Showing 21001 words to 24000 words out of 32781 words

tace
"Ni dayane a cikina,scanning ya nuna" baki ya kama yana murmushi
"Idan kuma Allah boye dayan yayi fa?" Dariya yabata sosai,wai duka yaran gabanshi basu isheshiba,kalen 'yan biyu yakeyi
"Dayanma an godewa Allah,banda abinka bbn amir duk yaran dake gabanka?,ga wanda idan Allah ya nufa amarya zata haifa maka?"
"Dozen biyu fa nakeso" sosai dariya ta qwace mata ganin bilhaqqi da gaske yake
"Ina zakakai dozen biyu"
"Da gaske nake miki,yara ai rahamane" tana dairiyar take gyada kai,daidai sanda rufaida amarya tashigo.


Sanye take da wasu matsatstsun baqaqen riga da skert da suka fidda dukkanin jikinta sosai,taku take d'ai d'ai tana taunar chewing gum tashigo da sallama.


Kai tsaye kusa da bbn amir tazauna kamar zata shige jikinsa,dauke kai mmn amir tayi kamar bata gani ba
"Kin sha magungunan dai ko?" Bbn amir yakuma fada yana dan janye jikinsa ganin yadda ta matseshi sosai,fuskarta a sake tana murmushi kamar dai daxun tace
"Bamu jima da dawowa ba dukka nasha,shinema nadan samu barci"
"To ma sha Allah,Allah ya qara lpy"
"Amin amin,na gode" ta fadi tana maida hankalinta ga wasu jaridu dake kusa da ita ba tare data dubi sashen da rufaidan ko bbn amir din yake ba.


Tanajin yadda rufaida ke janshi da hira irinta soyayya,amma sai tayi kamar batasan sunayi ba,ta maida hankalinta sosai tana duba jaridar,rufaidan rabin hankalinta nakan mmn amir din,so take taga sauyawar fuska ko yaya tattare da ita,saidai taqi bata dama,hakan yadan sosa mata rai,tasake bada qaimi,amma azahiri saikace ko a jikin mmn amir wai an mintsini kakkausa,duk da zuciyarta cike take da kishi fal.


Ganin abun na neman wuce gona da iri saita rufe jaridar tana duban bbn amir
"Ko za'a yiwa mmn ummi magana ne?,inason in sha magani na kwanta dawuri"
"Eh to,to ayi matan" yana rufe bakinsa mmn ummi tashigo dakin dauke da ummi,mmn amir tasoma mata tafi tun kan su qaraso yarinyar tasoma daga mata hannu,suna qarasowa ta karbeta,tahau qyaqyata dariya kuwa,don yau duka basuga juna ba.


"A ina zan zauna kenan?" Mmn ummi tafada fuskarta tsaf a dinke,duka suka dubeta shida rufaidan don basu gane me take nufi ba,shi yasoma magana
"Ko inama,ai akwai wajen zama"
"Amma ka kiramune don muzo mu ganta nanuqe da ita,toni indai irin wannan zaman za'ayi wallahi bazan zauna ba" sai sannan rufaida tagane me take nufi,saboda haka tasake shige masa tana duban idanunta
"Ayyah mmn ummi,aiga daya side din can saiki zauna na wani abu bane ko?" Ta fada tana fakar idanun baban amir ta watsa mata harara,sarai ta ganta,kuma itama batayi qasa a gwiwa ba ta maida mata,kafin tace wani abu bbn amir yadubi rufaida
"Koma can kema ki xauna" ya nuna mata kusa da mmn amir,ranta yabaci sosai,saidai duk da haka taci riba tunda ta bata ran koda iya mmn ummin ne.


Cikin nutsuwa ya musu dukkan jawabin daya dace kowanne maigida yayiwa matansa,yaja hankalinsu kansu xauna lafiya,kuma kowa ya girmama na gaba dashi,kaf maganar bata yiwa rufaida ba,ta tsammaci xai bata wani matsayine na daban a gabansu cikin maganarshi,mamaki ita gaba daya take,kaman ma ba jibril dinta ba,duk wani fifiko datake zatan ta dara saura dashi bata ganshi ba cikin bayananshi,yana bayani kaman daya take da matanshi?,ya zama lallai ta nuna musu akwai banbanci,ba zata lamunta yazama tana hangen dala ba tana tunanin birni zata shiga ashe ba birni bane.


"Sai zancan rabon kwanaki zai zama bibbiyu kamar yadda aka saba ko?,mai magana ko qorafi kuma bismillah kafin mu tashi" shuru dukka sukayi,kowa da abinda yake saqawa cikin ranshi,ganin haka sai mmn amir tagyara zamanta
"Nidai ina da magana ko qorafine zance" waiwaya yayi yana dubanta sannan yabata dama
"Yauwa,inajin gsky zan sadaukar da kwanakina da kuma girki zuwa hannun 'yan uwana,saboda yanayin jikina,da kuma hutun da likita yabuqata na dinga samu" dukkaninsu suka zuba mata idanu,rufaida tayi caraf
"It means mu zamuna miki girki kina kwana da miji?" Ta fada ranta na mata zafi,kallonta mmn amir tayi sosai kana tasaki murmushi
"Wannan ba damuwa bace,nabarmiki bbn amir harsai na haihu,kiyi girki kuma ki riqeshi" can qasan ranta taji wani mugun dadi,a fili tasaki murmushi tana qiyasta bagidajiya a ranta,banda bagidajiya ta yaya za'ayi ki barwa kishiya mijinki?,ai idan itace ko naquda take ranar ba zata taba yarda ta barwa kishiyarta mijinta ba.


"Tabdi,to wallahi ni ban yarda ba,ta yaya zakiyi haka baki nemi jin ta bakina ba,kina nufin tayi kwana hudu nidata samu a gidan nayi kwana biyu,wallahi ko sama da qasa zata hadu ban yarda ba,da sake an baiwa mai kaza kai,saidai muyi uku uku" mmn ummi tafada tana kumfar baki,haushin mmn amir ya cikata taf,tana ganin kamar akwai maqarqashiya ko hadin baki tsakaninta da rufaida ko bbn amir,sun hada baki da kaine kawai don a zalunceta ko a cusa mata baqinciki"
"Kinga jimana maryam,kamar yaya?,kwana dai ba nata bane kuma tace tabarmin har saita haihu,tunda ba'a baki ba aisaiki saka na annabawa,kinata abubuwa na saka miki idanu daga jiya zuwa yau,shine yanzun ma dai dole kin saka nayi magana,ni banson aikin zubda aji gaban miji" ta fada tana kada idanu hadi da kada qafarta data dora daya saman daya.


A zabure mmn ummi tamiqe tana nuna rufaida
"Ke dakata karkimin rashin kunya,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa wallahi niba sa'ar yinki bace" dariya rufaida tabushe dashi
"Ikon Allah,yanzu duk saboda ba'a baki......"
"Dakata ya isheni da Allah malamai haba!" Bbn amir yafada cikin bacin rai
"Wane irin abune wannan?,to ya isa,zata riqe kwanakinta,sannan ku zaku ci gaba da girki har Allah ya sauketa lafiya,ke maryam zaki riqe girki har kwanakin da rufaida zata karba,zakuci gaba dayin kwana uku uku" hakan yayiwa mmn ummi dadi,saboda tasani dama ita ko mmn amir duk wadda cikinta ya tsufa haka 'yaruwarta ke amsar girki harta haihu,ko banza an soke kwanan da aka qarawa rufaida,saboda haka ita bata da damuwa,saidai girkin da zatayi har tsahon kwana shida tana basu sunaci bataji xata iya gaskiya,ta wannan bangaren ma kamar bbn amir din duka gidan ita yafi rainawa kenan,mata biyu kowacce nakwance zata dinga dafawa tana bata?,gaskiya da sake an baiwa mai zaka kai.
"Nifa gaskiya bazan mata girki har kwana shida ba,don ba baiwar wani bace ni" ta fada tana harare harare,mamaki ya cikashi,wato wanzan baison jarfa kenan,ya tuna sanda mmn amir tadinga mata girki kwana da kwanaki,harda qarin kwana uku tayi mata saidata cike kwana goma cif
"To shikenan,mu zuba nidake naga waye mai gidan"ya fada akusashe cikin bacin rai,fuuu ta amshe ummi daga hannun mmn amir tafice daga dakin,binta da kallo mmn amir tayi harta fice,saita miqe itama a tausashe
"Nikam ina neman alfarmar akarbi kwanan idan zaiyiwu don Allah,saida safe" daga haka tayi gaba,duka ranta babu dadi,taya mmn ummin zata bari daga shigowar matar tsakanin jiya dayau amma su soma irin wannan tataburzar,harta bari taga warginta da zata dinga fadi in fada da ita?.


Itakam batasan ya aka kwashe ba,tunda tashige dakinta tadan zauna cikin yaran kana tawuce tayi kwanciyarta,bata farka ba saida asuba.


Da safe ya leqosu kamar yadda yasaba,ta gaidashi a ladabce sannan tace
"Yau salima zata koma gida"
"Au,ai na zaci zata tayaki zamane harsai kin haihu" kaita kada
"Inna ba zata barta ba"
"Data qyaleta kuwa aida hakan yafi,shikenan,idan zan fita zan baki saqo ki bata"
"Tohm,sai alfarma da nake nema" harya soma takawa ya tsaya
"Wacce irin alfarma halima?"
"Yaran nan nakeso tawucemin dasu,saboda indai suna nan din bazan huta yadda nakeso ba,idan suka danyi koda sati ne sai adawomin dasu don Allah" ta fada atausashe,saboda tasan halinsa sarai,baiso ko yaya yaranshi su matsa daga kusa dashi,shuru yayi na wasu mintuna sannan ya amsa
"Banaso halima,amma yadda kike kyautatamin dole naso abinda kikeso,su bita din,babu damuwa"
"Na gode qwarai"
"Madalla" ya amsa yana ficewa.


Saida saliman tayi mata duk wani gyara sannan suka shirya tsaf ita da yaran,sanda suke hada kayansu ahmad yashigo
"Umma inasu hanifa xasu?"
"Zaku anguwane,amma bazasu dade ba zasu dawo" nan kuwa ya narke kan saiya bisu,da dabara tasamu ta turashi dakin mahaifiyarshi,don tasanma babu batun mmn ummin tabarsu suje.


Sai data rakosu har farfajiyar gidan sunata murna zasu gidan innar, taga tafiyarsu sannan tadawo cikin gidan,sai takejinta sakayau da suka tafi yaran,koba komai kafin su dawo tana saka ran lamuran gidan su daidaita tagama gane kan komai da yadda zata bullowa kowanne matsala da yadda zata fuskanci komai.


Tana komawa ciki ta sakaya qofarta tayi kwanciyarta hankalinta kwance,tasan koma wacce matsala ce zata taso zata zo mata da sauqi,lokaci kadan kuwa bacci ya kwasheta .đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


ÂŠī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA GOMA*


*zaku iya saurarar litattafaina a tasha ta ta SAUTIN HIKIMA dake youtube,litattafan sune kamar haka*


*Alkawarin Allah*

*Daurin Boye*

*Kundin Kaddarata*

*Mutuncin Mace*

*Dangantakar Zuci*

*_karku manta,nan gaba kadan acan zaku dinga samun ci gaban kowanne littafi nawa*đŸ¤Ģ





Tunda ta kwanta bata farka ba sai bayan sallar azahar,tamiqe tana ambaton sunan Allah ganin lokaci na neman qurace mata bata sallaci azahar ba,bandakin dake falonta tashiga ta daura alwala tazo ta gabatar da sallar azahar din,tana nan saman abun sallar tana tasbihin data saba bayan kowacce sallah me 33 taji yunwa tasoma sakadarta,duk da haka bata katse ba amma saita qara sauri harta gama,tashafa addu'arta tamiqe tana tunanin abinda xataci.


Bata qaunar fita ma tsakar gidan bare tasan meke faruwa,batasan yata qarke ba,saboda haka saita jona heater anan falon nata tazauna tana jiran ruwan ya tafasa,mintina kadan ya tafasa,ta duba cikin dakinta ta laluba cikin kayan abinci da lokaci lokaci wanta yakan bata,dayake gidan basu da matsalar abinci majority bayarwa take,na qarshen ne daya aiko mata dashi bata bayar ba ta aje din,a sannan bikik bbn amir yakusa,batasan me zaije yadawoba shi yasa ta aje din.


Kwalin taliya ne dana indomie,ta farke taliyar taciro guda daya ta karya taxuba,ta ciro miyar nama data saka salima tayi mata daga fridge ta dora saman botikin da take tafasa taliyar donta dumama,cikin mintuna kadan tagama,taxuba tazauna sosai taci ta qoshi,saidai tana cidin taba tunanin su usman,sam bataji motsinsu ba,kodon ta rufe qofarta ne?.


'Yan halak kuwa tana gamawa saiga usman din yashigo,ta dubeshi sosai,fuskarshi qayau qayau da alama ma ba'a mishi wanka ba,ga jirwayen hawaye nan layi biyu kan fuskarshi
"Umma zanci" ya fada yana kallon sauran taliyar data rage
"Bakaci abinci bane?" Kai ya gyada mata
"Mama bata gama ba,tun daxu nakejin yunwa saita dakeni wai ba yanzu zata dora ba" mamaki ya kamata,wai wanne irin banzan haline mmn ummin ta tsiro dadhi,yaran nata take hadawa suda ubansu take musu horo gaba daya?,wannan ai shashancin banza ne da wofi,su yara me suka sani?,tana qara dasa rashin jituwa tsakaninta dasu bata sani ba,da alama bbn amir ya turasasata zatayi girkin ne,shine ta qulla muguntar qin dorawa da gamawa da wuri,banda haka gidan tunda mmn ummi tazo itama tasamu tsarin gama abinci da wuri saboda yara,haka tsarin mmn amir din yake,itama haka tazo tasamu ta dora akai,amma ace har uku na rana na neman gotawa amma ace ba'a gama girki ba?.


Da wadan nan tunane tunanen ta xuba ma usman abincin,tana zaune bayan tasha ruwa tana kallonshi yana cin abincin a yunwace hannu baka hannu qwarya,nan da nan yagama da abincin,ya nemi ruwa tabashi yasha,saiya bingire yahau bacci.


Ranar wuni tayi sur dakinta babu inda ta leqa,don bata da abinda zatayi a wajen,bata fito ba sai bayan sallar magariba,bayan tayi wanka ta sanya daya daga cikin dogayen rigunan atamfofinta,duk daba kwalliya tayi ba amma tayi kyau,tana ta qamshin turare,ta kama hannun usman wanda sai sannan yatashi a bacci,ya tsula fitsarinsa ta sake masa wanka saboda haka tayi nufin kaishi wajen mamarshi tasauya masa kaya.


Tsakar gidan nasu babu kowa sai hasken wutar lantarki,dayake haka unguwar tasu take akwai lafiyar samun wuta,sukanyi kwana uku da ita,shi yasa take cinikin ruwa da lemonta sosai,banda bikin nan da akayima da tuni ana sintitin zu siya,saidai tana tunanin gobe ko jibi zata koma sana'arta.


Duban tsakar gidan take adan kaikaice saboda yanayin tsaftarsa da tsarinsa bai mata ba,ba'a wani share yake fes yadda take masa ba,hakanan tawuce tana furta Allah ya kyauta,tadaga labule tashiga dakin mmn ummi.


Tana zaune falon tana shafa mai,da alama wanka tagama,ta daga kai fuskarta ba yabi ba fallasa ta amsa sallamar tana ci gaba da shafa manta.


Tana daga tsaye tasaki usman ya isa wajen mamarshi yaxauna yana gaya mata umma ce tayi masa wanka
"Wanne irin bacci kayi haka usman?" Ta tambayeshi tana dubanshi
"Ki barshi da yunwa ba dole yayi bacci ba,da kika hana yara abinci ke aisaiki hada kici" ta fada tana jefa mata harara,don sam ta kasa hadiye takaicinta,ta tsani a cuci yaro,shida bai gama sanin ciwon kansa bama bare na wani.


Dubanta mmn ummi tayi kawai batace komai ba tana ci gaba da shafa manta,itama saita juya tafice daga dakin,tana fitowa tanufi nata dakin tajiyo dariyar rufaida daga soro,saiga bbn amir na biye da ita,riqe take da hularshi,taci kwalliya da qananun kaya.


Sarai taga mmn amir na fitowa,hakan kuwa yayi mata dadi sosai,saboda haka ta tsaya anan tasoma shagwaba tana bubbuga qafafu kan saiya dauketa.


Shi sam baiga mmn amir din ba,saboda haka ya sungumeta,tahau kuwa qyalqyala dariya cikin jin dadi,bai ankare ba saidaya kusa da dakin rufaidan sannan yaga shigewar mmn amir dakinta da rufe qofarta,ya sauke rufaida da hanzari yana fadin
"Subhanallah,ashe matan gidan suna kusa" fuska ta turbune sannan tace
"Su waye matan gidan?,naga nima matar gidance,kuma kawai saboda wasu saika kama ka saukeni bayan baka qarasa dani ba" ta fada fuska kicin kici,cikin nuna fushi tayi gaba tashige dakin,yabi bayanta da hanzari yana kiranta.


Washegari mmn amir din tana zaune dakinta tana karyawa,yauma kamar jiyan bata leqa waje b,bbn amir din yashigo dakin cikin shirin fita kasuwa,ya kasa hada ido da ita saboda abun jiya,bayan sun gaisa yahau kame kame
"Kin zama hajiyar daka ko?,haka kawai kin koramin yara daga gida" kofin da take shirin kaiwa bakinta ta dakata ta dubeshi
"To ko aje a daukosu?" Ta fada cikin gatse gatse,don itasam bata sha'awar yaranma su dawo gidan nan kusa,saboda ta fuskanci take taken rufaidan,ko dazu tana jin ihunta daga daki,shima kuma yasan sarai sunji,abinda yasake sakashi kunya kenan,kuma ba wani abu yayi mata ba,kawai dan tsere ne haka da ba'a rasa ba na sababbin ma'aurata ya kamota shine tasaki wannan ihun,shi kansa abun yabashi mamaki don baikai tayi ihun ba
"Ni na isa,inna fa akai kaiwa su,aita isa damu gaba daya" shuru yadan ratsa don bata sake ce masa komai ba,sai kuma yayi gyaran murya
"Ni zan fita,ko akwai wani abun?" Kaita kada kawai tana ci gaba dashan shayinta
"Shikenan,saina dawo"
"Allah yatsare" ta amsashi a taqaice.


Har yakai qofa sai kuma tasake cewa
"Amm jimana" waiwayowa yayi yana dubanta,shi kansa sai yakejin wani shakka shakkarta yadda ta tsare gida,hakanan vabu wani abun magana da mutum xai tankata dashi,ta ga abubuwa amma kamar bata gani ba,taji amma kamar bata cikin gidan
"Don Allah kome zai faru kayi qoqarin kula da kiyaye tarbiyyar yaranka,don dukkaninsu sun taso,sannan kowanne da irin baiwa da kaifin basirar da Allah yabashi,so kome zai kasance yadinga zama cikin tsari da kiyayewa idanun yaranka" yasan magana ce tayi masa mai harshen damo cikin hikima da fasaha ba tare data kama sunan kowa ba,ya kuma fahimci inda tadosa,donko shidin yasoma wannan tunanin,saiya gyada kai
"Gaskiyane,nakuma gode da wannan tunasarwa uwar gida sarautar mata,Allah yayi albarka"
"Amin" ta amsa can qasan maqoshinta,saiya saka kai yafice daga dakin.


Daga nan dakin mmn ummi yanufa,don dama yakanbi girma girma ne,zaune yasameta itama ga abun karinta ta saka a gaba,saidai bata taba komai ba,sai usman da mubarak dake karyawa abinsu.


Qafarta na dore daya saman daya tana karkadata,kana kallonta sau daya zakasan akwai abinda ke cin zuciyarta kuma tanason ta amayar,da qyar ta iya amsa sallamarsa kamar wadda aka shaqe takuma bishi da banzan kallo,bai wani lura ba harsai daya gama biyewa yaranshi yana yiwa ummi wasa sannan ya dubeta
"Mun tashi lafiya" yasoma gaidata maimakon ita ta gaidashi
"Gashi nan kaga alama"
"To madalla" ya fada a taqaice,tunda yaga yanayinta da yanayin gaisuwarma yasan wani abune kuma na daban,bata rabo da qorafi sam a rayuwarta,kullum cikin matsala daga wancan sai wannan,shi yasa bai fiya jimawa a dakinta ba,hakanan ko ranar girkinta ba wani doguwar hira suke ba idan ba ita taso ba.


Da dafari sanda yake dokinta yana ganin tafi mmn amir iya komai saboda karatunta ya dara nata bai ganin illa da aibun dukka wadan nan halayen nata,saida tafiya tayi tafiya sannan ya tantance tsakanin aya da tsakuwa.


Yana dire ummi yace
"Xan fita,akwai wani abu?" Ya qarashe zancan yana dire mata kudin cefane,da harara tabi kudin kafin ta maida dubanta kanshi
"Wallahi wallahi kana bani mamaki jibril,bansan rainani dakayi dukka cikin matanka yakai haka ba,ku gama tiqa dariyar kaida waccar me zubin karuwan,kashig dakin mmn amir ka kusa kashe minti goma sannan nika shigo a wani tsaitsaye kabani kudin cefane,wato bauta itace aikina ko?" Yaran yaduba,baison wani cecekuce gabansu,wanda wannan dabi'ar mmn amirce takoya masa ita,da fari bai dauki hakan a bakin komai ba,sanda yake ganiyar neman auren mmn ummi yakan iya fadata da fada gaban yaran,koya caccaba mata maganganu,iyakaci tayi shuru,idan sun mata zafi da yawa tayi kukanta ta goge hawaye.


Sannu sannu sai Allah ya canzashi,wanda yasan ba komai bane yakawo hakan face addu'a data saka a gaba babu dare babu rana.


Yasha raba dare suna waya da mmn ummi suna kwance gado daya da mmn amir,baya shayi ko shakkarta,takan tashi ko kallonshi ba zatayi ba,tun a sannan bata da bandaki cikin falo sai tsakar gida,nan zata fito ta daura alwalarta ta koma falo tayi shinfida tahau sallarta,tabarshi shi kuma cikin dakin ya qaraci wayarshi har yayi bacci,wani lokacin bai sake ganinta sai zashi sallar asubahi.


Yakanyi mamaki idan washegari tatashi wasai tashiga sabgarta da yaranta,fuskarta cike da annuri,wanda duka hakan bai rasa nasaba da wannan sallar dare data kusa kwana yi.


"To tashiga hankalinta,idanma tanayine saboda muji n bata a gabana,saidai idan ita bata da tarbiyya mu muna da ita ehe" bai saurareta ba sai yunqurin danne zuciyarsa da yake,yasa kanshi yafice daga dakin.


Ya tabbatar da cewa kura ce tayi lafiya,ko kuma yakoma kan tarbiyyar mmn amir ne,inda ta sameshi a lokacin da yake a bbn amir dinsa bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman ba yana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login