Showing 18001 words to 21000 words out of 35734 words

Chapter 7 - TUN KAFIN AURE

09 Nov 2024

3657

ido.
Suna idar da sallar magriba akace Hafsi ta shiga wanka. Komai na toilet din daban yake...oh su Hafsi a toilet din matar sanata. Tana fitowa Hajiyan dangi ta tarar suna hira da mommy sai ta kasa fitowa. Hadiza da Nafisa wadanda tuni jininsu ya hadu kamar sun dade tare suka fara mata dariya. To yan nema da girmanku kuna tsokanarta ko. Fito kinji Mamana ni da nake so nan da yan watanni nazo yi miki wankan jego. Ai Hafsi ji tayi kamar ta nutse a kasa Mommy tace Hajiya banda kwacen 'ya fa. Fita suka yi aka hau shirin amarya. Kwalliyar yau tafi ta sauran events din. Suna gamawa kowacce ta dau ado jiki da fuska aka fito. Motar da tafi kowacce kyau daga tsakiya wani abokin Junaid ya bude mata kofa ta shiga ya rufe. Taso kwarai Ummati ta shigo sai kawai taga angon nata ya bude kofa ya shigo. Ko tari bata yi ba don ganin yadda yake mata wani irin kallo. Ganin abin yayi yawa tace ya dai? Kamar ya, ya bata amsa. Ta dan turo baki kallo dai idan yayi yawa kuma zai shiga babin haramun. Yayi yar dariya Hafsi Hafsi kenan malaman karya. Wa ya fada miki kallon miji ga matarsa yana ciki. Yadda tayi da bakinta yasan sarai murguda masa shi zata yi. Yarinyar nan akwai tsiwa. Yace to basai kin murguda min baki ba idan kina son kiss, you just need to ask. Sakin baki tayi tana kallonsa lallai ma mutumin nan..dole ta fasa ta kara hararsa. Yayi dariya sannan yace karamar mara kunya kawai.Hular kansa yasa ya rufe fuskarsa. Idan mun isa ki tasheni jiya banyi baccin kirki ba. Ko kula shi bata yi ba ta juyu tana kallon garin da bata taba tunanin zuwansa ba nan kusa.
Nicon Hilton suka shiga. Manyan mutane da dama sun halarci taron. Su mommy ma da sauran matan manya sunzo amma shadaya suka koma gida. Sai wurin shabiyu da kwata mommy tayi wa Junaid waya kan su taho gida haka saboda Hafsi da suka yi zaman mota.
Ummati da Hafsi suna ta hira kafin motar da zasu shiga su karaso gabansu idon Hafsi yakai kanta. Tabbas matar da tazo wurin dinner dinsu ta kano ce. Matsowa tayi gaban Hafsi tana tafiya duk jikinta na girgiza amarya mun sake haduwa ko. Ga naki gift din nasan Juni boy da rowa baiyi sharing nashi dake ba. Wai wacece matar nan ne ta tambayi kanta? Tana mika hannu zata karba Junaid ya doke hannun. Da bomb ne ma haka zaki karba ko ya fada yana zare mata idanu. Mota na tsayawa yaja hannunta ya tura ta ya kalli ummati kema shiga zan biyo abokina. Yana rufe musu motar kafin su fara tafiya Hafsi taji yace cikin daga murya what the hell do you want? Suna tafiya a zuciyarta Hafsi ta kara yarda akwai wata a kasa tsakanin Junaid da yarinyar nan.
Ka zama uba ga abinda ke cikina. Ka rabani da rayuwar da nake ciki. Maana ka aureni. wadannan ne amsoshin da Tilly ta bawa Junaid. Imi dake ta yiwa Junaid horn ya shigo su tafi ya fito daga mota ganin yadda abokin nasa ya rude.
Ya mutumina wannan ce akuyar dake neman daga maka hankali? Ai ka barni da ita na farfasa mata jiki kawai. Yana magana ne yana kokarin dauko wani katon dutse cikin wadanda akayiwa wurin ado dasu. Imi baya daukar raini shiyasa Junaid ya tabbatar yana daukan dutsen nan jikin Tilly zai dire shi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐25
Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke cikinki ba.
Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su mommy ba a wannan yanayin da suka tashi. tana turo kofar dakin da take tsammani ma na masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya...haba Juni boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai karamin dan iska ne don giyar kudi ce ta kaika tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya fadi.
Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa. Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta. Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci yana neman kayan maye ko yaya ya gusar masa da hankali ya manta da bacin ransa.
Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake fada maka bayan kunne yake bi. Bakin gado ta zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake son na canja halayyata kuma sai wannan masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce. Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan karyata ba kila da gaske ne.
Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka yarona komai zaizo da sauki. Hafsa tayi min yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna da kai lafiya.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐26
Neman Hafsi aka rinka yi a cikin gidan an rasa ina ta shiga. Mommy sai kuka take ko don taji zancen ciki ne ta gudu. Wata mai aiki mai suna Amaka ce ta tafi bakin gate ta tambayi securities din wurin ko sunga fitarta. Kusan awa biyu ana abu daya har Hajiyan dangi da Junaid suka shigo gidan don ta matsa masa akan yazo ya nemi gafarar iyayensa. Ganin gidan a hargitse Hajiya tace Salma me ya faru ne haka. Mommy cikin kuka tace bamu ga Hafsa ba Hajiya. Kinga har babansu ya fito nemanta.
Tunda akace Hafsi ake nema Junaid ya dena gane me ake fada. Na shiga uku Mommy ta gudu. Tilly da Rosie dake zaune a gefe ko a jikinsu. Ya nufo su cikin tsananin fushi ku sa a ranku indai banga matata ba wallahi kun gama ganin farinciki a duniya. Banzaye Matsiyata, karuwai....kafin ya kara magana Amaka mai girki ta fito daga dakinta da gudu. Madam amariya dey for my room. Bangaje ta Junaid yayi ya shige dakin. A daidai lokacin Senator ya fito yana waya da IG na police kan a baza masu nemanta. Me zai fadawa Mal Aminu? Duk kudinsa mutumin kwarjini yake masa sosai.
A kwance ya sameta kan gado tana ta rawar sanyi. Hafsi me ya faru ya fada yana shirin taba ta. Doke masa hannu tayi da kyar don wani zazzabi ne ya kamata sosai bayan tayi kuka mai isarta. Zuciyarta a cushe take da tsananin bakinciki. Badon abinda tayi ba tun kafin tayi aure tasan Allah bazai hadata aure da mazinaci ba.(don ma bata san yayi shaye shaye ba).
Ganin yadda ta hade fuska ga wasu hawayen sun taro a jajayen idanunta. Kasa ya sunkuyar da kansa kiyi hakuri Hafsi ki bari na taimaka miki ki tashi naga kamar ba kya jindadi. Harararsa tayi tayi tsaki a hankali zata mike. Ke ba kya gajiya da harare harare ne , wata rana sai na tsire miki ido. Duk da suna tare da damuwa da bacin rai amma sai da duk sukayi murmushi. Nafisa ce ta fara shigowa sannan su Mommy suka biyo baya. Hajiya tace mamana duk kin samu cikin damuwa tun dazu ana nemanki. Sai a lokacin suka kula da idanunta. Mommy ta zauna a bakin gadon. Kiyi hakuri yata nasan duk abinda zan fada zakiyi tunanin ko don bani na haifeki ba. Hafsi ta share hawaye ba haka bane mommy. Hamida tace wai ni me ya faru ne shi yazo yana mana fada dazu mun shigo kuma ance ana neman ta.
Babu wanda ya bata amsa. Mommy da kanta ta taimaka wa Hafsi ta tashi. Zazzabi ne a jikinki ko? A'a kaina ne kawai kuma zai dena idan nasha magani. Mommy tace ku zama shaida idan har yarinyar nan tace bazata zauna da Junaid ba sai an raba aurensu. Hajiyan dangi zancen bai mata dadi ba ta kama hannun danta. Muje Allah Ya kyauta.
Kwanaki uku bayan zuwan su Tilly jikin Hafsi ya warware sosai ga kulawar da take samu daga wurin iyayen Junaid. Hajiyan dangi taso komawa kano amma dole ta zauna har a shawo kan matsalar data kunno kai gidan. Su Nafisa kuwa kowacce ta koma gidan mijinta. Kirikiri aka hana Junaid ganin Hafsi gaba daya gidan ya masa zafi. Addua da yawan sallah yanzu kamar sabon limami don tsoronsa baya wuce a raba shi da Hafsi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐28
Fizgo ta yayi har jikinsu yana haduwa da juna. Bata yi attempting ta gudu ba ta dai ki yarda su hada ido. Thank you kawai ya ce mata a daidai kunnenta a hankali ya fice daga dakin. Tunane tunane ta rinka yi barkatai game da feelings dinta akan mijin nata. Karshe dai ta tabbatar tausayinsa kawai take ji. Sai kuma ta koma tunanin yadda zata yi da su Tilly. Ita dai bazata je tace karya suke ba kanta tsaye don tsoronsu ma take ji. Dadin abin ma tunda suka kawo kansu gidan ai sun san abinda suka taka. Ita a wa taje ta karyata su ace garin yaya ta sani. Da kunya aji amarya tana labe.
Tana ta tufka da warawara ita kadai har Hajiyan dangi ta dawo. Bayan sun gaisa tace kiyi hakuri na barki aikin jira ko. Ba komai Hajiya. Flask din kunun ta kalla au ina Junaidu? A nan na barshi fa zai sha kunu. Ya sha ya fita inji Hafsi. Kan wata kujera ta zauna tace Hafsatu. Naam ta amsa. Kin sanar da iyayenki abinda ya faru kuwa? A tsorace ta dago ido. Wallahi ban fadawa kowa ba. A'ah kwantar da hankalinki ai tambayarki nayi. Munyi shawara da su Rufai ne yace zaije har kanon ya sami babanki ya sanar dashi. Domin idan akwai cikin nan dole mu tsaya yarinyar ta haihu mu karbi dan. Gashi ma dai ana tunanin gara suyi aure saboda gori a nan gaba. Ko kadan ba haka muka so ba amma bazamu yi wata barnar ba don mu boye wata. Idan har kinsan bazaki iya zama da Junaid ba a haka kada kiji kunyar sanar dani. Ta dan gyara zama. Nasan iyayenki ma bazasu taba yarda ba. Kuma bazanga laifinsu ba ko nice abinda zanyi kenan.
Duk maganganun da Hajiya take Hafsi ta gane so suke suji ko zata bukaci a raba aure. Ko kadan bata so iyayenta ma su san maganar. Ai idan auren ya mutu wani kashin kazar zata shafa wa kanta. Dama ummati ta fada mata a groups din whatsapp babu irin abinda baa fada a kansu. Da masu zagi da masu kiranta karuwa ma. Ai auren rufin asiri ne gareta sosai. Dan murmushi tayi cikin kunya tace Hajiya in sha Allah zan zauna.
Har ranta taji dadi kuma tayi mamakin saurin amincewar Hafsi. Allah Yayi miki albarka Ya baku rayuwa mai albarka duniya da lahira. Ta kama hannayen Hafsi ta rike. Mungode sosai kuma zan kara jan kunnensa aka neman lahira da gudun duniya. Har hawaye Hajiya tayi tace bari na tashi na sanar da su Salma don su kunyarki ma suke ji. Baki ga baban naku bai neme ki ba. Yace bai san yadda zaiyi ya kalleki bane.
Ranar da Hafsi ta cika sati su Nafisa suka zo gidan zasu yini. Hira suke sosai da Hafsi kamar sun dade da sanin juna. Suna nan zaune Junaid ya shigo dakin. Rabon da su hadu tun a dakin Hajiyan dangi. Wata doguwar riga ce fitted a jikinta kanta ba dankwali Nabilan Nafisa tana ta jagwalgwala mata kai wai zata mata kitso. Yana yin sallama tayi saurin sunkuyar da kanta. Sis ina ta nemanku ance min kunzo sai Amaka ce tace kuna nan. Hamida ta ce ai yanzu mu Hafsi ce yar uwarmu. Ka zama dan karo ko Yaya? Nafisa tace Hafsi baki gaishe shi ba. Kafin ta amsa yace kyaleta bashi take ci. Nabilatu na kice kike ja min kan mata haka ko? Ku kuma duk kun kyaleta sai ta tsige mata gashi. Dariya duk suka yi kaji mai mata donma kayi saa tana mata gyaran gashi. Yace nasan dai kara kike musu to baa yiwa dangin miji haka sai su raina ki. Filo nafisa ta jefa masa. Sannu kanwa uwar hadi tun yanzu zaka fara nuna hali. Ke Hamida dauko min 'yata mu tafi kai kuma ka zauna ka gyara mata. Nabila sai ihu take da Hamida ta dauko ta...ni kichu kichu anti. Tanayi tana dukan Hamida.
Sai a lokacin tayi magana. Don Allah Hamida ku kyaleta. Ganin basu saurareta ba ta dauki hijab dinta zata bisu. Kafin ta gama sun fice harda rufo kofa.
Suna fita harda tafawa. Bawan Allah Ya Junaid duk ya zama abin tausayi. Kiri kiri anki kai masa matarsa gidansa. Nafisa tace nasan fushi su Mommy suka yi amma ai zasu bari ta koma. Ko ba komai yanzu da kudi Junaid bazai kara bin wasu matan ba a waje. Abinda ya wuce kuma Allah Ya yafe mana baki daya. Amin Ya Allah.
Batul Mamman💖
.TUN KAFIN AURE💐27
Hajiyan dangi ce kadai ke shiga sabgar Junaid. Shiyasa kullum yana dakinta. Hafsi kuwa dakin da aka bata kusa da na Mommy ne ko fita bata yi. Ranar laraba tana zaune a daki duk shirun ya isheta ta fito zata dakin Hajiyan dangi don yau bata leko sun gaisa ba. A bakin bene suka hadu Hajiya tace ina zuwa mamana? Ta dan sunkuyar da kai, dama gaisheki zanzo yi. Tayi mata murmushi to bazan amsa gaisuwar a nan ba. Karasa dakin ina zuwa. Zanje wurin babanku ne muyi magana.
Ba musu ta karasa sauka. Sai dai kuma bata san ina ne dakin Hajiyar ba gashi ba damar ta koma sama ta tambaya. Wani corridor tabi tana tafiya sai ta jiyo maganganu daga dakin. Babu shakka wadannan matan ne ke maganar. Kamar ta wuce sai ta tsaya daf da kofar. Daga ciki ta jiyo daya daga cikinsu tana magana da fada fada...kai banza so nake kawai kayi karyar kaine babana. Ka sami wasu da zaku zame min iyaye. Wallahi babbar harka zan baro mana idan kuka yi kuskure kuma Allah kashimu ne zai bushe. Sai wata tace ke komai akayi dake sai kinyi hauka ki rage muryarki mana. Wannan karon sai da Hafsi ta hada kunnenta da kofar take jin me ake fada.
Bayan dayar ta gama wayar tace ni yanzu Rosie ya zanyi idan suka kaimu asibitin ayi min test. Gashi kece mai cikin bani ba.
Hasbunnallahu wa niimal wakil. Ashe karya suke babu wani ciki. Bata san dalili ba amma har ranta taji dadin wannan zancen. Rosie tace kada ki damu Tilly nasan yadda zamuyi da komai. Ke dai idan kika yi kokarin yaudarata idan kika shigo gidannan sai na koya miki hankali, itama wannan matsiyaciyar amaryar tasa sai nasan yadda nayi aka saketa ko ta nemi sakin da kanta. Ni bani maganin nan na kara sha naji cikina ya fara ciwo ciwo. Gara shegen yayi ya bare kowa ya huta. Tilly ta kalleta ki hakura ki haifeshi ni yanzu da ko shege ne ina so. Ai tunda likitan nan yace mahaifata ta lalace nake jin son haihuwa. Rosie ta tabe baki...wanan dai sai suck away in kin matsu kije gidan marayu.
A sanyaye Hafsi ta cigaba da tafiya. Wata mai aiki ta gani ta tambayeta dakin Hajiya ta nuna mata. Tana shiga ta tarar dashi zaune kan carfet yana shan wani abu a cup. Ganin tayi turus ita bata shigo ba ita bata fita ba yayi dan murmushi mai cike da bakin ciki. Hafsi Hafsi ko na fita ne don ki sami sakewa? Dan kwarin gwiwa da samu data tuna cikin ba nasa bane ta shigo. Ina kwana ta fada tana dan durkusawa. Ajiye kofin yayi yana kallonta cike da mamaki. Hala ta manta abinda ya faru a kwanakin da suka wuce. Kai fa ka fiye kallo kuma na fada maka babu kyau. To ranki ya dade na dena daga yau. Rufe idanunsa yayi ya dauki cup din kununsa ya cigaba da sha. Jin wani daddadan kamshi kusa dashi yasa ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login