Showing 21001 words to 24000 words out of 30884 words

Chapter 8 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novel By Halima Abdullahi K Mashi

shi, wani ustaz haka ko? Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke ajiyar zuciya.7�5⃣Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta, dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi'a kuma ta zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado. Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail data gani, hawaye suka soma sharara akan kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi'a ta tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin dake gurin.
Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi mata, sai suce, "Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo asibiti ko sau daya bai leqo ba.
Canjin rayuwa


7�6⃣Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona
ma kanki asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun
farko da kk qi nuna masa so. Zainabu tace, to ni
bana sonshi, kuma bazan koma gidansa ba. Inna
tace, sai kiyi tayi. Ga faten doya nan da mai
wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace,
bana ci. Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi
da tuwon da wannan ta kusa damu din ta bani
ba. Zainabu ta zame ta kwanta, idanunta na qara
hasko mata Ismail dinta ke baiwa matarsa abinci
a baki. Ta tabbatar da irin son da Ismail yake yi
mata, da ace ita ce, qila ma sai ya tauna a
bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora
abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi
shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na
musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun
rasa mai kawo musu, sai dai maqotansu na
kwanciya su sam musu. Da wannan takaici
Zainabu tayi varci mai cike da mafarkan
masoyinta Ismail.
Mahmoud ya kalli rabi'a kinyi qoqari domin mara
lafiyar nan bata ci komai ba tunda tazo
asibitinnan sai yau da kika kawo mata. Azaton
Mahmud Ismail baijishi ba yanayin jinjina ne ga
masoyiyarsa. Sai kurum yaji Ismail ya cafe da
cewa, ni kaina na jinjina miki rabi'a domin a
tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai abinda
basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce, kuma
farfesunshi rabi'a tayo da alayyahu. Haka nan ta
dai yo ne don batasan me zata yi ta kawo ba.
Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana saida ma
masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam mata
zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a
daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai
data qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha
sannan tace zata kwanta.
7�7⃣Tun lokacin da likitan ya taimaka masa suka
shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai
dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da
buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya
barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada
masa cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan
ruwa, kuma sun saka mata pampers ita da wata
nurse. Harma mimin tace, su sake canza mata
rigarta. Yaji dadin sannan ya dawo da murna sun
samu admission islamic ya nema. Mahmud kuma
sai suka bashi English baiso ba amma hakanan
ya haqura.
Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka
fito, Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din
Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma
wadannan Nurses din na gefensu da zai wuce,
sai dayar take tambayarsa dazun wata 'yar
uwarka ta gane gurin ku ko? Ismail yace, da yau
she kenan? Tace dazun nan kuma nice nayi mata
kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru kodai rabi'a
ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina dinnan
ko? Nurse tace, a'a ita daya ce tace, tana nan
asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai.
Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace,
naga lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton
tana tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya
sake dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take
nema? Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira.
Yace to gsky bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu
dama munga har kwatancenka anyi mata tace
kaine.
Canjin rayuwa


7�8⃣Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi wata baquwa? Tace A'a sai dai ina neman wata alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta."ina saauraronki" yadan rusuna sbd Mimi bayayin magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu. Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd suna ne mai dadi da ma'ana. Allah yasa halayenki su rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta farko data soma kar6ar musulunci a tarihi. Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci. Sa'annan itace ta haifawa ma'aiki 'ya'ya guda shida. Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta. Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba musulmi ba yasan mai tsira da Aminci.
Canjin rayuwa


7�9⃣Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za'a yi hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane. Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce masa qala ba. Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi. Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba. Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa.
Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan ya nufi gadon mimi yayi mata addu'o'i ya shafa mata, sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado masa, to ko wacece? Ko kuma cikin 'yan uwanta ne? Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane. Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba.8�0⃣Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo, kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo. Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau. Mimi tace, yaya don Allah za'a iya yimin wanka? Yaya Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, "yaya ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami. Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta sunsuna. Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija, don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta. Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? "Don Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai domin wani ciwon zai shigar ki.
Canjin rayuwa


8�1⃣Ismail ya miqe "yaya ni dai bari in barki da 'yar rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi, zan koma gida da wuri. Ismail yace, zan dawo da wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi? Ta girgiza kai alamun a'a. Taci taci gaba da kukanta. Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta qara sautin kuka. "yaya malam ya saba da ganin kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a'a bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in akace maka kayi haquri, to kayishi. Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma baku da 'yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin damuwa. Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa son 'yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai kawaici ce. Soyayyar uwa da 'ya na daban ne kinji. Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki? Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi, amma ina da hujjoji masu yawa.
Canjin rayuwa
8�2⃣Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu, ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba, da ynxun kun gudu.
Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky. Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka kawo 'yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba, sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo. Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In kuma za'a basu ragowar maganinsu, dubu shida da dari uku da saba'in. Ismail ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro 'yan dubu dubu ya miqa musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa na bari anan? Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace, an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya mana ki amshi sauran magungunan da kuma takardar shedar biya. 8�3⃣Ismail ya amshi canjin sa, sannan ya kalli innar Zainabu, "Allah ya qara sauqi" bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama tasa baki, ko zasu yarda za'a kawo musu daga baya. Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta. Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude. Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace, "yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni. Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin borin kunya tace, "kina ta an cuce ki. Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara. Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka. Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin.
Canjin rayuwa


8�4⃣Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu, ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum ba'ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu tace, kin masa jaje kuwa? Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da dariya. "huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na musamman da yake hadawa a gurin masu saida turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don amsa kiran malam Aminu. Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara'ar da ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace, malam ko anyi maka baiko da rabi'atu ne? Mahmud yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata. Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. "Zomuje kaji daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir din.8�5⃣Cike da fara'a suka gaisa da malam yace, malam Ismail yaya mai jiki? Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga gareka. "malam ya fadada fara'arsa, sannan ya kalli Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido da kallonsa ga Ismail, "Scholarship dinku ya samu. Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi. Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a mafarki. Wai malam madina

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login