Showing 1 words to 3000 words out of 19770 words
*HAUWA KULU WOMEN LEADER*
Oum yasmeen
Da sunan Allah me Rahman mejinkai
Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfanar da al'umma
*Perfectly pens*
*King and queen writing chamber*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga yan amanah kaf duniyar marubuta bani da kamar su
*Queen kaina Nainarh kd's*
Ahayye sama ruwa kasa ruwa sama....ai bata ƙarasa ba taja burki tace
"Kut melesi......tab yau ana yin'ta yasin in na yarda inya yawo ba kafa a garin nan....,
Tsit gidan yayi yawa ba magana take ba ƙara daga murya tayi tace
"Gwaggo gwaggo wallahi ki fito ki zame min sheda dan yasin in murɗe kan dabba in hullar ba wani aiki ne a guna ba....,
da sauri lami ta fito tana gyara daurin zanin ta abin da ta raya shi ya faru jidda ta zubawa tattabarun ta gyada uwar garken'ta ta zo tana ci dafe kirji tayi tasan halin jidda sarai ba kirkine da ita ba wannan abin da ta fada ƙaramin aiki ne a gun'ta ƙasa tayi da murya tace
"Yar gidan gwaggo kiyi hakuri ban san taxo ci ba gaba in xaki basu abinci ki dinga barin su a cikin wajan su ko dan sharar gidan nan ......,
Hamgame baki tayi ta saki kwafa tace
"Iyee baba lami kin ga kun kwana na yanzu ni kike fadawa wannan magana...? Wato daman yi dani kuke in bana nan to wallahi in kara fito da su wannan shegiyar figaggiyar tinkiyar nan taki tazo taci ki ga yarda ake banƙare tinkiya
Duka ta kaiwa tinkiyar ciki wanii kuka tasa ki....
Jikake ɓeeeyyy ɓeyyy
da saurin takama tinkiyar baba lami tayi ta jata har zuwa turƙen ta ta daure tinkiyar tata tasan halinta sarai yan zu labari zai sha banban sai ta yanka ta bawa kartin banza suci ba gaira ba dalili kai mata cibi ya zama ƙari
in Allah ya hadaka da mutumin banza sai addu'a
Tsaki taja ta buɗe duroɗin ruwa ta ɗiba tana wanke ƙafar'ta yawa ba siyan ruwan ake ba sai wanke kafa take
da sauri hansai ta fito tana cewa wanne dan durin uwar....ai kafin ta ƙarasa ta ci karo da uwar yan ɓarna jiddodo arnan daji haɗiye sauran zancan tayi tace
"a'a yar gwaggo kin dawo kenan.....,
banza tayi mata ta daki jikin diroɗin da kafa daman ruwan kaɗan ya rage aikuwa ya waɗi ruwan ya zube
Ɗaki ta shiga duk abin nan da ake gwaggo na kan wata yaloluwar katifa tana taunar goro ta turo dauri gaba kama kugu jiddah tayi tace
"Gwaggo yanzu duk kiran nan da nake kina jin kikai min banza....,
gyara zama tayi tace
"Kululu kwantar da hankalin ki yau ba yan tujararne akai na ba ƙarar su nakai gun Allah....,
hmmm kawai tace ta zauna kallon katifar da gwaggo take zaune tayi tace
"Gwaggo wallahi ni'ma harkar siyasar nan zan fara jibi fa baraka kawata yadda take shanawa....,
Wallahi duk lokacin da kika sake na ganki a gun yan siyasa sai na ɓalla kafar ki ban da daukar maganar da kike jamana a gari har sai kin tafi yawon siyasa cewar wani matashi daya ɗaga labulan ɗaƙin gwaggo
cikin faɗa gwaggo tace
"Wallahi Allah hamisu in baka dena abin da ake ba Allah sai yayi maka babbakar tsiri shifa maraya ba'a taɓa shi a zauna lafiya......wato baƙin ciki kake mata kai kana yi ita kar tayi hice ko kai ba yaron ASHARAF bane.....waya san irin arzikin da kake samu..,
tana magana jiddah na gyada kai ran hamisune ya ɓaci inde gwaggo tana gidan nan to fa baza ta bari ayiwa jidda fada ba kwata kwata shekarunta nawa dan dai tana da girman jiki amma ko sha shidda bata ƙarasa ba kasa magana yayi ya juya.......
Buda ta saki tace
"Allah ya barmin ke gwaggo wato in har kina garin nan bani ba kuka.....,
dariya ta saki tace
"Kululu kenan ai ni ba jahila bace irin su waya ce musu ana taɓa maraya tab ai ban shirya mutuwa ba .....
tashi tayi tsaye ba zaka kirata da kajeriya ba haka ba zaka kirata me tsayi ba wani irin sanyin kyau ne da ita zaka dade kana kallon'ta bare da ka kosa ba duk da kananun shekarun'ta amma kirjin'ta cike yake dam ga hibs kasancewar t-shirt ce a jikin'ta da jeans me irin matsai jikin nan hular kanta ta ture gashin kan'ta baƙi siɗik kitsone guda biyu wato (two step) akan'ta
Fatar ta ita ba fara ba ba kuma za a kira'ta baƙa ba wata irin fatace irin chocolate colour ɗin'nan kalar yan Ethiopia baby face din Ka dauke take da idanuwa dara dara ga beautiful point ɗin ta ko magana tayi sai ya loɓa
kallon sama da kasa gwaggo ke mata tace
"Ke kululu bana son rashin arziki...,
da sauri ta kalli gwaggo tace
"Gwaggo me nayi.....?,
taunar goron'ta ta ciga ba dayi bata son kayan arnan da take sawa zama tayi tace
"Hmm gwaggo nace ko zaki ban kuɗi wallahi bakina ba dadi yau balango nake sha'awar ci naga kamar yau su baba lami basu yi girki ba....,
ke kawo ƙunanki kiji matsowa tayi..raɗa tayi mata a kunnan ta wata dariya ta kwashe da ita tace yau za muci dabgeee
saurin rufe mata baki tayi tace
"Ni dadi na dake akwai shashanci maza tashi ungu wazobiya ki ziyo mana attaruhu na duka...,
amsa tayi ta tashi neman mayafi take da sauri gwaggo tace
"Da kata kinsan fa ni bana son dabi'ar arnan nan sa hijabi ko ki canza kaya,
zumɓuro baki tayi tace
"Wallahi gwaggo ni ina so...,
to amma ai kululu kalle ki fa jibi cinyoyin ki yawa na bijimin sa kina tafiya mazaunan ki na rawa yawa ana buga ganga ki daure ki canza tun da nasan bakya shiri da hijabi
tom shikkenan an gama uwar daki ta shiga ta cire kayan ta sa wani lace duguwar riga ta sa dauko mayafi ta yafa ko gwaggo batayi wa sallama ba ta fita a soro ta ci karo da lantana
fakar numfashin ta tayi ta rufe'ta da duka sai da tayi mata lilis sannan ta tashi ta riƙe kugu tace
"Wallahi lantana kadan kika gani inhar bazaki dena shiga sabgata ba.....,
kuka tasa tace
"Wallahi Allah ya isa...ta ruga gida a guje tsaki jidda tayi ta fita tafiya take cikin nutsuwa ......✍️
*Daga alkalamin oum Yasmeen*
*(Fatahiyyah Muhammad yakasai)*
*HAUWA KULU WOMAN LEADER*
*Perfectly pen's*
*King and queen writing chamber*
Story and writing
*Oum yasmeen*
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
Domin samun cigaba kuyi following din channel dina
Book 1
page 1 🔞
Ji tayi an buge'ta da sauri ta dago zata zuba uwar tijara sai kuma taga baraka tace
"Baraka ina zuwa haka...da tsakar ranar nan..?,
ke kai zan tambaya ina zaki ai ni kinsan inda nake zuwa
Haɗa rai tayi tace
"Baraka kin san halina sarai bana son rashin arziƙi ina tambayar ki kina tambaya ta...,
dariya tasa tace
"Maida hukar gidan gwamnati zani....,
washe baki hauwa tayi tace
"Dan Allah aikuwa nima gobe in zaki zani..,
Tsalle baraka ta daka tace
"Dan Allah gwaggo ta barki...?,
guntun tsaki taja tace
"Ai ita gwaggo bata da matsala inhar ina so to itama tana so kahu hamisu ne matsalata amma shima a sannu zan maganin sa..,
kai baraka ta jinjina tace
"Wallahi hauwa in kika shiga gidan gwamnati zaki iya da ko wanne shege barin shegun woman leader ɗin nan da basu da mutunci....
turo daurin ta gaba tayi tace
"Ke nima ai woman leader zan zama...,
dafa kafaɗar mara tayi tace
"Uhmmm kin san kuwa zaki iya...,
dariya ta sheƙe da ita baka ganin dariyar hauwa in ba mugun'ta ba zata yi ba tace
"Dan Allah ai kuwa kaf garin geza sai an san da zamana ke har fadar shugaban kasa sai naje...... siyasa sanadi..,
Jinjina kai Baraka tayi tace
"Allah ya nufa kin ga tafiya ta...,
To sai kin dawo ai zanzo kai kurun baraka ta gyada mata tayi gaba itama ta ci gaba da tafiya har ta isa gun me kayan miya washe baƙi yayi yace
"A'a rabebe arnan daji kece yau a gun nawa...,
haɗa rai tayi ta miƙo mai hamsin tace
"Bani attaruhu......na hamsin..,
da rawar jiki ya amsa saurin ja da baya tayi ta ya mutsa fuska tace
"haba jolu ka dinga tsabta gaka warin da kake kaga bani kuɗina in kara gaba in siya...,
ransane ya ɓaci yace
"To yar hau in baki ba ai ace bake bace shegiyar jikar masifaffiyar tsohuwa.......ai kafin ya ƙarasa ta daddage ta zabga mai kasa baki diɓar attaruhun'ta tayi ta fita a guje
kasa haɗe baƙin sa yayi
ya shiga tofar da yahu haɗe da kasa ya bita a guje da gudu ta shiga cikin gidan su ta rufo kofar langa langa dafe gwuiwoyin'ta tayi tana mai da numfashi tasan tun da tazo gida ta tsira zuwa gobe kuma zata ƙara shammatar sa ta rama zagin da ya yiwa gwaggon'ta yar aljanna tana jin irin zagin da yake yi
nan zuciyarta ta har zuƙa ta shiga gida ajiye attarun da ta siyo tayi yafi na dari......
ta shiga ɗakin da mage yake ajiye karan..... farautar mage
ta kunto da yake sun saba da karan in ya kace yabi mutum binsa yake duk inda ya shiga sai ya bi wan da kanuna mai buɗe kofar tayi ai jolo yana ganin karan a guje ya fita bama takai da sakin sa ba dariya ta sheƙe da ita ta kamosa
mai dashi ma'ajiyar'sa tayi
gurin kahu musa ta nufa buɗe wajan da yake kiwon zaɓin'sa tayi ta kamu uwar garken'sa ta mai da ta kulle jikake tana kuyat kuyat kuyat
Da saurin kama baƙin zabuwar nan tayi ta salallaɓa ta fito sai ta kanta tayi a rariya zata ta yanka saita kan tayi ta yanka ta murɗe kanta a fuka fuki ta ƙari burburwar'ta
Wanke hukar tayi ta wanke gun
daman kafin ta dawo gwaggo ta dora ruwa fige'ta tayi tsab ta sa gashin a baƙar leda duk bidirin nan da take ba wanda ya sani a gidan
hakan kuwa baƙaramin dadi yayi mata ba dan haka ta cikin sauri take komai gwaggo tane gefe tana jajjage tace
"Amma wannan attaruhu yayi araha...,
ta gefen ido ta kalli gwaggo tace
"In ana cin ɓaure ba'a tone tone...kawai ki ci gaba da daka,
banza tayi mata har ta gama ta kwashe ta koma ɗaki
tafasa zabuwar nan tayi sannan soya zabuwar nan tayi sannan ta soya attaruhun nan tayi tare albasa yaji kayan kamshi saka ta tayi a cikin soyayyan attaruhun nan ta juja'ta nan fa kamshi ya baza ko ina
gafaran ku dai masu gida gaban jidda ne ya waɗi sai ta dake ta washe baki tace
"Kahu musa barka da dawo wa..,
mamaki ne ya kama shi to jidda hankali tayi ne ......har tana mai barka da zuwa in kana da rai zaka sha kallo ya raya a zuciyarsa yace
"yauwa kululu me kike dafawa haka...kamshi ya ƙaraɗe ko ina..na garin ɗurma..,
Sosa keya tayi tace
"yauwa kahu zo kai ma ka kwashi rabon ka biyan bashi akai min da kaza shine nace mun dade bamu motsa baki ba bara nayi mana dabgee muciiii...yau kowa ya mai da mugun yahu....,
tattare malin malin ɗin'sa yayi zuciyarsa tayi fari kal yau zai washe baki....da jajjaja..an dade ba ahaɗuba ƙaraso kujera ya samu ya zauna
dariya ce ta kusab kubbucewa jidda gashi dai yana giwo amma ba wanda ya isa yaci shima ba ci yake ba sai dai su mutu ba wanda ya isa yaci aikuwa yau tasan ladan kowa na gidan nan domin sai sun tauna kashin uwar garken kahu musa tace
"Kahu lafiya naga kayi hurjajan da kai kaga fuskar ka kuwa...? yawa kwan lantarki duk ta motsi...,
haɗa rai yayi kome ta tuna sai kuma ya saki yace
"Am kululu bara in samo kwano ki zuba min nawa naga kamar ya dahu...,
Da sauri gwaggo ta fito tace
"Wallahi baka isa ba ko ni ban ciba sai kai daga zuwan ka da kafa yawa katafila kana cewa a zuba maka da sai miƙe huya kake yawa murriƙen lema...anya kuwa musa kana so kaga annabi...?,
me jidda zata yi inba dariya ba haɗa rai yayi ya kasa magana saukewa tayi ta zubawa gwaggo nata sannan ta zuba nata ta miƙowa haku tukunya da huya da kafafuwa zaman dirshan yayi yana ci yace
"Amma kululu wallahi baki da kirki jibi wanda kika bani me maƙon ki raba dai-dai ni da gwaggo ki dau karami shine kika nuna wariyar launin fata ko....?,
Kut gwaggo ta haɗe naman bakin ta taci
"Kululu dauko min tukunyar nan tun da bashi da godiyar Allah....duk wanda be godewa Allah ba zai godewa azabarsa..,
saurin jan tukunyar yayi ya zuge huya yace
"Haba gwaggo agaban yarinyar nan kike min haka..,
gyara zama tayi tace
"Wato jidda anya akwai tsuntsuwar da takai zabo dadi...?,
kasa haɗiye yar tsokar da ya cira yayi besan lokacin da ya zunduma ihu ba yace
"Wayyo Allah na shiga uku gwaggo me kike faɗa..,
saurin tashi kululu tayi ta sheƙe da dariya tana kallon kahun nata sai zare ido yake yawa wanda ya yiwa sarki karya ga dalalal da yahu da yake ya kasa haɗiyewa tace
"Wayyo Allah gwaggo kahu musa bashi da lafiya abin mahaukata yake....mu gudu...kar ya murɗe mana huya kamar yarda ya murɗewa zabuwar....sa,
Baba lami ce ta fito tana lasati tace
"Malam ban ga uwar garken ka ba...kuma kamar kwai zata fara Allah isa ɓarayi ne suka shigo ba...,
da hannun'sa ya shiga nuna su kululu yama rasa bakin magana
Karab jidda tayi tace
"Kar ka doramin jakar tsaba kaji su dinga bina biyan bashi akai min na zabuwa...,
malin malin ɗinsa ya cire yayo kan jidda a zafafe gwaggo ta jawo shi tace
"Wallahi ka taɓa ta zan ɓatar maka jidda ce tace tana son cin dabgee shine ni kuma bani da kuɗi nace ta zaɓo mana me tsoka da maiƙo a cikin zabin ka muci tun da nasan kai in na tambaye ka ba bani zakai ba shi kuma maraya ba a hanashi a bu...,
wani irin tukuƙi zuciyar kahu musa take kai ya gyaɗa yawa kadangare ya dauki malin malin ɗinsa bal yayi da tukunyar cikin daga murya gwaggo tace
"Kayi ball da ɗuwawun Rabi'u...,
tsalle jidda tayi ta dinga dariya ran baba lamine ya ɓaci ta bar gurin .....
fakar idon gwaggo yayi ya dauki kwanon jidda ya tafi
ihu jidda tayi tana ta zauna a kasa tana rusar kuka kai kace mahafin'ta da ya rage mata shine ya mutu
tsaki gwaggo tayi tace
"Na dawo gareki shine kika zuba naki yafi nawa Allah shiƙara da ya dauke miki..,
dakata wa tayi da kukan ta zaro manya manyan idanuwanta.....,
********
Cikin sauri ta ballo magani ta watsa a bakin ta ta dauki glass cup ɗin dake kan table ta sha daga shi sai trouser milk colour sai singlet ya shigo saurin boye
raguwar maganin tayi da sauri ya ƙarasa cikin haɗa rai yace
"Bani abin da kike sha...,
gaban tane ya waɗi kut ta haɗiye wani yahu duk rashin kunyar'ta tana tsoron mijin'ta saidai komai zai yi yayi bazata iya daukar ciki ba a wannan shekarun nata da yarinyar ta ta tsofa ya ga wata ya auro mata jikinta a sanyaye ta miƙo masa kara family planning da sauri ya dago fuskarsa har ja take saboda ɓacin rai yace
"Nadeeya daman ke kike hana kanki haihuwa me isa zaki min haka kinsan kuwa yarda nake son yara....?,
tashi tayi ta tushe kunnu wanta tace
"Please ash ka saurare ni ban yi haka ba sai dai da na tsaya nayi tunani a gaskiya bazan iya haihuwa ba sa da kananun shekaruna zan tsofa da huri ne bazan iya rainon yara ba a inzo cikin dare in kula da kai ga aikina bani da lokacin kai na balle naka sai in kara shigo da yara cikin lissafin mu....,
ai ba ta ƙarasa ba ya wanke ta da mari dafa kuncin ta tayi tace
"Asharaf yau nika mara...?,
A fusace yace
"Nadeeya ban san baki da tunani sai yau ashe daman ke kike hanani samin muradina...wallahi zan dau kwakkwaran mataki a kan ki..,
cikin kuka tace
"Wallahi yau a gidan mu zan kwana hulakancin naka har ya kai haka...,
Ransa in ya kai dubu ya ɓaci fita yayi cikin sassarfa yake tafiya har ya isa part ɗinsa murɗa handle ɗin yayi ya buda kofar kan royal sofa ya hau ya dafe kan'sa dake tsakanin sara mai
Allah ya jarab beshi da wata irin mata fadeela auran soyayya sukai amma a komai nuna mai gazawar ta take musamman ɓangaran auratayyah bata iya jure buƙatunsa
a kullum cikin korafi take Allah yayi mai son yaya dole ta dau kwakkwaran mataki a kan'ta bashi da burin auran mata biyu da a yau ba sai gobe ma ya daura aure
wayar sa ce tayi ruri be kula da ita ba har ta kusan katsaiwa sannan ya daga haɗe da yin sallama
cikin dadtako mutumin ya amsa sallamar yace
"Asharaf gobe ka biyo geza akwai Magana da zamu yi....,
Cikin ladabi yace
"Barka da dare to insha Allah zanzo...,
yauwa Ashraf ya harkar siyasar zaɓe na ƙaratowa..ko
Asharaf yace
"Eh wallahi abba...,
to Allah ya bada narasa da sa'a
Amin ya amsa
Abban nasa yace
"Ya iyalin naka...,
Ajiyar zuciya ya saki me nauyi har mahaifin nasa yana iya jiyowa shi mutum ne da ba'a gane inda ya dosa ga zurfin ciki yace
"Tana lafiya...,
sallama yayi mai ya kashe wayar tashi yayi yana zirga-zirga ya kai ya komo dole fa in har yana son farin cikin sa ta dore sai Nadeeya ta gyara halin'ta
inba ta gyara fa shashin zuciyarsa ya cillo mai wannan tambayar limshe idanuwansa yayi hakan na nufin zai dawwama ba farin ciki kenan ya cillowa kan'sa wannan tambayar cije lips ɗinsa yayi ya sami gu ya zauna system ɗin'sa ya dauko aiki ya fara saurin kallon tamfatsaitsan agogon dake manne abango karfe 10:00 cikin takaici ya girgiza kai
Yanzu Nadeela bazata gyara halinta ba yau shekarar su tara da aure amma bata sati biyar batare da tayi yaji ba akan ɗan karamin dalili wannan wacce irin mata ce bata san ta rufe sirrin ta ba sai daita bankada shi