Showing 30001 words to 33000 words out of 35734 words
Junaid shiriya. Shi kanshi senator da ya dage da istigfar ba karamin mamaki yayi ba yadda yake jin canji game da al'amuransa. Idan Junaid ya dawo garesu dole su koma a nemi ilimin addini sosai.idan da asiri a jikin junaid to harda sakacinsa ta bangaren addua.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐44
Junaid yace kowa ya tuba don wuya fa ba lada. Imran na dariya yace ai wallahi da lada tunda nayi nadama kuma dai ai ba bari saida nazo gargarar mutuwa ba. Yanzu dai abar zancena wane mataki zaka dauka game da Tilly? Gaskiya i cant say for now matsalar tafi yawa idan na ganta. Ita kuma dayar ina sonta sosai amma na rasa me ya hanani nemanta. Bayan dan tunani Imran yace na sama mana mafita. Cikin zakuwa yace wacce? Kana ganin zaka iya hakura da mace indai babu aure a tsakaninku? Jimm yayi na dan lokaci. Tilly ta zame masa jaraba yace in sha Allah. To indai haka ne ka kira ta yanzu a waya. Junaid ya dauko wayar ya kira. Imran yasa speaker kafin ta dauka yace kayi mata saki uku yanzu ka yanke ala.....hello? Juni boy ina ka shiga ina ta jiranka. Imran ya zungure shi yana magana kasa kasa. Saketa mana...a dan tsorace yace Tilly na sakeki saki u..u..uku. wata irin kara suka je imran ya kashe wayar yace to tura mata text don a sami shaida. Jiki ba kwari ya tura Imran yana masa dictating abinda zai rubuta. Yana tura send Junaid yayi wata ajiyar zuciya. Imran yace idan har bazaka iya ba ka barni na biyoka gidan. No ka barni kawai ina zuwa zan koreta.
Hafsi tana ta juya waya a hannunta ta kasa bugawa. Tun a kano Ummati ta bata shawara yanzu ma ta sake kiranta taji ko ta kira tace mata yanzu zata kira. Sai da ta tattaro dukkan courage dinta ta kira. Wayar tayi ringing har ta katse bai dauka ba. Kamar tayiwa ummati Allah Ya isa. Gashi ta zubar da ajinta kuma babu biyan bukata. A lokacin da take wayar Junaid da Tilly fada suke kowa murya a sama don bai ma ji karar wayarsa ba. Nishi take kamar wata kumurcin maciji Juni boy baka isa ba na rantse maka. Ni zaka yiwa wannan rashin mutumcin, saki har uku? Duk da bashi da kwarin gwiwa sosai yace ki fita kawai kafin na kira security. Daki ta shiga da gudu ta barbada dan sauran maganin a hannunta. Saboda kuka bama ta ganin gabanta sosai. Duk duniya babu wanda ya isa ya raba mu. Tana yin kansa cikin zafin nama ya tureta bai san lokacin da ya fara karanta La haula wala quwata illa billah. Zafi sosai jikinsa yayi sosai har yáji kamar kafarsa bazata iya daukarsa ba. Tilly kuwa kan wani muzurunta ta fada daya tureta. Wata kara muzurun yayi tare da yakushin tilly. Hannunta mai magani a jikin magen duk ta shafe masa shi. Ihu tasa sosai tana kuka ganin abinda tayi na shiga uku shine na karshe maganin. Wani irin kallo taga muzurun yana yi mata tare da biyota. Tuni tilly ta dago jirgin badai maganin yana yi jikin kowacce dabba ba. Tsere suka sa ita da muzurun tana gudu yana binta juni help me please. Ko dago kai baiyi ba yadda yake jin jiri na dibarsa. Tilly dai kitchen ta shiga ta rufo kofa tana numfarfashi. Muzuru kowa yana ta meoww daga bakin kofa yana karta iya karfinsa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐43
Kwanansu hudu da dawowa bayan sunyi sati uku a kasa mai tsarki Hafsi ta taje kano tayi sati biyu. Sun sha hira da ummati ta fada mata halin da take ciki. Gashi dai ta kara kyau ga hutu amma babu nutsuwa a tare da ita. Bikin dake gabanta ne duk yasa ta dan manta da halin da take ciki. Ansha shagali don ummati ita kadai ce mace a gidansu. Duk kayan da ta saka da ma wasu abubuwan Hafsi ce tayi mata. Idan aka tambayeta mijinta kuwa sai tace yayi tafiya ne. Haka suka sha biki aka kai amarya gidanta. Bayan an gama biki Alhaji ya turo mata da kudin jirgi tana zuwa mota na jiranta suka wuce gidan Nafisa.
Ya kusa rabin awa yana jiran Imi a kofar super market din sai ga Tanimu wanda yazo gidansu a matsayin baban Tilly yana bin wata mata da kaya niki niki a baya. Tabbas shine don ga uku ukun bakinsa nan. Rufe motar yayi ya fito ya karasa inda Tanimu yake shirin lodawa matar kaya a booth dinta. Assalam alaikum....ai kafin kace kwabo Tanimu ya zura da gudu don kuwa ko a mafarki baya jin zai manta wannan fuskar. Ita kuwa matar kyawun Junaid duk ya dauke mata hankali kana ganinta kasan tana da aure. Wani fari ta rinka yi masa da ido da kwarkwasa. Hafsi ce ta fado masa, gabansa ya fadi. Ya rasa dalilin da yasa baya iya bude bakinsa ya nemeta ko ma yayi zancenta. Hango Tanimu yayi zai tsallaka titi ya bishi da gudu. Wuyan rigarsa ya kama ya fizgo shi. Tanimu duk ya gama rudewa don bai manta yadda senator yace zai iya sa a batar dasu idan suka yi masa karya. Gwiwoyinsa a kasa ya daga hannu sama yallabai kayi min rai wallahi sani suka yi. Junaid yace meye alakar ka dasu? Ya cigaba da magiya faci nake a tsallaken titin gidansu kuma ina hada su da maza. Dama dai yasan matan banza ne amma dai baiyi tunanin iyayen karya ta kawo ba. Sam baya jindadin rayuwarsa yanzu kullum jinsa yake kamar an kulle shi a cikin kwai. Imi yaji ya taba shi ya Juni meke faruwa ne? Junaid ya kalli Tanimu dake zaune gabansa ya fadawa Imran ko shi waye. Imran ya kira waya ba dadewa ta shiga suna zaune police biyu suka zo yace a tafi da Tanimu har ya fadi inda sauran suke. Yallabai ai ba sai an dake ni ba muje na nuna muku su duk abokai na ne. Keyarsa suka tasa a gaba suka tafi shi kuma Imi ya dawo motar junaid ya zauna. Wai meyasa kaki yarda mu hadu a gidanka ne? Wani zafi jikinsa yake yi yace Imran ina cikin problem sosai, wallahi na tsani rayuwata. Ba abinda ke min dadi....yanzu fa ina shiga gida da naga matar nan babu abinda nake so kamar kusantar ta. Tun ana abu da marmari yanzu ya koma kamar cin tuwo. Ita kuma idan ba kudi ta gani ba ta rinka gara ni kenan. Imran yace ai laifinka ne, tun a wurin bikinka nace ka barni nayi maganinta kaki. Yanzu kuma gaskiya na tuba...junaid yayi yar dariya Allah Ya kara shiryamu. Amin dan uwa...ai in fada maka wata shegiya ce. Au wallahi na tuba fa. Hmmm yarinya na dauko bayan an gama abu sai da nayi kwana biyu bansan inda kaina yake ba saboda na kasa fitsari. Wani mugun ciwo tasa min in takaice maka labari sai da aka yi min aiki a Germany. Abinda ya gabata Allah Ya yafe mana amma ni da mace sai matata insha Allah.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐46
Ruwa Hafsi ta diba a wata roba taje falo ta kwance dankwalin kanta ta jika shi tana goge masa jiki. Nafisa taje tana bude buden dakuna har taga kayan junaid. Riga kawai ta saka masa suka fice. Ihun Tilly suka ji tana kada ku barni da muzurun nan. Sai da drebansu ya sha wahala kafin ya iya kulle muzurun a kitchn dama ta taga ya shiga. Bakin Tilly duk jini don ta sha faratansa masu tsini suka tausaya mata ta shiga motar tare dasu. Asibitin kudi suka je inda aka yiwa junaid gwaje gwaje likita ya tabbatar babu abinda ke damunsa sai yawan tunani da bacin rai. Mummy da senator ma sun zo ana yiwa Tilly dressing din ciwukanta. Babu wanda ya kula ta a cikinsu suka wuce wurin Junaid.
Washegari sai wurin shadaya na safe Junaid ya farka. Koda ya bude idanu iyayensa ya gani da yan uwansa. Hajiyan dangi ma tazo daga kano. Yunkurin tashi yayi yaji hannu ya danne shi ta baya Juni ka kwanta jikinka ba kwari fa. Na shiga uku ce ta subutu daga bakinsa. Don har zuciyarsa saida ta kada don yanzu tilly tsoro take bashi. Yace me kike a nan ba na sake ki ba? Wani murmushi mummy tayi har kana ganin hakoranta, ita kuwa Tilly me kumburarriyar fuska tace dont mind him zafin ciwo ne yake damunsa. Imran da yake asibitin tun safe bayan ya kira wayar hamida ta dauka yace ke bana son iskanci...sai yayi saurin rufe bakinsa Allah na tuba. A gabana yayi mata saki uku wallahi kuma harda text ma shaida. Karya yake Mummy don Allah kada ku rabani da Juni. Nafisa tace idan ma joni ne ke da shi har abada. Kuma idan baki fita ba Allah security zan kira miki. Ta kalli su Hajiya tace ai a kwance muka ganta tana wani tsafi muzuru na lasheta kamar maye. Duk shi yaji mata ciwo. Tilly cikin kuka da daga murya tace wallahi karya ne bana tsafi. A jikin Juni nayi niyar shafa maganin shine na fadi ya goge a jikin mage. Subhanallahi dama asirce shi kike yi. Saurin rufe bakinta tayi jin baram baramar da tayi. Tana girgiza hannayenta da kanta tace ba haka nake nufi ba wallahi. Hamida ce ta bude kofa zata tura Tilly waje sai ga muzuru ya shigo ji kake yana meooowww da yaga Tilly. Bayansa nurses biyu ne da wani cikin masu gadi sun biyoshi da gudu. Jikin Tilly ya dafe yana zazzare idanu harda wani lafewa a kafadarta. Ita dai mutuwar tsaye tayi ko motsi ta kasa. Maigadin yace kuyi hakuri muna binsa yana gudu kamar yasan inda zashi ne. Imran dariya har kasa ta kaishi yace no ka barshi kawai ga matarsa nan ya nuna Tilly dake hawaye ba kakkautawa. Tausayi ta bawa hajiya tace don Allah a raba ta dashi. To dai jikin Tilly kamar me wasan kura da kyar aka rabasu don sai da aka yiwa muzurun allurar bacci ya fado. Tana ta godiya nan ta fada musu duk sharrin data kulla ita da Rosie ta roki gafarar su. Hafsi da ke can gefe akan kujera Tilly ta kalla tace kema sharrin dana yi miki babu ma cikin kawai so nayi ya sake ki.
Nan dai kowa yace ya yafe Nafisa tace ina kudin da kika karba wurin Junaid. Sai lokacin ma ta tuna cikin kankanuwar murya tace yana drawer a gida. Nafisa ta sha kunu to babu ke babu su don har atm din Alhajinmu ya sata yana baki kudi. Daga nan ki san inda dare yayi miki.
Hajiya tace to kuzo mu tafi gida don a kawo musu abinci. Hafsi ce kan gaba Hajiya tace ni bana son gulma zauna wurin mijinki kinji ko. Kamar tayi kuka duk suka fice. A bakin kofar ta tsaya taki juyuwa ma ta kalleshi. Kusan minti goma tayi a haka har kafaŕta ta fara sagewa shi kuwa Junaid dama kyaleta yayi don yaga iya gudun ruwanta. Yana kallonta ta sa nauyi a wannan kafar idan ta gaji ta canja. Murmushi tayi don ta fara bashi tausayi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐45
Da kyar ya mika hannu ya dauko wayarsa don ya kira imran. Kansa ne yake juyawa saboda tsabar ciwo ga zazzabi da ya rufar masa lokaci guda. Missed call din Hafsi ya gani take yaji zuciyarsa tayi masa sanyi. Kiranta yayi amma har wayar ta kare ringing bata dauka ba.
Tsaki tayi ganin me kiran ta wurga ta kan gado tare da tayar da sallah. Husna ce ta shigo dakin jin waya tana ringing ta dauka ta fita Maama ga wayar Mama Hafsa tana ringing. Nafisa ta ajiye remote din hannunta ta kalli Husna. Yanzu wa yace ki dauko mata waya? Maama sallah take yi. Kinga an sake kira ma. Nafisa ta karba ganin sunan Junaid tayi saurin dauka. Tana jin muryarsa ta mike tsaye Junaidu kana ina? Jikinta har rawa yake yace sis kece? Sautin kukansa taji yace i need you please. Kizo gidana yanzu. Kwalawa Hafsi kira tayi ki fito muje gidan Junaid Hafsi ina jin akwai matsala don maganar da yake ma ya dena. Hafsi najin haka itama kukan ta fara suka dunguma waje driver ya kaisu unguwar maitama inda gidan Junaid yake. A hanya ta kira mummy ta fada mata itama duk ta rude don tasan ko ba a fada ba dan nata yana cikin matsala.
A falo suka tarar dashi yana ta rawar sanyi ga gumi ya gama wanke shi har rigarsa ta jike. Nafisa tace da drebansu yazo ya dauko musu shi asa shi a mota. Hafsi tace bari a rage masa kaya jikinsa yayi zafi sosai. Ina ne kitchen ma, duk ta rude tayi nan tayi can. Nafisa ta nuna mata da hannu tana dago kan Junaid.
Wata irin faduwar gaba taji lokacin da taga Tilly kwance muzuru yana bin jikinta yana lashewa. Ko motsin kirki ta kasa yi don duk inda ta motsa sai ya yakushi wurin. Yanzu ma cinyarta muzurun ke lasa. Auzubillahi minash shaidanir rajim. Abinda ya fito daga bakinta kenan. Tilly cikin kankanuwar murya tace taimake ni...muzuru ne ya dare kan fuskarta yana lasar mata baki saboda ta motsa bakin.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐47
Dole ta ajiye fushin ta koma kan kujera ta zauna. Tana zama ya soma dariya ai na zata kinyi short service ne shiyasa kika dogare a tsaye kamar soja. Dan turo baki tayi tana harararsa... shafa kansa yayi yace God how i missed that. Hafsi don Allah dan dawo nan ki zauna. Kujerar gaban gadon ta kalla daya nuna ta kawar da kai gefe sai hawaye. Kamar tana kara masa ciwo da kukanta ya taso a hankali ya dawo kusa da ita akan wata doguwar kujera. Janyota yayi ya rungume ba tare da yayi magana ba sai saukar hawayensa taji a wuyanta. Tayi saurin dago kanta kukanta ya kara tsananta. Fuskokinsu ya hada suna kallon juna yana shaqar daddadan kamshin jikinta. Ki yafe min Hafsa, ki yafe...bakinsa ta rufe da hannunta daya wanda yasha lalle mai kyau tace Allah Ya yafe mana baki daya. Hannun nata ya zare ya cigaba da magana. Nasan na zalunci kaina da irin rayuwar danayi adopting tun kafin nayi aure. Na janyo ma kaina da duk wanda ya rabeni bacin rai da bakin ciki. A yau nayi dana sanin duk wani shaye shaye da bin mata dana yi, rashin kyautatawa iyaye da keta dokokin Allah. Kuka Junaid yake sosai da sauti Hafsi ta kara rungume shi sosai tana share masa hawaye. Kasan lesson din dana dauka a rayuwarmu? Ya girgiza kai tace Allah Yana bawa bayinsa chance din tuba da dama don baa makara da tuba sai an mutu. Kaddarar aurenka tasa nayi abinda ban taba tunanin yi ba kaima kuma kabar abinda kake yi. Ni bazan dauki fushi da kai ba don idan Allah Ya yafewa bayinSa baya rike su ko Ya cigaba da kamasu dashi. Ni da kai duk da sauran musulmi duk muna bukatar inganta imaninmu mu tsayar da zukatanmu wuri guda a hanyar neman lahira. Kudi ba hauka bane face wani nau'i na jarabawa daga Allah. Sai dai munyi rashin saa da yawa cikinmu musammam 'ya'yan musulmi idan muka ganmu ko iyayenmu a madafan iko a kasar nan sai muyi ta barna da dukiyar da ba tamu ba. Yace hakane kuma gashi da sanin iyayenmu muke yi. Zanyiwa Alhaji magana kinga duk abinda nayi a da bai taba hanani kudi ba. Nagode da Allah Ya hadani dake Allah Ya yi miki albarka tace amin. Dago fuskarta yayi yana kokarin kissing dinta ta sake sunkuyar da kai. Au bayan duk kin gama zance ni shine zaki wani sunkuyar da kai kasa. Dama fa na gano ki tun dazu abinda kike jira kenan shiyasa kike ta wani shige min jiki. Hararar nan mai burge shi tayi masa ta tashi da sauri. Kada ka manta ni amarya ce samuna sai anyi da gaske. Yanzu ma don baka da lafiya ne. Yayi mata murmushi me kashe zuciya Hafsi Hafsi tawa Allah Ya barmu tare.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐49
Kana ganin Hafsi kaga amarya sai zuba kamshi take. Hamida ta kalli agogo tayi dariya kinga Hafsi karfe takwas ta wuce ki tashi ki tafi wurin mijinki don yau babu mai raka ki. Sunkuyar da kanta tayi kasa don kuwa mummy na falon. Mikewa tayi itama tana dariya rabu dasu kinji Hafsa ni sai na raka ki da kaina. Ba shiri Hafsi ta tashi da gudu ita kuma mummy ta haye sama tace bari kiga ni na tafi wurin nawa tsohon. Ku kuma kowacce ta tashi ta tafi gidanta a barni na huta. Tana bace musu Nafisa tace to nidai nayiwa Hadiza alkawarin kaiki da kaina so wuce mu tafi. Haka suka je side din Junaid ana ta hira. Hamida na sallama ya bude yana wani harare harare sai yanzu kuka ga damar kawota. To sai da safenku yaja hannun hafsi ciki. Nafisa tace yaro kaci bashi mu kwana lafiya.
Kallon dakin take wanda ya kawatu da kayan more rayuwa kala kala. Zauna mana Hafsi Hafsi ko kauyancin ne ya motsa. Ta sha kunu yau wacece bakauyar eyye. Toooohhh ni kike zarewa idanu? Duk mace mai zarewa mijinta ido fa hukuncinta.......mamaki da jindadi ne suka ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa lokacin da yaji ta hade bakinta da nasa. Sai da suka jima a haka ya rinka kokarin su hada ido taki. Kaji wani sabon salon gulmar kina wani kasa da kai kamar mutuniyar kirki. Ita kanta tayi mamakin abinda tayi. Ya kama fuskarta da hannayensa biyu...Hafsi ki fada min abinda zai karasa cika min farinciki na. Kunnensa ta kama tace I love you J dear. Tana gamawa ta hada da cizo a saman kunnen sannan ta gudu. Binta da zaiyi yaji an buga musu kofa ga wayarsa dake aljihu tana ringing. Hafsi ta dawo tace ni na ga ta kaina. Menene ya tambaya a firgice ta nuna masa hanyar kofa. Kullum aka kawoni sai wani abu ya faru. Kanne mata ido yayi kaga su Hafsi ke kuma kina bukatar kadaicewa da mijinki ko. Dundu tayi masa har yayi kara sannan ya duba mai kiran wayar. Ya nunawa Hafsi kinga