Showing 3001 words to 6000 words out of 30884 words
Chapter 2 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novel By Halima Abdullahi K Mashi
Kwanciya tayi akan cinyarsa, "baka wasa dani, amma yau zamu fara" ga mamakinta sai kawai taga ya hankadeta, ta fadi kan kafet. Ta dago rai 6ace, duk da aunties dinta suna fada mata cewa kar tayi zuciya da duk abinda zai fada mata, ta kalleshi, "A zato na masoyi ya dara maqiyi, menene laifi na don na soka? " Cikin daga murya yace "shine kuwa babban laifinki a guri na. Bana ra'ayinki, amma keda mahaifinki kun liqemin, sai da akayi wannan auren"
Ta soma kuka, ni fa taimako nayi sbd kar aji kunya, yace aikuwa zakiyi da kin sanin wannan taimakon. Inaso kisan wani abu, ni mutum ne wanda in naga abu inaso, to so ne na gske, kuma ba zanyi wasa da son ba. Haka nan kuma qi, don bana yin qi da wasa, mimi na gani nace inaso, tunda tace bata yi ai sai abarni inji da ciwon rashin ta, ba wai akwaso min ke ba, baqi qirin! Ni farar mace itace ra'ayina, kin gane?
Canjin rayuwa
1�2⃣Na'ima ta soma kuka wiwi, tana cewa, toni ynxun ka fatamin matsayi na, ya miqe tare da nufar dakin varcin sa. Gashi na fada miki kuwa, banda wannan matsayin wanne kk son ji? Don Allah tashi ki fita a daki na, Na'ima ta miqe jiki babu qwari, ta nufi dakinta cikin kunya da kuka, ta kira momy nafisa a waya, momy tace lfy da wannan daren? Na'ima cikin kuka tace "momy Abbas baya so na, ya fadamun " momy tace sakarya! Baki dai iya kissa ba kawai zaki ce. Har akawai namijin d zai raina mace? Bare ke da kyanki da komai, amma dai ki vari zamuyi magana dake zuwa da safe, na fada miki jikin dadynku ne ya motsa, gashi ma anyi masa waya mimi tayi hadari. Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci, bayan likita ya gama dubashi. Na'ima cikin sauri tace "sis mimi din ce tayi hadari momy? " tace eh itace, sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu. Na'ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji'un! To ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace, dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin jiki. Na'ima tace Allah sarki sis mimi! To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra'ayin mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu, Na'ima tace a'a momy kar ta mutu, tunda dai mun samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min ba, tace shikenan zanzo da safe. Na'ima tace Yauwa gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai nazo din, sukayi saida safe.
Canjin rayuwa
1�3⃣Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi, cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki? Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman, da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari. Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci, sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta, sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani 'yan kudina. Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane farin ciki nake samu gurin 'yarta da har zan dinga bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa uwata.
[8/17, 11:04 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�4⃣Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba'ayi ba, tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji, sauri nake zan fita.
Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al'amuransa bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka. Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya, shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa, amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta. Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da qyar ma tadan kur6i ruwan kunu. Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba. Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe rabonki da al'ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai.
Canjin rayuwa
[8/17, 11:10 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�5⃣Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki cewa kina da ciki ne? Kice masa a'a shawara ke damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani, kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata. Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko, ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho' to kina shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani kamar wani dodo?
[8/17, 11:10 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�6⃣Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga kai, alamun eh. Cikin yace to shikenan vari inzo in nemo miki magani. Ko ke fa? Ynxun zaki san kinyi aure. Amma zan vari yau ki huta tunda baki jin dadi, amma gobe da safe zanzo ko? Tace eh, yana fita ta nufi ban daki ta dinga kakarin amai, don gsky shi kansa wari kawai yake yi mata.
Washe gari yana shigowa, haka tayi qoqarin yi masa duk abinda yake so, tare da maida masa martanin duk abinda yayi mata. Tasha wahala matuqa, amma haka ta jure ta nuna masa tana tare dashi, yaji dadi matuq a. Dazai fita ya kawo dubu biyar ya bata. Ya ce ki jirani da daddare, gabanta ya fadi, tace a ranta na shiga uku, a fili tace ai yau ba'a dakina kk ba, yace ina ruwana da wani inda nake, karki damu, abinda kawai na sani dukkanku matana ne, kuma zan shiga gurin duk wacce raina ya biyamin ko kina da ja? Cikin sauri tace, A'a haka ya fita ya barta tana mamaki, tare da tambayar kanta wai daman haka auren yake, ayi ta abu sai kace cin tuwo, kuma ba gajiya? Ita kam ta gaji wlh. Ta dinga juya kudin a hannunta, sannan ta bude akwati nta ta saka, tana yin wanka, sai kuma zazza6i ya rufe ta, ta qudundu ne akan gado cikin bargo. Bata san tsawon lokacin data dauka ba akan gadon nata. Can kamar daga sama sai taji muryar su innarta suna salalla ma. Da sauri ta tashi suka shigo, itace da aminiyarta inna yelwa. Suka iso bakin gadon suka zauna. Inna tace lafiya na ganki cikin bargo haka? Zainabu tace banida lfy ne inna, tace me kuma ke damunki? Ta sunkuyar dakai, tace wai uwar gdnsa ce tace ciki ne dani, shi kuma gashi baya son haihuwa, inna tace to ynxun daya ji kina da cikin me yace?
Canjin rayuwa
1�7⃣Zainabu tace, bai sani ba. Uwar gdn tace, kar in fada masa, shine nace m
asa shawara ce ke damuna kawai, kuma tun ina gd take damuna, shine ya siyo min magani. Inna yalwa ta ce, anya kuwa gsky wannan matar ta fada miki? Ance kar ki sake ki saurari maganar kishiya. Har wata soyayya ce zaki samu a gurin kishiya? Zainabu tace Allah kam tana sona da gske. Don tana fadamin gsky, kuma in tabani shawara in nabi ina ganin daidanta. Jiya ma saida ta matsa kan cewa in na saki jiki dashi zan samu kudi, wai anan ne zan samu nayi siyayyar kayan Jariri. Shine nadan daure na saki jiki dashi, shine ma har ya bani dubu biyar. Kuma dama ko yaushe tana fadamin cewa inyi hakan, don dai naqi yi ne.
Inna tace kedai akwai sakarya, dama qin sakin jiki kkyi dashi don ubanki? Shiyasa ni kaina ya rage bani abinda yake bani, don jiya na aiko ya bani dubu goma, amma sai ga dari biyar, yadda kk san in yaga ta don haushi, amma na fasa, to tashi ki dauko min dubu biyar din, Zainabu ta turo baki, to zan tara ne fa inna, don fa an fadamun har in ya gano cikinnan, bazai bani komai ba, kuma kayan Jariri ma fa nice zan nema. Inna yalwa tace, jaririn banza, ke kk ta Jariri, waya ce miki za'a barshi? Yanxun nan zamu je a hado maganin da zaibi makwarara, ko yaya kk gani Aminiyata? Ta kai qarshen zancen da kallon innar Zainabu. Inna tace tace, yadda kk ce dinnan haka za'ayi. Zainabu ta soma kuka, don Allah inna kar ku bani maganin zabar da ciki, ance fa wata matarsa ta rasu sakamakon shan maganin zubar da ciki. Inna yalwa tace to shikenan don ta mutu sai aka fada miki cewa kema .mutuwar zakiyi ko? Inna taja tsaki, bar sakarya! Duk abinki cikinnan baza'a barshi ba.
[8/17, 11:06 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�8⃣Inna yalwa tace, saurara kiji Zainabu. In an zabar da cikin, sai kinfi jin dadin kar6ar kudin a gurinsa. Duk lokacin daya zo gurinki, ki tarairaye shi. Zainabu tace shifa ko wane lokaci, sai yace zai shigo dakina, koda ba anan yake ba, inna yalwa tace saurare ni dakyau, in kullum zaizo gurinki, karki sake kice masa NO, inji ku 'yan boko, kuma kar ki nuna kin gajiya. Sannan zamuje a hado miki kayan da'a a gurin 'yar jibiya sbd aqara samun kansa. Kinga ya qara sakin miki baki n aljihu. Inna tace shikenan sai a shigar mata zubin adashi, ai kya san abinda kk tara ko? Ta kalli inna yalwa. Tace qwarai kuwa. Inna tace to yaya batun zuwa gdn malaminnan yalwa? Inna yalwa tace, abar batun zuwa gidan malamin nan, tunda shi ga inda yasa gaba, sai mubishi tana gurin. Tayi ta dirkar maganin da'a masu qarfi. Inna tace shikenan hakan yayi, inna ta miqe, ynxun dai tashi muje yalwa, zamu dawo zuwa Anjima. Zainabu ranta 6ace tace anjima kuma? Nidai zaku fa sa ace iyaye na suna ta sintiri a gidannan, ayi min gori. suka ce a daura miki goruba! Anjiman nan zamu zo. Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe. Don haushi ko sallama bata yi musu ba, ta sake qudundunewa akan gado tana ta kuka.
Canjin rayuwa
1�9⃣Ismail kusan kusan tare suka shigo da likitan, har lokacin daddyn ta take kira cikin sarqarqiyar murya wadda take a galabaice. Likitan ya isa gaban gadon ya dafa goshinta, sannu khadija ? Bude idanun ki in gani. Ta soma yunqurin budewa, dishi-dishi take gani. Yace kin sanni? Ta sake lumshe idanu. Ya waiwaya ya kalli Ismai l sannan ya yafito shi da hannu, Ismail ya matso. Likitan yace yi mata magana. Ismail yace bude idanunki ki ganni. Yakai hannu ya dafa goshinta. A wahalce ta bude idon ta numfashin ta sama sama, tace malam ina khalil di na? Yace yana nan yana varci acan dakin maza. Bai mutu ba? Yana samun sauqi, sannu kinji. Ta daga idanunta a wahalce, ta kalleshi, malam ka kaini gurin daddy na zan mutu ne kaji? Zan mutu. Hankalin Ismail yayi mugun tashi. Ya kama hannun likitan. Don Allah ka bata magani. Wlh Yarinyar nan amana ce a gurina likita. Likitan ya kama hannun Ismail zuwa bakin qofa, yace karka damu, tambaya daya zan maka, Ismail yace to. Sunan data ambata wanene? Ismail yace daddy mahaifinta ne, shi kuma khalil .shine wanda yasu, ina nufin wanda sukayi hadari tare. Likitan yace Alhmdlh. Ynxun ina ganin matsalarmu wannan karayar ce. Sai dai kafin zamu qara mata jini, don ta zubar da jini sosai, daga nan sai mu dora ta. Ismail yace babu matsalar jini, a gwada nawa, in zan iya bata, sai asa mata. Likita yace babu matsala, da safe zamu gwada jinin naka. In zaiyi sai mu ta ce asa mata. Sannan maganar dori, nayi maka batun mai dori, ban nemi shawararka ba, ko kuna son na gd, Ismail yace to ni dai likita, wanne kaga yafi? Domin wannan Yarinyar amana ce a gurina.
[8/18, 6:18 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�0⃣Likitan ya dafa kafadarsa, kar ka samu damuwa. Mu dai a gurin mu wannan likitan, kamar yadda na fada maka zaizo ne daga kano, kuma yana yin dori sosai anan asibitin, kuma bamu ta6a ganin wata matsala ba. Amma kayi shawara da 'yan uwanka. Yace to shikenan zuwa da safe duk yadda muka yi zaka ji. Likitan yace, babu komai. Ni zan tafi dama na jira ne sbd inga farkawarta. Ismail yace, to yanxu ba zan iya bata wani abu ba ko da tea ne? Likitan yace kai ka damu, zaka dai iya bata ruwa ne in ta buqata. Nurse zasu zo su saka mata ruwa tare da yi mata allurai, domin ta samu varci da kuma sauqin radadin. Ismail yace, nagode likita, saida safe. Ya girgiza kafadar Ismail, kar ka damu. Insha Allahu zata samu sauqi, 'yar amanarka. Akwai likitan dare ma, wanda ina zaton ma yazo. Inda wata matsala sai ka fadawa nurses, zasuje su kira likitan. Ismail yace nagode sosai likita. Bayan fitar likitan ne Ismael ya sake dawowa ya tsaya akan mimi. Yana matu qar tausaya mata. Ji yake kamar ya kar6ar mata ciwon. Nunfashin ta dai-dai yake fita. Yasoma karanta addu'oi don nema mat a sauqi daga mahaliccinta. Bada jimawa ba Nurses guda biyu suka shigo suka sa mata ruwa tare da yi mata allurai. Suka ce, ka lura ko da cikin dare, kar ka bari ya goce. Yace musu, to suna fita ya zauna yana riqe da tattausan hannunta, wanda shine mai lafiyar, yana ta kallon fuskarta tare da tuno yadda abubuwan suke ta faruwa tamkar cikin mafarki. Alamun tayi varci yasa shi ajiye mata hannun a gurin da ba zata gotar ba. Sannan ya tashi ya koma kan dayan gadon ya kwanta yana fuskantar ta, har ynxun yana ci gaba da kallon abubuwan kamar almara ko kuma mafarki. Ina mabya farka ya ganshi a dakinsa na zauren su, ace ma shi baisan wata mimi ba. Amma da ya dan ciji yatsansa, sai ya tabbatar cewa ba mafarki yake yi ba, domin yaji zafi. Amma