Showing 9001 words to 12000 words out of 35734 words
a cewarsa sa hadu idan an daura aure. Duk abin duniya ya isheta gashi dai zata auri wanda take so amma babu wannan farincikin ko kadan a ranta. Duk surutunta yanzu ta zama wata abar tausayi. Yan uwanta kuwa sai shirye shirye suke yi hankali kwance.
*******************
Ya kusa awa biyu a gefen gidan sannan yaga fitowar wanda yake jira. Tabar hannunsa yayi saurin kashewa ya tada mota ya bishi a baya. Yinin ranar duk inda Saif yayi Junaid na binsa a baya ba tare da ya sani ba. Takaici ne ya isheshi don kuwa baiga alamun anzo gidan da yake nema ba. Karamin tsaki yayi ganin sun kusa karasawa gidansu Saif din. Horn ya rinka matsa masa kamar hauka dole Saif ya tsaya yayi parking. Wannan takun kasaitar ya dinga ya har ya isa kusa da motar Saif. Ganin bai sanshi ba sai ya mika masa hannu su gaisa. Kin karbar hannun Juni yayi daya tuna yadda suka kankame abar sonsa.....abar sona??? Ya tambayi zuciyarsa. Sannu dai, Saif ko? Eh ya amsa masa fuska a sake...Saif akwai fara'a. Shiru yayi don bashi da abin fada abin har ya fara isar Saif. Ban fa gane ka ba wa kake nema ne? Hoton cikin wayar ya nuna masa idanun Saif har wani kankancewa suka yi don tsabar bacin rai. Yayi imani ko mutum daya bai turawa hotunan ba kuma Hafsi ko wayar kirki bata da ita shiyasa ma bai tura mata ba. Juni ya katse masa tunani I want her kuma zan iya biyanka ko nawa ne ka kaini wurinta. Ikon Allah....kai kuma daga ina? Kana ma da hankali kuwa? ba ko kunya balle tsoro kake fada min hakan. To bari kaji na fada maka this coming saturday zata zama mallakina. Kasa karasa magana Saif yayi saboda tsabar takaici ya tsaya yana magana da kwancen hauka. Shafa kai Juni yayi plan dinsa is working. Sai kuma ya yamutsa fuska tunda baka jin lallami kasani cewa nan da ....sai ya dubi agogonsa kamar 20 minutes yarana zasu dauko min ita su kai min ita hotel. Wani mari yaji a kuncinsa kamar wuta kafin ya dawo hayyacinsa kuwa Saif ya shiga mota ya tayar. Shege ya fada yana shafa kunci amma fa marin da zafi...kodayake its worth it.
Bayan Saif yabi har kofar gidansu Hafsi. Yana tsaye a can gefe ya hango wani dattijo mai cike da kamala ya fito sunyi magana da Saif. Yasan bai wuce barazanar karyar da yayi ba Saif din yake fada shi kuwa bukata ta biya dama plan dinsa yaga gidan kuma ya gani. Sauransa jin sunanta duk da a zuciyarsa ya rada mata suna pretty.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐13
Wallahi Baffa kamar mahaukaci fa yake magana kuma nayi tunanin da gaske yake. Gyara tsayuwa yayi to Saifullahi ai kadan ma kuka gani. Illar irin wannan abin dama ba na lokaci daya bane. Me zaku fadawa yaranku idan suka ci karo da hoton nan gaba? Shin kuna da bakin tsawatar musu bayan sun san borin kunya kawai kuke yi. Allah Ya kyauta ka tafi gida kawai in Allah Ya yarda babu abinda zai faru. Saif kallon Baffa kawai yake yi don yaga kamar bai yarda da abinda ya fada ba. Shi kadai yasan abinda ya gani a idon yaron nan. Jiki a sabule ya juya ya tafi.
********************
Wannan tafiyar kasaitar yake yi har ya shigo gida yana dan fito don yau zuciyarsa fes take. Tunda yazo kano bai sha giya ba sai taba da shisha suma duk a waje saboda sa ido irin na Hajiyan Dangi. Tsohuwar nan akwai hana ruwa gudu. Turus yayi da ya ganta zaune a kan gadonsa. Fuskar nan babu fara'a koma waje kayi sallama ka shigo kamar dan arna kana min fito kamar mai kiwon kare. Haba Hajiya ai dakina ne kuma nasan babu kowa a ciki meye na sallama kuma. Ashe baka san cewa akwai aljanu da malaikun Allah a ko ina ba. Don baka ganinsu hakan ba yana nufin babu su ba. A duk lokacin da zaka shiga wurin da babu kowa sai ka ce Assalamu alaina wa ala ibadullahis salihin. Ai na iya Hajiya bafa complete jahili bane ni. Naji koma dai kayi. Fita yayi yayi mata kyakkyawar sallama ta amsa sannan ya shigo. Cire kaya ya fara yi yana wurgi dasu tace maza ka gama ka tsince min su ga tsintsiya nan ka share dakin. Me??? Ni din Hajiya? Kai mana Junaidu ko kana jin saurayi kamar ka zan bari a share masa daki. Ni wallahi bacci nake ji duba fa ki gani na dawo da wuri shadaya bata yi ba. Ta mike Allah sai ka gyara dakin nan idan ba haka ba zaka ga yadda zanyi da kai. Tana fita ya fada gado sai dai bai gama gyara kwanciya ba ta dawo. Yauwa kayi sallah kuwa?... .au kwanciya kayi ko to tashi ta fada tana dukansa da slipas din kafarta. Dole ya mike Hajiya bana so fa. Sallah kuma nayi don nasan ina da ayyuka a gabana shiyasa ma tun da Baba yazo muka je muka yi sallar asuba ina dawowa nayi duka sallolina ya kare maganar da murmushi. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shi kawai take fada. Junaidu lalacewar taka har ta kai haka? Shiyasa ka gagara shiryuwa mana. Ta share wasu zazzafan hawaye dake sauko mata. Ashe baka san cewa wutar masu barin sallah daban take ba? No Hajiya nifa nayi ko bakiji abinda na fada bane. Bakin gado ta zauna Junaidu babu wata sallah da zaka yi ba a lokacinta ba da gangan Allah Ya karba. Harma gara lokacin ya wuce maka bisa kuskure sai ka rama. Ita fa sallah kariya ce daga aikin sabo da alfasha. Rayuwa da mutuwa gaskiya ne Junaidu, azaba ko rahmar kabari gaskiya ne, wuta da aljanna ma gaskiya ne. Maganar Hajiyan Dangi da hawayenta sun taba masa zuciya har bai san lokacin daya dora kansa a cinyarta ba yana bata hakuri. Junaidu ka kiyayi Allah sai Allah Ya kiyaye ka. A yau alkawari daya nake nema a wurinka shine na tsayar da sallah. Nayi miki bazan kara bari naji kiran sallah na kasa tashi ba. Ta shafa kansa Allah Yayi maka albarka. Amin
******************
Ummati ana ta rawar kai biki ya gama matsowa da kyar aka barsu zuwa salon don ko gyaran jiki Hafsi bata yi ba. Wannan kuma duk yana cikin punishment din da aka tanadar musu a gida saboda laifin da sukayi don a cewar Maman Ummati itama haka zaayi mata tunda bakinsu daya.
Sai da Saif yayi jan ido sosai sannan kanwarsa Zainab ta fada masa gaskiya ita ce garin binciken waya taga wadannan hotunan a wayarsa ta tura wayarta, daga nan kuma ta tura wa kawayenta. Da belt ya zane ta tana ihu tana bashi hakuri. Ko da mamansu taji dalilin dukan Allah Ya kara tace musu duk su biyun. Ke banda gulma me ya kaiki bincika masa waya....bayan zainab ta koma daki da kuka Maman tace gobe ma ka sake daukan yar mutane kuje yin hoton rashin kunya....istigfar ya rinka yi a zuci. Allah Yasa daga wannan bazasu fuskanci azabar Allah ba. Don kam shi da Hafsi sunyi nadama sosai.
Batul Mamm
TUN KAFIN AURE💐 14
Duk abinda yayi niyyar yiwa Pretty kamar yadda ya saka mata suna maganganun da Hajiyan Dangi tayi masa yasa duk jikinsa yayi sanyi. Washegari bai bari ya makara sallar asuba ba domin kafin lokaci ma yayi setting alarm. Suna dawowa ya shiga dakin Hajiyan Dangi. Har ka manta yadda ake sallama ne? Ba shiri ya fita yayi sallamar ya jira tayi masa izini ya shigo. A kasa ya zauna cike da ladabi tace yau dannan nawa akwai magana a bakinka. Fadi inji Allah Yasa alkhairi ne. Shafa kai yayi alkhairi ne Hajiya. To ina jinka. Wai yau shine da jin kunya abin ya bashi mamaki... dama yarinya na gani ina son aura kuma idan da hali da wuri nake son auren. Allah mai girma da daukaka ta daga hannu sama ta yabi Allah SWT sannan ta kalle shi. A ina take kuma ya sunanta? Nan fa daya yace a ransa, sai kuma dabara ta fado masa. Nasan gidansu dai amma banyi mata magana ba domin mafi son ki fara nema min izini. A'a wai kuwa Junaidun da ta sani ne wannan? Yau komai a hankalce yake yi. Allah Yasa bata yi masa zancen Sayyada ba itama yarinyar bata sani ba da yazo ya bata kunya. Kwantar da hankalinka bari na fadawa Baba sai musan abinyi zuwa karshen sati. Sanin cewa nan da kwana uku zaa daura mata aure Junaid ya fittike mata shi lallai yau yake son taje. To naji bari dai na fada masa tunda da kanka ka zo da maganar. Tana fita yayi ajiyar zuciya yarinyar da har yanzu baiga zahirinta ba yake tunanin aura....sai dai kuma irin yadda yake jinta a ransa yasan da gaske yake burin rayuwa da ita, baya jin zai taba iya yarda wani ya shiga tsakaninsu.
Sai bayan laasar Hajiyan Dangi ta shirya tare da wata yar uwarsu Gwaggo Mairo suka nufi unguwar sabontiti inda Junaid yayi musu kwatance a matsayin gidansu Pretty. Karba ta mutumci da karramawa Mama tayi musu bayan sun gama gaisawa ne Hajiyan Dangi ta gabatar da kanta tare da fadin dalilin zuwansu. Mama tace kuma nan gidan yaron ya fada muku? Nan ne domin ya kwatanta min gidan ta waje sosai Hajiya ta bada amsa. To Hajiya ni dai banda yaran nan biyu da suka gaisheku bani da wata 'yar sai Hafsa wadda asabar dinnan zaa daura mata aure. Babbar kuwa shekararta uku ma da yin aure. Shiru Hajiyan Dangi tayi sai Gwaggo mairo ce take ta basu hakuri tace nasan yaronnan kam ba kananan yake nufi ba zamu sanar dashi yayi hakuri. Hajiyan Dangi ta fiddo kudi a jakarta tace gashi a bawa amarya. Allah Ya sanya alkhairi. Mama taki karba itama hakurin ta basu. Hajiya sai ta ajiye kudin a kan tebur. Suna kofar fita Hafsi ta dawo daga salon duk a gajiye. Har kasa ta durkusa ta gaishesu. Ko baa fada ba Hajiya tasan wannan ce Hafsar da danta ya gano. Lallai ya rude don yarinyar tana da kyau. A sabule suka fito don ba haka aka so ba. A tunaninta indai yayi aure wasu daga cikin ayyukan barnar da yake aikatawa zasu ragu ko ma ya bari gaba daya.
Tun a mota ta kira shi domin taga missed calls dinsa da yawa sai dai bai dauka ba. Suna isa gida Sayyada ta sanar da ita ai ya tafi masallaci ne. Dadi ne ya cika mata zuciya sannan ta shige daki. Cike da doki ya shiga dakin yana ta washe baki. Har zuciyarta take tausayinsa... junaidu yarinyar nan ashe ranar asabar za'a daura mata aure. Kayi hakuri ka nemi wata. Mikewa yayi hakuri fa kika ce Hajiya. To ma baki basu kudi bane? Ai wallahi da sunga kudi magana zata chanja. Murmushi tayi zauna Junaidu. Ina so ka sani ba fada ta bace Annabi SAW yace babu kyau wani ya shiga cikin cinikin wani ma balle harkar neman aure. Ai ba'a hada nema akan nema. Abu daya zaisa ka iya nemanta sai dai indan wancan yace ya fasa. Wani irin bacin rai yaji a ransa idanunsa sun kada sunyi ja. Fita yayi fuuu ya buga mata kofar daki har sai da ya tsorata ta. Allah Ka shirya mana ta fada a fili.
Jan mota yake a guje kamar zai tashi sama. Baya ganin gabansa ma da kyau. Club ya shiga ya tayar da kura kafin ya tsayar da motar. Idanu duk a kansa ya shiga. Waiter na shirin zuba masa giya ya sunkuce kwalbar yana kafa kai. Sai da ya bugu sosai ya jawo hannun wata yarinya suka fita tare yana tangadi. A waje ya dauko wayarsa ya bata yana lumshe idanu kira min oldman. Waye kuma oldman? Ki dduba za zaki gani a wayar. Ringing biyu ya dauka sai yayi mamakin jin muryar mace ta sanar dashi wurin da dan nasa yake ya daga masa hankali. Yana ajiye wayar ya kira Hajiyan Dangi ya fada mata. Nan tayi masa bayanin abinda ya faru sannan ta sanar da maigidanta inda Junaid yake. A can abuja kuwa Mommy Senator Rufai ya tasa yace mata gobe zamu kano.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 15
Hajiya da maigidanta sun rasa yadda zaayi a dauko Junaid saboda Baba baya iya tuka mota idan dare yayi. Suna ta shawarwari ne suka ji karar motar sa. Da sauri suka fito motar duk ya buge ta a hanya har fitila daya ta lotse. Haka suka kama shi yana ta tangadi sosai suka shiga dashi dakinsa. Hajiyan dangi sai kuka take jin yana ta sumbatu yana cewa ko a aura masa pretty ko ya saceta ta karfi. Haka Hajiyan Dangi ya zauna dashi har yayi bacci shi kuma Baba ya kira senator Rufai ya sanar dashi halin da ake ciki.
Jirgin karfe 7 na safe suka biyo shiyasa kafin karfe 9 sun iso kano. Motoci uku ne suka je tarbar maigirma senate president da matarsa Hajiya Salama.
Gyadigyadi suka nufa gidan Hajiyan dangi. Mommy tana ganin Hajiya ta soma kuka. Bana son irin haka Salama baki san hawayen iyaye cuta ne ga 'ya'yansu ba? Share idon tayi tace kinga irin yadda nake fama da yaronnan ko. Ni fa har cewa nayi baban nasu ya dena saka masa kudi a account amma yaki. Hajiya tace abar maganar nan yanzu bari mu gani ko ya tashi. Su hudu iyayen suka dunguma zuwa dakin da Junaid yake mahaifinsa ya bude kofar ya tarar dashi a kwance yana ta busa taba. Kwarai yayi mamakin ganinsu ya tashi da sauri...mommy na sannu da zuwa. Hannun daya kawo zai tabata ta doke tare da jan tsaki. Yasan fushi take yayi murmushi kawai ya kalli babansa. Oldman ya hanya? Wannan karon Hajiya ce ta doke masa baki. Uban naka kake kira oldman kuma junaidu? Dole kayi ta ganin ba daidai ba a rayuwarka tunda iyayenka ma basu da kima a idanunka. Da ace ka maida hankali kan addini da kasan cewa iyaye sun fi karfin wasa. Duk zama suka yi Senator Rufai ya cire hularsa yasa hannuwansa ya dafe kansa. Ya rasa yadda zaiyi da Junaid fitinarsa kullum karuwa take. Hajiyan Dangi ce ta labarta musu dukkan abinda ya faru game da yarinyar da Junaid yace yana so mai suna Hafsa. Ya maimaita sunanta a ransa yafi a kirga. Baya jin komai game da maganganun da suke yi. Hankalinsa ya tafi can tunanin yadda zai mallaki yarinyar nan mai suna Hafsa.
A wace unguwa suke? Ita ce kalmar da yaji daga bakin mahaifinsa. Da sauri yace sabontiti. Shi kuma wanda zata aura fa? Nan ma Junaid ya bada amsa. Alhaji zaka nema min aurenta? Wallahi nayi maka alkawarin zan shiryu indai na aureta. Hajiyan dangi tace Rufai me kake shirin yi ne? Shima Baba cewa yayi hala ka manta haramcin neman aure akan na wani? Mommy dai binsu ta rinka yi da ido don itama bata san me mijin nata yake nufi ba.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 16
Senator Rufai dai bai iya basu amsa ba ya fito ya shiga mota kafin a tayar Junaid ya fito da gudu ya shiga shima. Yana zama senator yace sai ka kwatanta wa Bulus hanyar gidansu yaron. Yaron kuma Alhaji? Ba nema min auren zaka yi ba? Junaid just do as you are told kaina har ciwo yake. Ba gobe ne daurin auren ba? No sai saturday.
Gidan ya fara cika da 'yan uwa da abokan arziki yan daurin aure da biki. Da gudu ya shigo gidan har yana zubar da abincin dake hannunsa wata yayarsu ta janyo shi. Adnan saurin me kake yi ne haka? Yauwa yaya ina baba? Ya amsa yana ta haki. Wannan mutumin da ake nunowa a tv na gani a waje sun zo a cikin motoci masu kyau sai wani mai bindiga yace babanmu suke nema. Kai mai bindiga fa kace...eh wallahi amma na hango na tv din mai kudi ne fa. Jin kamar yana shirme Zainab ta leqa wajen da kanta ai kuwa babu karya wasu jeeps ne guda uku duka bakake amma ta tsakiyar tafi kyau. Ga mutane sun sha suit kowa rike da bindiga.ba shiri ta koma cikin gida ta nufi dakin baban su sai dai a hanya suka hadu har Adnan ya isar da sako. Shima dai mamakin yayi ya matsa wurin daya daga cikin guards din yace shine mai gidan. Yana kallo yaje wurin motar tsakiyar sai ga wasu mutane su biyu sun fito. Ba ko shakka senate president ne Rufai Bukar yasha wata ash shadda kana ganinshi kaga kudi da tsantsar jindadi. Dayan kuwa saurayi ne kyakkyawa amma fa kayan jikinsa kamar anyi wasan kura dashi. Guard din yace ciki zamu shigo. Nan Alh Bashir yace to cikin hanzari yayi musu jagora. Suna shiga jamaa sai binsu ake da ido har falon sa. Maman su Saif ta bi bayansu. Ganin waye bakon ta fito da sauri ta bada kudi a siyo lemuka da ruwan roba.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona ne Junaid... ..haka dai senator ya labartawa Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar dan da....kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba da magana wadda sai da hawayen da yake kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya janyo min magana fiye da yadda baka zato ga shaye shaye