Showing 3001 words to 6000 words out of 32781 words
Chapter 2 - Hangen Dala
qwatarwa kanki 'yanci ki barni nina qwaci 'yancina"
"Don Allah kiyi shuru mmn ummi,haba mana"
"Qyaleta halima,barta tayi,dani take zancan na rantse da girman Allah,tunda aka tada zancan nan kin hana kowa hutawa?,saikace ke daya ce macw cikin gidan nan?,to kiyi duk haukar da zakiyi ki gama,aurene dai babu fashi sai nayishi"
"Ka fada duk abinda kakeso mana jibril,ai namiji kake,batulu,namiji ai dama hankaka ne,gabanka fari bayanka baqi,ka manta lokacin daka dinga daukarmin qawuran bayanni babu wata?,kamanta sanda kake neman aurena ido rufe kanason nashigo gidanka na haska maka shi na zamemaka fitila saboda gidan ya maka duhu acewarka a sannan?,shine zakayimin butulci a yanzu?"duk ya tuna,ya tuna komai,nauyi da kunyar mmn amir suka dabaibayeshi,gashi da alama mmn ummin tonon silili takeson masa,da sake tada husuma,tanasone ya rasa kwanciyar hankali da biyayyar da yake samu wajen haliman kenan?
"kinga maryam,tunda ke baki da mutunci,bakisan darajar mijinki ba to xama babu dole,ki tattara ya naki ya naki ki tafi,don bazan zauna kina haddasamin bala'i da masifa ba tun yanzu"
"Ashasha,haba baban amir haba?,wannan ma aiba zance bane" inji mmn amir duk ranta a jagule,baiko sauraretaba yafice abinsa,don tabarmar kunya yakeso ya nade dama da hauka kada ya baro wani zance daya shafi tsakaninsa da mmn amir din.
Kuka sosai mmn ummin take,ta nemi gefan kujera taxauna tana ci gaba da kukanta,amir ta qwalawa kira tace yayiwa 'yan uwan nasa wanka,ya saka musu unifoarm tan nan fitowa,sannan ta sake maida hankalinta ga mmn ummi
"Kinga irinta ko?,kinga irin abinda nake gaya miki,akan wata can a waje da batama kai ga shigowa ba har yanzu zaki girgide aurenki,ki fita kibar yaranki wanda baki da yaqini ko tabbacin yadda rayuwarsu zata kasance,yanzu wa gari ya waya?" Itadai batace komai ba sai kuka da take faman sheqa,mamaki duk ya cikata tana tuna soyayyar da suka zuba ita da baban amir,ko a mafarki bata taba tsammatar irin haka zata faru ba,shuru ya ratsa dakin kafin mmn amir tamiqe tana cewa
"Ba inda zaki,ina zuwa" ta juya tafice daga dakin da niyyar baiwa baban amir baki,saidai koda taje dakin nashi bainan,ahmad ya gaya mata yafita,saboda haka ta sauya akalar tata zuwa dakin girki ta dorawa yaran ruwan tea,tanayi tana tunani cikin ranta.
******************
"Haba don Allah dear,nifa banason ka dinga bata ranka a banza a wofi,yanzu kamar kai ace kana teburin me shayi wannan ai zubarmin da mutunci kawai kayi" jim tayi ma wasu mintina sannan tace
"Aini wallahi banga wani abu da xakayimin da har zai kaimu ga haka bama,nidai don Allah ka koma gida koka qaraso nan gidam anty luba na hada maka break,tunda su duka basu damu dakai ba nina damu dakai" sake shuru tayi kafin daga bisani tace
"Toh shikenan,i love you" daga haka ta aje wayar tana murmushi
"Uhmmm,rufaida kenan,ke naga ko a jikinki ma,da aketa jiye miki shiga tsakiyar mata biyu" dariya tasaki kafin ta tabe baki
"Mata biyu ko muna mata,nifa wallahi anty ko a jikina,wadan nan niban daukesu a bakin komai ba,kada madai uwar gidan nan tashi taji labari,wadda ko isasheshen ilim boko bata da,yadda kikasan matar ladar noma,gwara gwara ma ta biyun itace kawai nakega tafi fada a wajensa fiye data farkon,haba anty,me zanji,kamata?,nida nake da karatu har matakin degree dame zasu tsoratani?,wancan mai kwalin diploma din ko dayar da banda kwalin secondry bata da komai?,wucenan wallahi"
"K'nnnn,to ai shikenan,yanzu yaushe zaki shiga kasuwar?" Dan shuru tayi sannan tace
"Ina tunanin anjima kadan,don akwai wasu magunguna da zan siyo wanda yakamata ace nashasu tun last week amma ban samesu ba,to tayimin waya ta kawo nazo na amsa" baki anty luba ta kama tana dariya
"Lallai rufaida,kurman tanadi kawai akewa auren nan" fari tayi da idanu cikin jin dadi
"Kedai bari kawai anty,burina kawai nazama tafisu,duk da yanzun ma nasan tafisu dince" dariya tayi ta juya tafice tana cewa
"Idan kin tashi tafiyar kimin magana inada saqo"
"Tohm" ta amsa mata tana maida kanta tasake gyara kwanciyarta,tanajin dadin yadda take juya jibril son ranta,kamar sitiyari a hannun driver ba tare da wata matsala ba,hakanan ba tare data nemi komai ta rasa ba.đī¸âđ¨ī¸đī¸âđ¨ī¸ *HANGEN DALA* đī¸âđ¨ī¸đī¸âđ¨ī¸
_Ba shiga birni ba_
Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi *Musa Huguma*
*BABI NA UKU*
"Adawo lafiya,Allah ya tsare" maman amir dake miqewa daga duqen gogewa baban amir takalma da tayi ta fada
"Allah yasa,shikenan babu wani abu?" Ya fada cikin sigar tausayi,har cikin zuciyarsa yana jin tausayinta,girmanta da qimarta na kuma daduwa cikin ransa,sai a yanzu ya gane ba qaramin haquri tayi dashi ba a wancan karon da yake fagamniyar kawo maryam gidan,gashi yanzun maryam din ta kasa daya cikin goman haqurin da ita halima tayi dashi,bayan shi a karan kansa yasan cewa bai mata kwatar abinda ya aikata ga halima din ba wancan lokacin
"Babu komai,saidai awo kawai da nakeso naje" baice komai ba yashiga laluba aljihunsa,yaciro naira dubu daya da dari biyar,cikin mamaki ta saka hannu ta amsa tana dubanshi,yadan saki murmushi
"Kije kiga likitan,sauran canjin ki riqe kya sayi wani abun a hanya" da mamaki saman fuskarta take juya kudin,ba kasafai yake mata kyauta irin haka ba,duk da cewa dama itadin ba wani damuwa tayi ba,don tana sana'arta tasaida ruwa da lemo da qanqarar yara,kuma ta rufa mata asirinta sosai,tana ciniki ba kadan ba,don ada firji daya gareta ta sake siyan wani ya zama biyu,daya tazuba ruwa zalla,daya tayi lemo zobo ginger da kunun aya da qanqarar yara,daya daga cikin abinda yasake kawo rashin jituwa da kishinta a zuciyar maman ummi kenan,don tana tsammanin bban amir din ke boyewa yana mata abubuwa ba tare datasan cewa guminta bane,da farko burga ta dinga mata na ita ta girmi sana'a,don miji ya tsaya mata,bata neman komai ta rasa,lokacin ludayinta nakan dawo,maman amir din takanyi murmushi kawai don tasan qarshen labari ko ba'a rubuta mata shi ba,itama tahau wannan siradin,sai a baya ta gane ashe duka kurace da fatar akuya,tadauki darasi ta kama sana'a tana bidar na kanta,sai gashi a yanxu bayan wasu shekaru abun yana neman zamewa maman ummin dan zani,ya fara tara iyali,hakanan mata biyu gareshi gata uku nan zuwa,tilas abubuwa da yawa suka soma sauyawa,wanda basuyiwa mmn ummin dashi kanshi dadi ba,suka dinga samun sabani,ta riga ta sangarce da saidai ta tambaya a bata,bata iya nema ba,hakanan take zaune,duk abinda mmn amir din tayi kuma ta zargi baban amir shiya mata,tun tana qoqarin fahimtar da ita harta tattarata ta watsar ta qyaleta,daga bisani idanuwanta suka gane mata.
"To na gode,Allah ya qara budi"
"Amin amin" ya fada yana sanya kai zai fice daga gidan,duk abinda ke faruwa mamn ummin tana bakin famfo duqe tana wanke kayan da yaranta suka cire,qasan zuciyarta tana jin kamar ra kama mmn amir ta daka,tana ganin duk ita ke daurewa baban amir gindi,har wani durquson goge masa takalma take da tsohon cikinta?,tana masa addu'a?,mutumin da zai musu kishiya aoba masoyinsu bane,kamata yayi su hada kai su yaqeshi harsai ya gaji don kanshi ya janye,amma tafi yarda da zancan hadixa data gaya mata idan ta tona zuciyar maman amir din qila fal take da farincikin za'a yiwa mmn ummin kishiya,tunda kishiya tabiyu tana bin wada kebi mata ne ba matar farko ba.
Tana kallonshi amma qyashi take tace masa a dawo lafiya,har yakai soro wata zuciyar ta tunzurata,donme zai baiwa mmn amir kudi amma ita data aika yara jiya suka gaya mishi ya bata cikon kudin me takalmi yace bashi dashi?,wuf ta miqe ta rufa masa baya.
Dab da zai fita ta rafka masa kira,da mamaki yajuyo yana kallonta,ta qaraso dab dashi fuskarta kamar tasowar hadari hannunta aqugu
"Wannan rashin adalcin da kake gwadamin ya isheni hakanan,jiya jiya nace ka bada cikon kudin takalmina kace babu amma yanzu ita ka narka mata kudi zataje awo,toni ka gayamin a wacce bolar ka auroni ne?" Sakato yayi kawai yana dubanta cike da dimbin mamaki,ta manta lokacin da yake bata ninkin kudin da ake buqata a asibitin,kuma yadauketa cikin motarshi ya kaita yadawo da ita,wani lokaci harda qwalama ta masu ciki amma mmn amir din koda ta nuna damuwa a fuska badai kaji abakinta ba,ta manta sanda take tsiro da ankon qawaye na babu gaira babu dalili ya dauka kudin ya bata ba tare da mmn amir din tace komai ba.
Kafin ya furta komai kira yashigo wayarsa dake gaban aljihu,ya zaro yana duban me kiran,rufaida ce,murmushi ya subuce masa wanda ya tunzura mmn ummi
"Ina magana dakai kayi banza dani kana kallon waya kanamin dariya kamar wata tababba?" Daga kai yayi ya dubeta sannan ya maida kansa kan wayar yana shirin dagawa fuskarsa washe da fara'a
"Baki da amsa ne ai" kafin yakai ga kara wayara a kunne tasa hannu ta warce wayar cikin fushi da fusata tana duba me kiran,dama jikinta ya bata ashe kuwa itace,a cike take da ita dama,wancan kwanakin ranar girkinta data turowa baban amir din saqonni har guda biyu,wayar na kusa da ita tadauka ta karanta,ta mata reply na zagi itama ta maido mata,kafin ta sake maida mata baban amir ya karbi wayar,da sauri ta kanga wayar a kunnenta,kafin tace komai kalaman sun daki kunnenta
"Honeeeyyyyyyy" muryar rufaida ta ratsa dodon kunnenta cikin shagwaba
"Honey din uwarko kona ubanki,shegiya karuwa,masifa annoba,to bari kiji na gaya miki,wallahi sai kinyi danasanin shigowa gidan nan in gaya miki,banza shashasha kawai,ballazaga mebin mazan jama'a" ta qarashe maganar tana barin soron da sauri saboda amsar wayar da baban amir ke qoqarin yi,ta saka sakata a qofarsu ta tsakiya cikin hanzari,ma'ana ta rufe baban amir din daga can soron do ta samu damar cin karenta babu babbaka,wata dariya rufaida tasaki kaman taba kallonta ta tabe baki
"Tooo....yau kuma da haukar da aka tashi kenan?,bari na soma tambaya cikin gawarwarkin daya aje gidan wace ke a ciki,ta farkonce kome bi mata don insan yadda zan ciwa mace uwa dakyau"
"Ta uwarkice,nace ta uwarkice wadda bata ramin kanta saina wani stupid" dariya takuma yi saboda tunda taji ta jefo kalmar bature to ba shakka maryam ce
"Kice dai bama ramin kanmu saina wani,ina cewa kema saura kika tarar shi yasa zan shigo na tayaki muci tare,to bari kiji,ni bana fada a waya,ki tanadi duk wata masifa da bala'i da makamanki da bomabomai saina qaraso gidan,don waya tayimin kadan wallahi,wawuyar mace wanda batasan inda yake mata ciwo ba,saikin gane uwarki bata koya miki komai na game da yadda zaka mallake miji,ki jirayi shigowar rufaida zaki gane komai da babban baqi" daga haka ta kashe wayar qit
"Abu ta kazar uba,ni zata zagawar uwa?,wallahi yau saita gane shayi ruwa ne" mmn ummi tasoma kumfar baki tana banbami tare da qoqarin sake kiranta,cikin haka Allah ya bawa baban amir damar bude qofar wadda sabida sauri sakatar bata gama shiga ba dai dai bata sani ba,yana shigowa yakai hannu ya finciki wayarsa
"Ka bani,wallahi saina rama zagina"
"Bazan bayar ba ki qwata idan kina da qarfi"
"Allah ya isa ban yafe ba wallahi,da ita da wanda ya daure mata gindi,macuci azzalumi,aina haka mukayi dakaiba sanda kaje zaka auroni,Alla ya isa ban yafe haqqina ba,kuma zagina da tayi sai Allah ya mana hisabi dakai" juyowa yayi yana dubanta cikin matuqar bacin rai,zaiyi magana kiran rufaida yasake shigowa
"Kiyi haquri don Allah my rufeee...." Abinda yasona cewa kenan cikin kwantar da murya kana yayi shuru na wani sakanni,wanda hakan yabaiwa rufaida damar jiyo bambamin da mmn ummi wadda ke tsaye a bayanshi takeyi,murmushi yasaki yana cewa
"Yauwa dear....na gode" baiko waiwayeta ba ya saka kai yafice yana ci gaba da wayarsa da rufaidan,wanda tana sane tajanyeshi dama,hannu maman ummi ta dora aka ta zube a wajen,tana jin kamar zata tayar da bori,ita baban amir yayiwa haka?,mutumin dako bacin ranta baison gani shine a yanzu zai watsar da ita yawuce abinsa?.
"Haba mmn ummi,wai sau nawa zan gaya miki wannan?,yanzu meye amfani ko ribar abinda kikeyi,maqota da masu wucewa duka sunajinki?,kafin a tsinewa baban amir sau daya an tsinemiki sau goma koda mala'iku kuwa" harara tayi kaman zata watsa mata saita fasa,cikin qunar rai da fusata tace
"Kome baban amir yayi yasamu goyon bayanki ne,tunda kinsan hannu daya baya daukar jinka,ba yadda banyi dake mutare abinnan ba amma kika qi bada goyon baya,yanzu kinsan muggan kalamai da alwashin da yarinyar takeci a kanmu nida ke?,to nida ke mu shirya kayanmu dukanmu gaba daya saita fitar damu" murmushi maman amir tasaki tana kada kai
"Kome ta gaya miki maman ummi kece kikayi babban kuskure,ina ruwanki da budurwar mijinki?,meye hadinki da ita?,kin fita kusa da mijinki,kin fita daraja koda ba haka bane to a wajen Allah haka ne babu kuma wansa ya isa ya kankare,koda tashigo gidan kuwa karki manta zata jima bata cimma matsayin dake kike kai ba,tunda ko banza kin rigata samunshi,kin rigata samar masa da diya,to me yayi saura?,me zai daga miki hankali?,maman ummi...." Ta kira sunanta cikin nuna da gaske zata furta mata maganar
"Inada yaqinin nafiki son abban amir,na kuma fiki kishinsa" saitayi jagale tana kallonta,magana takeson gaya mata kenan kome?
"Qwarai,ina tare da abban amir tun auren saurayi da budurwa,tun baida wani abun azo a gani,amma daga sanda yasoma neman aure na sanyawa kaina salama,inajin kishinsa kamar na mutu,ina kuka saboda kishi,ina kasa ci in kasa sha saboda kishi,amma dana fuskanci wanda nake abun saboda shi shi jin ransa yake kamar sallah saina sawa raina haquri da dangana,na kawo idanu na zuba akan duk wani abu da zaimin cikin sani ko rashin sani,wanda zumudi da rawar kaine ya sanyashi dama wanda yayi saboda radin kansa,yanzu gashi an wayi gari na barshi da kunyar abinda ya aikatamin a baya,na tsira da mutuncina da darajata a idanunsa saboda ban aikata duk wani abu da zai nuna rashin nutsuwata ba,babbar zubewar girma ko daraje a wajenki na matar gida budurwar miji ta zageki,bari na tambayeki..."shuru ta sakeyi tana dubanta
"Tunda kuke da baban amir har kika shigo gidan nan kin taba kiransa na daga wayar?,kona taba kiranki dai dai da rana daya?,kin taba jin muryata ko ganina?" Kai mmn ummi ta girgiza sannan tace
"Duka ban taba ba,amma Allah yagani ni mmn amir bazan iya koda rabin abinda kikayi ba,wayar dare,kiran dare amma ace duka baki nuna ko daukan mataki ba?,bazan iya ba wallahi,babu wata shegiya data isa ta takani wallahi ko wace saina maida mata,duk wadda ta nunani da yatsa saina karyashi" ajiyar zuciya mmn amir tayi tana kallon mmn ummin,shi yasa a rayuwa duk abinda kasan bakaso kada kayima wani,idan ba haka ba kuwa,watan watarana saiya fado a kanka,sai an maka,sai an ramawa wanda ka cuta ko ka cusgunawa koka zalunta.
"Shikenan,Allah yabada sa'a" ta fada tana miqewa gami da bar mata dakin.
******* **** *******
"Wai maman amir mu mmn ummi zata wulaqanta?,har ta ganmu ta dauke kai tawuce daki?haka ta koma?,to do n yaya zai qara aure shine me?,me za'a fasa?"
"Mtseweeew,kice fa kika damu wallahi,ni tayita kumburinta idan taso ma ta fashe,qarin aurene babu fashi sai yayishi ehe" murmushi kawai halima tasaki tana zama bayan ta aje musu kwanon abincin da ita da kanta tashiga kitchen tazubo musu,ganin mmn ummi dake da girkin bata da niyyar basu din,shuru tayi na sauraron qorafinsu da yadda kowacce ke zuba baqar magana kan mmn ummin,dubansu kawai take don bata data cewa,zuciyar musulunci da ilimin addini kadai daya ratsata yasanya taci gaba da mu'amala dasu,a shekarun baya babu tamkar ya maryam a wajensu,a sanda ya niyyaci qara auren babu abinda bata gani ba daga gunsu,basa boyewa har a gaban idanunta
"Na qagu wallahi maryam tashigo"
"Wai kinga matar yaya kuwa?,tabdi,wallahi yaya yayi zabe"
"Ke ai wannan kankat ce,tayi a rayuwa,ga ruwan mutunci zallarsa,bakiga yadda takesonmu muda umma ba"
"Kinga kyautar data aikowa umma da ita kuwa?,ke yaya kanshi fa yamato,donta iya soyayya"
"Nce gareta mafa,wallahi da yaya zai barta tsaf zata dinga fita aiki,amma tace masa ma ita tafison tazauna gida takula dashi" ire iren wadan nan maganganun dama wadansu wanda ba zata iya tunasu ba ba wanda basu fadi ba a gabanta,babu kara alkunya ko kawaici,sunsa qafa sun shure duk wani alkhairi nata kyautatawa da haba haba da take dasu,a lokacin ambaton Allah datake yawaita yi shi kadai yazame mata haske,uwa tagari kuma da take da ita tayi mata jagora,matakin farko data soma mata dannar qirji,ta kuma kwabeta,a yanzun taga alfanun hakan
"Wallahi maman amir ni yadda kike yafi komai burgeni" cewar jidda qanwar baban amir,sai a sannan tadago ta dubeta
"Kishi na hankali da nutsuwa ba irin nata ba na jakan mata,ai rannan rufaida ta gayamin komai,wallahi ta burgeni data rama abinda tayi mata" cewar jidda tana ci gaba dacin abincinta
"Indai rufaida ce dai dai da ita take,yarinyar da takejin quruciya da karatu akanta" dariya haula tayi
"Nifa harso nake naga ya zatayi idan rufaidan tashigo,gaskiya tana ruwa,maman amir kedai wallahi kinyi a rayuwa da kika iya kama girmanki,kaman baki da kishi" kai ta girgiza kawai tana fidda dan qaramin murmushi,sa'annan cikin nutsuwa ta dubesu
"Babu wata mace da bata da kishi,duk matar datace bata kishin mijinta toba shakka an samu matsala,kuma idan aka zurfafa bincike akwai wata a qasa,zan muku maganar daban taba muku makamanciyarta ba,abinda kawai zanja hankalinku akai shine,ku gane cewa dukkan mace macace,kuma ba'a cewa jifa idan yawuce kaina yafada kan uban kowa,koda baku da aure ke jidda kina dashi,kuma kuma wataran matan wasune,gidan wasu zaku je,cikin dangin wasu,Allah yasa kun fahimceni"
"Eh hakane,amma wallahi kawai dai duk wanda yadebo da zafine bakinsa,ni banga abun wannan kishi hakaba ina dalili?" Cewar jidda tana watsa hannu,sai kawai mmn amir din ta watsar da maganar tadauko musu wadda ta kawosun,wunin da za'ayi cikin gidan.
*BAYANA AWANNI*
Tunda ta kawo masa abincin ta tattarashi ta watsar,banda ma 'yan nasihun da maman amir tayi mata da babu abinda zai sanya ta saurareshi,shima cike yake da ita,hakan ya sanya baibi ta kanta ba yaci gaba dacin abincinsa,yana wasa da ummi daketa sabgarta saman carfet,lokaci lokaci yana diban abincin yana bata da cokali harya kammala,yasha ruwa yadauke ummin ya karkade mata jikinta yadorata saman cinyarsa sannan ya dubeta
"Me dame kike da buqata keda yara,inajin saura baifi sati uku ko biyu ba tariya" wani kallo ta watsa mata,kishi na tokare mata a qirji,ta rasa ma me zatace masa
"Kaje ka qarawa