhaji ya dawo.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐42
Sau uku tana katse wayar tare da yin tsaki. Ya kalleta fuskar nan babu fara'a. Ya rasa dalilin zamansa da ita don ko kadan baya sonta. Bashi da sukuni indai ba kusantarta yayi ba shiyasa take gara shi sosai. Parties kala kala yake dawowa ya tarar ta shirya a gidan samari da yan mata su taru su hole. Idan yayi magana kuwa ranar sai ya kusa kuka zata bashi hakkinsa. Yana dai zuwa gaida iyayensa idan ta gadama amma zancen Hafsi tace ko zuci yayi zata sani kuma tayi rantsuwa ranar sai dai hawayensa su kare bazata bashi kanta ba.
Kallon wayar yayi waye ke kiranki? Mtsw rosie ce duk ta dame ni tana son na taimaka mata da kudi. Ina wanda na baki last week baki bata bane? Ta kara yin tsaki kasan gayyar tsiya na rasa me take da kudin. Yace to bari idan na fita zan kawo ki bata. A ranta tace kyayi kya gama bazan bayar ba don yanzu kam yadda yake yawan hade mata rai tasan magani ya fara ja baya kuma da kunya ta koma gidan rosie. Wata biyu rabon da taje kudin da take karba ma account dinta yake shigewa..
Rosie ta kalli wayarta da katon cikin dake gabanta. Kudin abinci ma yanzu gagararta yake amma Tilly taki taimakonta. Gidan da ta tare ma bata sani ba bare tabi sawu. Shawara daya ta yanke ta neme malaminta a warware abinda takewa Junaid ya dawo hayyacinsa ya koreta.
A kasa mai tsarki hafsi da sauran iyalan senator Rufai Bukar sun dage da yawan sallah da adduoi don nemarwa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login