Showing 1 words to 3000 words out of 30884 words
Chapter 1 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novel By Halima Abdullahi K Mashi
CHANJIN RAYUWA
book 3
(1)hankalin isma'il yayi mutukar tashi lokacin da aka juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan mahmud yazoya kama kafadun isma'il yana cewa karka damu isma'il mutafi asibiti sun nufi motar kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana cewa kaiba ni kayan nan konakane? yace ammm dama inace za aje gurin yansadane mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada in anyi hadariko? mutumin ya miko akwatin tare da cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan sannan ya shiga yana cewa "muje hamisu!" kuwwar motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso. sannan suka nufi asibitin tare. cikin sauri aka amshi su aka yi emergency dasu, musamman dayake angansu da yan sanda.isma'il yana tsaye cikin matsanancin hali.addu'o'in da isma'il yake yine sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya abin yafarune? mahmud yakalli dan sandan gudu yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune?sai wani ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne suke dauko mota suzo sunamugun godu atiti.mahmud yce,yarinyar da suke tare matar wannance, yanuna isma'il.jiya aka daura musu aure shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma'il batason kane?isma'il yace,babanta ne yahada nida ita ranka yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce,kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara.sannan suka ce,allh yajikansa da gafara.isma'il yakama hannun likitan yana fadin"doctoh itafa?"yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu karaya guda biyu a kafarta,da kuma guda daya a hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta, saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda,kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka wadannan,yanxun kakawo mana.isma'il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana.daga nan sai mutan gadan su san halinda ake ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba agata mimi ba. hamisu yajasu,kai tsaye gidan suka
Canjin rayuwa bk3
(2)
koma,inda isma'il ya aje jakar mimi,sannan ya dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi.ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai magungunan.lokacin ne ma dansandan yake fada musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki gawarsa.isma'il ya girgiza kai don jinjina yadda mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira hamisu don yaji ko ya kosa kaduna.zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace xaiba shi,don shima yaji dadinsa. hamisu yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba har yanxun.alhaji ya ce,meya faru kuma?hamisu ya sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai yace ma hamisu,"kataho kawai!"yace,alhaji yarinyar nan tana
(3)cikin mawuyacin hali sosai,don duk akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar.babu abin da zan iya yi mata,kaima bbu abin daxaka iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace,shikenan,alhaji zan taho yanxun."yace,"to,kana kusa dashi malam isma'il din ne?yace, "eh ina kusa dashi.yace,toka bashi!"ya mikama isma'il wayar.sun gaisa,alhji yace,"ashe abinda yafaru kenan?"isma'il yace kwarai kuwa alhji.yace allh yakyauta."cikin tashin hankali isma'il y2e,alhji kayi mata duk abinda takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya rasuma."duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar khalil a ransa,amma afili sai yace,"karka damu malam isma'il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar."isma'il yace alhji kuzo ku taimaka mata."alhji yace,isma'il inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu wayar!"cikin rawar hannu,isma'il ya mika ma hamisu wayar.
Canjin rayuwa
5⃣A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya sauda. Ya kalli mahmud, "ya kamata in sanar da mahaifiyar yarinyarnan ko? " Mahmud yace, "tabbas ya kamata ka sanar da ita" kan benci ya zauna, sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne? Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar zuciya, to da sauqin dai za'ace amma shi ya rasu... Ya rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,. Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe wayar.
Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba, yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran 'ya'yanki banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji? Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe wayarsa.
[8/14, 15:02] A~PROF: 6⃣shi kansa Alhajin cikin damuwa yake,
amma ya tsara ma kansa cewa, dole ya haqura
don wani dalili nasa, sannan yasan cewa, abin
Ya ta6a zuciyar hajiya sauda, sbd hk ya yanke
Shawarar sake kiranta. Ta daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai nayi hakan. Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin wannan. Nasan zaki iya saka 'ya'yanki su dangana da zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya, shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya kawo ka lfy.
Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata. Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili. Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne? Tace a'a ba zan samu zuwa ba, in dai ta tashi kace ina gaisheta.
[8/14, 15:24] A~PROF: 7⃣Yace hajiya kema baki samun damar zuwa kenan? Ta soma shesshekar kuka, mahaifinta yayi mana iyaka da zuwa gurin ta, cikin sauri yace sbd me? Don Allah ku yafe mata, sbd tana cikin wani hali, wanda ba dole bane ta tashi. Hajiya tace na yafe ma ta duk abinda tayi min, wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma nima bansan dalilin sa nayin hkn ba, amma idn ya fadamun zan sanar dakai. Sannan kuma malam Ismail zan sake baka amanar mimi, ka qadd ara batada kowa, sai kai kadai mijinta. Lokaci zuwa lokaci zan dinga jin yadda jiki nta yake, amma ta waya daga bakinka. Ismail yace shikenan nayi miki alkawarin zanyi iyakar iyawata, sai Anjima.
Ya kalli Mahmud, bayan ya kashe wayar, wannan wace irin qaddara ce ta hau kaina? Alhaji ya hana su zuwa ma. Mahmoud yace wanna n abin da Mamaki, amma tunda kai iyalinka ce, nauyinta ya rataya ne a wuyan ka. Kai ya cancanta kaci gaba da kula da lfyr ta har zuwa lokaci n da zasu huce. Nawa zaton sunji zafin guduwar data sake yi ne. Amma in sun huce zasu zo. Ismail yace Allah ya sani, tunani na dama banida qarfin dazan iya kula da lafiyarta. Mahmud yace, kar ka damu Allah zai duba maka. A sanyaye Ismail yace Allah ya duba mana, suka hada baki gurin cewa Ameen! Saida lokacin sallah yayi sannan suka miqe suka nufi masallaci. Daga masallaci ne Mahmud ya nufi gd don sanar wa malam Aminu. Ismail yace kabi ta gdn yaya Amina ka fada mata don bata sani ba, Mahmud yace zanbi insha Allahu.
Canjin rayuwa
8⃣kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu'a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen.
Bayan la'asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu'ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a'a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a'a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a'a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s
Canjin rayuwa
8⃣kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu'a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen.
Bayan la'asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu'ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a'a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a'a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a'a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s
Canjin rayuwa
9⃣sun kai kusan minti goma, sannan wata nurse ta leqo, ta kalli Ismail, tace masa wanene khalil? Yace mata shine wanda sukai hadari tare ya mutu. Ta juya da sauri, Ismail dai yanata kai komo. Ya kai kusan rabi sa'a sannan likitan ya fito, ya kalli Ismail yace masa, zo muje! Ya bishi zuwa offishinsa, inda suka zauna, ya kalli Ismail, kai wanene dinta? Ismail yadan yi jim kadan don yana jinjina kalmar, duk lokacin da zai furta ta. Tsakanin jiya zuwa yau, ya lumshe ido, "ni mijinta ne" likitan yace ok to zamu kaita dakin jinya, domin ynxun ta farka, amma yanxu munyi mata allurar varci sakamakon tana ta kiran sunan marigayin. Ya ajiye biron daya dauka, sannan ya kalli Ismail yace, wazai zauna da ita? Ismail yace nine, likitan ya girgiza kai, babu dama ka zauna da ita, sbd kai namiji ne, kuma dakin akwai matan mutane, sai dai in zaka biya daki na musamm an, sannan za'a buqaci kudi sbd likitan da zai mata dorin zaizo ne da ga kano, kuma gashi dorin har guri uku ne, Ismail yace to likita kamar nawa ake nema? Yace kasan shi likita ne mai zaman kansa, dauko shi akeyi, qila yakai gurin dubu sittin, banda magani. Ismail yace insha Allahu za'a san yadda za'ayi, Amma likita bata samu matsalar da ake tunanin ta samu ba ko? Ya girgiza kai, bana zaton ta samu wata matsala, Ismail yace Allah yasa dai, zan biya kudin daki na musamman din.
Likitan yayi masa kwatancen inda zai biy a kudin dakin. Har ya miqe sai likitan ya sake kallon sa, ba tada iyaye ne a garinnan? Eh, kawai yace, to ko cikin dangin ka ba wanda zai iya zama da ita? Cikin qosawa yace nima yayata ce guda daya, kuma tana da qananan yara. Baya son doguwar magana, shiyasa ya amsa a qagare, shikenan ka iya tfy, inji likitan, an kaita daki na musamman akan kudi naira dubu ashirin a sati biyu. Dakin akwai TV da dan fridge, sai na'urar sanyaya daki. Ismail yana tsaye yana kallon mimi, an manna mata bandeji a gurin da taji ciwo. Addu'o'i kawai yake yi mata, har lokacin da yaje yayi sallar magrib a bata farka ba.
Canjin rayuwa
1�0⃣Yana shigowa yaci karo dasu yaya Amina, suna neman dakin da aka kaisu. Ya amshi kular hannunta sannan suka nufi dakin, suka gaisa da abbab saddam, yayi masa jaje. Basu jima ba suka ce zasu wuce. Yabi su don yadan taka musu, anan ne take tambayarsa ko 'yan gdansu sunzo? Yace kinsan dai koda zuwan ne, sai dai in mazan, amma matan ban sa rai ba, mazan ma daqyar in sunji, tunda lokacin da naje gdn basa nan, tace to ba komai Allah ya bata lfy, yace Ameen, tace tuwo ne fa akular da muka zo da ita, naga kana son tuwo, yace nifa yau ko karyawa banyi ba, dama zan samu ruwan zafi, tace vari to inje in dafa maka, sai abban su saddam ya kawo maka, tunda ga mashi n ahannunsa. Ismail yace to na gode. Suna fita, wayar Ismail ta soma ringing, ya daga ashe Mahmud ne ya kawo innarsu zata duba ta, suna cikin gaisawa da innar sai ga kiran hajiya sauda. Bayan sun gaisa take tambayarsa jikin mimi, yace da sauqi, amma tana varci, bata farka ba, tace to zata kira zuwa gobe, sannan ya turo mata account number dinsa, yace to insha Allahu, sannan yayi mata godiya. Kusan qarfe goman dare, mimi ta farka, lokacin Ismail yana zaune kan sallaya, ya idar da sallar shafa'i da wutiri. Sai yaji tana cewa, "daddy na, daddy na!" cikin wani irin sauti mai ban tausayi. Da sauri ya miqe ya nufi gadon da take, ya kama hannunta yana "khadija, sannu kinji. Kin tashi ne? Bari in kira likita" ya miqe ya nufi qasa da sauri domin kiran likita.
Canjin rayuwa
1�1⃣Daidai da Na'ima ta shiga dakin Abbas, yana akan kujera yana shan 'ya'yan itatuwa. Tun daga qasa ya soma kallon Na'ima har sama, sannan ya dauke kansa gefe. Cikin jin kai yace lafiya? Duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa yin abinda tayi niyya ba, kai tsaye kujerar da yake ta nufa ta zauna a hannun kujerar. Tasa hannunta akan kafadarsa, tare da fadin, "sweety ashe ka dawo, ka shigo lfy? Tsawa ya daka mata. Duk da ta firgita, amma bata tashi ba. Yace ke ni abokin wasan ki ne, ko na ta6a wasa dake?