Showing 9001 words to 12000 words out of 32781 words
Chapter 4 - Hangen Dala
da qawayenta,kuma na tabbatar zuwana zai quntata musu,ya hana bbn amir rawar gaban hantsi,sai naga tunqwal uwar daka"
"Kiga tunqwal uwar daka ko ko gano abinda zai tashi hankalinki ya hanaki barci?" Mmn amir ta fada cikin ranta,don tasan wanda yayi nisa bayajin kira,koda ta gaya mata baji zatayi ba,saboda haka ta aje ajiyar zuciya tana miqa mata kudin hannunta
"Allah ya kyauta,gashi inji hajiya tace zata kiraki" kudin ta harara kafin daga bisani ta amsa
"Nifa ku daina sakani cikin wannan sabgar taku,wadan nan sabbin kudinma da alama amaryar xai baiwa ya tsakuro a ciki ko?"
"Bansani ba wallahi,saidai idan kun hadu ki tambayeshi" baki ta tabewa mmn amir din sannan tace
"Yanzu ba zakije din ba?"
"Saikun dawo Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya,amma ki dauki ummi kawai basai kinje da yaran ba bare su bata miki kwalliya"
"Kin kawo shawara kuwa" ta fada har cikin zuciyarta,ita kuwa mmn amir tayi hakanne saboda kada aje a tafka wani abun kunyar gaban yaran,batason duk wani abu da zai sakawa yaran negative tunani kan iyayensu ya dinga giftawa ta idanuwansu.
A tsakar gida akayi clashing da bbn amir da mmn ummi,sai aka hau kallon kallo,kowa da abinda yake saqawa a ranshi,ran mmn ummi fal kishi take dubanshi,ko ran aurenta gani take baiyi kwalliya irin haka ba,yayin da gabanshi ya fadi,yayi tsammanin ba zataje na kamar yadda mmn amir tace,yanzu ya zaiyi kenan?,ga rufaida nacan tana jiranshi,duk saiya daburce,duka basirarsa tadauke
"Na shirya" ta fada tana tsareshi da idanu
"Toh....toh,ina zuwa" ya fada yana juyawa da sassarfa yafita daga gidan.
Daya daga cikin abokansa yakira ya gaya mishi abinda ke faruwa
"Kaga kasan ya za'ayi?,bari nazo na tuqaku,idan yaso sai aje a dauko rufaidan ka zauna dasu duka a baya nina kaiku wajen" dan jim yayi saboda yana tunanin yadda zata kaya,yasan yadda rufaida taci burin lokacin nan
"Yanzu hakan xa'ayi?"
"Kana da wata mafiyar ne bayan wannan?,idan akace za'akai wata sannan axo a dauki wata za'a bata lokacine kawai"
"Shikenan,sai kazo"
Cikin minti ashirin murtala abokinsa ya iso ya daukesu a motar,suka zarce gidan kwalliya inda tacan za'a dauki rufaidan.
Yana zaune a cikin motar yakirata yace gashinan ya iso ta shaida masa gata nan fitowa,a sannan anata kiciniyar rufe mata zip din gown dinta,saita aika qawarta ta sanya mata jakarta da kayan data cire cikin motar kafin tafito.
Da sauri xahra ta dawo
"Ke rufaida?,garin yaya,naga kamar bashi daya bane,shida wata mata ne harda yarinya a hannunta"
"Mata kuma?,yarinyar hannun tata macace?"
"Eh ba zata wuce shekara biyu ba" wani mugun ashar rufaidan ta lailayo ta maka
"Amma bansan matar nan jaka bace sai yau,zuwa zatayi wajen kenan?,lallai lallai yau zatasan da rufee take zancan,rabi'ah qyale rigar nan basai kin zugeta ba,shi zai qarasa zugewa da kansa" ta fada tana qwace jikinta,saita ciro wayarta daga jaka ta kirashi,bugu daya ya daga,ta narke masa sosai
"Kaga kasa qawayena sunatamin dariya wai bakaji dani tunda baka iya shigowa ciki mu fito tare" sosai ta rikitashi,saiya hau kallon mmn ummi dake qame a gefe ta gefan idanu
"Haba dai?,bari naxo to" ya fada yana kashe wayar
"Ina zuwa" kawai yace musu ya fito,saiya zagaya gefan murtala ya masa rada a kunne sannan ya wuce.
Tare suka jero shida ita,mmn ummi ta juya don gyarawa ummi xama a jikinta ta hangosu,wani abu taji yariqe mata wuya,ta zuba musu idanu sanda suke tahowar,sarai rufaida taga cewar ta gansun,hakan ya sanya tasaka hannunta cikin na bbn amir gami daci gaba da janye masa hankali har suka kawo bakin motar,idanunta nakan maryam din a fakaice,don babu laifi kwalliyar datayin ta mata kyau sosai,bata tsammaci ta iya ado yakai haka bama.
Shiya soma bude murfin motar yashiga sannan rufaidan
"Thanks my zuma" rufaidan ta fada tana kashe murya,murmushin yaqe yayi saboda mmn ummi dake motar,cikin tabara saikace qaramar yarinya soma tittirjewa
"Shine kayi shuru ba amsa?,wallahi kaci bashi,zaka sani"
"Yi haquri karki tasarmin yarinya" mmn ummi ta fada cikin matuqar tunzura,tanajin zuciyarta kamar zata fito,saita dan dago tana duban mmn ummi fuskatta cike da murmushin cusa takaici
"Au,ayyah antyna,kiyi haquri ai bansan kina ciki ba,ina yini?" Ta gaidata tana jefa mata wani kallon raini.
Lallai rainin hankalinta yakai,ita zata faki idanun bbn amir ta dinga jefawa kallon banza,sannan ta gaidata daga bisani,dauke kanta tayi tayi banza da ita,sai bbn amir din da baisan me ake ba ya waiwaya yana duban mmn ummin
"Ana gaidaki fa maryam" juyawa tayi ta jefawa rufaidan harara da kuma kallon banza sannan tace
"Lafiya" sama sama cikin shan qamshi,hakan ya batawa rufaidan amma saita share saboda tasan cewa lallai zata fanshe.
"Zugemin dear don Allah,tun daxu muke fama amma yaqi" sai kuma ta dubi mmn ummi
"Ki haquri anty zan dan ari mujinmu xai rufemin zip" wannan qaton asharne yazo bakinta,amma wanzuwar murtala a wajen yasa ta kasa furtawa,don tana ganin mutuncinsa kamar yadda shima yake ganin mutuncinta,hakanan tanajinsa yana zuge mata zip din tana wani shagwaba gami da cewa
"Yimin a hankali dear da zafi".
Maganar murtala yasanya mmn ummin taji kamar ta ciro zuciyarta
"Malama rufaida wannan shagwaba ai a bari mudan kauce ko?"fari tayi da idanu,maganarsa ji tayi kaman an qaramata qaimi ne
"Kai haba malam murtala,normal nefa,wannan aiba wani abu bane,na saba indai ina gaban dear,wani abun aisai an shiga daga ciki wannan kam ba wanda zaiji ba kuma wanda zai gani sai wanda yakai ido ko kunnensa"
"Hakane kam" ya fada yanason rufe maganar don ya fara shanshano wani abu.
Sanda suka fara tafiya qawar rufaida na gaba,hira suke ita da qawar tata suna kwasar dariya abinsu ganin kamar bbn amir din hankalinsa ya kasu kashi biyu,duk da tayi qoqarin janyr hankalin nasa donta cusawa mmn ummin haushi.
Suna gab da shiga wajen taron mmn ummin ta dora masa ummin datayi bacci saman cinyarsa
"Dan riqemin ita bari naje na kama ruwa nadawo" ta fada tana balle murfin motar tafice abinta,abun ya batawa rufaida rai sosai,don su kawai ake jira aga shigowarsu,ga qawayenta daga can qofa suna tsaye sun shirya kansu suna jiran shigowar tasu,sanda tasoma masa qorafin sunbar mutane na jiransu saiya dubeta
"Komu shiga ta tadda mu"
"Kan ubancan kayyasa" ta fada cikin ranta,a ranar auren nata,ranarta rana ta musamman kawai saiya wani sungumi 'ya su shiga dakin taro da yarinya a kafada,dan hoton da zatayi na amarya a kafadar ango shikenan yasha ruwa yake nufi ko kuwa,sam ba xata lamunta ba.
Wayarta ta dauka ta turawa zahra dake zaune gaban mota tex,ba'afi minti biyar ba zahran ta juyo cikin nuna kulawa
"Ita kanta babyn kidan gurin nan zai tasheta,gashi da alama taji dadin baccin,ko zaka kawota na sami zani na goyata ta kwanta sosai?"hakan sai yaga kamar yafi,hakan ya masa,saboda haka zahra ta zagayo ta amshi ummi,yayin da su kuma sukabi ta cikin ayarin masu tarbar amarya da ango suka dunguma dakin taron.
Sai data tabbatar ta bata lokaci me yawa sannan tafito daga inda take boye,dab da zata wuce securityn dake wajen taji ance
"hajiya,ko wannan diyarki ce?" Da sauri ta waiwayo,saiga ummi kan kafadarsa tanata baccinta,wani irin bacin rai take taji ya sauko mata,ranta yabaci sosai,har wani daci daci takeji saman harshenta,qarasawa tayi ta amsheta tana tambayarsa wanda ya bashi ita
"Watace ina tunanin qawar amarya ce"
"Na gode" tace dashi tana amsar ummi,cikin bacin ta durfafi dakin taron tana qiyasta cin mutuncin da zata yiwa bbn amir da rufaidan ma gaba daya,ita zai wulaqanta?,ya bada 'yarta kuma 'yarsa ajiya?,yana nufin budurwarsa ta fita tafi 'yarsa?,ashe haka bbn amir din yake sai yanzu ainihin kalolinsa suke dake bayyanar mata,lallai da gaske,bataga laifin matan da suke cewa duk wadda ta riqi namiji uba ta mutu marainiya,da gaskene namiji hankakane,gabansa fari bayansa baqi,ko a mafarki bata taba tsammatar haka daga baban amir ba,ta zaci ko a fuska kadai ta nuna batason abu ya barshi kenan har abada,ashe ita biqin jegon jaka takeyi.
Gab da xata shiga hall din daya daga cikin samarin dake gadin qofar yasa mata hannu
"Hajiya ina zuwa?" Daga kai tayi tana dubanshi cikin mamaki
"Ciki mana,ina zan shiga idan ba nan ba"
"Saidai ki koma gaskiya,an hana shiga"
"Kamar yaya?,kasan me kake fada kuwa?,kasan wace ni?" Dariya taga sun sanya gaba dayansu bayan sun hada idanu
"To hajiya ko wacece ke kuwa saidai ki haqura ki koma".
Nan ta tsaya musu bayani amma suka watsar da ita a wajen sukaci gaba da hirarsu,abinda yasake bata haushi yakuma daure mata kai shine bayan ita wasu da yawa sun shige,ta musu magana sukace sudin ai an gayyacesune ansan da zuwansu,wani azababben bacin rai yadinga cinta,kunyar yadda suka tozartata ya kamata,saita koma inda suka aje motarsu,abin takaicin a rufe take,murtala kenan shima yana ciki.
Wayarta taciro a gaggauce tasoma kiran bbn amir,lallai ba shakka dukkansu saisun gane kurensu,da saninsa kenan za'a wulaqantata?,ta kirashi a qalla ya kusa sau ashirin saidai bai daga,kasancewar yawa da qarfin hayaniyar dake wajen ba zata barshi yaji ba.
Kamar zata saki kuka haka ta rungume ummi ta soma takawa zuwa titi donta samu abun hawa ta wuce gida,don ba zata iya zama har sai an tashi ba,bacin ran da takeji ita kadai tasan irinsa,inda Allah ya taimaketa da jakarta ta fita,da a cikin motar aka kulle batasan ya zatayi ba.
Kai tsaye dakinta tawuce ba tare da kowa yasan tashigo ba,yaran duka suna dakin mmn amir sunma yi bacci abinsu,kayanta tasoma cirewa tana watsarwa,jin zuciyarta take kamar anyi gobara,xani tasamu ta daura ta zauna jiran dawowar baban amir.
Awa guda harda rabi wayarra tasoma ruri,data duba saitaga baban amir ne ke kira,wani mugun tsaki taja,tanajin wayar harta gama rurinta ta katse,ya sake kira har sau biyu amma wayar bata isheta kallo ba bare ta daga.
Qarfe sha biyu da rabi na dare yashigo gidan,sanda yarufe qofar tana jinsa,miqewa tsaye tayi tana sauraren qarasowarsa.
A qofar dakinta yaga takalmanta,hakan ya alamta masa ta dawo kenan
Dakin mmn amir yashiga ya taddata sunyi bacci duka ita da yaran,yau duka yaranma na dakin,mazan na falo ita da matan suna uwar dakinta saman gadonta,saiya koma da baya ya rufe musu qofar yadda ya ganta ya durfafi dakinsa.
Yana tsaka da cire shaddar jikinsa ta bankado labulen tashigo,saiya daga kanshi yana dubanta tare da karantar yanayinta,har saman fuskarta takejin zafi saboda bacin rai,ta tsaya gabanshi tana dubanshi.
"Basai kayi haka ba zaka tabbatarmin da cewa kai namiji ne,lallai ka nuna halinku da ainihin kalarku,jibril kai munafiki ne maciyin amana da zakaci mutuncina,ku hada baki da budurwar da zaka aura ku wulaqantani,nayi nadama da danasanin aurenka,ba abinda zance tsakanina dakai sai Allah ya isa!" Ta qarashe fada cikin daga murya da zafin rai,daidai lokacin da wayarshi ta dauki ruri,hannu yakai zai dauka tayi hanzarin rigashi kana ta daga tasa handsfree ganin sunan rufaida
"Dear,na manta kayana dana cire a motarka"
"Allah wadaranki kwarkwasa fidda me giji,baqar daga qarshenki ya kusa zuwa" ta fada tana katse kiran,sannan ta daga wayar zata kwadata d qasa,duk kuwa da cewa tasan tsadarta sarai,da hanzari ya tsaidata
"Karki soma,bani wayata!" Ko kadan bata saurareshi ba ta daga wayar ta makata a qasa,take ta tawarwatse saman tiles din.
Cikin bacin rai ua durfafota,zaginsa da fasa wayar suka hadu suka masa zafi sosai
"Idan ka iso karka barni da raina" ta fada tana tsaye qyam tana jiran qarasowarsa,yana isowar kuwa ya dauketa da wani lafiyayyen mari daya sanyata sakin qara saboda yadda ya ratsata,take rigimar ta sake zama sabuwa,ta soma masa jaye jaye cikin dakin naduk abinda hannunta yakai tahau bannatarwa.
Wannan qarar ita tatashi mmn amir,cikin tashin hankali ta fito daga dakin ta nufi dakin bbn amir din inda tajiyo hayaniyar tana tashi.
Daidai lokacin daya sake daga hannu xaikai mata mari mmn amir tashiga tsakani cikin hanzari,wanda kadan yarage yasameta
"Bban amir,meye haka?,meya sameka?"
"Ki qyaleshi ya aikata abinda yayi niyya,zai auro wata dama babu abinda bazai aikata ba!" Mmn ummi ta fada da madaukakin harshe,fuska jazur,saita waiwaya tana dubanta sanda bbn amir yace
"Idan bata ficemin a daki ba zan aikata duk abinda yazo raina" qin fita tayi sukaci gaba da sa'insa,harsai daya kusa sake kai hannu jikinta sannan mmn amir din tayi nasarar fitar da ita.
Cikin fushi yake furzar da iska me zafi,yasamu gefan gadonshi ya zauna yanajin yadda kanshi ke sake daukar caji.
Gefan gadonta ta zaunar da ita sai kuma mmn ummin ta fashe da kuka tana rufe fuskarta,ji take gaba daya duniya ta mata zafi,kamar duk wata qofar walwalarta da farinciki an tosheta,tsayawa kawai mmn amir tayi tana dubanta,tome xata gayawa maryam?,kome zata gaya mata ta jima da gaya mata shi,ita kanta tagaji da ganin wannan bala'in,tayi a qalla minti ashirin tsaye a kanta kafin tace
"Allah ya kyauta,ya sawwaqe" ta juya tafita daga dakin.đī¸âđ¨ī¸đī¸âđ¨ī¸ *HANGEN DALA*đī¸âđ¨ī¸đī¸âđ¨ī¸
_Ba shiga birni ba_
Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
*BABI NA SHIDA*
Tunda safiyar garin asabar ta waye tasake shiga fita hayyacinta,tunda ta idara sallar asuba ta kasa komawa bacci,sai zirga zirga da take tsakanin tsakar gidan soro zuwa nata dakin,idanunta kacokam yana kan dakin baban amir,wani mahaukacin kishi takeji,yanxu nan da wasu awanni kenan yaxama nasu su uku?,tashin hankali,saita dora hannunta aka tana neman inda zata sanya zuciyarta da ranta taji dadi,wani irin radadi da zugi gamida qunci takeji cikin zuciyarta,saita dauki wayarta ta kirayi hafsat.
Bugu hudu ta daga
"Ya akayi mmn ummi,mun tashi lpy"
"Babu batun tambyar lafiya game dani,tunda kin san babu ita,yaushe zaki shigo,wallahi hafsat jin gidan nan nake kamar wata qiyamata ko lahira"
"Karki damu ina sallamar babansu minal zan shirya na taho"
"Don Allah karki dade"
"In sha Allahu" aje wayar tayi tana furxar da iska daga bakinta.
Wayar tatace tasake ruri,data duba sai taga lambar qanwarta ce,ba jinkiri ta daga sai taji muryar mahaifiyarta,kuka ta sanya
"Meye haka maryam?"
"Umma yaune daurin auren fa?"
"Sai kuyi haquri ai,haka Allah ya dora muku"
"Don Allah umma kixo,don Allah"
"A'ah,nikam bazanzo wannan gidan naku ba,zandai turo miki ruqayya da zakiyya,sai yayarku duka zasu taho tare"
"Toh umma"
"Zasu taho miki da saqo,saiki sawa ranki haquri,tunda haka Allah ya dora masa" daga haka sukayi sallama,saita danji sanyi da maganar da sukayi da ummantata.
Qarfe takwas tasoma jin motsin yaran a tsakar gidan,tun cikin satin suma yaran ta sallamasu gaba daya,mmn amir ce keta hidima dasu,hattasu abun ya shafesu,ita kuwa maman amir ko a jikinta,saboda kai kawon yaran da kula dasu da takeyi ya dauke mata hankali gami da debe mata kewa da bacin rai,idan tana tare da yaran sai taji ta manta da wasu abubuwan.
Miqewa tayi ta isa bakin window tana leqen abinda yake faruwa a tsakar gidan,mmn ummin ce zaune saman kujera 'yar tsugunno,gabanta sabbabin shaddodine ruwan omo,saman cinyarta wasu daga wandunan yaranne tana saka musu tazuge,mubarak na tsaye a kanta da alama yayi wanka ya shafa mai yana jiran ta gama saka masa tazugen tabashi ya saka,yayin da mmn amir din ke aikin tana gyarawa hanifa wankan da takewa usman.
Wani baqinciki da bacin rai ya kamata,wato har wani anko ya yiwa yaran na xuwa daurin aurenshi kenan,ita batama sani ba?,kafin tayi kowanne yunquri baban amir din yayi sallama yashigo gidan,hannunshi dauke da wata shaddar kalar ta yaran,da alama tashice ya amso.
Qurawa fuskarshi idanuwa tayi sanda yake qarasowa gaban mmn amir,fuskar da ada babu wata fuska da takeso da qaunar gani amma a yanzu babu fuskar data tsana take jin haushi da takaicin gani irinta
"Sannu da aiki maman yara" ya fada yana murmushi,har cikin ranshi kuma yanajin dadin yadda take shirya yaran zasu daurin auren tare dashi
"Yauwa" ta fada ciki ciki fuskarta sam babu wannan fara'ar daya saba gani,duk sai yaji jikinsa yayi sanyi,tayi qoqari matuqa kuma tana kanyi,yasani cewa baiwa Allah yayi masa da uwar gida,wadda ta tsaya kai da fata wajen ganin ta hade kan gidan waje daya,ya tabbatar da maryam ce uwar gidansa tofa sai abinda hali yayi,yasani sarai cewa suk maigidan da yayi rashin dacen uwar gida toya kade ya gama yawo,duk wadda zai aura daga baya mawuyacine idan batayi koyi da wasu dabi'u nata ba,uwar gida itace ginshiqin gida,itace kuma kamar turken mai gida da dukka wani ahu daya mallaka,idan ka dace a ita saika godewa Allah.
Yanayin dayaga fuskarta yasa ya gaza wucewa,saiya soma kame kame,inda daga bisani yac"wannan zaman bazaki gaji ba?,kawo tazugen na qarasa saka musu kije ki huta"kai ta kada
"A'ah,barshi kawai,aiba lokacin hutu bane yanzu koda naso na huta din" haka ya tsaya yana ci gaba da tayata gyara kayan yaran har kowa ya sanya nashi sannan ya shige dakinsa donya shirya shima,ta bishi da kallo tanajin wani bacin rai da kishi yana taso mata,ta dauke idanunta taba karanta "hasbiyallau la ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim".
Mmn ummi dake bakin window din tana kallonsu ta saki labulen cikin tafasar zuciya,wato ta fuskanci wani dama dama yake da mmn amir,itace banza kenan?,fushinta banza farincikinta banza?,anya ko matar nan haka ta zauna?,sai wani sashe na zuciyarta ya gargadera,don tunda suke da mmn amir din nata taba ganin wani abu guda daya tattare da ita daya sata shakka ba,abu dayane tasan cewa tana da yawan azumi kamar ma bata damu da abinci ba,hakanan tana da yawan tashin dare harta dinga zargin ada wani abu take cikin daren,saita gane sallar dare ce.
Sai data zauna saman kujerar sannan ta qwalawa yaran nata kira da sunayensu daya bayan daya,usman ne ya soma shigowa
" gani umma"cikin dakinta ta nuna mas"shiga ka cire wadan nan kayan ka samu wasu cikin kayanka ka saka"dum yayi yana dubanta sannan kuma yace
"Amma umma,wajen daurin aure zamuje"
"Iyee,ni kake gayawa wajen daurin auren kishiyar uwarka zakaje?,to shiga kayi yadda nace maka tun ban tashi na zazzabga maka mari ba" hakanan yaron yashige ciki sum sum,ya sauya kayan yafito,zai fita ta tsaidashi ta nuna masa saman kujera
"Zauna nan" ta fada tana dubanshi,haka yakoma yazauna,yayi lakur saman kujerar har zuwa sanda usman yashigo.
Cikin murna yana nuna mata shaddar jikinsa
"Umma,kalli sababbin kayana zamuje unguwa mu dasu abba dasu ya amir"jawoshi tayi da sauri sannan tahau tube mishi kayan,saiya riqe rigar da hannunsa yana kallonta
"Nidai umma karki ciremin,karki batamin kwalliyata,mama ce ta sakamin unguwa zamuje"
"Unguwar ubanka ko?,maza ni kama min bakinka a nan" yaro da baisan hawa ba baisan sauka ba,ganin tacire kayan da gaske kuma tana niyyar sanya masa tsofaffi saiyahau kuka da ihu harda tsalle,haushi ya cikata,ta janyoshi tahau duka,tanajin mmn amir dake tsakar gida tana tambayarta lafiya amma tayi banza da ita tashiga takoma saman kujera tayi zamanta tana baiwa ummi da kukan usman ya tasheta nono.
Bai gaji ba yazauna dirshan yaci gaba da kukanshi,har bban amir yagama shiryawa,ya gaji dajin kukan saboda haka ya daga lebulen yashigo yana kallonta
"Me aka yiwa yaron nan ne wai?" Sai idanunsa ya fada kan ahmad dake zaune kan kujera yana rarraba idanu
"A'ah,kai kume me kake