Showing 12001 words to 15000 words out of 19770 words

Chapter 5 - HAUWA KULU WOMEN LEADER Book 1

16 Oct 2024

1070

duk kishinta da Allah ya nufa Aryan sai yayi aure sai da ya auri ilham yarinyar da takewa kallon yar aiki...yar tallah..,

My fan's kar ki sake a barki abaya in baki karanta littafin KIN CUCE NI BA ki gaggawar nemansa ta wannan hanyar 09061890481 yasha banban da labarin da na saba kawo muku


kafa ɗaya kan ɗaya ta ɗora tana girgiza wa tace



"Amma ai halina da na Fateesat daban...,


Daga mata hannu yayi yace



"Duk da haka shin kinsab mene dalilin da marubuta suke rubutu....?,


a'a


Kamamo hannun'ta yayi yana ɗan messaging ɗinsa yace


"Saboda su faɗakar da al'umma ta hanyar nishaɗi cikin sauki su isar da saƙon su bawai suna rubutu ne kara zube baba a'a sai sunyi dogon na zari me ya faru a DESTINY LOVE baki dauki izinar da NUCY ta dauka ba duk kuɗin ki ko duk ta ƙamar ki Ubangiji yanayiwa mutum talala ne in ya tashi kama shi yayi mai kamun kukun kaza...,



zare hannun'ta tayi domin har ta fara jin ƙasala tace



"Sweetheart.......taja ƙarshan sunan...,


Gira ya ɗaga mata yace



"Na'am honey me ya faru....,



Noƙe kai tayi tace



"Bakai bane...,



Kama kunnansa yayi yace



"Na tuba me ya faru...,


tashi tayi ta juya bayan'ta tace



"Kai nake so.....,


Dariya ya saki ya tashi ya kama ƙugun'ta yace



"Kin sameni.....,



Juyowa tayi ta sheƙe da dariya kama gemun'sa tayi ta na wasa tace



"My man duk randa ka gujeni wallahi mutuwa zanyi bazan iya zama a doran duniyar nan niƙadai ba...,




Kura mata ido yayi yace



"insha'Allah bazan guje ki ba .....amma NADEEYA ki daina shan kwayoyin da kike sha zafa su iya a effecting ɗin ki ....,



ɗan ya mutsa fuska tayi ta buɗe baki zata yi magana ya haɗe bakin su wani irin nishi ta saki sakamakon hannun'sa da ya zura a rigar'ta yana wana shafa breast ɗin ta zare bakin'sa yayi ya maida kan kirjin'ta mur kicewa tayi


Ansh yasan lagwan mace nan danan zai hautsina miki lissafi bare da sanin ki ba shiyasa a koda yaushe take cewa tafi kowa sa'ar miji


*NI KUWA NACE KO WACCE MACE JI TAKE MIJIN'TA YAFI KO WANNE MIJI A DUNIYA KO MY FAVOURITE SPECIAL HUSBAND MY LOVE YOU ARE THE BEST.......🗣️🗣 happy birthday to you my lovely ️*


Ganin abin ya fi karfin floor ya dauke ta suka shiga bedroom sai da abu yayi nisa taga baza ta iya ba ta saki kuka dakyar ya sarara mata







Komawa gefe tayi tana sakin kukan tabbas ta gurzu lallashinta ya shiga yi narke mai tayi tare sukai wanka suna dawo floor wayar sace tayi ƙara alamar shigowar messages ta gefen ido Nadeeya ta kalle'sa ganin bai da niyar dauka tace



"Dear kamar wayar ka message ya shigo....,


ɗago kansa yayi ya cire medical glasses ɗinsa saukar da laptop ɗin'sa akan Centre table yace




"Najii.....,


Kauda kan'ta tayi ta taɓe baki halin mijinata sai addu'a miskiline na bugawa a jarida daukan remote tayi ta canza tasha cikin sa'a kowa ana haska program ɗin jidda da sauri ya ɗago


Duk wannan dambarwar da ake be taɓa ganin jidda ba mai da hankali yayi sosai gurin hirar tata inda take tallata ɗan takarar shugaban kasa SA'EED MAI GORO da matemaƙin sa Joseph aken wale tsaki nadeeya ta saki tace



"Wallahi sweetheart na tsani yarinyar nan a haife ka haife ta kalli wai kai ne gurgun mage ga wannan cin mutunci...?,



ɗan murmushi yayi yace



"Nadeeya ke aka ce wa gurgun mage...da har zakiji zafi....?,



Amma dai daga mata hannu yayi yace



"Sau dadama Nadeeya ina koya miki wani darasi da kika kasa dauka ita siyasa dole kasamu maƙiyi da masoyi dan haka ba abin da muwa bene dan kaji ana kushe zaɓin ka ba...,


Kai ta juyar tace



"Kai jama'a jibe ta Dan Allah wallahi sweetheart woman leader nan yan iskane karuwai...,



Ki neda aibata ta baki san gaibuba kar Ubangiji ya tsaidake ranar tashin alƙiyama nadeeya kiyi shaida


Daukan remote tayi ta canza tasha dauka yayi ya mai da ita



Cikin fada tace



"Wai kai wanne irin mutum ne....? Kamar bakai ake zagi ba na lurama kamar jindaɗin kallon wannan karuwar kake.....,



banza yayi mata fuuu ta bar flooe bedroom ɗinta ta nufa daukan wayar ta tayi da take kan dressing mirror cikin contact ɗin ta ta shiga ta kira wata number bugu daya aka dauka cikin hanzari tace




"Hello tani kisa yarin ki suje gidan su waccan yar iskar su yi mata kaca kaca wallahi na gaji da abin da takewa mijina...,


Dariya ta saka tace


"Uwar ɗakina an gama yanzu zansa su jagwal su ya mutsa mata hazo...,



Okay turomin da account number ɗinki


Godiya tayi mata ta kashe wayar

Komawa tayi ta zauna ta shiga charting da kawayan'ta ..........✍️




*Oum Yasmeen*




*HAUWA KULI WOMEN LEADER*



*oum Yasmeen*


Sauran page two in gama book one


Book 2 paid book 500 duk meso zai iya biya ta wannan hanyar



8141785374

Amina alhasan Muhammad opay



Yan niger zaku iya turo da katin Airtel na 300fcfa Ku dauke shiku turu min


Ta wannan number 09061890481




*Kun zan zarta payment domin shiga group da huri*

*Book two 🔞*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



*******



Karfe 7:30 garine yayi shiru abin ka da sanyi ba masu zaman majalisa kai tsaye yan daban nan gidan su jidda suka shiga hukakensu suka shiga kartawa a ƙasa suna bada wani sauti ran gwaggo ne ya ɓaci cikin faɗa tace




"Wannan wanne irin ɗiban albarka ne badamar abar mutum ya ji kunne sai an ƙara shigo da wanni ibilisancin wallahi na fito nan na lahira sai yafi mutum jin dad....,


Ai bata ƙarasa ba aka dalla reta da futula wani uban ashar ta lallayo zatayi sai ta tsaya mata a maƙogaro sakamakon qallin huka da ta gani yana yawa a fuskar ta zaro ido tayi tace



"Na shiga uku.....,



Ina woman leader...,



Cikin rikicewa tace



"Mene man leda....?,


Ɗaya daga cikin sune ya cije baki yace




"Ke tsohowa Bama son rainin hankali ina take ko yanzu inyi gun duwa gun duwa dake.....,






Jikin gwaggo ne ya shiga rawa ita ba kifi ba ko nama ya za'ai ayi gunduwa da ita tace



"Kuyi min rai wallahi ban san me kuke faɗe ba.....,



Ke tsohuwa bara muyi miki gwari gwari inna waccar yar akuyar yar ki take....?,



Cikin tashin hankali tace



"Kululu...,


Ɗayan ne ya zaro wata siririyar huƙa yace



"Au tambaya ma kike Bara in naɗo hanjin ki sai ki mana bayani....,


Kuka gwaggo tasa tace



"Yara bansan inda take ba wallahi ni kakar ta ce in cewa kukai in bar gidan nan wallahi a yau sai in barshi..... wannan tashin hankali dame yayi kama sai ta fyece majina...,


Ganin abin da ta faɗa gaskiya ne babban su yace



."wallahi taci sa'a da sai mun mata walmu ƙali fatu.....amma zamu ƙara zuwa ku zo mu tafi





Kai baba haka zamu tafi bare da mun reɗi naman fuskar'ta ba



Ƙara sautin kukan'ta tayi tace




"Haba yaron nan kuyi hakuri in wacce kuke nema tazo ai sai ku reɗi nata ko...amma ni na tsohuwa ba abin da zaku samu...sai fata..,



Tafiya sukai bare da sun kulata ba



Gyara fuskarta tayi ta fito tace




"Kuna ina mutanan banza.....ai gashi nan na nuna musu jiya ba yau bace har ni yan daba za su zo guna...,


Fitowa sukai lantana tace


"Haba gwaggo kamar fa har kukanki naji...,


Aa na uwarki kikaji haka ta ƙare musu tanadi tas ba wanda yace ƙala sai da tagaji dan kanta ta koma daƙin'ta






************


Wannan littafin ne kuɗine domin karanta book 2 ki gaggawar payment ₦500

Wanda bazai iya jira ba book 2 ₦700 ne complete na gama shi




Sai bayan magariba dan isiya yazo dan haka ba ɓata lokaci ta hau a hanyar gangare suka haɗo da yaransa sai gidan su BARAKA a kofar gida suka tarar da mahaifin'ta jidda saukowa tayi tace



"Baba ina annamimiyar yarka take....,


daga tawa yayi da alwalal da yake ya dago yace



"Jidda wace kuma annamimiya...,


ɗan ya mutsa fuska tayi tace



"Baba ba dogon jawabi ne ya kawo Ni gun Ka ba kalli da mutanan da nake tare da su....,



kallon su ya shiga yi yana jinjina kai yace



"Eh na gani me ya faru.....,



Naxo ne ka jawa yarka kunne ba ita bani dan wallahi ta sake ta ƙara shiga harka'ta sai na sa anyi filla filla da ita har Ni za ta ciwa amanag ta auri ILIYA



kai ya jinjina yace


"To zata ji....,


ɗur kusawa dan isiya yayi ya kai huƙarsa kusa da kunnan mahaifin baraka yace



"Kaji abin da oga tace ko sai na bar maka shedar da za a gani asan kunnan kashe ne da ku.....,


Bakinsa na rawa yace aa basai ka bari ba


Tafiya sukai suka barshi da sakakken baki


Sai tara da rabi ta shiga gida


Sallama tayi da sauri gwaggo ta fito tace


"Kululu yau ni yan daba suka rutsa ai kuwa yan bantan uba har karyawa ɗta hannu nayi haka suka fita suna kuka wai inja kunna ki....,


Turus tayi tofa wannan shi ake kira da game over tayi anyi mata tace



"Dan Allah gwggo....,


Goro ta ɓantara tace



"Zancan kike so....,


Ƙarasowa tayi ta shiga ɗaki


Washegari da sassafe jidda tasa aka tara mara mutane tana siyan kuri'unsu ran kahu hamisu in yayi dubu ya ɓaci lamarin na jidda yawa wacce ake mata baki daga wancan sai wannan da ta addabi al'ummar gari yan zu kuma ga abin da take girgiza kai yayi ya huce sai kuma ya dawo yace



"Jama'a ina jan hankalin ku kar ku siyar da yan cin ku domin ita wannan kuri'a yan cin mutunce da shi za kuyi zaɓe ku zaɓo adalin shugaba wanda zai ji tausayin ku....,



Taunar cingum take aikuwa ba shiri ta tofar ta kunce damarar da tayi a kugu tace



"Kahu me zan gani ba gwaggo tayi min iyaka da akai ba...?,


Jidda wallahi ki guji randa duniya zata koya miki darasi



Turo dauri gaba tayi ta ci gaba da abin da take shiga cikin gida yayi ya barta




To a kwana a tashi ba huya gurin Ubangiji yau ta kama asabar yau za ayi zaɓen GWAMNA dana yan majalisu wani satin ayi na shugaban ƙasa


Al'ummar garine sukai turuwar ƙadawa sagir fegi kuri'a dan takarar jam'iyyar haske party jam'iyyar su ANSH tuni hankalin su me goro ya tashi duk yan daban da suka ajiye hukumar yan sanda ta nannaɗe su


Ga uban tsari da suka fito da shi amma ji kake shiru ranar jidda huni tayi tana yawa a maza ɓa daban daban


Har dare yayi dole ta koma gida sai jiran sakamakon shugaban jam'iyyar haske party ya tsaya tsayin daka ganin ba ai maguɗi ba inda baturan zaɓe ya sanar SAGIR FEGI yaci zaɓe gurin roɗewa yayi

aka fara faɗa da kone basa yi hankalin SA'EED MAI GORO ne ya tashi ya din ga zirga-zirga dole a zaɓen gaba suyi shi ne musamman bazai laminci faɗowa ba shi kuwa dan takarar gwamna waɗowa yayi sai gadon asibiti aka kai shi

Sosai suke tashin hankali sai da aka sa kafiyu


Gidan ANSH kuwa sosai ya shiga murna ganin sun yi nasara zasu kawo karshen zalincin me goro


Rana bata ƙaraya sai dai uwar ɗiya taji Kunya yau ta akama da ai zaɓen shugaban ƙasa


Tun safe Ansh me ɗakin sa Hajiya nadeeya da tawagar sa suka isa mazaɓar sa ya ƙadawa ƙasan kuri a dagowa yayi inda kowa ya gani tuni yan jarida suka shiga dauka ake haskawa kai tsaye a gidajen rediyo da talabijin Wato (live)


jidda ce ta iso ita da tawagar'ta ayayin da ANSH yake kokarin fita sai yau tayi gaba da gaba da wanda take zagi a gidajen rediyo da talabijin kallon kallo akai tsakanin ita da shi yayi da yan jaridu suka saita Camera ɗin su dan jin me zai faru wani irin kwarjininsa ne ya cika ta daman wai haka yake tsakanin su da tazara amma sai taga ta koma wata tsakuwa akan'sa gaban tane ya waɗi kamar ta taɓa ganin photo sa a gun inna ta gabas kardai ace shine wanda innar take bata labari



wani ɗan jarida ne ya matso yace


"Jidda woman leader me akice game da wannan zaɓen shin kina ganin zakuyi nasara.....?,


Da sauri ta dawo daga dogon tunanin da ta shiga lokacin har an buɗe mai mota buɗa bakin'ta tayi da ya bushe yahun bakin ta yayi wani irin kauri tace.......✍️



Yanzu ainihin wasan zai fara


Insha Allah mune da nasara tana faɗar haka tayi gaba

ƙara binta yayi yace



"Kamar kim karaya ba wani abu da zaki ƙara cewa...?,


banza tayi mai in ban da ikon Allah da tuni kowa ya fahimci hankalin da take cikin tun ganin farko da tayi wa ANSH hankalin ta ya tashi bata da wata kwanciyar hankali saboda kallon da ya jefe ta dashi kamar fa .......kallo ne me cike da alamomi kala kala


Kan Ansh dan jaridan ya koma lokacin har ya shiga mota yace



"Me zaka iya cewa game da zaɓen nan da ake yi shin kana ganin nasara...duk da ga al'umma sai kada kuri'u suke...,


Tsayawa yayi yace




"Nasara tana gurin Ubangiji Allah ya zaɓawa al'ummar kasar GEZA adalin shugaba na gari.......wanda zai iya sauke nauyin da ya daukowa kansa ba wanda zai baba kere da duniyar al'umma...,


kamar wannan maganar da kake gogar zana ce



Dan murmushi yayi yace



"Dan jarida wannan ai gaskiya ce ko ban faɗa al'umma da yawa sun san haka samu da rashi duk yana gurin Ubangiji.....,



To ranka ya dade shin gwamnatin ka me ta tanadar wa mata...?,


daidai karasowar jidda dan murmushi yayi yace



"Su mata abin a killace a gida ne macan kware bata fita yawo dan haka zamu basu jari su zauna a gida su yi sana'a.... duk macan da take da daraja bata fita yawo mace fa kamar kwatankwacin buredi ce da wanda ake siyarwa a bakery da wanda yake siyar da shi a kan taburin shayi ai kaga ba darajar su ɗaya ba .......kina mace be kamata ki shiga harkar siyasa ba da namiji ya dace....dan haka zamu tallafa musu su tafi gida su zauna... sannan duk wanda muka kama da siyan kuri'a sai mun kama shi shekara biyu a gidan yarin na zaɓin tara... sannan zan gyarawa kowa zama..,



da sauri jidda ta shiga mota ran'ta inyayi duba ya ɓaci bata ankara ba taji hawaye na suntiri a kumatun ta driver motar ne ya ya zaro tissue ya bata



amsa tayi tace



"Nagode....,


Kai ya jinjina yace



"Ki hakuri mutumin nan magana ya faɗa miki a fakaice....amma ai matar sa ma'aikaciya ce kin ga kenan ita ma ta shiga sahun marasa daraja....,




Hakane kai ni gidan inna ta gabas kar ka kaini gidan


To yace da yake ya taɓa kai'ta tafiya sukai me nisa tukunna suka isa unguwar Tanko fitowa tayi ta rufe kofar tace



"Nagode isuhu daga nan zaka gidan gwamnati ne...,


Tab wanne gidan gwamnati su kansu takan su suke kina ji dazu fa your excellency sai da ya waɗi Saboda yaji kuri'un da waccan gurgur yake samu shifa na uku yake zowa na gari uku kacal aka faɗi yana da kuri'a miliyan daya da dubu dari bafa a zo nan ba ai ba wanda zai saurareka in kaje ke dai Allah ya fitar da muke....



Ajiyar zuciya ta sauke zuciyar'ta sai lugudan tara tara take gaban ta waɗowa take in ta tuno kallon da yayi mata tace



"Amin dai in muka waɗi wallahi mun shiga uku yawo a gari sai ya gagare mu wallahi....,



hakane sai dai kawai Allah ya fidda mu


Amin ya Allah ta juya ta fara tafiya wani kawatatcan gida ya shiga iya kyau da tsarowa ya tsaru daidai zaman mace ɗaya sallama tayi cikin fara'a tsohuwar ta fito fara tas da ita tace



"Jikalle yau ni kika tuna....?,



murmushi ta saki tace




"Inna kullum kina raina....,



ja'ira kamar gaske shigo


Shiga tayi kallon mamaki takewa dakin inna ta zauna a wasu hadaddun kujeru tace



"Inna sake kayan daki kikai...,



kitchen inna ta shiga ta tace



"Dan albarka ne ya canza min...,


Kai jidda ta jin jina tace



"Masha Allah sunyi kyau....cak ta tsaya sakamakon arba da katon photon ANSH da tayi tare da inna da sauri ta tashi ta mustsika idonta tabbas zahiri photon sane a gidan innar'ta

Inna CE ta fito hannun'ta rike da plate cike da fruit da kuma jug a hannun ta a Centre table ta ajiye tace



"Jidda zo ki rabu da wannan photon in kika kwantar da hankalin ki zaku zauna ke da shi zama na har a badah...,



da sauri ta juyi tace




"Inna da wa .....zan zauna?,


zama inna tayi tace



"Zo ki ci wannan sai in miki bayani jiya ma naje gurin gwaggo da mahaifinki domin cika alkawarin da muka daukarwa marigayyah....,



Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta tako ta zo zama tayi tace



"Gwggo wane shi a gun ki....?,



tsohuwar me ran karfe kallo ɗaya zakai mata kasan hutu da jindadi ya zauna mata tace




"Jika nane dan gidan Khadijah ne ya'ta da nake fada miki wacce ta mutu ita da mijinta....,



Zaman dirshan jidda tayi tace




"Uhmm.....ta tsakuri kankana tasa abakin'ta duk zakin ta dacin ta take ji


ta rasa meke mata dad'i yau inna tace



"Jidda....,


.dago manyan idanuwan'ta tayi tace



"Na'am inna...,


.amma dai kwana zaki ko



girgiza kai tayi tace


"A'a inna ina da abin da zanyi kinga muta nan tsaka mai huyar dole gobe ko yau da safe a faɗi zaɓe in mu muka ci to komai dare zan tafi gidan Gwamnati....,



cikin mamaki inna tace



"Jidda ashe daman abin da ake faɗa gaskiya ne....kin shiga siyasa to wallahi ba inda zaki koma da raina haka daman kika koma jidda gaskiya ban yiwa karima adalci ba da na barki a hannun gwaggo duk da nasan halin'ta ba saiti ne da ita ba...dan uwanki shi kike cin zarafi abin da yayi shi......shi yayi ki..,


ran jidda ne ya ɓaci domin ita kaf duniya bata da sama da gwaggo tayi mata komai matar da ko zata huni bata ci ba ita zata bata taci zare hannunta tayi daga cikin kankanar da take ciya ta tashi gyara mayafin'ta tayi tace



"Inna ni Zan huce daman ziyara na kawo miki...naga kina wasu zance ban gane kansu ba ni zanyi gaba saduwar alkairi...,


Ba inda zaki da sauri ta juya jin wanda yake magana kahu isa cikin mamaki ta buɗa baki maganar ce ta kakare mata ta kasa wannan abin bakinci da yawa yake da basu san cinta ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login