Showing 15001 words to 18000 words out of 32781 words

sannan yace
"Halima.....don Allah ki kwanta kiyi baccinki sosai kodon abinda yake jikinki,karki sakawa ranki damuwa don Allah"kai ta jinjina tana qoqarin hadiye abinda ke taso mata sannan ta sanya kai cikin dakin.


Kusan sakan goma sannan ya taka ya juya yafice yana jin tausayinta sosai cikin ranshi,ta nuna dukkan wata jarumta da haquri,ba shakka haliman baiwa ce da Allah yayi masa na macen da ba kasafai ake samun irinsu ba,maryam kawai ta zame masa ishara.


Daga nan dakin mmn ummin yashiga,itama da sallamar yashiga,tana tsakar falon tana kai kawo goye da ummi a bayanta wanda ta jima dayin bacci,fuskarta kawai zaka kalla kasan bala'i da tashin hankalin da take ciki.


Dauke kanta tayi sanda taga shigowarsa,qirjinta yaci gaba da zafi,ko sallamar ma bata da lokacin amsa mishi
"an yini lpy" ya fada itama yana zama hannun kujera,banza tayi dashi,saima tasoma tattare kayan dake zaune d'ai d'ai tsakar falon kamar batasan Allah yayi ruwanshi ba,qoqarin danne bakinta take ta hana kanta ruga masa ashariyar daketa yawo saman harshenta,data gama saita wuce dakinta tarufe qofar tabarshi nan zaune.


Yasan cewa lallai anzo gabar da duk dauriyarki dole gazawarki ta bayyana,saboda haka baiyi qasa a gwiwa ba yanufi qofar dakin yasoma qwanqwasa mata
"Bude mana maryam"
"In bude inyi uwar meye?,jibril kafice min daga daki wallahil azim idan nafito ba zamu kwasheta da dadi ba,maciyin amana kawai,Allah dai yayimin sakayya" saita rushe da kuka sosai mai fidda sauti,kanshi kawai ya girgixa saiya koma da baya ya aje mata ledar ya juya yafice zuwa sashen rufaida.


Cikin so da qauna ta taryeshi,cike da nuna wayewa da sanin me rayuwa take ciki,hakanan ya biye mata,saidai can qasan ranshi yana mamaki kadan kadan idan tayi wani abun,sabida ko maryam daren farkonsu batayi ba bare halima,daga bisani saiya share shima,komai ya kauce daga ranshi ganin cewa ba wani abu daya tadda tattare da ita wanda ba dai dai ba ko zai saka zuciya ko rai cikin zargi.


Wanka mmn amir tasamu tayi cikin bandakinta sannan tasauya kaya,ganin idanunta yasoye,tunani yana neman hanata bacci,saita dauko qur'aninta da dama kullum bai rabo da gefan gadonta,ta bude wasu shafuka tasoma karantawa,babu jimawa taji bacci yazo mata,idanunta har rurrufewa suke,tasamu ta maida qur'anin batayi wata wata ba taja filo ta kwanta.



Mmn ummi kuwa a iya cewa kwanan zaune tayi,sai zirga zirgan shiga bandaki data sameta saboda tashin hankali,tayi kuka har batasan iyaka ba,haka tazauna tasaka agogo a gaba tana kallo,duk daqiqa daya da zata wuce tana lissafawa gamida qissima yanzu abu kaza baban amir din yake,yanzu yaci ace yayiwa rufaidan abu kaza,saita sake rushewa da kuka,haka takusan kwana,kafin wani lokaci kuwa kanta yadinga ciwo,da qyar gefin asuba tasamu bacci yayi awon gaba da ita cike da tarin baqinciki da quncin zuciya.


Qarfe biyar da rabi yashigo dakin,a lokacin tana zaune saman abun sallarta tana jan carbi,duka yaran sun gama sallarsu sun koma baccin,itama jira take ta gama addu'o'inta takoma ta kwanta din kafin gari ya qarasa wayewa,saboda tasan gidan a kacame yake sosai,gashi yaudin tanason zuwa awo ranar da zata likita ne.


Kallo daya tayi masa ta dauke kai,saidai abun ya bata mamaki,batama tsammaci shigowarsa ba adai dai wannan lokacin,don kuwa zamanin maryam bataga idanunshi ba sai goma na safe.


Shi yasoma gaidata har taji abunma bambarakwai,saita amsa kawai,ya tambayi yaran tace sunyi sallah sun koma
"Sannu da qoqari,Allah yayi albarka"
"Amin" ta amsa tana ci gaba da jan carbinta ba tare data sake tanka masa komai ba,tana kallonshi ya gama kame kamensa sannan ya juya zai fita
"Idan gari ya gama wayewa zanje naga likita" waiwayowa yayi cikin kulawa
"Au...lafiya dai ko?"
"Qalau,lokacin komawa awona ne yayi tun wancan satin ban samu zuwa ba saboda hidima"
"Me yasa zaki fashin zuwa ganin likita?,wannan ai sakaci da lafiya ne,ki shirya da wuri ki barma mmn ummi sauran ayyukan,idan kin gama saiki sanarmin" zataso ya sallameta ne kawai a lokacin basai ta tsaya wani binbinin nemanshi ba,amma batason doguwar magana a yanayin da take ciki,saboda haka tace masa to kawai


Qarfe bakwai ta tashi salima suka shiga gyaran gidan,ita kuma tashiga kitchen tadora abin karin safe,don tasan idan tabiye ta mmn ummi bataqi ranar gidan yakuma yini a haka ba,hakanan uban kowama cikin gidan yawuni da yunwa ba damuwarta bane.


Duk zirga zirgar mmn amir din kan idanun mmn ummi,don tunda tafarka qarfe shida tayi salla bata koma ba,saita koma saman kujerarta dake bakin qofar dakin tazauna ta yaye labulen tana ganin duk wani abu da zai gitta ta tsakar gidan,tunanin abinda zata qirqira kawai take wanda zai fiddo bban amir daga dakin rufaidan da farar safiya,yadda zata cusa mata haushi da takaici.


Ranta a bace takebin mmn amir dake kai kawo tsakar gidan tana hidimominta,ji take kamar ma farinciki mmn amir din keyi da wannan lamarin,qwafa taja haushinta na sake cikata,ita ko wani dan bacin rai bata karanta saman fuskarta ba,kamar ma ba matarshi ba,shine zata wani tashi da sassafe tahau aiki,itakam baiwar Allahn batasan ma tanayi ba,don abinda ta iyakancewa ranta zatayi komaine don saboda yaran da kuma karan kanta.


Sai data gama abun karin yaran sukayi wanka gaba dayansu suka karya,tabar saura a kitchen saboda sauran mutanen gidan,ta kintsa tsaf,tana daga zaune tana karyawa don karta zalunci abinda ke cikin nata,saboda jiya batasamu damar sanya komai a bakinta ba,tunanin yadda zata aika yaran kiran abban nasu take,batason shigarsu dakin
"Amir miqomin wayata" ta fada tana kai kofin tea bakinta,dakinta yashiga yafito mata da wayar ya miqa mata,tasa hannu ta amsa sannan tafara laluben number abban amir din,sau biyu tana kira bata shiga,saita aje wayar taci gaba da karyawarta.


Bayan ta gama ta duba jakarta,taga akwai sauran kudade,saboda haka ta zura hijabinta ta miqe tana duban salima
"Zanje,don Allah ki kula dasu,karki barsu suje ko ina,tunda akwai wuta ga cartoons can dana ware musu wadanda duke kalla ki saka musu,kiyi zamanku a daki,tunda mmn ummi nanan zata kula da sauran komai"
"To saikin dawo" daga haka tamusu sallama tafice ba tare data tsaya neman bbn amir din ba.


Qarfe sha daya nasafe tashiga bandakin dake falonta ta silla wanka,sannan taxauna gaban mudubi ta tsara kwalliya tagani ta fada,ta zabi riga da skert da suka kaamaata cikin kayanta tasanya,ta tura daurin dankwalinta gaba goshi sannan ta dawo falo inda tabar bbn amir zaune yana kallo.


Wani fari ta sakar masa gamida sauya takun tafiyarta,ya buda mata hannayensa yana sakar mata murmushi gamida fasa mata kai kan yadda tayi kyau,ta narke ajikinsa sosai tana zuba mishi shagwaba shi kuma yana tambayarta daren jiya
"Yunwa mafa nakeji dear,su mutanen gidan nan basu iya adana baqonsu ba?"
"A'ah na tabbata akwai abinci a kitchen,may be basason matsa mana shi yasa ba wanda suka aiko,bari naje na duba miki sweet,amma ya kamata ki fita ki gaisa da mutanen gidan"fuska ta yatsine tana jin abun wani banbarakwai,don bata tsammaci zaice haka ba
"amma ai nice baquwa,niya cancanci a gaisar" kai ya kada
"Eh,amma idan kika duba ai kece qarama ko?,keya kamata ki dinga zuwa gaidasu" kan ubancan,yo koshi ita yau bata gaisar ba ballantana wasu gajarabul din matanshi,batason bata plan dinta saboda haka tace mishi
"Ba damuwa,amma yunwa nakeji,bari na qoshi tukunna"
"Karki damu,bari na duba gidan"murmushi ta sakar masa
"kayi sauri kadawo,akwai wani daddadan labari dana tanada maka"
"An gama gimbiya" daga haka ya juya yafice,wani wawan tsaki taja tana yatsuna fuska,gaida matanshi kamar wani a qauye?,koko zamansu take?,itakam ba zata juri wannan iskantar ba wlh,duk wadda ta matsu da ita tashigo ta gaidata.


Dakin mmn ummi yanufa yana don yasan aikin gidan kamata yayi ace yana hannunta,tana zaune tun safe yadda tatashi da kayan jikinta,ita daya cikin dakin daga ita sai ummi itama data gaji da zaman ita daya,tana ta 'yan qananun rigingimu tana neman wanda zai dauketa ya fita da ita.


Aiko yana shigowa tagudu daga wajen uwar tayo wajen,ya dauketa yana cillata sama yana mata wasa,ko ummin ba'a yiwa wanka ba bare uwarta tasamu yi tana zaune tana dacin rai,sosai ta qureshi da idanu kamar zata gani sauyawar wani abu daga jikinsa,sai kuwa taga kamar walwalarsa ta dadu,fuskarsa ta qara kyau,wani abu ya tokare mata wuya,tsantsar tsanarshi da haushinsa kamar tatashi ta rufeshi da duka haka takeji
"An gama abincin kari ne?" Wata uwar harara ta watsa masa,ta masa kallon sama da qasa
"Na maka kama da wadda zata zauna tana muku girki kuna ci?,toni ba jaka bace nasan inda yakemin ciwo" daga haka tashige daki abinta,baiso kulata bare subar wani abun fadan,saboda haka yajuya yafice zuwa dakin mmn amir.


Suna zaune yaran a nutse duka suna kallo cikin tsafta,ya tambayesu ina mmrsu,usman ne ya amsa mishi data tafi asibiti,saiya juya yana neman qarin bayani wajen salima,ta gaya masa cewa takira wayarshine taqi shiga,shuru yayi kana yasoma qoqarin fito da wayarshi daga aljihu yasoma kiranta,saidai wayar taqi shiga,maidata aljihu yayi yana rayawa cikin ranshi,kishinne yamotsa itama shi yasa taketa shakulaton bangaro da shi,saidai koma meye baiga laifinta ba sam,tayi namijin qoqarin da sai an tara mata dari ba'a samu wadda zatayi abinda tayi ba
"Kuzo muje ku gaida antynku" bbn amir ya fada sanda salima ta gaya masa kayan abincin yana kitchen.


Kowa yasan yaro da zumudi dason amarya,sai suka miqe kuwa dukkansu suka bishi,sai salima kawai tarage,ya soma biyawa ta kitchen ya diba abincin ya baiwa amir yadauka suka nufi dakin rufaidan.


Tana zaune sosai tana shaqar iska dai dai,jiran dawowarshi kawai take tana tsara yadda yau zata haramta kowa ganinsa da kuma walwala cikin gidan,sai taji sallamar yara,ta daga kai da sauri tana dubansu,take duk wata fara'ar dake fuskarta ta bace bat
"Meye hakan?" Take tambayar kanta cikin zuciyarta,zuciyarta na wani iri zafi ganinshi tare da tarkacen yaranshi duka.đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


ÂŠī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA TAKWAS*





Amir ne ya qaraso ya dire tire din dake dauke da kayan abincin,ya duqa har qasa ya gaidata,ta bishi da wani kallo tana amsawa da qyar kamar wadda aka cusawa tsumma a baki,tana jin zuciyarta na mata daci,takaici ya cikata.


Duka yaran suka qaraso cikin falon suma,da daya da daya suka soma gaidata,daqyar take iya amsa gaisuwa daya tak,duka tana qare musu kallo a kaikaice,sai taga kowannensu yasamu waje ta zauna.


Dubanta ta maida kan bbn amir,tayi tsammanin zai musu magana su tafi,sai taga sabanin hakama shima wajen zama yake nema dauke da ummi a hannunshi,hakanan dukka hankalinsa yana kansu yana musu tambayoyi kan abinda ya faffaru jiya a gidan.


Dif tayi yana shaqar wani baqinciki da takaici,ummi tasoma daga mata hannu taba bangala mata dariya,amma saita dauke kai kamar bataga yarinyar ba,saida babanta ya kula ne yace
"Antynsu,so take ki dauketa fa,kinsan ummi dason yawo kuwa dason a dauketa" yaqi tayi tana qoqarin sakin fuskarta amma sam ta kasa,don bata saba da hakan ba tun asali,bata fiya iya biye abinda kecin zuciyarta ba
"Ki sauko muci abincin,usman ku matso maza aci abinci" ya fada yana saukowa qasan carfet gami da janyo farantin abincin gabanshi yasoma bubbudewa,amir ne kawai yace yaqoshi
"Abba suma bamu dade da gama karyawa ba,tun kafin umma tafita ma" ya fadi kasancewar dukka yafisu hankali da wayo
"Qyalesu suci,kasan hali ai ko sunci abinci idan sukaga zanci sai sunci ko abikaina?" Suka saka dariya duka harda yara matan.


Waiwayawa yayi da zummar sake cewa rufaida tasauko suci abincin sai yaga wayam ba ita a wajen,abinda bai sani ba tun sanda yasoma tattaro kansu suci abincin tamiqe tabar falon
"Ikon Allah,ina antyn taku?" Ya fada yana duba falon
"Tashiga daki abba" hanifa ta fada,saiya dire ummi yace yana zuwa.



Zaune ya sameta gefan gado qafarta daya kan daya tana cika tana batsewa,cikin kwantar dakai da kwantar da murya yace
"Haba amarya wadda bata laifi,ya zaki taso ga yaranki sun shigo gaidaki,ga kuma abinci can bakici ba?" Taso boye fushinta amma saita kasa,taga idan taboye abinda ke ranta kamar ta cuci kanta ne
"Ai gwara nabaku waje kuci sosai ko?" Dan jim yayi cikin mamakin me kalamanta ke nufi,bai gama wannan tunanin ba tadora
"Ta yaya ina amarya ranar farko a gidana zanci abinci da mijina kawai saikaje ka debomin tarkacen yara suxo su cikamin daki,fusabilillahi haka ake?,niwa nayiwa gaka duk cikinsu?" Mamaki sosai ya kamashi,don bai tsammaci jin wannan furucin daga bakinta,sakamakon a baya yadda take haba haba da yaran,har gidansu take sawa yaba kai mata su,sannan idan baizo dasubama zatasa yakira gida da wayarshi a bata yaran su gaisa,saisu kusa cinye masa kudin waya ma suna hira.


"Yanxu rufaida yaran nawa na cikina kika gayawa haka?,ko kunyar idanuna bakyaji?"dubanshi tayi,taga alamun maganar batayi masa dadi ba,amma sai ba zata iya bashi haquri ba,don a ganinta ita akaiwa laifi,maimakon haka ma saita soma qanqanun gunguni,ta maida kanta saman filo ta kwantar
"Nidai bawani mummunan abu nake nufi ba,saidai idan kaine ka fahimci haka".


Ganin da gaske ba zataci abincin ba yaga bai kamata tun ranar farko haka ta faru tsakaninsu ba,saboda haka ya juya ya fice daga dakin,ya debo mata abincin ya aje mata
"Gashinan saikici anan" miqewa caraf tayi daga kwanciyar ta kamo hannunshi,cikin narkewa kamar maishirin kuka tace
"Wato baka ma damu dani bako?,to wallahi ba inda zaka fita anan zaka zauna kaima muci tare" hakanan yazauna din kodon abinda yafaru daren jiya yana ganin dole ya haqura ya lallabata.


"Ya kamata kije ku gaisa da mmn ummi,mmn amir bata nan tafita asibiti,in yaso zuwa anjima saina ganku kuma gaba daya ko?" Kamar ya soka mata wuqa a qirji haka taji,wanne irin taje ta gaidata don tsabar son ya siya mata raini?,ina laifi ma ita ta leqo?,amma batason wani dogon jayayya muma da abinda zai bata mata amarcinta yadda ta tsarashi,sabida haka tana hadiye bacin ranta haka tamiqe ta isa gaban mudubi tana sake goga hoda,zaya fita tace ya tsayata su fita tare,yace ta taddashi a falo.


Sai data sake kwalliye fuskarta sannan ta feshe jikinta da turare,ta ciri chewing gum cikin wanda tazo gidan dashi ta jefa a bakinta ta turo daurinta gaba sosai sannan tafito.


Tsaki taja qasa qasa tanajin takaicin ganin har yanzu yaran suna nan,haka suka dunguma gaba daya suka fice.


Tana nata falon tana tsintsince kaya zata soma shara,ranta cike fal da qunci da daci,musamman lokacin data fuskanci yaran sun shiga dakin amarya ne,ta qudira a ranta yau saitayi musu dukan tsiya,ta kuma zauna ta karanta musu kada tasake ganinsu dakinta,idan maman amir tasake to ita tabbas ba zata sakeba bare ta rainata,idanma basuyi wasa ba ko dakin mmn amir din sunbar zuwa bare su shiga dakin wata amarya.


Shine a gaba dauke da ummi,sai rufaida a bayanshi da sauran yaran daga bayanta,tsayawa tayi da ninke zanin goyon ummi wanda ta kwantar da ita dashi dazu saman kujerar tana dubansu.


Rufaida ta hango daga bayanshi,tana qarewa mmn ummin kallo,wadda ke sanye da t.shirt nai kwala harda aljuhu a gaban rigar,a tsaye t.shirt din take babu shape da alamu ta maza ce,sai zanin atamfa sungul wanda daya daga cikin zunnuwan goyon ummi ne.


Murmushi rufaida ta saki tana danne dariyar dake cinta,wani raini na musamman game da mmn ummin ya taso mata,ba shakka dukkan yadda tayi hasashensu haka suke,ta bangaren mmn ummi kuwa kunya da takaici suka cikata,ko a mafarki bata taba tsammatar rufaidan xata shigo dakin nata ba,dako da wasa ba zata taba yarda tazauna ta ganta a haka ba,hannu tasa ta amshe ummin tana cika tana batsewa,yayin da rufaida tazauna hannun kujerar mmn ummin tana qarewa falon kallo,babu wata qazanta tattare dashi,saidai da alamu bata damu da gyaran dakinta da sassafe ba a matsayinta name yara
"Mun tashi lpy mmn ummi" rufaidan ta fada tana murmushi wanda ita kadai tasan manufarsa
"Lafiya"
"Ya kwanan yara kuma?" Takuma fada da wani salo na daban
"Qalau" ta amsa mata tana cirewa ummi wandonta daya jiqe da fitsari.


Bbn amir ne yajuya zai fita rufaidan ta miqe
"Tsayani mana dear,bacci fa nakeji" daga haka tabi bayanshi,wani abu yatsaya mmn ummi a ranta,tabusu da kallom harara da ashariya cikin zuciyarta,sai usman yamiqe yana cewa
"Abba tsayani zani" finciko usman din tayi da hannu daya,ya saki qara kuwa saboda yaji zafi sosai
"Dakin uwarka ne kona ubanka?" Ta fada tana zarewa yaron ido,yaji ihunsa hakan yasa yadawo,hannu yamiqa masa
"Taho" da hanzarinsa yatashi,hanifa matace zata koma,haka suka sake binsa su ukun.


Tana shirin miqewa kan kujerarta tana tsara tadda zasu wuni tare saigashi tare da yaran,qugu ta riqe kawai tana kallonsu,ranta yasoma suya,ya aje usman yana shigewa daki saita bishi.


Sanda ta isa taras dashi tayi yana kira a waya,don haka ta tsaya tana kallonshi har computer ta shaida masa is not reachable,yasauke wayar tana sakin tsaki
"Taqi shiga" ya qarashe maganar yana duban rufaidan
"Dear,gaskiya bacci nakeji,kuma yarsn nan kasan bazasu barni nayi ba,niban saba da bari bari ba,infact ma bacci ni nakeji,tunda farfajiyar gidan nada yalwa ai zata ishesu wasa ko?" Bai samu sararin bata amsa ba kira yashigo wayar tashi,saiyaga mmn amir ce,da hanzari ya daga har hakan yaja hankalin rufaida tasoma son sanin waye yakirashi haka har yake zumudin dagawa cikin kulawa.


"Test test ne yanzu likita yarubutamin,kuma kudin hannuna danazo dasu duka sun qare,idan ba damuwa ko zakamin transfer ta accnt dina saina tsallaka nan titin asibitin akwai atm na cire?" Ta fada bayan ta gaidashi,hakanan yaji duka babu dadi
"Ke zakije ma ki cire kudi da kanki?,wayace ki tafima baki gayamin ba bayan nace ki shaidamin idan kin gama shiryawa?,kuma inata kiran wayarki a kashe?"
"Babu network ne inda nake din,sai yanzu dana fito" dan shuru yayi shima sannan yace
"Jirani ina zuwa" daga haka ya sauke wayar,saiya dauki agogonsa daje gefan gado yasoma daurawa.


Tsuke fuska rufaidan tayi,donta fuskanci dawa yake wayar
"Ina kuma zakaje?"
"Zan duba mmn amir ne a asibiti,tana buqatar wasu kudi zan miqa mata" idanu ta qanqance ranta nasake baci
"Amma inaji tace ai kayi mata transfer taje tacire da kanta ko?" Tsaiwa yayi da daura agogon dayakeyi yayi yana dubanta,ya tsammaci zata qarfafashi ne akan yaje dinma
"Matata da tsohon ciki a jikinta nabarta taje layin atm cire kudi?,yau qarshen wata anyi salary,kuma kema kinsan yadda wajen yake cika da masu cirar albashi duk qarshen wata ko?"
"Nidai gaskiya dear ban yarda ba,wannan wanne irin abune,duka yadda naso zama dakai hakan yaqi samuwa haba" ta fada cikin fushi tana juya bayanta.


Murmushi yasaki yana mamakin kamar batasan yana da iyali ba,amma dayake ance amaryace bata laifi saiya rungumota ta baya yace
"Haba sarauniyar mata,yanxu zanje na dawofa,abani aron lokacin baxan jima ba,afwa zamu samu lokaci har saikin gaji,kwana shidane dake fa nan gaba?" Wannan maganar ta sakata tadan sassauto,amma duk da haka fuskarta a hade take,zafin kishi takeji sosai idan tatuna wajen wadda zaije,musamman ma dataga ya dauki muqullin mota,mai yiwuwa ma yasakota agaban motar kuma duka da sunan matarshi,haka tana gani ya debi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login