Showing 12001 words to 15000 words out of 30884 words

Chapter 5 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novel By Halima Abdullahi K Mashi

account number na, nace mata banida shi, amma zan turo mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai, Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi sallama. A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa hajiya Account number din, bada jimawa ba ta kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi sallar magriba, yanason sai yayi isha'i zai dawo don haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar isha'i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci. Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har zuwa shigowar wannan matsalar.
[8/22, 11:47 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�5⃣Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace, nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take? Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa kacemin Mahmud? Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba, sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi. Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita? Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba. Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu'a, ki roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan. Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi.


Canjin rayuwa
4�6⃣Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi. Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba.
Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka hada da Addu'a. Zamu taya ka, wata rana sai labari, ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in tafi, gidansu rabi'a zanje. Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen. Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba? Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu goben.!
[8/22, 8:04 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�7⃣Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala don yin shafa'i da wutirinsa tare da da addu'o'insa daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan saudatu bashir. Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace, kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen, inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya. Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin zamansa shiru ya isheshi. Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za'a yi mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace, naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace, haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa? Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya, hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan zuwa anjima.
Canjin rayuwa
4�8⃣Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya. Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta turo kudi a account din makaranta zanje in cire. In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka kwantar da ita akan gadonta tare da maqale qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis, likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya doctor salis yace ma Ismael, "yar amanarka zata warware. " Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka. Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula 'yar fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce, daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun gode, Allah ya saka. Sukace Ameen.
[8/23, 1:49 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�9⃣Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna. Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, "ina zan san abin da ya janyo. Kai sama'ila yaya abin ya faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan. Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja "Mtsss" sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne kaji cikinsa. Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa. Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da rabi'a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka akan wani super market. Yace ma dan acha6an don Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace, amma ba dadewa zakayi ba ko? Daidai lokacin da ya tsaya, A'a insha Allahu bazan jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga mashin din. Ya shiga tafkeken super market din tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci ko sha. Da makilin ya soma cin karo, gasu nan kala kala, ko wanne da kudinsa manne a jiki. Sai ya dauki mai tsadar ciki, ya sai brush da sabulun dettol na wanka. Sannan ya koma gurin kayan sha. Ya rasa wanne irin drink take sha. A qarshe sai ya dauki maltina a nasa tunanin kowa yanasha. Ya sai katan din ruwan gora guda biyu, sai kayan tea na manyan gwangwani. Suga na kwali. Ya sai flask din ruwan zafi. Daya fito wajen gurin ne kuma ya isa gurin masu saida kayan marmari, ya sayi Apple, lemon zaqi, sai kankana da abarba. Dan acha6a yace, gsky malam za fa kaimin qarin kudi. Ismail yace, babu komai, Allah dai ya kaimu lfy.
Canjin rayuwa
5�0⃣Da kaya niqi-niqi ya hau samansu, gabansa har faduwa yake yi daya tunkaro asibiti. Haka dai ya nufi dakinsu, tunaninsa a wane hali zai samu mimin aciki? Don yasan zaiyi wuya in bata farka ba. Ya tura qofar cikin sallama, k idanunsa suna kan gadon. Yaya Amina ta amsa Sallamar tana kishingide a dayan gadon. Yace sannu yaya na barki ko? Ta sauko tana tana fadin, banyi zatonka a wannan lokacin ba, ko har kunje zariyan? Ya nufi gadon mimi yana cewa, mun bari sai gobe, sbd yau yamma tayi. Bata farka bane? Yaya Amina ta iso gaba gadon. Tace, ta farka, ko ido bata bude ba, kuka kawai take yi. Don nima nishin kukan ta yasa nasan ta farka. Tsaki yaja cikin damuwa yace, nidai Allah ya sani wannan kukan yana damuna. Yasa yatsansa ya debe mata gashin kanta daya watso kusa da idonta, ya maida mata shi bayan kunnenta. Ya tsura ma fuskarta ido, wadda tayi jajur don kuka. Idanunta kuwa sun kumbura sunyi luhu-luhu. Ya dora tafin hannunsa akan goshinta. A fusace ta bude idanunta, qwayoyin idon sunyi jajur. Ta zuba masa harara, sannan ta girgiza kanta, alamun ya cire mata hannunsa daga goshinta. Yace bakisan in dafa miki goshi ne? To na cire. Amma ynxun ki tashi kici wani abu. Ya rusuna ya soma ciro abubuwan daya siyo daga cikin ledar. Yaya Amina tace, Yauwa yanada kyau ta wanke baki kuwa, ga makilin da brush. Amma ka manta baka siyo roba 'yar mai fadi ba, da FO sbd fitsari, don kaga tana varcin nan duk ta fitsare kayan jikinta da na kwanciyr. Gashi Kaje gida amma baka dauko mata kayan sawa ba. Ismail yace, fitsari kuma? Ya dago ya kalli mimi, fitsarin lfy? Sabon kuka mimi ta saka. Domin farkawar da tayi taji ta sharkaf cikin fitsari ya tada mata hankali. Wai ita mimi ce haka? Mimin daddy mai shanawa. Sam bata son ta bude ido ta kalli asibitin bare malam Ismail, wanda ta tsana fiye da kowa. Ta tuna lokacin da tayi wani zazza6in mura, waje suka fita, can England aka duba lafiyarta. Tunda ta taso, duk bayan wata uku dad yake kaita a duba lafiyarta a qasar Misra. Amma yau gata a wani qazamin asibiti kwance cikin fitsari. Ina ma dai mutuwa tazo ta dauke ta. Da ma da sukayi hadarinnan itama ta mutu da yafi mata wannan Rayuwar.
[8/23, 1:50 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�1⃣Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana qafafu a sagale taya za'a sata tayi fitsari? Yace hakane. To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma ynxun ya kk ganin za'ayi gurin cire mata kayan? Ko inje in fara dauko mata wasu in dawo? Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo. Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani, mafi yawa daga cikin kayanta 'yan kanti ne, riga da wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta data debo sbd guduwar su. Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin. Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki. Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba. Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki 'yan shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku. Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki. Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun kalli abinda bai ta6a gani a fili ba
Canjin rayuwa
5�2⃣Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data yi. Yaya Amina tace, "mun yi miki fami ko? " Malam Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin. Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun. Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci, ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude haka, matar kace. A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri, ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush, taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora. Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama? Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa. Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa shiga dakin.5�3⃣Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya kalleta. "tafiya zakiyi? "Tace, eh, kaga yamma tayi, ga girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a cikin daki. In ba ayi sa'a ba sai yayi ta dukanta. Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace, haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima. Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben. Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah ya kaimu. Har gurin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login