Showing 27001 words to 30000 words out of 32781 words
Chapter 10 - Hangen Dala
da zagin mmn ummi gamida lalubar number bbn amir,tana ganin gwara tatareshi da zancan tun kafin yazo a rigata lauya maganar.
A falonta ta cimmata tazauna tanata huci gamida maimaita kiran lambar bbn amir
"Wa kike kira?"mmn amir ta tambayeta sabida sanda tafito ta fuskanci itama rufaidan bbn amir din take kira
"Shi wanda ya daure mata gindin nake nema yakwana da sanin abinda yafaru" kai ta girgiza tana duban mmn ummi,batasan sai yaushe zata soma gane dukkan lamura ba,idan rufaida farin shiga wadda batasan ciwon zamantakewar aure da ciwon jibril din gaba daya da qimarsa ba ita ta aikata,ita mmn ummi da yake uban yaranta kuma wadda tadan dauki wasu shekaru cikin mu'amalar aure,tasan ciwonsa yaci ace tayi?
"Yanzu abinda zaki aikata din kina ganin kinyi dai dai kenan?" Dubanta tayi cikin jin haushi tace
"Kamar ya?"
"Yanzu kinwa uban yaranki adalci kenan?,ya fita neman abinda zaici gaba da tufa miki asiri keda yaranki,amma ki rasa dame zaki saka masa saida kiransa ki daga masa hankali?,ke kina kira ita tana kira?"
"Auto,me kike nufi?,na qyaleta kenan tatakamu tabarmu da yunwa taci karenta babu babbaka?"
"Idan tabarku da yunwa baki da hannun da zaki sarrafa abinda zakici koda dai dai cikinkine?,ki jirayi dawowarsa idan yaso kya kai masa qorafin?"
"Au....to ko bakinku daya?" Da mamaki take duban mmn ummin harta gane hakan saman fuskarta,duk da tadanji nauyin abinda tafada din saboda ita kanta tasan ba hakan bane,amma da yake idanunta a rufe suke saita dora
"Idan ba haka bane toki qyaleni,don wallahi saina gaya masa yasan sa saninsa,ai dama duk qanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa,niba irinki bace dazan zauna inaji ina gani a cuceni na qyale,duk wanda ya cuceni saina qwaci haqqina koda tsiya koda tsiya tsiya ne ehe,tunda ya jajibo wata toya shirya tarbar duk wani qalubale"
"Allah ya bada sa'a" mmn amir din tafada tana miqewa tabar mata dakin.
Kitchen din takoma sharp sharp tayi jallop din taliya da tattasan leda,da yake gwanar girkice tayi dadi qwarai kuwa,ta diba tazubawa usman da ahmad tawuce da saura daki,donko gyaran dataso yiwa kitchen dinma saita fasa,hakaza tsakar gidan,takoma daki abinta ta sakaya qofarta.
Dai dai sanda kowacce cikinsu ta taqarqare tana zabga mishi kira,sam bai sani ba,wayar tana a silent kuma cikin aljihunsa yana fama da custumers,sai daya sallamesu sannan yasamu waje yazauna yaga kiran,hankalinsa yatashi ganin kira wajen sha biyar na rufaida da mmn ummin,saiya rasa ma wazai soma kira,hankalinsa ya tashi yana fatab Allah yasa ba wani mummunan abu bane yasamu iyalin nashi.
Yana cikin wannan taraddadin kiran rufaida yakuma shigowa,babu jinkiri yadaga
"Lafiya meya faru?" Shine abinda yasoma fada
"Mmn ummi tayi kiranka ne?"
"Me yafaru?,naga miscal dinta"
"Yauwa,kome zata gaya maka karka yarda da zancanta,idan kadawo gida zakaji komai" shuru yayi yana nazari,tunaninsa nason hasaso masa abinda ke faruwa,jin yayi shuru ya tabbatar mata bata fada masa komai ba,saboda haka cikin jin dadi tace
"Saika dawo,i lov you" ta katse wayar takoma ta kwanta abinta saman gado tana juyi hadi daci gaba da charting dinta.
Jin maganar da rufaidab ta fada yasashi jan mugun tsaki,ya gama hasashen komai,haushi yacikashi,wanne irin kira ne wannan haka na rashin tunani?,yana shirin maida wayar kiran mmn ummin yashigo itama,saiyaqi dagawa yamaida wayar yaci gaba da sabgoginsa,amma sai hankalinsa yagaza kwanciya,ya fiddo wayar yanemi mmn amir
"Lafiya lau,ba wani abu daya faru,kowa lafiyarsa qalau" tace dashi sanda ya tambayeta,don tunda taga kiran tasan bai rasa nasaba da daya daga cikinsu ta sameshi,jin amsarta ya kwantar masa da hankali,saiya sauke ajiyar zuciya yayu hamdala kana yace saiya dawo sukayi sallama,ta aje wayar tana lulawa cikin duniyar tunani da mamaki,daga bisani ta ture duk wasu guntattakin tunani taci gaba da lamuranta.
Hakanan taci gaba da kwanciyarta saman gadonta,batako motsa ba ballantana tafito,don ta riga data saba ko a gidan idan tahau online tasoma charting bata tashi saita kai intaha,kota cikinta batayi bare sauran lamura,tana baiwa wayarta da charting muhimmanci matuqa,koda qannenta suja dameta da hayaniya idan tana charting din takan iya makesu,shi yasa ba kasafai suke zama kusa da ita ba idan suka ganta ta sanya waya a gaba.
Har sha biyu da rabi na rana bata gyara dakinta ba bare gidan bare ayi batun girki,saida kamfanin wayar da take amfani dashi suka tura mata saqon data dinta yaqare sannan ta haqura tasauka,data duba balance dinta kuma na waya taga bazai isa ya siya mata data ba,anan taci karo da lambar wayar mardiyya(wadda suka hadu gidan lallen biki sukayi musayar number),rabonta da ita tun ranar dinner din mardiyyan dataje mata,sukaci dariyarsu ita da qawayen mardiyya na matar shamsudden din angon mardiyyan,kan taqi zuwa dinner din,suna ganin kawai tsorata tayi,tasan ba zata iya hada kanta da mardiyyan ba.
Yankewa tayi kafin tatashi bari takirata taji yaya ake ciki,don ita gata tana nan tana nata yaqin dasu mmn ummin,kuma tanajin a jikinta akwai nasara cikin abinda tasoma din,ba zata dauki wata wahala ko wani tsari ba,dole yadda takejin tafisu karatu,takuma fisu matsayi a gun miji to a harkar gidan ma tafita daban.
Bugu hudu ta mardiyyan ta daga wayar,cikin farinciki da walwala takama sunan rufaidan.
"Amarya,amarya" mardiyya ke fada cikin fara'a,dariya itama rufaidan tayi
"Amare dai,ya kike qawa,ya gida ya al'amura" cikin walwala tace
"Komai normal,al'amura suna tafiya yadda ya kamata,kefa?"
"To alhmdlhi" ta bata amsa a taqaice,duk da har yau ita abun bai mata ba,bata samu yadda take hasashe tasamu ba,kota samu sama da hakan ba.
Gyara zamanta mardiyya tayi sosai tana cewa
"Ai qawata duk matar da bata auri mai mace ba bata bata cika mace ba,ai ki shiga kawai inda za'a dinga takara,a goga dake kisam cewa eh yes kema macace kin isa,ke kinga yadda abubuwa ke tafiya kuwa?,fiye da yadda nake xato da tsammani?" Ta fada muryarta na cike da farinciki da kuma zumudi,gyara xama rufaida tayi cike dason jin lbarin
"Allah qawata?"
"Wallahi kuwa,ashe dai hasahenmu qawata haka yake,uwayen gidan nan idan banda gidadanci basu aje komai ba,sai uban haihuwa da tara yara,matar nan ban sake raina ajawalinta ba saida nashigo,kinsan wata biyu tabani?"
"Ke don Allah?" Rufaida ta fada cikin sigar tambaya da kuma mamaki,
"Wallahi nake gaya miki,tunda nazo gidan nan take bauta har nayi wata guda,bana komai kuma miji na wajena,yana hannuna sai yadda nayi dashi,ke ko bita kanshi ko kulashi ma bata fiya yi ba,kullum tana can tana dubgar aikin gida dana yaranta,idan zai kwana biyu bai leqa su ba bazata koda kira wayarshi ba bare ta nemeshi,idan yafito ma iyaka gaisuwa,ko zaman hira na minti goma batayi dashi,ni kuwa hakan yayimin na kame abuna tsaf,kullum muna qule a daka muna diban soyayya madararta" ta qarasa fada tana qyalqyalcewa da dariya,tayata rufaida tayi,tanajin lallai ashe ita tayi sake da yawa
"Waikinsan wani abu kuwa?"rufaida tasake fada
"Matar nan kamar babu zuciyar kishi a jikinta,kinga yadda take nan nan dani,saboda tasan saita hanyata zata samu fadar wajenshi,bari kiji wani rashin zuciya,randa nacika wata daya da sati biyu saura sati biyu ta amshi miji ko?" Kao rufaida ta gyada cikin zaquwa kamar mardiyya na kallonta
"Kawai shashashar saita tsiri tafiya garinsu,yanxu haka tana can,har kwanakinta sun shigo bata dawo ba,kota gajima tatafine gaba daya oho" ta sake sakin dariya,abun yaburge rufaida sosai,saita gyara zama itama ta bata nata labarin
"Tabdi,wallahi ki zage damtse,yaci ace matsayinki yafi haka,ki bude wuta kawai qawata" daga nan ta qara dora rufaida kan wasu shawarwarin irin nasu sannan sukayi sallama.
Aje wayar tayi tahau nazari,lallai saita sake bude wuta fiye da wadda tabude a baya,amma bari zata sake bude duk wani shafi nata,da wannan tunanin tasauko daga gadonta tasoma gyaran dakin tana duba agogo dake nuna mata qarfe daya harda rabi na rana.
_ina miqa fatan alkhairu a gareku,da kuma shuru da kukaji na tsahon wani lokaci,Allah ya zame mana jagora a duk lamuranmu amin_👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA*👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
Haske Writers asso 💡
*BABI NA SHA BIYU*
*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*
*ALKAWARIN ALLAH*
*DAURIN BOYE*
*KUNDIN KADDARATA*
*MUTUNCIN MACE*
*DANGANTAKAR ZUCI*
_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_
Sai data kammala gyaran dakin nata sannan tafito tsakar gidan,batako damu da yanayin data samu tsakar gidan ba na rashin shara ba,saima harara data gallawa tsakar gidanbda qofofin dakinsu mmn amir taja tsaki,cikin quna quni tace
"Lallaima,rainin wayi,sunafa nufin girkina ne,nizan gwaggwafe nayi musu shara,toko tsakar gidan tsohona baxan iya tuna lokaci na qarshe dana share musu shi ba,idan sunaso suga gidansu dakyau saidai momiyo ko hasana su share(qannenta kenan)" daga haka tayi gaba tahau sabgarta.
Sanda almajirinsu yazo tabashi yamata cefane,taja kayan miyan ta aje takoma daki abinta,tana lissafi gami da tunanin me zata dafa da daddare,wanda bazata kunyata ba,sannan bazai wahal da ita ba,don itadin bawai ta wani iya kalolin girki bane ba.
Bata sake fitowa ba saida ana gab da sallar la'asar,tazo taja kayan miyan tahau gyarawa,aka kai mata markade tadora shinkafa da miya,wanda bata kammala ta ba sai da aka kira sallar magariba,akayi sallahr aka gama sannan tasamu gamawa,ta samu fulasai tazuba nata dana bbn amir,sauran tabarshi cikin tukunya,ba tare data yiwa kowa magana kan ta kammala ba ko suxo su diba,tashige wanka abinta,tana jin uwar gajiyar datayi saboda girkin,ko a gida idan ka ganta a kitchen tota baci,ko mamarta ta matsa mata saita shiga,ko babu kowa a gidan sai ita kuma an tafi anbar girkin.
Ranar Allah bai kawo dawowar bbn amir dawuri ba,sunyi baqi a kasuwa sun dan tsaidashi,hakan yasa harta kammala shirinta bai shigo ba,cikin wata doguwar riga streetgown wadda taba daga cikin qananun kayan data dinga siya tana adanawa saboda irin wannan ranar,riga ce mai hannun vest,wadda talafe tafidda duk wani tudu da kwari na jiki ta,hakanan daga bayan rigar an tsagata tun daga wajen agara har zuwa ramin gwiwarta ta baya,ta gyara kanta tafeshe jikinta da turaruka,sannan tadawo falonta tazauna tana kunna tv,cikin sa'a tashar tauraruwa sun saka waqa,saita qure sauti abinta,wanda yakarade gidan,takoma takwanta saman doguwar kujera tajawo wayarta tahau chartinga tana jin gajiyar aikin datake gani tayi yana ratsa qasusuwanta.
A qagauce take duba duka hirarrrakin da akayi bata nan,haushi tadinga ji,saboda ada tana daya daga cikin wadanda akeji dasu cikin duka grps din da take ciki,saboda yadda take particpating,amma sai gashi yanzu tana neman komawa kurar baya,sai ayita hira bata kusa sabida aikin gidan ko wani sanga ta babbn amir,haka tadinga jan tsaki tana maida amsa daya bayan daya tana wucewa,ba tare data lura da macene konamiji ne yayi magana ba,don duka grps dinta babu wanda tafita a ciki koda kuwa akwai maza,bare tayi tunanin sauya layin waya,sabgarta taci gaba dayi kamar yadda takeyi a baya sanda bata da igiyar kowa a kanta.
Kasancewar unguwarsu irin anguwannin da basa rabo da wutar nepa ne,koda sun dauke mintina qalilan suke dawowa da ita,hakan yasanya mmn amir ke matuqar cinikin lemo da ruwa,banda yanzu data sanya qalula saboda yanayin ciki.
Yana sanya qafarsa a tsakar gidan yagashi wani iri ba yadda yasaba ganinsa ba,babu kintsi babu shara,mamaki ya kamashi,saboda abune mai wahala yadawo gidan yasameshi haka idan ba wani taro ko sha'ani akayi ba,duka daga mmn ummi har mmn amir suna da tsafta,kada ma mmn amir taji labari,donko ummi bata kama qafarta ba,don wani lokaci itake tashi ta gyare gidan har harabar,tasamu almajirai su gyareta tsaf idan iskancin mmn ummin yamotsa ta biyasu da kudi,batabi ta kanta ko kadan,to amma saiyau yaga sabanin hakan.
Dauke kanshi yayi daga wannan nazarin,sautuka biyu suka karade mishi kunne,na qarar kida dana kukan ummi,mamaki ya kamashi,don bazai iya tuna yaushe aka kunna kida kamar haka na qarshe ba cikin gidan,saidai duk da haka kukan yarinyar yafi jan hankalinsa,saboda haka yanufi dakin mmn ummi kai tsaye.
Goye yasameta da ummi tana fama jijjigata,gefe daya ga usman da mubarak saman kujera xaune a takure,fuskar mmn ummin kadai xaka kalla kasan cike take fal da bacin rai,yayin da yaran suma kana iya karantar akwai abinda ke damunsu.
Bata amsa sallamarshi ba,saiya jeho mata tambaya yana nufarta da zummar amsar yarinyar yana cewa
"Meya sameta haka taketa tsala kuka da daren nan?" Tofa,dama mai kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,kamar dama jira take,kasancewarta mace wadda bata iya shanye ko danne bacin ranta ba,hakanan bata iya nuna abu na kara ko alkunya ba,idan batason abu ko bai mata ba kai tsaye take fadi kota nuna gaba gadi
"Eh,ai dole kasameta tana tsala kuka,tunda an hanata abincin gidan ubanta kuma wuni guda sur me yayi saura?,ai kawai abinda yarage kuma inaga shine rufaida tace mu tattara kayanmu mubar gidan shine inaga abu nagaba" ta fada cikin fada,hasala da haqiqancewa,kai kace shiyacewa rufaidan ta aikata,ko kuma yana da masaniya kan abinda ta aikata din.
Dubanta yake cikin mamakin abinda yafaru,dakuma mamakinta ita kanta,kamar tana magana da usman ummi ko mubarak,duk da kusan idan dasabo yariga yasaba,sam mmn ummi bata iya furta lafuzza mai taushi ba,sai lokaci lokaci idan taso hakan,ko kuma tana da wata buqata daga gareshi,bata iya controlling fushinta ko bacin ranta,duk sanda yazo mata saita amayar,har takan manta a gaban waye ma take wasu lokuttan sai bayan ta gama
"Abinci kuma?,wuni guda garin yaya?"
"Shina kiraka na gaya maka dazu,amma dayake nidin bani da muhimmanci,muma baka daukeni a bakin komai ba baka daga wayar tawa ba,kuma nasan billahillazi daga dazun zuwa yanzu dawowarka ko kaffara bazanyi ba kaga kirana,amma ka gaza biyoni saboda bani da muhimmanci,na rantse da girman Allah da halima ce ko rufaida saika bi kiransu,ba zaka iya shanyewa ba" ta qarasa fada kuka yana qwace mata,ranta na mata suya,kishi sosai yake cinta ga baqincikin abinda rufaidan tayi musu wunin yau din,tana tuna yadda ya tilastatata sai data amshi girki a sanda take cewa ba zata karba din ba,gani take kawai cikin duka matansa itace koma baya,hakanan yafi tsanarta fiye da kowa.
Shuru yayi ransa na masa suya shima,sai a sannan yadubi su mubarak da sukayi tsuru tsuru suna rarraba idanu a tsakaninsu
"Kuje dakin ummanku,daga nan kuce mata tazo yanzu ina kiranta" duka suka amsa dato suka sauka suka fice.
Yana jinta tanaci gaba da kukanta da qananun mitoci,saiya ciro wayarsa yakira rufaida
"Honeyy,baka shigo bane har yanzu?"
"Nashigo ina dakin mmn ummi"sosai ta bata rau,ta qanqance idanu kamar yana gabanta
"dakin mmn ummi kuma?"
"Eh,kizo yanzu inason magana dake" daga haka bai jira jin me zatace ba ya katse wayar.
Jin yakira rufaidan zuwa dakinta yasanya ta hanzarin goge fuskarta,kana tahau kalle kallen meye ba dai dai ba cikin dakin,saboda wunin yau sau daya tak tayi shara tun safe,bacin rai ya hanata,haka take,aduk sanda ranta ke a bace,haka yake mata tasiri ya hanata aiwatar da duk wani abun kirki,hakanan sai taji bacin rai yashafi kowa da kowama har yaranta,haka take fama dashi har zuwa sanda zai dusashe da kansa.
Balaifi dakin,saidai duk da haka ba neat yake sosai ba,lokaci yaqure ba abinda zata iya gyarawa,saboda haka tazauna tana ci gaba da kumbura,yayin dashi kuma yayi shuru saboda nazari daya fada,idanunsa sun dan sauya launi saboda bacin rai,ko almajirinsa baya yarda matan gidan su bari da yunwa,bare ace yau cikin gidansa aka wuni da yunwa?,harda yaran cikinsa?.
Mmn amir ce tasoma shigowa,tasamu waje tazauna bayan tayi masa sannu da zuwq,duba daya tayi masa tasan ranshi a bace yake,tasan dama hakan zai iya biyo naya,saitaja bakinta tayi shuru,idanunta kan tvn dake aiki volume can qasa,duk da itama rabin hankalinta yatafi ga tunani.
Tsayin mintina kafin rufaida tashigo dakin,hakanan tafito sanye da rigar,ba tare data nemi dan kwali mayafi ko hijab ta saya jikinta ba.
Tana shigowa mmn amir tadauke kai,ta sake maidawa ga tv kamarma bataga shigowarta ba,yayin da mmn ummi tazuba mata ido tacika tayi fam,ta dinga jifanta da harara,ji take kamar ta tashi ta rufeta da duka ko zataji sassauci cikin zuciyarta.
Kai tsaye ta isa inda bbn amir yake,niyyarta tayi hugging nashi duk da ummi dake hannunsa,amma kallo daya tayiwa idanunsa da fuskarsa ta fahimci cikin bacin rai yake,saboda haka ta gimtse,ta isa daura dashi sosao tazauna tana cewa
"Sannu da dawowa sweethert"
"Yauwa" ya amsa a gintse.
Sai daya tabbatar da kowa ya natsu sannan cikin dakakkiyar murya yajehowa rufaida tambaya
"Meya hana ayi girki yau duka a gidan nan?"duk da tasan wannan tambayar dama na iya biyo baya amma ba haka taso ba,taso ace yayi yadda tace ne ba tare daya titsiyeta a gabansu ba.
Ido ta zaro tana dubanshi
"waya gaya maka haka?,to nikam nayi girki don yanzu haka ma nasu yana kitchen,saidai idan basuje sun dauka ba kawai".
Wani abu ya tsayawa mmn ummi iya wuya,harta kasa magana,tazubawa rufaidab idanu tanajin kamar tatashi tayita jibgarta.
Waiwayawa yayi yadubi mmn amir
"Anyi girki yau a gidan nan?"kai ta kada sannan tace
" gaskiya yau gaba day....."bata qarasa ba rufaida ta tari numfashinta
"Banyi ba?,au hade kai xakuyi kuyimin sharri?,to aje a duba kitchen din agani idan banyi ba".
" ya isa"bbn amir ya dakatar da ita,sannan yacewa mmn amir taci gaba,sai data aje numfashi cikin nutsuwa sannan tace
"Daga safe zuwa rana dai babu abinda aka dafa,saidai ban sani ba koda daren nan".
Sake waiwayawa yayi ga rufaida ya kafeta da ido cikin bacin rai
"Kikace kuma kinyi girki" ciki ciki kamar mai guna guni tace
"Girkin dare ba,ai nayi"
"Meya hana ayi na safe da rana"
"Banajin dadine tunda kafita,hasalima ina kwance tunda kafita"
"Qarya take wallahi....dakaina nashiga namata magana ta gaggayamin magana yadda ranta yaso,shine dalilin daya tunzarani nakiraka kai kuma baka daga ba"
"Ha'an....ina ruwankine?,dake nake maganata?,ki bari a kasa dake saiki dauka ko?" Hayaniyace taso barkewa tsakaninsu ya tsawatar musu kafin kowa yakoma taitayinsa.
Fada sosai yarufe ido yayi musi gaba daya saboda barin yaran da yunwa,duk da mmn ummin ta gaya masa mmn amir tadafa musu wani abu,amma saiya hada duka,saboda dagashi har ita sunsan dasu su biyun yake,sai daya gama mai isarsa sannan yace yana duban rufaida
"Allaha yarufamin asiri saboda haka ban lamunci zama da yunwa ba a gidana,koda almajirin gidan nan banyarda a barsu da yunwa ba bare ku iyalina,qa'idane kowaccw mace ta gama abinci akan kari,daga na safe na rana zuwa na dare,idanma kinyi kan rashin sani to daga yau ki gyara kar in sake jin irin hakan takuma faruwa,koda baki da lafiya ki sanar musu,koki nemi daya daga cikinsu ta amsar miki girkin,kina jina ko?".
Tabdijan danqari kan uba?,yau ita jibril yarufe ido yake mata masifa sabida shirgin yaransa da kucakan matansa?,da idanu take kallon mmn amir zuwa mmn ummi,baqinciki fal yacika zuciyarta,matan da take ganin basu kaita komai da komai ba,amma yau yazaunar da ita yana neman daidaita matsayinta da nasu,har yana mata fada a gabansu?.
Sai kawai tamiqe tana cewa
"Naji" sannan tawucw tafice fuu,mazaunanta na juyawa cikin matsatstun kayan