Showing 30001 words to 32781 words out of 32781 words

Chapter 11 - Hangen Dala

jikinta,wanda su kansu sun bata ran bbn amir din,donme zata dinga irin wannam shigar tafito da ita har waje?,bayan tasani yana da yara wadanda suka fara tasawa,kuma kowa yasan yadda yaro yake da saurin fahimta da tsinkaye,dukkaninsu da idanu suka bita harta fice,yayin da gefe guda farinciki yacika zuciyar mmn ummi,tunda ko banza yau rufaidan tasha fada a gabansu,an kuma bata rashin gaskiya.


Waiwayowa yayi yana dubansu su biyun,duk da yadda ranshi ke masa suya tare da sake shiga mamaki kan sabbin halayen da rufaidan ta tsiro dashi,idanunshi akansu yace..đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


ÂŠī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA UKU*



*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*


*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_

13



"Idan ita batasan tsarina ba,batasan qa'idar gidan ba aiku kun sani,saboda haka daga yau koda wata cikinku keda lalura ban yarda abarmin yara da yunwa ba,kada irin hakan tasake faruwa kunajina?" Mmn amir ce tasoma magana,cikin qanqan dakai da tausa murya
"In sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba", mmn ummi bakinta taja ta tsuke,duk da ranta ya mata dadi na fadan da yayi ma rufaidan,kuma wala'alla yaudin suyi kwanan takaici,daga haka mmn amir ta miqe tafice,mmn ummi ma tarufa mata baya saboda shiga kitchen tadebo abincin.


Shima miqewa yayi yafice da ummi a hannunshi wadda taqi yarda ya ajeta,yunwa yakeji sosai don yau yajima akasuwa,abinci yake da buqatar ci,don haka yawuce dakin rufaidan kai tsaye.


Zaune yasameta a falo,qafarta daya kan daya,kallo daya ta daga kai tayi masa ta watsar dashi taci gaba da kada qafarta.


Falon cike da sautin waqa,baice da ita komai ba yasoma wucewa ya rage waqar sosai ta yadda ko tashinta bakaji kwata kwata sannan yadawo yazauna kan daya daga cikin kujerun falon yana dubanta.


Qwarai take bashi mamaki,batasan idan tayi laifi ta nuna tayi laifi ba bare ta bada haquri,kullum ita keda gaskiya,saita dauki fushi da kumbure kumbure,tsahon zamansu bazai iya tuna sau nawa tace kayi haquri ba,saiya kauda wannan tunanin yace
"Bani abinci" kai ta tada ta dubeshi kana ta dubi yarinyar hannunshi wadda tuni ya direta saman kujera ta kama kujerar tamiqe abinta tana ta tsalle,saikace shi yafi kowa yara a duniya,motsi kadan yaranshi bini bini yadebo mata yara yashigo mata dasu,ba shakka sai tayi maganinsu,ba zata dauki wannan abun ba wlh,a rubar mata da carfet da katifar kujeru tun bata haifi nata ba ina dalili?
"Saikamaida yarinyar tukunna sannan kaxo kaci abincin" ta fada taba gyara xamanta,yabita da kallo mamakinta yana sake kamashi,yana ganin abun kamar almara amma yaga yana neman wuce gona da iri
"Ki bani abinci kawai ba ruwanki da ita" yafada adan kausashe,saita sauko tanufi inda abincin yake tana qunquni qasa qasa,sarai yajita amma saiya danne kamar baiji ba.


Tun a idanun yaga abincin bai masa ba,uban mai saman miya,ga qamshin attaruhu tun baikai gaci ba,abinda sam baicikin tsarinsa,saboda basir da kuma yara da kowa yasan ba kasafai sukeson abincin mai yaji ba,matan gidan sun riga da sun saba ma,kuma itadinma yasan ta jima da sani din tun kafin suyi aure,har sukayi auren ma bai fasa gaya mata ba idan hira tashigo,to amma sai bai tanka ba,harta gama zubawar ta tashi,ya sanya cokali yasoma ci.


Lomar farko yasoma jin matsaloli game da abincin kala kala,na farko miyar tacika gishiri,sannan bata gama soyuwa ba,baya ga uban mai da yayi mata yawa,na biyu kuma ita ka ta shinkafar batayi laushi na,gatanan dai tayi tsage tsage,a haka yadaure yatafi loma ta biyu wanda anan yaji ya kaure kan harshensa,tilas ya dakata ya dubeta
"Bani ruwa" ya buqaceta da hakan,tunda tsurar abinci ta dire babu mahadi,dan qaramin tsaki taja bayan ta aje wayarta data koma charting dinta ta dora daga inda ta tsaya dazun,don a rayuwarta ta tsani adinga tashinta ana aikenta,ta isa qaramin fridge dinta taciro ruwan babu cup ta aje masa takoma tazauna abinta,baice mata komai ba yadauki kofin yabude yasoma sha.


Daga can dakin mmn ummi kuwa usman ne ya wurgar da cokalin hannunsa yana yarfar da hannun gamida dalilen yawu saboda azabar yaji,mubarak kuwa tuni idanunsa sun hada qwalla donshi yafi usman ma qin abinci mai yaji,dai dai sanda mmn ummi tafito ashirye bayan tayi wankan da masifa ta hanatayi daxu ta dubesu
"A'ah,wannan wanne irin iskancine wannan?,me haka?"
"Yaji umma" usman yafada yana shirin fashewa da kuma,saboda yunwar da yakeji yaso yaci abincin sosai amma babu hali
"Wanne irin yaji?" Ta fada tana zama gefansu,gamida daukar cokalin tayi loma daya ta dandana
"Um,um_um,umum" ta fada tana gyada kai
"Tabdi" ta sake furtawa,ita abun ya mata dai dai,domin kuwa tasamu hanyar cin zarafin rufaida a daren nan,zata qarasa huce takaicinta,saita dauki kwanon abincin tace
"Ina zuwa" fuuu tayi dakin rufaida.


"Garin yaya rufaida abincin nan yayi yaji haka?" Ya jefa mata tambayar yana kallonta,sauke wayar tayi ta dubeshi
"Yafi dadi ai,abinci babu yaji kamar na 'yan ruwa?"
"Amma dai nasha gaya miki ba'amin girki mai yaji ko?,saboda ulcer da basir,ga kuma yara"
"To nidai gsky haka na iya girki na" kafin yace komai mmn ummi ta bankado labulen tashigo riqe da kwano a hannu
"Wannan wanne irin abincine haka?,bbn amir kaga muguntar da matarnan tashirya ashe ko?,to gashinan dai yara sun kasa ci,babu abinda suke sai kuka,wannan ai mugunta ce da rashin mutunci".


Da sauri rufaida tamiqe rana aje wayar hannunta
"Ke maryam ki iya bakinki ki kama kanki,kibar ganin ina daga miki qafa wallahi tausayinki nakeji,banason hauka banason dabbanci kinji ko?,banson jahilci da qananun maganganu....."
Sakin farantin mmn ummi tayi ya tarwatsewa rufaida a daki,ta daki qirjinta tana cewa
"Waye jahilin waye dabba?,wallahi yau saikin gayamin...."
Tsawa bbn amir ya daka musu wadda ta tsaidasu daga yunqurin da kowacce takeyi.


"Waiku wadanne irin mutanene da basu qaunar zaman lafiya sai tashin hankali" cikin raunin murya mmn ummi tace
"Nice bana qaunar zaman lafiya ko ita?,kana gani yautun safe da kalar wulaqancin da takeyi cikin gidan nan amma banga wata cikakkiyar tsawatar mata da kayi ba,yanzu wannan zancan danazo dashi shine rashin qaunar zaman lafiyar?"
"Da kika shigo baki ganni ba zaune?,me yasa baki mutuntani ba kin kawomin qara kigani mezanyi akai?"
"Meko zaka iyayi tariga tashanye ka tamallake ka,sai abunda taga dama takeyi"
"Ya isheni maryam,wuce ki koma dakinki" yafada cikin bacin rai yana nuna mata hanya da yatsa,ta fuskanci yana dab da kaiwa maqura,saboda haka ta juya tana cewa
"Ni duk wanda ya cuceni Allah ya isa wlh,kuma kuyi lokacinku ne,akwai ranar qin dillanci ranar da hajar mai gari ta bata" da wadannan qananun maganganun tajuya ta fice.


Tsahon mintina falon yadauki shuru,saiya dauki ummi yafice,ya direta a qofar dakinsu ba tare daya shiga ba yajuya yafice daga gidan.


Da sauri rufaidan ta qarasa gaban kwanon abincin daya tashi akai tadauki cokalin tayi loma daya,saita hau zaro idanuwa saboda yaji da gishiri,itakanta batasan yajin da gishirin sunkai har haka ba,yaron daya kai mata markden dai yace tarage attaruhun tace haka takeso,yakai mata haka,saita koma tazauna tana jin yadda shinkafar ta tsaitsaya mata a maqogaro tana raba idanu,tare da da tunanin yadda zata nade tabarmar kunyarta.


Can bayan layinsu ya zagaya wajen wani maisaida fura da noni,gefansa kawai mai balangu,ya siya leda daya mmn ummin da yaranta,leda daya mmn amir don yasan bazata iyaci ba itama don bata qaunar yaji,leda daya tashi,yadawo gidan yashiga dakin mmn ummin,tana zaune ita daya,yana iya jiyo motsin yaran cikin dakinta,ya aje ledar yana dubanta
"Maryam,ki fita daga idanuna,banason fitina banason tashin hankali,ki kiyaye tun baki kaini bango ba" daga haka bai saurareta ba yafice yashiga dakin mmn amir.



Fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa sallamarshi,itama yamiqa mata ledar idanunshi nakan farantin dake aje gefanta tarufeshi da wani farantin,da alama itama tadebone ta kasa ci,ya tsammaci zatace wani abu,saidai batace komai ba har ya mata sallama yafito.


Cikin ranshi yadinga ganin qima da martabarta,har kullum kunya sake kamashi take idan yatuna abinda ya aikata mata a baya,sanda yana kan ganiyar neman aure da aurenshi da maryam,yakanji kamar yajawo baya yagoge duk abinda yafarun a baya,saidai babu damar haka,saidai danasani da hausawa ke cewa qeyace.


A baya idan tayi kawaici irin wannan yace munafuncine dason goga masa baqinjini wajen mutane,idan tayi magana yace tacika qorafi duk da ba maganar takeyi ba,duk wanda tayi bata tsira ba,sai a yanxu martabarta take sake fitowa muraran,darajarta take sake yauqaqa a idanunsa.


Wannan karon dakinsa yakoma,yayi shirin kwanciya abinsa kana ybude gurasa balangu da furar yasoma ci.


Baiyi nisa ba taturo qofar dakin cikin kayan barcinta tashigo dauke dai da kwanukan abincin,donta tsara abinda zatayi,dubanta kawai yake takaici yasauko masa,rigar barci ce transparent ana iya ganin pant da bressier dinta,amma ace haka ta ratso cikin gidan zuwa dakunanshi?,yanzu idan wani cikin yaran yaganta fa?.


Sai data aje abincin sannan ta bata rai sosai tana dubanshi,baqinciki biyu,yasiyo abinsa yanaci ba tare daya bata nata ba,sannan ga girkin datasha wahala akanshi baici ba
"Yanzu haka xakamin dear,wallahi na fuskanci an riga da an gama shiga tsakaninmu,randa nasoma girkina na farko ace kaqici ka bige dacin abincin kan titi?"saita fashe da kukan kissa wanda yadinga jinsa har saman kanshi,wannan matsaloli da yawa suke,daga ka toshe matsalar waccar saita waccar ta danno kai?,daga wannan sai wancan?.


Ganin kukan nata nayin yawa yasa dole bayan ya kammala cin abincin yakira sunanta,tadago da hawayen qarya tana dubanshi.


"Gaba daya rufaida kin bani mamaki,yadda na tsammata gaba daya ban tadda haka daga gareki ba,na zaci cewa zan sake samun wani nutsuwar da kwanciyar hankaline daga gareki,sai gashi kina neman bani mamaki,ina shirin ganin abinda ba haka ba daga gareki" fuska tadan yamutsa,saboda babu abinda zancan nasa suke mata sai bata mata rai,itafa arayuwa babu wanda ya taba mata kwatankwacin abinda jibril din yake mata yanzu,donko saurayi magana daya zai gaya mata yanzu ta sauyashi,bata lamunci a dinga gaya mata magaba kai tsaye ba
"Kaman yaya?"
"Kamar yadda nake gani" ya bata amsa shima kai tsaye
"Yanxu duk qoqarin da nakeyi kai baka gani,baka yabamin saima kusheni da kawo matsalolina,duk yadda nake haquri a gidan nan baka gani ba?" Ta fada cikin kuka,don ita harga Allah bata gano laifinta ko daya ba,sai tarin laifinsa dana matansa
"Tunda hakane saika fadi dame dame nake maka".


Tiryan tiryan ya lissafo mata komai,saidai cikin zuciyarta tsaki take ja kawai,tanason maida masa wata zuciyar na kwabarta,saboda tana lissafe nan da rana ita yau zata amshi kudin ankon bikin qawarta,kuma taji daga bakin qawayenta masu aure,idan kika sake wani abun ya hadaku yana iya hanaki kema abinda kike buqata,saboda haka ta faki idanunshi ta yatsina fuska sannan tace
"Shikenan naji,xan gyara"
"Da dai yafi,saboda na auroki ne don dukkaninmu munason juna,na auroki don dukkaninmu muyi farinciki datarayyarmu da juna har lahira,abu nabiyu,irin wadan nan kayan banaso kina yawo dasu cikin gida haka,saboda yarana da sauran masu shigowa wadanda suke ba hurammanki bane,a qa'ida ta addini bai kamaci ace suna ganinki haka na,bugu da qari tarbiyyar yaran gidan,kinsan yaro da riqe abu da fahimta,bare kusan dukkaninsu sun riga dasun tasa,balaifi zaki iyamin ado dasu sanda muke daga ni saike,don Allah ki lura ki kuma gyara" wani abune yasake tsaye mata a wuya,kusun uba,waime jibril yake nufi ne?,kwalliyarma da zata ringa da qananun kayan zai hanata,abinda taci vuri ta kashewa kudi,aqalla ita kanta batasan nawa ta kashe wajen siyan kayayyakin ba,gaskiya ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa,bataga uban wanda ya isa ya hanata shigar datayi niyya ba cikin gidan,wannan shine babban abinda zata daina suyi galaba muraran a kanta,ba shakka dole ta rage mishi son yaran nan ba,idan ba haka ba ita za'a cutar da yawa,kuma akwai dambarwa ba 'yar qarama ba,amma a fili saita cuno baki
"To naji" kai ya girgixa cikin mamaki,wasu lokutan halayanta kanyi kamanceceniya dana mmn ummi,mmn amir ce mace daya tak dakan saka gwiwoyinta a qasa ta bashi haquri a duk sanda tayi masa laifi.


Da wannan tasamu tasha kanshi,komai yawuce,don dama shi bamai daukar dogon fushi bane ko a baya,idan yayi dogon fushi to tabbas ka qureshi ne.


**** **** ****** *****


Washegari hakanan badon taso ba tatashi da wuri ta dafa mishi shayi da chips,kamar xata fadi haka ta dinga ji saboda tashin wurin datayi,haka ta dinga aikin takaici nacin ranta,saboda tariga ta saba a gida bata tashi a irin wannan lokacin,suma sun sani ba'a tashinta sai sanda taci baccinta ta gyatse,ko aiki zaiwa mamanta kanta kuwa ba ruwanta,idan ta tashinma batason aikin wahala,zata karbi aikin da zatayi daga zaune ne,shima idan yadauki lokaci saita kawo wani uzurin da zata aje aikin ta barshi.


Bayan ta sallameshi saida ta koma takwanta din kuwa,bata tashi ba sai bayan goma na safe,yara tuni sun soma jin yunwa,tadora shayi a gurguje ta dora musu indomie,ta jibagata ta sauke sannan tashiga sharan gidan,wanda kafin tagama ta jigata ainun,haka ta dinga qorafi da surutai ita kadai,yaran kuwa duk wanda yayi kuskuren yin wani abu ba dai dai ba zaici gyatumarsa.


Mmn amir ce data fuskanta tayi hikimar tattare yaran a dakinta,don tasan tabbas idan mmn ummi ta fuska ta to yauma sai an raba abun fada,itakuwa sam batason tashin hankali,uwa uba kuma tasan hankalin jibril xai tashi fiye da jiya,abinda ita kuma bata fata kenan.


Haka taci gaba da karbar aikinta harna tsayin kwana biyu,wanda kafin sannan ta jigata qwarai,ta zaci abun akwai sauqi bata tsammaci haka ba,randa zata sauke girki tanason ta huta amma tana tsananin kishin miqawa mmn ummi jibril,babu yadda ta iya haka tasaki mmn ummi ta kama,saidai taci alwashi itama kafin mmn ummin tafita saita baro musu bacin rai.


Tunda gari ya waye ranar da zata karbi girkin take cikin walwala da farinciki,bini bini minti daya biyu kaji ta saki waqa wadda ke cike da habaici da baqar magana,sosai ran rufaida yabaci don ta gama yankewa da ita mmn ummi take,tayi qwafa ta quduri abinda zata mata ta huce yakai sau shurin masaki.


Mmn amir kuwa batasan ma me suke ba,tana kwance abinta tana duba wasu daga cikin litattafan marubuta masu ma'ana,sosai takejin dadin karatun,don tana qaruwa da abubuwa a ciki ba kadan ba.


Bayan yagama shirin fitarsa daga dakin rufaidan,yasoma leqa mmn amir din,tana zaune tafito da duka kayanta tana gyarawa da safen kasancewar bata da wani aikin yi,lemon siyarwar ma ta dakata dayi harsai ta sauka,sai ruwan pure water kawai da take saidawa yanzu,tanason bayan tasauka dinne tasake fadada sana'artata,ta qara wasu kalolin lemon da sauran abubuwan sanyi nasha.


Jin shigowarshi yasanyata fitowa falon nata
Kamar koyaushe suka gaisa ya tattambayeta jiki tace alhmdlh
"Idan nadawo ku shirya zamuje mu dubo hajiya bata jin dadi"
"Ashasha,me ya sameta?" Ta tambaya cikin nuna damuwa
"Ciwon qafarta ne yatashi"
"Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bata lafiya"
"Amin ya rabbi" ya amsa yana sanya hannunshi cikin aljihunsa.


Dubu guda yaciro
"Kekam kawaicinki kamar yaso yayi yawa"batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,kana tace
"Name fa?"
"Indai ba asibiti zakije ba,ko kin qure da yawa bazaki bude baki kice bbbn amir bani kaza ba,yanzu yadda baki girkin nan baki samun 'yar biyar da 'yar naira goma ya kenan?" Murmushi tasaki kawai ta kada kai,babu mutumin da zaice baison ace mishi ungo,to amma idan ya kasance bake daya bace wajen miji,sa'annan bani baninki tayi yawa to babu shakka zakifi kowa baqinji ne a cikinsu,bugu da qari Allah S W T ne kadai baya gajiya da roqo,wannan shine cikakken alfanun sana'a a wajen diya mace.


"Baka ganin ina saida ruwa da lemo?" Ta fada a tausashe
"Ah,kice hajjaju ce nan a gabana" yadda yayi maganar saiya bata dariya
"Duk da hajjajun ce dai ungo amshi wannan ki riqe,don nasan lalurorinku na masu ciki,kar a je a rugurguje ribar da jarin duka" hannu biyu ta amsa zata karba tana godiya saiga rufaida tashigo.


"Idan kagama inada magana" ta fada idanunta akan kudin hannun mmn amir da take niyyar ajewa,wani takaici ya kamata,ai ita datake kan ganiya ita yafi cancanta yadauki kyauta irin haka ya bata,wayasanima ko kullum sai ya bata?,shi yasa baya fashin shiga,kuma dakinta kullum yake fara shiga
"Ganinan zuwa muje" ya fada yana nuna mata hanya,yadda bata kula mmm amir din ba itama saita sake tsumewa,tayi kamar nata ganta ba,tunda aqa'idance ita yakamata tasoma gaidata,na farko ta girmemata a wajen miji,nabiyu kuma har dakinta ta taddata
"Shikenan saina dawo"
"Allah yatsare" ya amsa mata kana yafita.


Yana fitowa sukayi kacibus da mmn ummi wadda aketa gyare gyare tun safe za'a karbi miji,yayin da rufaida ke daga kitchen tana diban abincin kari,saidai duka kunnuwanta na tsakar gidan,gaisawa sukayi itama sannan yamiqa mata kudin cefane,ta amshe cikin walwala ta rakashi da addu'o'i,kana itama yashaida mata zasu duba hajiyan idan yadawo,wani murmushi rufaida tasaki,anzo wajen,plan dinta zai tafi dai dai kenan
"To Allah yakaimu" ta amsa ba tare data tambayi me zasuje yi din ba.


Fitowa rufaidan tayi daga kitchen din,itama gaya mata yayi
"To" tace kawai itama tayi gaba,ganin batayi magana kan nemanshin da tace tanayi ba saiya sanya kai yafice daga gidan,yayin da rufaidan tawuce dakinta tana waqar
"Ahayye sama ruwa qasa ruwa..." Tana wassafa tsiyar da zata tsula anjima.


*kuci gaba da haquri dai,duk sanda kukaji shuru ba shakka wani babban uzuri ne ya kawo tsaikon,sannu sannu bata hana zuwa,jigon ko manufar labarin dai daukar darasi da koyi da kyawawan halayen ciki*.....

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login