Showing 30001 words to 30884 words out of 30884 words

Chapter 11 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novel By Halima Abdullahi K Mashi

sannan suka nufeshi. Ya ce, ku zauna bakin gado kyawawan 'yan biyu na. Suka zauna. Ya dora hannunsa akan kafadar ko waccensu. 'Yan biyu kuma fa kun girma, masha Allahu. Hajiyarku tace min zakuyi jamb da Waec ko? Suka sake kallon juna, sannan sukace "eh daddy mun kusa mu fara. Yace, to Allah ya baku sa'a. Suka ce Ameen.
1�0�0⃣Ya sake cewa, me kuke karantawa ne? Ina nufin Art ko science? Usaina ta kalleshi "'Hassana ce take science class, ni Art nike. Yace, Hassana zamu doctor kenan? Ta kalleshi cikin Jindadi tace, eh daddy inason in zama medical doctor. Yace, Usaina fa? Tace, daddy nikam 'yar jarida nakeso in zama, ina sha'awar haka, shiyasa mass com zan karanta. Cikin farin ciki yace, nagode ma Allah. Allah ya cika muku burinku yara na. Daidai lokacin Hajiya sauda ta turo ta shigo da sallama. Ta kallesu da fara'a " 'yan biyu azo aje ayi varci ko? Suka miqe, sannan suka sake cewa, daddy Allah ya baka lfy. Yace, Ameen nagode. Suka ce, Hajiya saida safe. Tace, mu kwana lfy karku manta da Addu'a. Suka ce, to. Ta zauna tana kallon fuskarsa, "sun dameka da surutunsu ko? Yace, inason su saki jikinsu dani. Tace, ya kamata kam. Yace, "ynxun wace shawara zaki bani? Ta kalleshi "tame? Maganar da nayi miki dazun, ta damqa harkoki na ahannun yara, kamar yadda kike ta bani shawara tuntuni. Tace, ynxun kwanta kasha magani fa, in ka samu varci, gobe idan Allah ya kaimu, sai muyi maganar ko? Ya kwanta tare da cewa, Allah ya kaimu. Itama ta kwanto masa, tare da kashe fitilar dakin.
Alhaji Bashir ya jima bai samu varci kamar na yau ba. Yaji dadin jikinsa daya farka, har masallaci yaje. Sannan da gari ya dan yi haske, sai yace, ki fitomin da kayan motsa jikina, zan dan fita. Likita yace, in dinga motsa jiki sosai, zufar da zan fitar tana fita da cutar.
Canjin rayuwa


1�0�1⃣Hajiya sauda tace, tunda yarannan suna hutu, to ka fita dasu Abdullahi mana da Sadiq da Ameen da Umar. Take ya yarda sbd ynxun kam burinsa bai dara kusantar duk 'ya'yan nasa ba. Suka fito cikin kayan motsa jiki. Yaran sun sa gajeran wando da riga mai gajeran hannu, yayin da uban yasa mai dogon hannu da kuma dogon wando. Yaran cikin murna, domin suna son fita motsa jiki sosai, Hajiya ce take hanasu, wai tace, batasan da wadanne irin abokai zasu hadu ba in sun tafi can gurin motsa jikin. Alhaji ya dube ta, "sai mun dawo." Cikin salon tsokana tace, "to Alhajina. "Ta kalli Abdullahi, "Yarana masu albarka, ku lura min da mijina. Gaba daya suka sa dariya. Tace, da gske nakeyi Abdullahi, kar yayi gudu, tafiya kawai zakuyi. Suka ce "To" suka jera suka fita, biyu nan, biyu nan, suka sa mahaifinsu a tsakiya. Kafin ya dawo tuni ta dama masa kunun alkama da qosai. Qarfe takwas suka dawo, duk yayi zufa, yaran suka nufi dakinsu don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka masa tayi tayi, yayi wanka don nuna kulawa. Bayan yaci abinci, yasha magani, sai yace, ki shirya zamu fita. Tsaf tayi kwalliya cikin koriyar super da hijabinta wanda kyansa ya nuna tsadarsa. Qamshi take yi, ta bar sallahun komai gurin masu aiki tare da sauran yaran, sannan suka fita. Direban shi ya taso, Alhaji yace, je ka huta. Nine zanja motar. Saida ta zauna a gidan gaba, sannan ta kalleshi da murmushi. "kai da baka da lfy?1�0�2⃣Yace, sauda kowane lokaci in muna tare bana son mu samu na uku. Sai inga tamkar mu kadai ne a duniyarmu. "Tasa dariya, daidai lokacin daya tada motar. Tace, to kaba ni in tuqa mu. Kaifa jiya kazo. Yace, baki lura ina ganinki na samu sauqi ba. Ynxun ma kinsan ina zamuje? Tace, a'a. Sai da ya hau titi sosai, sannan yace, gidan saukar baqina. Inason muyi hirar da muka dade bamu yi irin ta ba. Sannan mu tattauna muhimman zantuka. Murmushi tayi batace qala ba.
Kwance suke a tsakiyar gadon na dakin baqin, suna fuskantar juna, yace sauda na buqaci muzo nan ne musamman don in baki haquri, sannan in fada miki dalilaina. Sauda nasan cewa, na sa6a miki lokacin dana rabaki da 'yarki na kaita ga wata, wanda harga Allah lokacin soyayyar Mimi ta rufemin ido har na aikata haka. Amma kika yi haquri. Sannan na biyu kece kadai zanyi wa 'yarki abinda nayi mata, wato aurar da ita ga talaka ba tare da kin dagamin hankali ba. Da wata ce, cikin sauran matan, na tabbata da ranar aurenmu da ita zai mutu. Sai na qarshe kece kadai 'yarki zata samu hadari, in hanata zuwa, kuma ta hanu. Sauda duk inda ake neman mace ta gari, kin kai. Ina roqon Allah yasa ki zama shugabar matana a gidan Aljannah. Cikin murmushin jin dadi tace, Ameen Alhaji. Ya tashi zaune. "sauda dalilina na aurar da Mimi ga malam Ismail, tare kuma da yanke duk wata alaqa da ita tare da cire ta cikin ahalina shi ne........
Kashhh! Mu hadu cikin littafi na hudu, kuma na qarshe. K. Mashinku ce, sai na jiku a 08081165107

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login