Showing 6001 words to 9000 words out of 19770 words
wani kwatatcan lambu suka tsaya waya luba ta fito da ita tayi dan danne danne ta kara a kunne tace
"Shegen gari kana ina ne....?,
Daga can ɓangaran yace
"Ina cikin lambu...,
Tsai wayar tayi tace
"Zo mu shiga to tace ta bisu samun sa sukai a zaune ya ɗora kafa daya kan ɗaya yana busa yahaƙi jan kujera sukai suka zauna nima ganin tsayuwa ba zata kai ni ba na zauna cikin sanyin murya nace
"Ina kwana....,
Cire glasses ɗin'sa yayi yace
"Lafiya qalau luba yar jila ina kika samu wannan....?,
Far tayi da idanuwan'ta tace
"Sabuwar yar gwagwarmayar siyasa muka samu me jini a jika....,
Dariya ya sheƙe da ita yace
"Daman honourable Mustapha Umar jiran lokaci ya sani in samo sojojin baka wayan da zasu yaƙi waccan gurgun magen to zaki iya.....,
Dan jim tayi tace
"Yi min bayani yadda abin yake....,
ajiye tabar hannun'sa yayi yace
"Bani abu bane me huya zaki shiga gidan Radio GEZA zan rubuta miki komai zaki karanta tare ma zamu yau za ayi hirar Insha Allahu muka ga aikin ki yayi kyau tofa zamu yi tafiyar nan dake...,
Jikin'ta a sannayaye tace
"To...,
Tashi sukai suka bar luba yar shila a gun suka ci gaba da busa taba yawa ba gobe
# *oum Yasmeen*
*HAUWA KULU WOMEN LEADER*
*Ban yarda wani ko wata su mai damin da littafina Document ba ko audio wallahi kun yi min yarda kuka ga dama a DESTINY LOVE wannan karon bazan yarda ba kar wanda ya samin shi a website ba tare da sani ba*
*Masu yimim fantan alkairi ina godiya my lovely fan's my real fan's masu yimin aka sin haka ma ina godiya daman shi ɗan adam ba'a iya mai 🤗😏*
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
Book 1
🔞
Lumahe idanuwan'sa yayi kansa ke masa wani irin ciwo abubuwa sun mai yawa wayar'sa ce tayi ƙara share'ta yayi ganin me kiran yana ƙara nema ya tunzura ciwon kan'sa ya ɗaga cikin muryar shagwaɓa tace
"Honey kazo gida in anjima mu tafi.... wallahi nayi kewar ka..,
Wani takaici ne ya tukare mai huya yace
"Bada sa hannuna ba kika tafi dan haka kar ki ƙara kirana akan wannan maganar wallahi nadeeya in har bazaki sauya ra'ayi ba tofa kina gab da rasani ta har a bada sanin kankine bana son yin mata biyu amma kiyi ƙoƙarin kaini bango me al'umma zasu ɗauke ni nakasa riƙe gidana ina neman ƙarin nauyin al'umma da dama...,
cikin ɗaga murya tace
"Sai me Asharaf kafito fili kace min aure kake nema kadeba kwana kwana wallahi in har ina numfashi asharaf bakai ba wata mace wacce mace zata zauna dakai bayan nima zaman hakuri nake dakai....,
Be jira me zaka ƙara cemai ba ya kashe wayar dole zai tauna aya ɗan tsakuwa taji tsoro amma wazai aura wace zata iya riƙe mai sirrin sa wacce mace ce zata yi dai-dai da ra'ayin'sa turo kofa akai aka shigo da sauri ya dawo hayyacin'sa yace
"Wa'alaikas salam jafar...,
Zama yayi yace
"Abokina lafiya ka lula duniyar tunani ko dai har nauyin ƙasa ya fara hawa kan ka...?,
ɗan murmushi yayi jafar baya rabo da abin dariya yace
"Ina file ɗin....?,
Miƙo mai yayi buɗewa yayi yace
"Wayan nan sunayan mene amfanin su....?,
Shugaban jam'iya ne ya bani yace sunan wayan da zaka bawa kwangilane in Allah ya bamu nasara sun yi hidima da jam'iya....,
Tsaki yayi ya ajiye yace
"Wacce hidima ba cancanta za a duba ba ina cewa Sani me dala shi ne wanda efcc ta kama tana zarginsa da amsar kuɗade batare da yayi aikin da aka sa shi ba tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta NBB ne ya dawo tafiyar nan saboda sun ƙi bashi wasu kuɗaɗe....,
dafa kai jafar yayi yace
"Wannan haka yake wai me isa a yan kwanakin nan bara gurbi suke yawan shigowa jam'iyyar nan anya ba kura bace da fatar akuya.....
Wata kila kasan haka suke in suka ga mulki yana yane neman ƙarewa sai su koma jam'iyya me ci nidai wallahi cancanta zanbi duk wanda na bincika ya taɓa sama da dukiyar al'umma bazan yi tafiyar nan da shi ba saidai suyi abin da za suyi ace duk azzalumai suka taro suke mulki ba me son al'umma ...,
Hakane Allah ya datar da mu yanzu kenan bazaka sa hannu ba ..?
dafa kansa yayi yace
"Jafar kamar bada hausa nayi maka wannan bayanin ba kace mai na ajiye zan duba shi....,
To yace mai ya tashi ya fita ɗaukan mukullin motar'sa yayi tare da brief case ɗinsa ya fito cikin nutsuwa yake takawa wanda be sani ba zato zaiyi ɗan ɗin gisa ƙafar da yake gayo ne duk inda me kyau yake ya kai
cikar haiba da kalama suka bi suka mai da shi wani irin nagartatcan mutum ilimi hutu jin dadi fatar sa yawa kafasa jini ya fito
ba macan da zata gansa ta ɗauke idon'ta akansa shiyasa mata da yawa suke ɗilmiya cikin kogin'son sa kallo ɗaya zakai mai kasan a cikin maza ma sunan sa mazaje
Da sauri John ya karɓe jakar hannunsa buɗe mai kofar mota yayi gurin me zaman banza ya shiga zaka yowa yayi ya shiga ya fara tuƙi a hankali yake tafiya har yabar katafaran asibitin nasa
Kai tsaye hanyar GEZA suka nufa jaridar**CIKI DA GASKIYA DAILY NEWS**
ya ɗauka gabansa ne ya waɗi da sauri ya ɓan ƙaɗa shafin Farko inda ake cewa
Asifiya yau ne Jidda ita da Barde Tsula tsiyar ka ka gama lafiya suka cakcaki ɗan takarar shugaban kasa Inda suke bayyana al'umma cewa Asibitin koyarwa na jami'ar A.I.GEZA Teaching general hospital ya daɗe yana kashe rayuwa kan al'umma sakamakon ma'aikatan sa ba ƙararro bane
Sauri rufewa yayi be karasa karantawa ba wacce wannan jidda woman leader dole ya nemo ko ita wacce ɗaukan waya yayi cikin sauri ya shiga nemo number ɗin hamisu bugu ɗaya ya dauka cikin girmamawa yake gaishe shi
Amsawa yayi yace
"Hamisu ka duba jaridar ***CIKI DA GASKIYA*** abu na biyu ka binciko min wacce wacce sukai hira da Barde a ina take zan dau komai amma banda sharri da taɓa martabar iyayena da addini na
Cikin ladabi yace
"To katsai wayar yayi dai dai isowarsa gaban wani tabkeken gida daga gani kasan me gidan baƙaramin attajiri bane a kofar gidan yayi parking fitowa yayi ya shiga cikin gidan cikin taƙunnan nasa na kasaita yake tafiya har ya isa kofar da zata sada shi da floor mahaifinsa cire takalmin sa yayi ya shiga baƙinsa dauke da sallama ya shiga
Samin sa yayi yana kishin giɗe gaban sa kayan marmari ne ga ƙira'ar al'kur'ani ɗaukan remote yayi ya kashe cikin fara'a yace
"Sannun ka da zuwa uban masu gida...,
zama yayi cikin ladabi yace
"Barka da war haka abba da fatan ka tashi lafiya....,
Tashi yayi zaune yace
"Lafiya qalau asharaf ya iyalin naka....?,
Ƙasa yayi da idanuwan'sa dan ƙaramanin aikin mahaifinsa ne ya iya gano wanne hali yake ciki yace
"Alhamdullahi na same ku lafiya..,
Tufa mahaifinsa ya gutsura yace
"Lafiya qalau ɗauko waccan jakar.....,
Tashi yayi ya dauko ta ya ajiye a gaban mahaifin nasa
Abba buɗewa yayi wani daɗaddan photo ya dauko miƙawa asharaf yayi
Amsa yayi ya duba gabansa ne ya waɗi na hannun dama ya tabbata mahaifin'sa ne na hannun hagu kuwa kamar su ɗaya sak yawa an zana shi lokacin yana yaro
Dauko wani kaya yayi na sojoji lumshe idanuwansa yayi tuni kwallar da ta cika kurmin idon'nasa damar zubowa cikin kiɗima Ansh ya ɗauko tissue ya miƙawa mahaifin nasa ƙin amsa yayi yace
"Muhammad gwara ka barni nayi kukan da najima ina so inyi Muhammad wannan na gefen nawa shine mahaifinka bani na haife ka ba..,
Cikin kuɗi ma ya juyo ya kalli mahaifin nasa buɗa baki yayi zai magana abba ya daga mai hannu yace
"Dalilin da kuwa yasa na fada maka nasan zuwa yanzu ka mallaki hankalin kan ka in zaka tuna lokaci kana yaro har zuwa girman ka bana barin karaɓe kowa ciki kuwa harda matana babban tashin hankali da na shiga lokacin da ka kawo min fadeela a matsayin matar da zaka aura har istahara nayi.... naga ba makawa sai anyi wannan auran shiyasa na haƙura ka aure'ta....,
Ɗan nisawa yayi ya cije lips ɗinsa yace
Shekara arba'in da biyar bayan
Muhammad Yusuf Maɓaya shine asalin sunan mahaifinka ɗan asalin karamar hukumar maɓaya ne dake GEZA aiki ya kawo mahaifinsa GEZA BUZUNU ne inda ni kuma mahaifana barebari ne
aminina ne na kut da kut haka muka taso cikin so da kaunar juna haka ma mahaifan mu aminai ne sai an faɗa maka sannan zaka gane cewa mu ba yan uwa bane
Da muka gama secondary ni na zaɓi low inda na tafi jami'ar ibadan dake Nigeria naje na karanci low shi kuma ya zaɓi zama soja sai da aka kai ruwa rana tukunna aka kyale sa tare da binsa da addu'a
Cikin hukuncin Allah muka fito da sakamakon me kyau bayan mun gama ni na sami aiki a koton musilci dake garin geza
Inda shi koma suka tura shi barikin sojoji ta Afrika ta Kudu badan iyayan mu sun so ba haka suka haƙura ya tafi
Ni kuma ba dadi nayi aure ba amma shi Muhammad ba zancan aure a rayuwarsa dan ko waya muke na ce mai yau she xai aure sai yace sai Allah ya nufa har matata saudat ta sami ciki
Muhammad be dawo ba
Ko sau daya be taba bani labarin takurawar da shugaban ninsa suke mai ba akan roƙon gaskiya da amana
Cikin saudatu ya girma wata rana Litinin ta haihu amma dan barai ko da jin haka sai Muhammad ya dawo
Duk wannan kyan nasa yayi baƙi ya rame na yi tambayar duniya ya faɗa min meke damun sai sai yace tension din aiki ne
Kwansa biyu yaje maɓaya tare dani mun zaga ɗanginsa ana haka ya hado da khadiya ba adade na akai auran su ya dauke'ta suka tafi in da yake aiki
Mahaifiyarta bata son auran saboda kankantar shekarun ta saidai Allah ya nufa matar sa ce
Tafiya ta nisa tun muna samunsa a waya har abu ya faskara mahaifin nabeela shima sojane dan haka yau naji ance yazo na wanke kafafuwana
Na tafi unguwar ɗan burmu sallama nayi a kofar gidan su shiru ƙara sallama nayi huru huru na shiga yi domin inne mo yaron da zai shiga yayi min sallama da shi gabana ne ya waɗi lokacin da kunne na suka jiye min bakin labari
Mahaifin nabeela ne ya fito yana waya yace
"Oga ya tura kanal Muhammad Yusuf maɓaya yaƙin tsibirin birni nanɗi amma da biyu ya tura shi in ya je can bazai dawo ba za'a kashe shi shi zai jagoranci yaƙin tsibirin birni nanɗi...,
Bansan me aka ce mai ba naji ya bushe da wata mahaukaciyar dariya da baya da baya ba juya ban zame a ko ina ba sai a tashar mota
Wacce zata kaini Nigeria kwanana hudu ina tafiya tukun na na isa Afrika ta Kudu
Da yake lokacin da akai bikin naje nasan gidan sallama nayi Khadijah ta fito da tsohon ciki ta buɗe min har ƙasa ta gaishe ni na amsa nace
"Lafiya kwana biyu bama samin wayar me gidan ki....,
Hawayan da take riƙe wa suka sami damar kwaranyo wa tace
"Yau wata guda kenan da tafiyar sa birnin nanɗi...nima tun ina bugawa ina samu ba'a dagawa har ta dena shiga...,
Innalilahi wa'inna'laihir raji'un kalmar da nadin ga faɗa kenan
Wata baƙar mota ce ta tsaya a gaban gidan nasa yayin da wasu suka fito dashi ruƙe da cikin sa yayi wani irin fari kal suka ce
"Sun tsince shi a ƙabar tekun sindi sun duba jikin'sa suka ga information ɗin'sa godiya mukai musu suka tafi......inda suka ajiye mana wannan kwatin da take gaban ka
Tashin hankali da dimuwa yasa mahaifiyar ka atake anan ta fara kaƙuda da maƙoncin su da matar sa tare muka kai Muhammad asibiti kallon ana haihuwar ka aka kawo ka gunsa.....
Duk halin irin na ciwon da yake ciki hakan be hanashi daukan ka ba ya samaka albarka...naga baƙar rana guna dawo min da kai yayi ya damkamin amanar ka da ta Khadijah da kuma jakar da ya dawo da ita ya cika da kalmar shahada..
Iya firgici na shiga haka Khadijah itamana tana ji ya mutu ta bishi haka mu ka kawo gawarsa gida su nanne sun shiga tashin hankali domin iya shi suka mallaka binciken likitoci bayan harbinsa da akai har wata guba an bashi a hankali take mamaye jiki sai dai kawai aga mutum ya mutu
haka na dauki ragamar komai ta rayuwar ka domin ban bawa su nanne kai ba ni na ke kula da kai ba ruwan saudatu da kai.....akwai lokacin da har sakin'ta nayi sakamakon ture ka da tayi ka waɗi shine sanadiyyar ɗingishin nan da kake
Kabi a hankali Asharaf bance lallai sai ka faɗa min abin da ke faruwa da iyalanka ba amma jikina ya bani akwai wata munufa da yasa mahaifin nadeeya ya baka yar'sa bayan baya son mahaifin ka da haɗin bakin sa aka kashe da wasu manyan ƙasar nan na fara bincike abun ya faskara direct daga aka aikomin da takarda daga fadar shugaban kasa cewa in janya hannuna daga batun kisan kanal Muhammad maɓaya ba daddara ba na ci gaba sai da sukai min barazana da kai sannan na haƙura
Mutanan gidan nan ma ba abin yarda bane saboda ko su nasan suka sami dama wallahi sai sun aikaka lahira ASHARAF wata irin sarkakiya ke tare da banso Ka shiga siyasar nan ba Asharaf saidai na fahimci burin kane
Iɗagowa yayi idon'sa yayi ja jijiyoyin ƙansa sun fito rada rada da kyar ya iya buɗa baki yace
"Abba jininsa bazai taɓa tsulwan'ta a banza ba insha Allah sai duniya tasan wayan da suka kashe shi ƙasar nan an gina tubalinta a rashin gaskiya duk wanda zai gaskiya ɓatar da shi ake.....,
Fito da wani littafi yayi duk yayi kora yace
"Ungo wannan shine mahimman abu da sa mahaifinka yace abaka wannan akwati in Ka girma kaje kai bincike akai...,
Amsa yayi hannu bibbiyu ya riƙe yace
"Insha Allah komai zai zamo karshe nima akwai wasu ayoyin tambaya da nasawa mahaifin nata da ita kanta saidai duk abin da suke ina lura da su yanzu ainiyin wasan zai fara...,
Kai ya jinjina yace
"Allah yayi maka albarka ka cika ɗa na ƙwarai..,
Amin yace sun ɗan tattauna wasu batutuwa akan takarar sa yayi mai sallama ya fita kai tsaye gurin hajiya sauda ya nufa dan mutuncin abbansa badan halinta ba
Saminta yayi a zaune ta ɗora kafa daya kan ɗaya baƙinsa dauke da sallama ya shiga sauran yaranta suka amsa mai kadaran kada ham suka gaishe shi gaishe'ta yayi cikin mutun tawa
Ɗan yatsuna fuska tayi ta amsa mai
a guje wata sanye da riga da wando ta fito ƙanwar hajiya sauda ce yar autar su cikin so da kauna tace
"Ya ansh barka da warhaka...,
Tashi yayi cikin halin ko in kula yace
"Yauwa ya juya yace na tafi ba wanda ya tamka maganar'sa ya fita shima ko kuwa ko a jikin sa dan adam yasan hali
Komawa gun abba yayi ya dauki akwatin nan
yafita kofar gida yayi tuni ya cika damƙam da mutane da yake duk sanda zai ziyarci mahaifinsa sai sun taro kuɗi ya bawa john yana rarrabawa
Dakyar suka barsa ya huce tafiya me nisa sukai kafin suje inda gidansa yake
Gaban wani tabkeken gida suka tsaya John yayi horn me gadin ya buɗe
Parking space ya shiga inda ya ajiye motar ya fito ya buɗewa uban gidan nasa ya fito cikin izza yake tafiya John biye da shi har izuwa kofar da zata sada shi da shashinsa
Amsar akwatin yayi John ya juya shi kuma ya shiga ciki
*******
Sai yamma liƙis suka dawo gida a kofar gidan su me a napep ya kawo ta sauka tayi ta biyashi kuɗinsa ya ƙara gaba da baraka.....sanadin program ɗin nan da tayi gwamna ya cika mata jaka da kuɗi dan haka yau ji take tana shawagi a sararin samaniya
da yar wakar'ta ta shiga gidan kahu hamisu ta yi kicibus da shi a tsakar gida cikin baƙin ciki ya kalle'ta yace
"Yanzu jidda abin da kikai ya dace to wallahi bazan boye miki ba A.I.GEZA yasa inyi bincike akanki yace zai yarda ba wallahi in yayi miki wane daurin ko su wayan da suka saki basu isa su kunto ki ba....,
Wani takaici ne ya kamata tace
"Kahu wallahi siyasa yanzu na fara faɗuwar gaba a sarar na miji kasani sarai bana jin tsoro wallahi in ya fasa shi ba ɗan halak bane....,
Tau ya dauke'ta da mari da sauri ta kama kuncin'ta tace
"Ni ka mara to wallahi yau kowa na gidan nan bazai kwana cikin kwanciyar hankali ba MUZU BA MUGA NI ( shin KO kinsan me littafin MUZU BA MUGA NI nace kin sani ko kema ambarki a baya....?) tana kaiwa nan ta shiga ɗaki gwaggo ce ta fito cikin kumfar baki tace
"Wallahi hamisu ka fita a idona in rufe kowa na gidan nan ya tsani marainiyar Allah nan..,
Cikin takaici yace
"Gwaggo yarinyar nan siyasa fa tashi ga .....,
Turo daurin ta gaba tayi tace
"To sai mai hamisu karkai ma ka fara yi mata hassada ne dan kaji muryar ta a gidan rediyo tab wallahi ka shiga hankalin ka tun kafin Ubangiji yayi mak kunar baƙin wake dan kaga shi wancan me fubfar kafurawan farko ba shi take ba ta tafi siyasar su tsula tsiya ka gama lafiya yo kululu akwai wayo ba ta tsaya fagen su yan kuci ku bamu ta tafi sama ɗoɗar...,
Wani kululun takaicine ya tukare mai ma ƙogaro yace
"Gwaggo ina jiye miki ranan na dama wallahi domin kar jidda ta ɗebo abin da yafi karfin ku...,
Tub aniyar ka ta bika masaharranci ba ruwan ka da ita
Fita yayi domin bazai iya zaman gidan ba shi yanzu besan me zai fadawa oga ba jidda ta cuce shi wallahi
Cikin gida kuwa tana shiga ta cire kayanta zama tayi daga ita sai daurin kirji tana lissafa kuɗin da ta samu dubu hamsin cas gwaggo ce ta shigo ta washe baki tace
"Kululu duk wannan su suka baki....?,
Ajiye su tayi a gefe tace
"Eh wallahi zan ware kuɗin motar tafiya kamfen sannan in baki ke da malam...,
Buɗa tasaki tace
"Ta gaban mota insha Allahu wata ran sai kinyi Kwamishina....,
Cikin farin ciki tace
"Amin gwaggo...gobe ma da huri xan fita